Showing 150001 words to 153000 words out of 168002 words

Chapter 51 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

662

"Ba dan kin farka ba fa? idan ta yi masa wani abin, ni ina banWaki ke ki na bacci fa?"

Nana ta ce "In sha Allah babu abin da za ta yi masa. Zo mu je na raka ki gida"

Nene ta ce "Nana ki rabu da ita ta tafi gidan"

Nana ta ce "Nene zan raka ta, ni duk inda na ga mai irin larurar nan, tausayi yake bani"

Nene ta ce "Can ta matse muku ke da ita, ku je can ku ?arata, ni dai na sake ganinta a gidan nan, ta taSa yaron nan, sai na yi mata shegen duka da itace"
Nana ta kama hannun Ashura da ke ta rarraba ido, suka fita daga gidan.

*
Hajiya Sa'a ta tattara hankalinta a kan Abba da yake zaune a gabanta a bedroom Win ta.

"Magana nake yi maka, ka Wago ka kalle ni, mene ne a tsakaninka da yarinyar nan Jamila?"

Ya ce "Ba komai"

"To ka buWe kunnenka da kyau ka saurare ni, na sanya katanga a tsakaninka da ita, babu kai babu ita, kar ka kuskura na ji wata magana a tsakaninka da ita, kuma matar aure na samo maka ita, zan baka lambarta ka kira ta ku gaisa. Ka je ku gana, kuma nan kurkusa za a yi komai a gama. Ka fita daga harkar Jamila, ka fita daga harkar ta na gaya maka na kuma nanata maka, idan ba haka ba daga kai har ita ba za ku ji daWin abin da zai biyo baya"

Ya jinjina kai jiki a sanyaye ya ce "To in sha Allah zan kiyaye"

"Tashi ka bani guri" ya yin?ura ya tashi jiki a sanyaye, ya fice daga Wakin,? zuciyarsa na wani irin zafi. Bai taSa zaton za ta nuna adawarta da maganar haka ba, ganin yadda take da Jamila.

Ko da ya tafi Wakinsa, kiran Jamila ya shigo wayarsa, jiki a sanyaye ya Waga wayar ya ce "Hello Jamila"

"Jamila kuma, yau ba ?anwartaka?"

"Afuwan a yi mini afuwa"

Cikin damuwa Jamila ta ce "Yaya lafiya kuwa?"

"Lafiya ?alau, ina fatan kin je gida lafiya, ba ki bari na dawo na mayar da ke ba"

"Ina sauri ne, kuma ba na son wahalar da kai gaba Waya. Ko dai Mummy ta yi maka magana a kan ka daina kula ni ne?"

Da sauri ya ce "A'a ai kin san ba za ta hana ba ko kaWan"

Jamila ta ce "To shikenan, amma dan Allah in anjima ka zo na ganka"

Ya yi murmushi ya ce "Ni ki ke son gani?"

"Eh mana, ko na ha?ura?"

"Ina ni na isa, ina yin sallar isha'i za ki ganni a bar ?aunar Abba"

"To abin ?aunar ?anwarsa, sai ka zo" ya sauke wayar yana murmushi, sai dai yana sauke wayar ya Wan yi shiru cikin damuwa, bayan tuna abin da Mummyn ta gaya masa na kashedi.


Muhsin Win Nana tamkar ana hura shi, saboda girma ya cika ya yi fam. Ga shi fafur Nana ta ?i bari a yi masa aski, ta cewa Nene babansa ma ba ya aski, dan haka a bar masa sumarsa.

Nene ta fara jinginar da shi, a tsakanin fululluka tana koya masa zama.

Nene ta ce "Nana bari na hanzarta na fita, ki kula da yaron nan dan Allah, ban da shiririta, ko ki ?yale shi yana kuka ki yi masa banza"

Nana ta ce "To Nene ki goya abinki ki tafi da shi mana, tun da kullum ba na yi muku abin arziki"

"Kya dai ji da shi, ni dai na gaya miki, kuma wallahi mahaukaciyar can ta shigo, ki ka Wauki yaron nan ki ka bata, sai na Sata muku rai daga ke har ita"

Nana ta ce "Ni dai ba wannan ba, Nene so nake na fara bin ki gurin sana'ar nan, zaman gidan nan yana damuna, ba akin fari babu na ba?i"
Nene ta ce "Nima na yi wannan tunanin Nana, amma bai kamata a ce kina matar aure mu din ga fita bakin titi babu iznin mijinki ba, kin san halin maza wasu ba kirki ne da su ba, mussaman ke ga ?uruciya ma. Sam ba mutuncinki ba ne ba, dama jira nake yi Muhsin ya ?ara ?wari, na nema miki ko gurin Winki ne ko makamancin haka, ki din ga zuwa sannan mu ga ta ina za mu fara laluben mijinki, amma tun da Muhsin ya yi ?wari, mu fara lalubawa zaman haka ba zai yiwu ba, motsi ya fi laSewa ai"

Ta jinjina kai ta ce "To shikenan Nene, duk yadda ki ce Shikenan, na gode sosai da sosai Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"

Nene ta ce "Amin yarinyar kirki"

Fitar Nene babu jimawa sosai, sai ga Ashura ta faWo gidan.
Nana ta ba ta ce mata ta shigo Wakin, amma ta ?i.

Nana ta tashi ta fita ta shimfiWa mata tabarma, sannan ta Waukko Muhsin, ta zo ta zauna ta ba wa Ashura shi.
Ta karSe shi tana buWe baki cikin murna, ta kalli Nana ta ce "Ina son yaron nan"

Nana ta ce "Da gaske?"

Ta jinjina wa Nana kai, ya jima a hannun Ashura, sannan ta ba wa Nana shi, Nana ta mayar da shi Waki ta kwantar. Sai dai tana dawowa ta tarar da Ashura a tsaye tana kuka, gefenta ga ?warangwal Win nan.
Nana ta ce "Me ka ke bu?ata ne?"

"Ki na ganina kenan?"

"Eh ina ganin ka, sannan wannan mahaifar da ka ke lasa mene ne ma'anar hakan? Tun da ?azanta ce"

Ya ce "Lokacin da aka haife ta ne, da za su dawo daga Asibiti, aka manta mahaifar, shi kuma mai motar ya yar a bola, ni kuma na tsinta na biyo ta."

Cikin damuwa Nana ta ce "Amma baka kyauta ba, tun da babu wanda ya yi maka wani laifi ka ke yi mata abin da ka ke yi mata".

Ya ce "Ai mu ba sai an yi mana abu ba, idan mu na son mutum. Kin ga ke ma da ki ke addu'a wasu lokutan, ba dan tasirin Addu'a da ki ke yi, da kuma tsoron uban du?usa da ake yi ba, da bataliyar da za su shiga jikinki da yawa. Saboda da guda Waya ya yi hanya, wasu ma suke samun kafar shiga jikin mutum. Kuma Allah ya taimake ki, Sarkin baka ya rage tasirin uban du?usa a tare da ke, da duk inda muke sai kin din ga ganinmu, kuma muraran za ki din ga ganin cututtuka da sihiri a zahiri, sai kin kusa haukacewa idan ba ki bayar da magani ba. Kawai dai shi yana lallaSa ki ne"

Nana ta ce "Yaya aka yi ka san ?aisar, kuma ka san Sarkin baka?"

Ya ce "Jaddul Jinn babu wanda bai san shi a nahiyar nan ba, dan haka sanin jikansa uban du?usa ba abin mamaki ba ne. Sarkin baka kuma shi ne ya mayar da ni ?warangwal, mun taSa artabu da shi da na shiga jikin sata mesa, ya ?ona ni. Kuma na ga kin haWa jini da shi, ba yadda na iya da ke ne kawai, da sai na Wauki fansar abin da aka yi mini a kan ki"
Nana ta yi shiru jikinta ya yi sanyi, su na gama maganar Ashura ta juya ta fita ya bi ta a baya.
Nana ta din ga jinjina azabar naci da ri?o irin na halittun nan.



BAYAN WANI LOKACI.

Girman Wan mutum babu wuya, in ji masu iya magana, Muhsin ya cika watanni bakwai, Nana na zaune tare da Nene.
Nene ta kai ta gurin koyon girke-girke, yanzu kuma tana zuwa koyon Winki. Nana har mamakin yadda Nene take yi mata take. Sai dai ta fara karaya da yanke tsammannin haWuwa da Sayyid.
Nene ce ta shigo gidan, bayanta goye da Muhsin, yana ta mamular cukui.
Nene ta sauke shi ta zaunar da shi ta ce "Wannan Wan naki, idan bai nuna mini halinsa ba, ai ba za a ce Wan buzaye ne ba, mun taho hanya ya ga ra?uma, wai sai ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? dai mu tsaya ya kalli ra?umi, sai zillo yake a bayana yana ihu, sai da na tsaya na Sata lokaci yana kallon ra?uma yana mi?a musu hannu. Ya cire hular kansa ya yar, kowa ya ga kansa da wannan kitson sai an tambayi mace ce ko namiji. Ke ma da taurin kan tsiya, kin ?i bari a yi masa aski, kuma kina yi masa kitso kamar wani mace."

Nana ta yi murmushi ta ce "Ni babu ruwana, ba shiga faWanku zan yi ba, balle na ji kunya ku gwale ni"

Shi kuwa cukun hannunsa kawai yake mamulawa a bakinsa, Nene ta juya za ta fita tsakar gida ya rarrafa ya bi ta yana kukan ta Wauke shi.

Nana ta sake yin murmushi ta ce "Na haifa wa Nene Wa"
Tana jiyo rigimarsa da Nene, ya hana ta aiki, idan ta hana shi wannan ya koma wancan.
Nana ta din ga dariya daga Waki, aka jima kuma Nene ta zuba masa shayi sai kuma ya nutsu, guri Waya, yana sha yana wasa da gashinsa.
Ashura tana son zuwa gidan Nene gurin Nana, amma tana tsoron Nene, ga Muhsin da ya ganta yake sanya ihu, tsoronta yake ji.

?angare guda kuma, zuciyar Nana na sa?a mata ya kamata ta gusa ta bar gidan Nene, saboda ta ja lokaci a gidan. Amma tana tuna tijarar Nene, da rashin sanin ina za ta dosa. Ba ta san wani irin mutum ne Sayyid ba, mutumin da za a yi alfahari da haWa nasaba da shi ne ko akasin haka, duk da tana kyautata masa zato. Shi yasa take Soye wasu abubuwan, dan kare mutuncin sa da rashin sanin a yaya za ta haWu da shi.

Washegari da safe Nana ta tashi, ta jiyo hirar Muhsin a tsakar gida.
Ta tashi ta fita kar ya yi wata Sarnar, sai ta gan shi a lungun kitchen Win Nene, ya juyo bayansa, kamar dai wani abun ya samu yana wasa da shi.
"Kai babyn Sayyid, me ka yi a gurin nan, taho ka sha" bai waiwayo ba ya ci gaba da abin da yake yi. Nana ta nufe inda yake. Wata irin narkekiyar mesa ta gani a cikin lungun, shi kuma yana ta du?un?una kanta da hannu bibbiyu yana hira.
Ji ta yi tamkar an Waure ta tamau, ta kasa gaba ta kasa baya, kuma ta kasa magana.
Mesar ta mi?e sai ga ?aisar ya bayyana a gurin. Muhsin ya Waga kai yana dariya yana kallon ?aisar.
?aisar ya ciro wani abu a kwalba, ya buWe bakin Muhsin ya zuba masa, Nana ta rikice amma ta kasa motsa kowace gaSa ta jikinta.
Muhsin ya kama rigar ?aisar yana wasa da ita, yana yi yana kallon ?aisar Win.
?aisar ya saka hannu ya shafa kitson kan sa, ya mi?e tsaye ya Sace. Sai da ya Sace Nana ta iya motsawa, amma duk da haka ta kasa zuwa inda Muhsin yake, sai shi ne ya rarrafo ya nufo inda take.
Ta saka hannu da ?yar tana dudduba jikinsa, ko wani abin ya yi masa amma jikinsa lafiya ?alau. Ta shiga fargaba da tsoron me ya ba shi ya sha?.
Ta ja jikinta ta koma jikin bango, ta fara shayar da shi, tana ro?on Ubangiji Allah ya kare mata yaronta daga sharrin su ?aisar da kowane irin nau'i na shaiWani.

Nene na fitowa, ya cika Nana ya tafi gurinta, sai da ya gama wasansa, ya sake komawa gurin Nana.
Tana shayar da shi, tana ganin fuskar Sayyid a tattare da shi, dan hatta idan ya Sata rai, tamkar mahaifinsa.
Sai dai tunani da tsoron abin da ka iya samun sa, ya gaza barin zuciyarta, tun daga ganin da ta yi wa ?aisar da shi.
Ta so gaya wa Nene, amma ta ja bakinta ta yi shiru ba ta gaya mata ba.
Sai dai tun gabatowar magariba, take jin sanyi.
Ta shige Wakin ta ?udundune, ta bar su Nene.
Tana tsaye a sahara, sai dai a wannan karon babu ?urar Saharar, ta hangi Sayyid a zaune yana shan shayi, shikaWai.
Ta taka sannu a hankali ta ?arasa inda yake, ya Wago ya kalle ta yana murmushi.
Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ka warke ne?"

"Da sau?i, na yi nesa da inda nake jin ciwon, kuma na yi nisa da gurin waWanda za su kashe ni"

Cikin damuwa ta ce "Ni fa?"

Ya ajiye kofin hannunsa, ya rungumota jikinsa yana kallon fuskarta, idanunsa cike da hawaye ya ce "Yadda ruhinki da gangar jikinki, suka gaza samun nutsuwa, tun bayan rabuwarmu haka nima nawa suka gaza samun nutsuwa. Ina kewarku gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, ina bu?atar ki a kusa da ni"
Ita Nana gaza ri?e nata hawayen ta yi, tuni ta ba su dama suke zuba.

Ya girgiza mata kai tare da cewa "Kar ki manta, muddin kina raye kuma ina raye a doron duniya, gangar jikinmu ba za ta samu nutsuwa ba, sai mun haWu. Ina kewar ki ma vie."
Ya yi maganar yana ?an?ame ta a jikinsa. Ta buWe idonta tana ji yadda hawaye ya ji?a mata fuska.
Ta tashi zaune da ?yar, ta yi shiru ta tafi tunani. "Nana ba a bori da sanyin jiki, ci gaba da zaman ki a gidan nan, tamkar ki na matsawa dattijuwar nan ne da take Wawainiya da ke, kuma ba za ki taSa haWuwa da Sayyid ki na zaune guri Waya ba, yakamata ki motsa".

Ta tashi ta yi alwala, ta yi sallar magariba da isha'i, ta idar ta shiga Wakin Nene ta Waukko Muhsin, ta dawo da shi Wakinta saboda ko zai farka cikin dare.
Nana ji ta yi tamkar ta fice daga gidan a cikin daren nan, amma ta kasa saboda ba ta san ina za ta nufa ba, a wannan uban daren.

Ta ha?ura da niyyar da Asubar fari, ta tashi ta fice, amma bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita, sai da aka kusa idar da salla, Nene ta tashe ta yi sallar Asuba.

Tana idar da sallar kuma, Muhsin ya tashi ya saka rigima, Nene ta Wauke shi suka tafi Wakinta.

Tun da wuri yaran Nene suka zo, suka Wauki kayan Abinci, amma Nene ta ?i fita ranar ta wuni a gida, yaranta ne suka je suka sayar da Abincin.

Abu kamar wasa a jere kwanaki huWu Nana tana yin?urin guduwa, amma Nene ta kasa ta tsare tamkar ta san abin da Nana take shiryawa.


*
Jamila ta nuna wa Hajiya Sa'a tamkar ba ta san ita ta taka wa Wan ta Abba burki a kanta ba, Hajiya Sa'a sai shirin bikin Abba take yi, yayin da gefe guda kuma Jamila ta yi blocking Win sa, ta daina Waga wayarsa gaba Waya.

Dama idan Hajiya Sa'a na nan, ba ya iya yi mata magana, da zarar ta fita kuma sai Jamila ta kulle ?ofar sashen. Ya rasa abin da yake yi masa daWi, har layi ya canza ya kira Jamila, amma tana Wagawa ta ji muryarsa ta kashe.

Ga shi tun da Hajiya Sa'a ta fuskanci abin da yake tsakanin su, ta daina yawan fita ta bar Jamila a gidan, idan ma fita za ta yi sai dai su fita tare. Sai dai yau Jamila ba ta jin daWi, dan haka Hajiya Sa'a ta fita ita kaWai, saboda ta sakankance Abba yana can kasuwa.

Awa guda da tafiyarta, Jamila na kan doguwar kujera tana bacci, ta ji tsayuwar mutum a kan ta. Ta buWe idonta a hankali ta ga Abba a tsugune a gabanta yana kallonta.

Tashi ta yi zaune tana tsuke fuska tare da gyara zaman rigarta za ta tashi.

Cikin zafin nama da tsoron rashin sabo, ya ri?e hannunta ya ce "Dan Allah Jamila ki tsaya ki saurare ni" ya yi maganar cikin marairaicewa kamar zai yi kuka.

"In saurare ka ka ce mini me Yaya Abba? Dan Allah ka rabu da ni." Ta yi maganar itama idanunta fal hawaye, saboda ba ta taSa sanin ta kamu da matsananciyar soyayyar Abba ba, sai yanzu da Hajiya Sa'a take ?o?arin farra?a su.

"Jamila dan Allah ki fahimce ni, kin san a son raina ba zan auri wata ke ga ki na bar ki ba, wallahi Jamila ina son ki, ban taSa son wata 'ya ba sai ke"

Ta kalle shi hawaye na zuba daga idonta ta ce "Ko ma mene ne, ai yanzu aure za ka yi, ka rabu da ni dan Allah"

Girgiza kai ya yi cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ganin yadda take zubar da hawaye, zai yi magana ta fizge hannunta ta shiga Waya falon, bai yi ?asa a gwiwa ba, ya sake bin ta yana ?o?arin rarrashinta.

Sai dai kash, garin ya rarrashi Jamila, sai shaiWan ya buga musu ganga su ka taka rawa, duk da Jamila ta fuskanci cin zarafi da keta haddi a ?ungiyarsu ta asiri, a wannan karon ma tsoro da rashin sabo suka yi tasiri a a gare ta, duk da a nasa Sangaren ma haka ne.

Daga shi har ita suka saka kuka mai cike da nadama da dana sanin abin da suka aikata.

Maganganun Nana suka din ga dawo mata daki-daki, na nasihar da ta din ga yi mata a baya. Duk da babu wanda ya san halin da Nana ne ciki, a tsawon wannan lokacin kusan shekara guda, amma gara Nana da ita, Ko ba komai Nana aure ta yi, ita kuwa fa da fari bokaye da aljanu sun kwanta da ita, a wannan karon kuma ruWin soyayya da sharrin shaiWan.

"Jamila, dan Allah ki yi ha?uri, ki kuma rufa mini asiri, ke ma kin sa hakan ba halina ba ne ba, amma duk yadda zan yi, zan aure ki, ni na fara aikata Sarnar nan, kuma zan gyara ta in sha Allah"

Jamila ta kalle shi ta kawar da kai, tana jinjina lallai Abba bai san komai ba, tun da bai iya gane ba budurwa ba ce ba, duk da bayan abin da Hajiya Sa'a ta kai ta aka yi mata, bazama ta yi neman magungunan gyara.

Ya lallaSata ta gyara jikinta, ta nemi guri ta kwanta, ya rasa abin da yake yi masa daWi. Ya koma part Win sa ya rufe ?ofa, kawai ya fashe da kuka. Bai taSa tunanin aikata zina a rayuwarsa ba, ba ta taSa burge shi ba, bai kuma taSa kawo ta a ransa ba. Sai dai yau ya wayi gari da aikata ta dumu-dumu.
Sai dai wani abin mamaki duk da abin da ya faru a tsakanin su, bai daina jin matsananciyar ?aunar Jamila ba. Ya rasa dalilin da ya sanya Mummy ba ta son ala?ar su, duk da irin kusancin da yake tsakaninta da Jamilar.

A kwance Hajiya Sa'a ta dawo ta tarar da Jamila. Ta ce "Daughter haryanzu jikin ne? Ko Asibiti

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login