Showing 135001 words to 138000 words out of 168002 words

Chapter 46 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

678

ta ya ce "Mai Jidda ban san ki da rashin ji ba, me yake faruwa ne?"

Jiki a sanyaye ta mi?a masa takardar da Nana ta bari a kan shimfiWarta.

"Wannan Win na mene ne?"

"Ku duba" ta yi maganar hawaye na zubo wa daga idonta.

Adda Saude ta karSa, ta buWe takardar "Assalamu alaikum, na san lokacin da za ki ga takardata, na riga na yi nisa. Mama ina mai baki ha?uri da matakin da na Wauka ban sanar da ke ba. Ba zan so a dadlilina nikaWai ki bar ?annena ba, dan Allah Mama ki yi ha?uri ki zauna da su. Na tafi neman mijina, a bawa baban su Walida ha?uri, amma kwana biyun nan da muka yi tare, ya fi kowane kwanaki yi mini daWi a rayuwata na gode sosai Nana Asma'u"

Shiru suka yi bayan da Adda Saude ta gama karanta rubutun, sai sautin kukan Maijidda da yake tashi. Cikin kuka ta ce "Shekara nawa ina yi masa kara, na ri?e nasa 'ya'yan? Amma ni sau Waya ya gaza yi mini kara, 'ya'yana sun tsane ni, a kan laifin da ba su suka yi ba, bai yadda su zo inda nake ba, nima kuma ba zan je ba. Idan na yi magana a ce na yi ha?uri, yarinyar nan ga tsohon ciki ina za ta tafi? Mijin da ita kanta ba ta san a ina yake ba" ta ?arasa maganar tana ?ara rushewa da kuka.

Kawu cikin sanyin jiki ya ce "To ita Nanan ya aka ta tafi babu sanarwa?"

"Tun da ta zo yake masifar sai ta bar gidan nan, babu irin magiyar da ban yi masa ba, amma ya din ga Waga murya yana bala'i, gaskiya bayan Nana zan bi, ko zan ganta, ban san ina za ta je ba, da ta fita da tsohon cikin nan"
"A'a ba za a yi haka ba, ki yi ha?uri Mai Jidda, rashin kyautawa Iliyasu ba ka kyauta ba, shi Wa na kowa ne. Kuma tabbas mun daWe mu na tausar ta, a kan ra'ayinka, ba tare da ba ta damar jin ta bakinta ba. Ka san raWaWin da yake cikin raba Wa da uwa kuwa? Ba ka kyauta ba"

Cikin kuka ta ce "Kawu dama ya bani zaSi, na zaSi 'ya ta, ya sauwwa?e mini na fita na nemi yarinyata"

Kawu ya ce "A'a ba za a yi haka ba, duk inda Nana take yanzu ta yi nisa, kuma idan aka ?yale ki, ke kan ki ba ki san ina za ki nufa ki neme ta ba. Amma tun da ba yarinya ce ?arama ba, na san duk inda take Allah zai kare ta, ki ci gaba da yi mata addu'a. Na san ina sha Allah, babu abin da zai same ta, amma batun ki ce ki kashe aure, ki bi ta ki zauna da ita ba mafita ba ce ba, ha?uri kin saba yin sa, a wannan karon ma shi Win dai zan baki, na san duk wanda aka ce wa ya yi ha?uri an zalunce shi ne, amma dai ki yi ha?uri.
Kai kuma Iliyasu magana ta domin Allah, ba ka yi kara ba, ba ka kyauta ba ko kaWan. Yaran nan saboda halinka sun daina zuwa inda take tsawon shekaru, amma daga zuwan yarinyar ka hau bala'i har ta ji, ta yanke wannan hukuncin. Ina kai auren ?anwarka ne ya mutu, mijinta ya ?i ri?e 'yar ka karSo ka kawo mata ta ri?e maka? Har zama fa ta yi da ?anwarka ta ri?e maka kan ta sake wani auren, amma kai ka kasa yi mata kara, a kan yarinya guda Waya tal".
Iliyasu ya zata a wannan karon ma, za a goya masa baya, kamar yadda aka saba tsawon shekaru goma sha, sai dai ya ji wannan karon ba a goyi bayansa ba, sai ya yi tsuru-tsuru, dan ha?uri tabbas ya san Mai Jidda na da ha?uri da kawaici. Kawai ya tsani babansu Nana ne, saboda yadda aka fasa aurensa da ita, ta aure shi, shi yasa tsanar ta shafi su Nana.
Haka aka din ga ba ta ha?uri, Kawunta ya yi ta rarrashinta.

Nana tana zaune a cikin mota, daga jikin taga, tana kallon hanya, yadda ake ta kwarara gudu a motar, tamkar direban zai tashi sama. Gudun da motar take yi, bai dame ta ba, fatanta Allah ya sanya matakin da ta Wauka, ya zama alkhairi a gare ta.
Duk da ta san Nijar ba gida ne ba, ba unguwa ba ba kuma Wan ?aramin gari ba, ?asa ce sukutum, mai Wauke da garuruwa daban-daban da ?abilu masu tarin yawa, balle kai tsaye tana zuwa ta doshi inda za ta gan shi. Duk ba abu ne mai sau?i neman mutumin da ko ainihin sunansa ba ta sani ba a gari kamar wannan, amma tana jin a ranta motsi ya fi laSewa, kuma rashin jini rashin tsagawa. Wannan shi ne mataki na ?arshe da za ta iya Wauka domin nemawa kanta mafita. Ta yarda da cewa Sar?ar, ?addara ce ta haWa ta da Sayyid, ta yi wa rayuwarta dabaibayi, mussaman da ya tafi ya bar ta da ajiyarsa a tare da ita. Sai dai bayan wannan tana cike da zullumin halin da yake ciki, saboda ta san kaso mafi yawa na mafarkin ta ya kan zama gaske, a jikinta take jin duk a inda yake, yana bu?atarta a kusa da shi.
Hankalinta ne ya dawo jikinta, bayan da ta ji ana cewa, an tsallaka boda sun shiga ?asar Nijar!.

AYSHERCOOL
08081012143
Nana ta ce "Dan Allah ka kwantar da hankalinka, kar ka tsorata wallahi ni mutum ce, ba abin da na isa na yi maka na cutarwa, ba kuma ni da nufin cutar da ku"

"To me ki ke yi mini a gida?"

"Wallahi ba?uwa ce ni, ranar da na sauka a garin nan, na shiga gidanka, matarka ta bani gurin salla, har da abinci, dan Allah taimakona za ku yi"

Ya ce "Baiwar Allah wallahi mu ma talakawa ne, ba wani taimako da za mu iya yi miki"

Ta ce "A'a amma ai ku musulmai ne, gudun zargi dan Allah idan babu damuwa, mu shiga ciki a yi maganar a gaban matarka, ku ji taimakon da nake bu?ata idan za ku iya yi mini, idan kuma ba za ku iya yi mini ba, babu komai sai na nema a gaba"
Kamar ya ce a'a, amma yanayin Nana sai ta ba shi tausayi, ya bata dama suka shiga gidan, yana gaba tana bin sa a baya.
Nana ta tsaya a tsakar gida, ya shiga ya taso matarsa. Ta fito tana mustustuke ido, ya nuna mata Nana ya ce "Kin san wannan?"
Ta Wan yi shiru sannan ta ce "Kamar shekaranjiya ta zo, ta ce mini ba?uwa ce za ta yi salla"

Ya ce "Yauwwa, sau uku ina ganinta a rilar gidan nan. Wai a nan take kwana, ta ce mini taimako take nema, amma a zo a gaban ki, sannan ta faWi me take son mu yi mata".

Matar ta kalli Nana,ta ce "Baiwar Allah, wane taimako za mu yi miki?"

Nana ta ce "Ni ba?uwa ce daga Nigeria, dan Allah ku taimaka mini da inda zan zauna, ban san kowa a ?asar nan ba. E"

"Gaskiya baiwar Allah, ba bu gurin da za mu iya ajiye ki a gidan nan" matar ta tari numfashin Nana.

Nana ta ce "A'a ba a nan za ku ba ni gurin zama ba, da kuWi a gurina, sai dai ban san kan kuWinku na ?asar nan ba, ina da wasu ma na Nigeria, ban san yadda zan canza su ba. Kuma ina tsoron na faWa hannun da ba na gari ba a cutar da ni. Haka kawai na ji na nutsu da nan tun lokacin da ki ka karrama ni, ko na tafi sai na dawo nan na kwana nake samun nutsuwa. So nake ku taimaka a sama mini gidan haya, ko Waki da zan kama dan Allah. Kuma wallahi ni ba macuciya ba ce ba zan cutar da ku ba. Ku yi wa Allah da ma'aiki ku taimaka mini, dan Allah"

Ya kalli matar matar ta kalle shi, ta Wan jinjina masa kai.
Ya kalli Nana ya ce "Kin san harkar taimakon ce wuya ne da ita yanzu, sai ka taimaki mutum amma ya sanya ka a masifa.
Nana ta ce "In dai kun yi niyyar taimakona, ko macuciya ce ni, Allah ba zai ba ni damar cutar da ku ba. Ku taimaka mini dan Allah, ko iya gidan hayar a sama mini"

Ya kalli matarsa ya ce "Hajara, bata guri ta zauna, zuwa gari ya ?arasa wayewa, sai mu san abin yi, mu duba girman Allah da ta haWa mu da shi"

Hajara ta ce "To shikenan babu damuwa" wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi, ta risuna ta ce "Na gode, Ubangiji Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi, yadda ku ka taimaka mini Allah ya taimake ku haka"

Suka amsa da Amin. Matar ta kai Nana wani Waki, ta Waukar mata kayanta ta shiga da su.
Tana fita daga Wakin, Nana ta zube ta yi sujjada tana gode wa Ubangiji buwayi gagara misali, ta san wannan Waukin kai tsaye daga gare shi ne, amma ba dan haka ba ta san ba ?aramar wahala za ta sha ba.
Sai yanzu da ta nustu, ta din ga jin ta a takure, saboda rashin wanka, ga cizonta da kayan jikinta suke yi.
Gari ya yi haske matar ta shigo ta ce wa Nana "Ki na bu?atar wani abu ne?"

Nana ta ce "Eh dan Allah zan yi wanka"

"To shikenan babu damuwa, da kin sani tun ranar da ki ka zo, ki ka yi mini bayani, ga ki da juna biyu, amma a ce ki na kwana a waje bai dace ba"

Nana ta ce "Larura ce, ba yadda zan yi, kuma babu daWi ka Wora wa mutane Wawainiya sama ta ka"

Ta ce "Haka ne" ta haWa wa Nana ruwa, Nana ta duba kayanta ta Wauki soso da sabulu, da brush.
Ba ?aramin daWin wankan nan Nana ta ji ba. Ta koma Wakin da suka sauke ta, ta fito koma Wakin da aka sauke ta.
Ta fito da mai ta shafa, ta saka kaya. Ta ji wata sassanyar iska na ratsa ta. Ta Waukko jakar kayan turarrukan Sayyid, da kayan gyaran gashin sa, ta yi zuru da ido, tana kallonsu.
"In sha Allah za mu haWu Sayyid, ina fatan Allah ya ?addara haWuwarmu nan kusa" ta yi maganar a sanyaye.
Sallamar Hajara ce ta sanya ta mayar da kayan cikin bagcconta, ta mayar da hankalinta kan ta.
"Ko ki na bu?atar wani abun ne?"
Nana ta girgiza kai fuskarta Wauke da murmushi ta ce "A'a ba na bu?atar komai, na gode sosai da sosai"

"Ba komai, bari na kusa gama abin karyawa"

Cikin murmushi Nana ta ce "Ba raina miki na yi ba, amma ni wannan taimakon da ku ka yi mini ya wadatar, ba sai kun ba ni Abinci ba, na gode sosai da sosai"
Hajara ta ce "Haba dai, ya ma za ayi ki na ba?uwarmu a ce ba za mu ba ki Abinci ba, ai ba zai yiwu ba sam"

"Ai kar Wawainiyar ta yi yawa ne, abin da ku ka yi mini ma, na gode Allah ya biya ku"

"A'a babu wata Wawainiya" ta yi maganar tana fita waje.
Ta so tambayar Nana me ya kawo ta Nijar, ga tsohon ciki, kuma ta ce ba ta da kowa, amma ta kasa saboda wani irin kwarjini da Nanan ta yi mata.
Tun da ta bawa Nana abincin safe, da rana ta bata fura Nana take amai. Har sai da Hajara ta ji babu daWi, ta yi zaton ko Abincinta ne ya saka Nana amai.
A sanyaye ta ce "Ko Abincin nawa ne ya saka ki amai?"

Nana ta yi murmushi ta ce "A'a kar ki damu, dama haka nake fama tun farkon cikin, ni na riga na saba ma"

"Kayya ai ba a sabo da wahala, kin yi amai ya kusa goma, ko Asibiti zamu je?"

"A'a zan daina in sha Allah"

Gaba Waya Hajara ta damu, ganin yanayin da Nana take ciki.

Nana ta ce "Ba ki taSa haihuwa ba ne? In dai mutum ya haihu ya san irin wannan larurar ta ciki ai"

Hajara ta ce "Ina fa? Watanmu takwas da aure, ban haihu ba".
Nana ta yi murmushi ta ce "Allah ya kawo mai albarka"
"To ai ni duk na tsorata ne, wannan aman ya yi yawa"
"Ai ni na riga na saba ma, ba ya damuna yanzu" haka suka Wan din ga taSa hira.

Mijin Hajara bai dawo ba sai isa'i, Nana na Waki tana shafa'i da wuturi. Ya ce wa Hajara "Ina ba?uwarmu?"

"Tana nan sai dai ba ta da lafiya"

"Me ya same ta?"

"Wallahi tun da na ba ta Abinci take amai, haryanzu jikina duk ya yi sanyi"

Ya ce "Subhanallah, kuma bai tsaya ba?"

"Tana dai ta yi"

Nana ta idar ta yi addu'a, sannan ta fito, ta dur?usa ta gaishe shi, ya amsa yana yi mata ya jiki.
Ta ce "Jiki Alhamdillah"

Ya ce "Baiwar Allah ba a samu gidan haya ba, duk inda na tambaya, sai masu tsada, kuma babu lallai a bayar, mussaman idan aka san ke kaWai za ki zauna, kuma zaman ki ke kaWai babu Namiji babu tsaro ko kaWan.
Amma na kuma bayar da cigiya ko za a samu wani, wanda yake da mutane a ciki sai a kama"

Nana ta jinjina kai ta ce "Na saku Wawainiya, Allah ya saka da alkhairi"

Ya ce "Ba komai" ya kalli Hajara ya ce "Bari na je na dawo, ko za ku yi hira kar na takura muku"

Nana ta ce "A'a ba komai, ka zauna ni sai na koma Waki"

Ya ce "A'a dama zan fitan"

Hajara ta raka shi soro, ta tsaya can su na hira Nana tana jiyo dariyar su. Sayyid ya faWo mata a rai. Yana daga cikin manyan ni'imomi da nasarorin rayuwa, mutum ya auri wanda yake son sa, ya kuma dace da shi. Ta yi musu addu'a da fatan samun dauwamammen zaman lafiya da kuma zuriya ta gari masu albarka.
Hajara ta dawo, ta zauna su ka ci gaba da Wan taSa hira da Nana.
Ta cewa Nana "Ko sunanki ban sani ba"
"Nana Asma'u, amma Nana ake ce mini"
Ta ce "Allah sarki, amma ki na da aure ne?"
Nana ta yi murmushi, ta ce "Kin yi mamakin yadda na taho inda ban san kowa ba ga tsohon ciki ko? Na san wata?ila, kina tunanin ina na samo ciki ne?"

Hajara ta ce "Laaa a'a wallahi"

Nana ta ce "Ai babu damuwa idan ma kin yi tunanin haka, Wabi'ar zuciya ce. Matar aure ce ni, ko a yanzu haka ka ma ina da igiyoyin aure uku a kaina, wani dalili ne ya kawo ni ?asar nan, kuma in sha Allah da na kammala, zan koma gida"

"Allah sarki, Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya a samu abin da aka zo nema"

Nana ta amsa da "Amin na gode sosai"

*

Su na zaune sun tattara hankalinsu a kan likitan, cikin matsananciyar girmamawa Likitan ya gaishe su.

"Ya ya jikin Imam?"

Ya amsa da "Jikinsa Alhamdillah, yana samun sau?i sosai da sosai"

"Ba yana samun sau?i muke son ji ba, mene ne sakamakon binciken ku da aka gudanar?"

Likitan ya ce "Eh sakamakon gwaje-gwaje, ya nuna babu abin da aka yi masa na cutarwa a jikinsa, gaba Waya babu wani abu na cutarwa a tare da shi"

"Shi kuma matsalar zuciyar fa?"
"Wannan yana da nasaba da hawan jini da yake da shi tuntuni, wata?ila ya daWe ba a kan magani ba. Shi yasa ya shafi zuciyarsa. Sai dai matsala Waya"

Cikin damuwa dattijon ya ce "Wace matsalar?"

"?wa?walwarsa, mun kasa gano abin da yake faruwa da ?wa?walwarsa, haryanzu bai samu nutsuwar da zamu tattauna da shi ba, yana bu?atar kulawa ta musamman a bangaren ?wa?walwa"

Sultan ya dafe goshinsa, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, idanunsa suka yi jawur. Ya Wago ya kalli Likitan ya ce "Ko gida za a mayar da shi, a saka duk abin da ake bu?ata na kula da shi a Wakin, ya zamana yana kusa da ni, hankalina ba ya kwanciya, yana nan ina can"

Abduou ya ce "A'a Sultan, idan aka mayar da shi gida, za a iya gane halin da yake ciki, wanda ba ma fatan hakan, dole a ci gaba da toshe duk wata kafa da za a san halin da yake ciki, har zuwa lokacin da zai warware. Kuma za a ci gaba da matsa yaran can, har sai ya yi mana bayanin abin da suka yi masa a Nigeria. Kuma Asibitin nan akwai tsaro babu wanda ya san yana nan. A kula da shi har zuwa lokacin da za a yi tafiyar"

Sultan ya yi ajiyar zuciya cike da gamsuwa, ya mi?e tsaye ya ce "Mu je na gan shi"

Su ka mi?e gaba Waya, Likitan yana gaba su na biye da shi a baya.
Cikin sauri suka ?arasa gaban gadon. Idanunsa a rufe yana bacci.
Sultan ya ?arasa gaban gadon, fuskarsa Wauke da damuwa.
Ya din ga dudduba jikinsa, tamkar yana son gano wani abin. Ya kalli Likitan ya ce "Kun tabattar a jikinsa babu wani abu na illa ko cutarwa a tattare da shi?"

"Babu ranka ya daWe, lafiya kalau yake, ba a yi masa komai ba, sai wannan matsalar ta ?wa?walwarsa. Ba na tunanin an tafi da shi Nigeria ne dan a cutar da shi, akwai dai wani abu...

"Ya isa ba kai ke hurumin zartar da wannan hukuncin ba, sai abin da bincike ya tabattar"
Babu shiri likitan ya ja bakinsa ya tsuke.

Sultan ya Wago hannun Imam na hagu, ya kalli yatsunsa ya ga yatsunsa biyu sanye da zobuna, ya Wago hannun damansa, ya ga babu azurfa Waya sai Waya. Cikin tashin hankali ya ce "Abduou. Babu zoben Imam guda Waya" Cikin sauri Abdou ya ce "Wanne daga ciki?" Ya Wago wa Abdou hannun Imam.
A rikice Abduou ya kama hannunsa ya duba, ya kalli Sultan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga abin da nake gaya maka ko? Kai ne ka ke ?o?arin kare yaron can, ka ke cewa a bi shi a sannu ba ka tunanin zai iya cutar da shi, to ga shi nan ai ga irinta nan, tabbas ya san inda zoben nan yake, dole a matsa shi a fito da shi. Dalilin da ya sanya su ka sace shi kenan ma, su ka bar ?asar nan da shi, su ka kai Nigeria. Zoben suke so su sace"
Sultan ya dafe kansa, ya rasa abin da yake yi masa daWi.
"Sultan wannan ma wani sabon sirri ne, da yake bu?atar duk tsanani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login