Showing 81001 words to 84000 words out of 168002 words

Chapter 28 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

681

tana mamakin, yaya aka yi ita, ko ta yi alwalar ta yi addu'a, ?aisar ba ya fasa cutar da ita.

"Da kin sani kin bar ni da matar nan, na ci gaba da wahalar da ita, yadda babarta za ta ?ara WanWanar takaici, ba ta da mutunci shi yasa ma aka sakar mata 'yar ta"

Nana ta ce "Ai ke ki ka saka a ka sakar mata 'yar, kuma Yusra ba bu wani abu da ta yi miki na laifi. Kuma ita kanta Hajiyar, tana da gaskiya mijina ba shi da lafiya ba ta yi ba dai-dai ba".

"Ai shikenan, yanzu haka za ki tafi na daina jin ?amshin girkinki mai daWi"

"Haula, dan Allah ko ke kin san waye Sayyid, daga ina kuma yake?"

Haula ta waro ido ta ce "TaS, so ki ke dattijo ya kashe ni? Ko kuma ya azabtar da rayuwata. Yo bai bar Wansa ba balle ni. Babu ruwana"

Nana ta marairaice ta ce "Dan Allah ki gaya mini, babu abin da zai yi miki "

"A'a ba ruwana. Ai ?aisar ya gaya miki, shigen Asirin da aka yi wa Alhaji Fatuhu, aka yi wa mijinki, amma ke ni babu ruwana a wannan lamarin naku"

Nana ta Wan yi shiru sannan ta ce "Da gaske, abin da ?aisar ya nuna mini a mafarki ya faru? Alhaji Zailani ya yi wa Alhaji Fatuhu Asiri da Wan Shukura?"

"Sosai da gaske ne, ba ?arya ya yi miki ba. Da zai ci gaba da buWe miki ido, ki cigaba da ganin Sarnar da bil'adama ku ke yi wa junanku, sai kin haukace.
Alhaji Zailani yana gadon Asibitin, da aka Wauke wa kishiyar Yusra Wa"

"Wace Yusran?"

"?awar ki mana, ita ce matar Sagir ta farko. Kin ga tafiyata kar na yi laifi, garin Sare-Sare na faWi abin da za a hukunta ni" Nana ta zabura ta dam?i hannun Yusra da sauri, domin sake tambayar ta. Amma ta ji jikinta ya yi sanyi ?alau, ta buWe idonta, ta kalli Sayyid, da ta ri?e masa hannu gam.
Ayshacool
Ta yin?ura ta tashi zaune, yanayin yadda ta ji jikinta, ta gane abin da ya faru.

Ummi ta ce "Nana kin tashi? Ki wanke fuskar ki, masu ?ur?urar sun kusa ?arasowa.Ta tashi ta wanko fuskarta.

Tana fitowa kuwa, masu motar suka ?araso.

Aka kwashe kayan su Nana tsaf, sosai Nana take jin kewar barin Wakin nasu. Ummi ta raka ta, suka shiga gurin Hajiy Halima, suka yi mata sallama.

Tar Nana take jin hirar da suka yi da Haula a bacci, tana dawo mata kanta, ba tare da ta manta komai daga hirar ta su ba.
Sai dai ta ?i yarda zuciyarta ta gazagata komai a cikin maganganun Haula, ta d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????age wa zuciyarta da cewa shirmen mafarki ne, saboda tana yawan tunanin Yusra da take yi.
Duk da tana jin kamar wani abu makamancin haka ya faru, wani abu mai kama da Alhaji Zailani ya yi wa Alhaji Fatuhu asiri, da kuma maganar jariri, amma ta kasa tuna komai.

Ummi ta fita waje, domin tabattar da an shirya komai, a kan motar.

Nana ta tarar da Sayyid a cikin Wakin, yana ?are wa Wakin kallo.

"Shugabana" ya waiwayo a hankali yana kallon ta.

"An tafi samo abin hawa, za mu tafi, na ga ka zo ka tsaya a nan"

"Nana"

"Na'am Sayyid"

"Ina kewar rayuwar da muka yi a Wakin nan tare da ni da ke, ban san ya zan misalta miki ba. Ga ki dai a tare da ni, amma ina kewar Wakin sosai. Sai na ji kamar ba zamu sake Rayuwa mai daWin da muka yi a cikin sa ba"

Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah, sai mun yi wadda ta fita komai da komai, da yardar Ubangijin talikai. Taho mu tafi" Da ?yar ta ri?o hannunsa, suka fito idanunsa jawur.

A adaidaita sahu suka tafi, da shi da ita da Ummi, sai dai ya ?ura wa gidan ido, tamkar ya ce a tsaya ya koma. Nana ta ri?o hannunsa cikin nata ta ce "Mu kyautatawa Allah zato, ina da ya?inin rayuwar da zamu ci gaba, ta fi wadda ka ke kewa daWi"

"Ina fatan haka Rayuwata"

Ummi ji ta yi tamkar ta yi tsuntsuwa, ta fita, ba ta san lokacin da Nana ta fitsare haka ba. Ta yi ta biye masa su na abu a gaban mutane, idan shi ba bahaushe ba ne, ai ita bahaushiya ce.

Sun Wan yi doguwar tafiya, daga Tudun yola, zuwa Kurna.

Babban abin da ya soki zuciyar Sayyid, bai wuce ganin gidan akwai maza ba, duk da masu aure ne, amma har cikin zuciyarsa hakan bai yi masa tsari ba. Amma babu yadda ya iya, tun da ba shi da wata mafitar. ?akin nasu bai kai wanda suka baro girma ba. Cif ya Wauke kayan su, sai dai babu sauran space Win kirki a Wakin. Ga zafi saboda wata 'yar ?aramar taga ce a Wakin, kamar Wakin tattabara.

Abin takaicin bai wuce yadda yaran layin suka cika gidan ba, saboda ganin ana sauke kaya ana shiga da su cikin gidan.

Sai da Ummi ta din ga korar yara, suka saka Sayyid a gaba da kallo, saboda ya yi shigar buzaye da rawani. Abin takaici har matan layin, wasu suka din ga le?owa, masu son ganin ?wal uwar daka kuwa, gidan suka din ga shigowa, da sunan sun zo gurin sauran matan da suke gidan, amma a zahiri, zuwa suka yi su ga suwaye kuma suka tare a gidan.

Ummi tana tare da su Nana, har aka gama shirya Wakin tsaf, duk da Nana su na da sauran kayan Abinci, amma ta yi waya aka kawo mata kayan abinci daga gidanta, ta girka wa Nana. Kasancewar Nana ba ita ta dafa ba, sai ta samu ta ci sosai.

Sai da Ummi ta aiko musu da maganin sauro, saboda akwai sauro sosai da sosai a gidan, ga zafi, shi kuma ga yanayin ciwonsa ba ya son zafi yana bu?atar wadatacciyar iska. Haka Nana ta yi ta aikin fifita.
Da safe Ummi ta sake aiko musu da Abin karyawa. Sai dai daga shi har ita, ba wani ci suka yi ba. Nana ta shirya ta ce "Sayyid, bari na je na yi musu sallama, mu gaisa da mutanen gidan"

"To"

"Yauwwa, kai ma zaka gaisa da mazajen su dan Allah, haka ake yi idan an je gurin, da ba a san mutum ba"? kallon ta ya yi, ya maze kamar bai ji me ta ce ba, amma ta san ya ji ta sarai.

Ta fita tsakar gidan, ta yi sa'a matan na tsagar gida, su na aikace-aikace. Nana ta ce "Sannu ina kwanan ku"

Suka amsa mata cikin sakin fuska.

Nana ta ce "Sunana Nana, ni ce muka tare a wannan Wakin"

"Allah sarki, sannu, ni sunana Barira, ga kuma Sajida, mai wancan Wakin"
Ayshacool
Nana ta ce "Allah sarki, to ma sha Allah, Allah ya iya mana" sun so jan Nana da hira, amma ta tashi tsam ta koma Waki, gurin mijinta.

****

"Alhajin Allah, aka ce ka tafi umara?"

Alhaji Zailani ya ce "?agawa na yi Alhaji Magaji, Madam ta tafi, saboda tafiyar ta yi karo da wani taro da za mu yi na shekara, shi yasa na Waga. Ashe kai ma na garin Abujan?"

"Wallahi kuwa, na ma kwana biyu, ina neman wata kwangila ne. Ya jikin amininka kuwa, Fatuhu?"

Alhaji Zailani ya yi wani irin makirin murmushi ya ce "Yana can ya kwanta dama"

"Subhanallah, rasuwa ya yi?"

"A'a na fa, yana nan a raye, amma rai ne kawai a jikinsa"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wallahi na yi mamakin yadda rayuwa ta yi wa mutumin nan tsutsun jaki lokaci guda, ga asarar dukiya, komai nasa an ?wace an biya masa bashi. Kai Allah dai ya kyauta. Da tuni yanzu ya ja tawagar tafiyar umarar maulidin nan, da shi da 'yan uwa da abokan arziki"

Alhaji Zailani ya ce "Sosai kam, faWuwar wani ai tashin wani, yanzu waWanda ya tare wa ?ofar arziki tun da ya gusa su ma za su Wago" suka tafa su na wata irin ?ya?yacewa da dariya.

*

Jamila bakinta ya ?i rufuwa, kasancewar a wannan karon a jirgi za su tafi babban birnin tarayya tare da Hajiya Sa'a.
Hajiya Sa'a ta ce "Ai sai ranar da za mu je Dubai, ko Qatar ma, wannan ai ba wani abu bane ba sam. Sai kin gaji da hawa jirgi, muddin za ki ci gaba da bayar da haWin kai"

Jamila ta ce "Kai, wa ya ganni a Qatar"

"Amm Jamila ina Nana kuwa?"

"Tana gidanta, kwanaki ma na ji an ce ta yi Sari"

Hajiya Sa'a ta jinjina kai kawai. Daga airport aka zo da mota, aka Wauke su aka tafi da su. Wani irin katafaren gida ne, da ko a irin finafinan Hausa da Jamila take gani, ba a taSa hasko mai girma da kyansa ba.

"Hajiya amma nan Hotel ne ko?"

"A'a gida ne, a nan za mu yi taron shekara"

"Ikon Allah, ai ganin gidan na yi ?ato guri-guri. To gidan waye?"

"Gidan wani ne" Hajiya Sa'a ta bata amsa tana dariyar, ganin yadda gidan ya ?ayatar da Jamila.

****
Kwanakin su Nana uku a gidan da suka koma, amma ita kanta, ba ta jin daWin zaman gidan, duk da a gehtto area ta tashi ita ma, amma zaman gidan nan sam babu daWi. Inda suka baro, sai ka wuni ba ka ji ?wa?w?waran sauti ba, sai na giftawar motoci. Amma gidan nan, musamman idan yamma ta yi, mata ne suke cika shi dam. A yi ta hayaniya, ana gulmace-gulmace, ga zantuttukan batsa da suke bajekolinsu a cikin gidan. A kafa dashi, a ci bashi, a yi gulmar wannan a yi ta mijin waccan. Hatta shimfiWar aurensu ba su bar ta ba, bajekolin ta suke yi a wannan gidan.

Yanzu ma yana kwance ya lumshe idanunsa, su na ta hayaniya su na musu, a kan kuWin cefane.

"Shugaba" ya Wago idonsa ya kalle ta.

"Sannu ya jikin?" Ya sake lumshe idanunsa ya ce "Na warke"

Ta yi murmushi ta ce "Sayyid, na san ba ka jin daWin zaman gidan nan, amma ka yi ha?uri in sha Allah, idan muka samu hali sai mu bar gidan nan"

Ya girgiza kai ya ce "Ba na bu?atar sauran jin daWi, in dai ki na kusa da ni" ya yi maganar yana shafa fuskarta.

"Sayyid"

"Husnah" sai kuma ta yi shiru. "FaWi mana"

"Ba komai fa"

"Shikenan zan shigo mafarkin ki, na ji"

Ta Wan yi dariya ta ce "Allah ne ya san dalilin da ya sanya ya haWa mu, gaba Waya rayuwarmu wata iri, daban da ta sauran mutane, mu dai gamu nan"

Ya yi murmushi ya ce "Shi yasa ba zan daina yi wa Allah godiya ba, da ya haWa ni da ke. Rayuwa da ke wata afuwa ce a gare ni Rayuwata" ta Wora hannunta a kan nasa tana murmushi. A hankali murmushin fuskarsa ya gushe, ya ce "Ba ni wayar nan, mu sake dubawa, ko wayar Habu za ta shiga"

Nana ta Waukko wayar daga gefen ta, ta mi?a masa, ya karSa ya danna lambar Habu, amma ta ?ara maimaita masa, wayar a kashe take. Ya sauke hannunsa cike da damuwa da fargaba.

"Sayyid ka daina damuwa, in sha Allah su na cikin ?oshin lafiya"

"Asmy, rayuwa ba za ta tafi a haka ba. Akwai Wawainiya da yawa. Ki yi ha?uri na san juriya da rashin son damuwata ya sanya, ki ke danne wa. Da nuna mini ba komai, amma na san Wawainiyar nan ta yi miki yawa. Wallahi zuciyata na yi mini zafi, idan na ga ki na wahala"

"Ni ba wahala nake yi ba" ta yi maganar tana tsuke baki.
Ayshacool
"Shikenan, na daina maganar"

Jin wayar na vibrating, ya sanya suka kai hankalinsu kan wayar a tare. Amma sunan Adda Saude ne yake yawo, a kan screen Win wayar.
Nana ta Waga tare da yin sallama. Adda Saude ta amsa Nana ta ce "Adda ina wuni?"

"Lafiya ?alau Nana, ya ki ke ya mijin naki?"

"Lafiya ?alau, ina Adda Fati?"

"Tana gidanta, ga Maijidda take son yin magana da ke" wata irin zabura Nana ta yi cikin murna ta ?ara nutsuwa.

"Assalamu alaikum"

"Mama"

"Na'am Nana ya ki ke?"

"Lafiya ?alau, ya gida ya su Walida?"

"Su na nan lafiya ?alau Alhamdillah, ya mai gidan na ki?"

"Lafiya kalau Mama"

Sayyid ya ?ura wa Nana ido, yana ayyana abin da take ji a zuciyarta. Saboda fara'ar da ta mamaye fuskarta.

"Ki na ji Nana, ina nan ina ?o?ari, duk yadda zan yi zan zo Kano, na ganku in sha Allah, ki ?ara ha?uri, na san kin yi ki ?ara, ina nan tafe in sha Allah"

"Kar ki damu Mama, ni jin muryar nan ta ki ma da na yi, na ji daWi sosai. Kuma in sha Allah kafin ki zo, za mu riga ki zuwa da yardar Allah"

"A'a ni Win dai zan zo na gan ku in sha Allah, ina fatan dai babu wata matsala?"

"Babu matsalar komai Mama"

"Yauwwa Nana, zan ci gaba da jaddada miki, ki ri?e Allah ki ri?e addu'a. Ki bi mijinki ku zauna lafiya. Ina fatan kin fafa sana'a Nana?"

"A'a Mama, amma zan fara in sha Allah"

"A'a Nana, kullum ki ce mini za ki fara, amma ba ki fara ba. Ina da buhun barkono, zan sayar na turo miki kuWin, ki fara sayar da wani abin. Idan kuma barkonon ki ke so, na aiko miki Nana. Ni dai ban taSa ganin mijin nan naki ba, amma yadda su Fati suka bani labari, da yadda nake jin muryarki, a duk lokacin da na kira waya, ina samun nutsuwa. Allah ya ?ara muku zaman lafiya. Amma ki yi sana'a, tun da mai ?aramin ?arfi ne, ki taimaka masa, kar ki sakar masa nauyi gaba Waya"

"To in sha Allah Mama, amma dan Allah ki bar barkonon ki, zan yi sana'ar nan da yardar Allah, na rasa abin da zan fara sayarwa ne. Amma zan fara"

"A'a zan sako miki buhu Waya a mota, ki gwada, kar ki zauna haka ba kya juya taro da sisi"

"To Mama in sha Allah, na gode sosai da sosai "

"Yauwwa, haryanzu ba ki da lambar Imrana ki turo mini"

Nana ta ce "Ba ni da ita Mama"

"To shikenan, ki gaida mijin naki" suka yi sallama, ta sauke wayar a hankali, ta yi shiru tana zancen zuci. Ta san da Mamanta su na tare da Baba, da ko ba za ta Wauke mata Wawainiyar da take ciki ba, za ta tausaya mata ta taya ta jajanta lamarin. Amma tun da ta je gida ta sanar da Baba halin da take ciki, ko ta waya bai kira ya tambayi ya suka ?are ba, ya kuma mai jikin ba. Dama Mama ba a magana, mutanen da tun da ta yi aure, ba su taSa taka gidan da take ba, yaushe za ta sanya ran su damu da halin da take ciki.
Tana iya ?o?arinta, gurin rintse idanunta, daga aibun iyayenta, saboda kar zuciya ta Webe ta, ta afka cikin fushin Ubangiji, amma daga yadda Baba ya yi mata gurin aurenta, zuwa yanzu zuciyarta na ?o?arin bijirewa.

"Ya ne?" Ta ji muryarsa. Firgigit, ta kalle shi ta ce "Babu komai. Mama na gaishe ka"

"Ina amsawa, ina son na yi magan da ita, amma ina tsoron na karSi wayar, maganar ta Wauke"

Nana ta ce "Haka ne, bari na fita da gas Wina waje, na dafa mana taliya, ga kayan miya na aika yaran Ummi, sun sayo mini, ai za ka ci ko?"

"Ke ma za ki ci ko?"

Ta yi dariya ta ce "In sha Allah" Ta Wauki kayan girkinta, ta fita kusa da Wakinta, ta Wora.

Gaisawa kawai suka yi da matan gidan, ta nutsu a kan aikinta. Tana zaune mata na ta shiga suna fita, kowacce da abun da yake kawo ta. Da tana da isasshen guri, a Wakinta, da babu abin da zai fito da ita waje yin girki, balle ta din ga kallon tumasancin da matan suke yi. Har da wadda daga ita sai hijjabi, da zani, babu riga babu brezia. Idan masu gidan suka dawo, haka suke tsallake mata su shiga Wakunan su. Tun da Nana ta kammala girki, ta tattara komai nata ta shige Waki.

Ta ji daWin ganin yadda yau yake iya cin abinci, dan haka ita ma ta zage, duk da ba wani daWi yake yi mata ba.

Saboda rashin kamun kai na matan layin nan, sukan kai har goma da rabi, su na shiga su na fita a gidan tamkar bariki.
Ayshacool
Nana har ta fara murnar abincin da ta ci ya zauna, lokaci Waya ya taso sai da ta amayar da shi baki Waya.

Tana fitowa daga banWakin, ya ?ura mata ido, har ta ?araso ta kwanta a jikinsa, tana Sata fuska.

Ya ?an?ame ta yana faWin sannu.

" ?an ka ya hana ni cin abinci, kuma yunwa nake ji" ta yi maganar hawaye na cika mata ido.

"Yi ha?uri, sannu, to mu je Asibiti"ya yi maganar a jere.

"A'a Sayyid, dole mu din ga tattala kuWi yanzu. Yunwa nake ji sosai" ta yi maganar cikin shagwaSa.

"Me zan sayo miki?"

"Ba komai" ji ta yi numfashinsa yana fita da sauri da sauri, a tsorace ta kalle shi ta ce "Sayyid jikin ne?"

"A'a" ya furta a hankali.

"Dan Allah ka yi ha?uri, da wasa nake yi maka, ai na san mata masu ciki, su na fuskantar irin haka, dan Allah ka kwantar da hankalinka. Ba na so mu zauna shiru, shi yasa na tsokane ka"

"Tom" ya amsa a hankali.

Kasancewar jikinta babu ?wari, ya sanya ta kwanta da wuri, ganin shi ma ya samu bacci.
A cikin bacci ta din ga jin wani irin rugugi, tamkar na hadari, ga shi ba lokacin damina ba ne. Ta buWe idonta, ta ji wani irin huci, na fitowa daga gurin da yake kwance, ga wani irin nishi da kakari da yake yi, tamkar an yanka rago.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Ta ja ta zauna ta yi shiru, abin duniya ya ishe ta, sai kuma ta koma tunani kamar yanzu ta yi rauni a ibada, shaiWan ya yi galaba a kanta, kan cewar idan ta yi addu'a wahala ta fi tsananta a gare ta. Domin hatta addu'a kwanciya bacci, ranar da ba ta yi ba, sai ta kwanta ta tashi lafiya ?alau, ba mafarkai babu ciwon ?afa ko baya, ko ma jikin baki Waya. Azkar ma ba ko yaushe take iya yi safe da yamma ba.

Ta yin?ura ta tashi, ta je ta Wauro alwala, ta zo ta sake haska shi, ta ga bacci yake yi, ta nemi guri ta kwanta, ta Wora hannunta a goshinsa, tana karanto addu'oin kwanciya bacci.

*

Jamila na mi?e a kan katafaren gadon, ga chips a gaban ta, ga kakkauran shayi, hannunta ri?e da zu?e?iyar wayarta.

Abba ne Wan gidan Hajiya Sa'a, yake yi mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login