Showing 42001 words to 45000 words out of 168002 words

Chapter 15 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

645

sauri ya nufi ?ofar fita yana waiwayen ta.

Yana fita ta silale ta faWi a gurin.

Fitar sa ke da wuya, ruwan sama mai ?arfin gaske ya sauka.

****

Dare ya tsala, Fadila na zaune bacci ya gagari idonta, ta kalli kusa da ita, mijinta Sagir yana ta baccinsa hankali a kwance, ita kuwa duk dare fargabar kwanciya bacci take yi, saboda miyagun mafarke-mafarken da take yi. Tun Sagir na damuwa har ya gaji ya rabu da ita.
Ta yi niyyar yin alwala ta yi nafila ko raka'a biyu ce, amma kasala ta danne ta, ga wani irin tsoro da take ji.
Dama ko normal sallar farilla a zaune take yin ta, saboda yadda cikin ya tsufa sosai da sosai ga shi da girma. Ga exams tana facing, ba ta iya karatun sam.
Ta dafe goshinta tana wani irin gumi, duk da sanyin A.C da ya sanyaya Wakin.

Tana jiyo surutan Haidar a cikin bacci, yana ta kiran sunan Nana.

Kawai ta zuba uban tagumi hannu bibbiyu ba tare da sanin abin yi ba.

****

Ko da Nana ta buWe idanunta, da hasken fitilar ?wan Wakin, ta fara karo.

Ta juyo da kanta, da ya yi mata nauyi tamkar zai tarwatse, kawai ta hange shi a bakin ?ofar banWaki, yana ta sanWa yana cire kayan jikinsa a hankali, da suke ta Wigar da ruwa, jikinsa yana ta wata irin karkarwa. Aka yi wal?iya ta hangi yadda ruwa yake zuba ta taga. A take ta tuna abin da ya faru, da azama ta tashi zaune, ta yin?ura ta tashi, ta nufe shi. Sai a lokacin ya farga da ta tashi. Sai da ya tsorata ya tsaya cak, yana tsoron kar ta sake rikicewa ta ce ba ta son ganinsa.

"Me yasa ka fita ruwa ya dake ka har haka? Subhanallah" ta yi maganar tana karSar rigar hannunsa. Babban abin da ya tsorata ta, bai wuce yadda jikinsa yake karkarwa ba, ha?oransa suke haWuwa da juna, su na bayar da wani irin sauti.
Ta buWe wardrobe ta Waukko zaninta, ta fara goge masa ruwan jikinsa. Cikin damuwa ta ce "Me yasa ka tsaya ruwa ya dake ka haka?" Kawai ya kalle ta.

Ta ajiye zanin, ta Waukko flask Win da ta zuba ruwan zafi, ta shiga banWakin ta zuba a bokiti, ta haWa masa ruwa mai zafi.

"Ka shiga ka yi wanka da shi, za ka rage jin sanyin" bai musa ba ya shiga banWakin, ta Wauko wando ta rataye masa a jikin ?ofar, ta rufe masa ?ofar.

Ta Waukko bargonta, ta ajiye a kan katifar, ta duba kayanta, ta samo man zafi ta ajiye. Ta tsaya tana jiransa. Ba a jima ba ya fito, sai dai jikinsa na ta ci gaba da tsuma, yana karkarwa.

Mamaki take yi, yadda dukan ruwa ya saka shi haka, ita ba ta san adadin dukan da ruwa ya yi mata ba, ko ciwon kai bai taSa saka ta ba.

Ta Waukko riga, ta mi?a masa, amma ya ture ta, ya nufi gurin da yake kwanciya.

Ta ri?o hannunsa ta ce "Zauna a nan" ta nuna masa gefen katifar. Ya zauna a hankali yana rintse idanunsa.

Ta Wauki man zafi tana shafa masa a jikinsa, sai dai jikinsa ya Wauki zafi rauuu.

"In baka rigar ka saka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

Ta gyara masa fulo ta ce "To kwanta" ya ja jikinsa a hankali ya kwanta, ta lulluSe shi da bargo.
Ayshacool
Ta yi shiru cikin matsananciyar damuwa, ita kanta ba ta san ya aka yi yau ta gigice har haka ba. Ba ta san yadda aka yi ta rasa nutsuwar ta har hankalinta ya gushe ba, duk da abubuwa irin haka na faruwa da ita, wasu lokutan kuma ta na iya sarrafa kanta.

Ji ta yi yana wani irin nishi, jikinsa tamkar ana girgiza shi. Ta Waga bargon cikin damuwa, ta ga yana jijjiga.

Ta rikice ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah ka yi ha?uri, tsoro ka ke bani ne, ba ina nufin ka fita ruwa ya dake ba ne ba."

Tana kuka ta Waukko Wan kwalinta, ta ji?o shi da ruwa, ta ci gaba shafa masa. Amma ta ga leSensa har ya fashe saboda karkarwa. Ta kalli gari yadda ake ta lafta ruwa, balle ta ce a taimaka mata a kai shi asibiti.

Ya yi mata alama da hannunsa ta matsa kusa da shi, ta matsa sosai a hankali ya ce "Zafi, ana ?ona ni, ?onewa nake yi"

Cikin kuka ta ce "A'a babu wanda yake ?ona ka, zazzaSi ne ka yi ha?uri"

"A'a, ?ona ni ake yi, sanyi nake so"

Cikin rashin fahimta ta ce "Sanyi kuma?"

"Eh, saboda ?onewa nake yi yanzu" yayi maganar ha?oransa na ?ara karo da juna.

Cikin damuwa ta ce "To mu koma bakin ?ofar Wakin?"

Ya girgiza kai ya ce "Sanyin da ki ke ji nake so"

"Sanyin da nake ji kuma? Ai ba na jin sanyi"

"A'a ki na ji, ki taimaka mini dan Allah, sanyin da ki ke ji nake so"

"To ta yaya zan baka?"

"Jikinki za ki bani, shi nake bu?ata ko zan daina jin zafin wutar nan" duk da jikinsa yana rawa, amma tana fahimtar abin da yake faWa.

"To ai ni ban san ta yaya zan baka ba"
Ta yi maganar a sanyaye dan ba ta san ya yake nufi ba.

"Kin yarda za ki bani?" Ya yi maganar yana buWe idonsa da suka kaWa su ka yi jawur ya kalle ta.

Ta jinjina masa kai alamar eh, cikin tsoro dan ba ta san ya yake nufi ba.

Ya buWe mata cikin bargon, ya saka hannunsa Waya ya janyo ta, ya mayar da bargon ya rufe., ya mirgina ta gefensa ya saka hannayensa ya ?an?ame ta.

"Wash Allah! Zafi zan ?one" ta yi maganar a gigice, saboda wani irin zafi da yake fitowa daga jikinsa, yana ratsa fatarta, duk da akwai rigar bacci a jikinta.

Ta yin?ura za ta tashi, sai dai ta kasa, saboda ya danne ta, ta kowane Sangare.

"Yi hakuri, ba za ki ?one ba, za ki daina ji"

Nana ta fashe da kuka tana girgiza kanta, shi da zafin yake fitowa daga jikinsa ya yake ji kenan?.

A hankali yake shafa gashin kanta, zuwa bayanta, yana sauke numfashi a wahale. Cike da ?arfin hali yake cewa "Yi ha?uri, na san ba zaki ?one ba, nikaWai nake ?onewa" ya din ga hura mata iska a kunnenta.
A hankali ta daina jin zafin, temperature jikinsa, ta fara komawa normal, ta ji ya daina wannan tsumar,? numfashin ma da yake ta saukewa ya daina. Sai ta Wan zabura a rikice ta Wago, ta kai hannu hancinsa. Bai buWe idonsa ba ya ce "Ban mutu ba, ina numfashi" ajiyar zuciya ta sauke tare da gode wa Allah ganin yana raye ya kuma dawo daidai.

"Sannu ka daina jin zafi?" Ya jinjina kai alamar eh.

"Dan Allah ka yi ha?uri ka yafe mini, tsorata ni ka ke yi ne, ba ina sane na yi maka ba"

"Ni ma ki na tsorata ni wasu lokutan"

Cikin mamaki ta ce "Ta yaya?"

"An gama ruwan ko?" Ya yi maganar yana basar da wadda ya yi.

"Eh an daina, amma dama ka na doguwar magana haka sosai?"

"Eh"

"Amma na yi ta magana Wazu ka ?yale ni" ta yi maganar da shagwaSar da ita kanta ba ta san ta iya ta ba.

Dariya ta ji yana yi, ya ?ara ri?e ta gam.

"Yanzu wai da gaske ba ka iya tuna komai game da kan ka?"

Ya Wan yi shiru sannan ya numfasa ya ce "Haka ne, ina iya tuna abubuwa na yau da kullum, wasu lokutan kuma ba na iya tuna komai ma. Tun da farka a cikin wannan duniyar da nake jin ta tamkar mafarki, nake iya ?o?arina na tuna waye ni, saboda na fuskanci babu wanda yake rayuwa shikaWai kowa yana da ahali. Amma a duk lokacin da na yi ?o?arin hakan, na takura ?wa?walwata, sai na ji wani duhu ya ?ara ninkuwa a cikin kaina, na ji kamar kan zai tarwatse. Kuma a ?arshe sai na yi rashin lafiya, ko dai na ji wannan zafin tamkar ana babbaka mini wuta, ko kuma na sake manta wasu muhimman abubuwan. Amma yanzu ke ce ahalina"

"Kenan ba dalilin dukan ruwan nan ne ya saka jijjiga ba?"

"Ba zan iya ganewa ba, abubuwan suke saka ni hakan da yawa"
Ayshacool
35

Nana ta motsa, ta ji taushin katifar da suke kai, ta fi ta Wakinsu. Ga ?amshin turaren da ya sauya, ya sanya Nana sakankancewa a kan a wannan karon ma, irin wancan mafarkin ne.
Gaba Waya jikinta rawa yake yi, a wannan karon ma ta kasa sarrafa kanta da nutsuwar ta.

Sai dai a wannan karon al'amarin ya banbanta da na farko.

"Kai ka rabu da ni" Ta faWa da ?arfi, tana ?o?arin ture shi.

"A'a" ya faWa ?asa-?asa.

Tabbas ba mafarki ba ne ba, bayan Buzun mijin nata ya dangana da ita, wani bugire mai girman gaske, bugiren da ba ta taSa kawo faruwar sa a tsakanin su ba. Ita a tunaninta tun da ba shi da cikakkiyar lafiyar ?wa?walwa ba ya jin komai, hakan ne ya sanya take yawonta ma babu hijjabi a Wakin, sai ta ga ya dame ta da kallo, ta rufe jikinta.

Cikin kuka ta ce "Dan Allah ka ?yale ni"

"je suis d?sol? (ki yi ha?uri)" ya yi maganar muryarsa ?asa-?asa.

Bayan wani lokaci da Nana ba ta iya tantance adadinsa ba, domin ta daWe da daina gane komai.

"Ma femme. (Matata)" Ya yi maganar yana Wan murza ya tsunta. Ta buWe idonta da ya yi jawur, da ?yar tana kallon sa.

A wannan karon fitilar Wakin a kunne take. Sai dai fatarsa ta yi jawur.

Ta sunkuyar da kanta daga kallonsa.

Ya saka hannu ya share hawayen da ke fuskarta, sai dai kuma ya kasa magana.

Ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta, ya kamo hannunta ma ya sumbata. Ta lumshe idanunta tana numfashi a hankali.

"Merci (Na gode)" shiru ta yi tana ?ara sunkuyar da kanta.

Ya saka hannunsa ya Wago fuskarta, amma ta lumshe idanunta, ta ?i buWewa.

"Kalle ni mana"

KwaSe baki ta yi, ta ci gaba da kuka. Ya saki murmushi yana goge mata hawayen fuskarta ya ce "A yi ha?uri"

Ya ci gaba da wasa da yatsun hannunta, daga baya ya tashi a hankali yana kallonta, sai dai ya rasa abin gaba Waya.

Nana ta yin?ura da ?yar, ta tashi zaune, ta ja bargon ta rufe jikinta.

Su na haWa ido ta sunkuyar da kai ?asa, fuskarta a haWe, hawaye na biyo fuskarta.

"Yi ha?uri" ya yi maganar yana kallon ta.

Kawai ta sake fashewa da kuka, har da sheshshe?a.

Shafa bayanta ya ci gaba da yi, cikin sigar rarrashi, amma ta maze ta din ga kuka.

Ya ce "Ki yi shiru"

Ba ta kula shi ba, ta janyo rigarta, ta saka ta yin?ura ta tashi da ?yar, ta nufi gas Win ta.

Ta d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????afa ruwa ta shiga banWaki, ta jima sannan ta fito, a ?ofar banWakin ta tarar da shi a tsaye.

Sai da ta Wan tsorata, ta na ?o?arin raSa shi ta wuce, ya ce "Ni fa?" Ta kalle shi.

Ya ce "Zan yi wanka"

Ta ba shi hanyar shiga banWakin, ya kalli hanyar ya ce "Ruwan sanyi? A a ina jin sanyi"

"Bari na dafa" ya koma gefe ya zauna, ta Wora masa ruwan, ta kalli agogon Wakin, huWu da rabi, ta san idan ta kwanta yanzu ba bu lallai ta samu sallar asuba.

Ta shimfiWa sallaya, ta ajiye wayarta a kai, ta ajiye hijjabinta.

Yana gefenta, sai bin ta yake yi da ido.

Ta kai ruwan banWaki, ta na haWa masa, sai a yanzu ta tuna lokacin da ya ce mata zai yi wanka, ashe ruwan sanyi ne ba ya so.

Ta kashe famfon kenan, ta yin?ura ya shigo banWakin. Ta tashi tsaye tsam tana rarraba ido.

Ya mayar da ?ofar ya rufe, ta Wago da sauri ta ce "Amm ga ruwan nan, idan zafin bai yi ba, sai ka kunna famfo ka ?ara sirkawa".

"Na kasa tuna yadda ake wankan, sai kin tuna mini"

"A'a wallahi nima ban iya ba" ta yi maganar idanunta a waje dan tsoro.

"Amma ke ki ka yi? Ko wankan kwanciya bacci ki ka yi?"

Gaba Waya mamaki ya cika Nana, mutumin da magana take yi masa wahala, shi ne ya ritsa ta da wannan maganganun kamar ana karanta masa.

"Dan Allah ka yi ha?uri, ni ban iya ba"

"Astagfirullah ba kyau ?arya" ya yi maganar yana taSa ruwan.

*

Doctor Sharif ne da wani likita a kan Shukura, su na gwada bp Win ta. Duk ta kumbura sosai da sosai.

Jininta ya hau sosai da sosai, ba zai yiwu a yi mata tiyata a wannan ?adamin a cire jaririn ba, saboda hawan da jininta ya yi. Ga shi lokacin haihuwar ta bai yi ba.

Sakamakon da ya fito daga lab kuma, still ya nuna jininta ya yi ?asa.
Ayshacool
Doctor Sharif ya fito cikin damuwa, ya dubi Hajiya Amina da Yusuf, da kuma mijinta Sagir ya ce "Wai me yake damun Shukura har haka. Normal teses Win suke tuk daga farkon cikin nata, amma lokaci Waya a ce jininta ya yi wannan mugun hawan ta kumbura har haka?"

Sagir ya ce "Wallahi doctor na rasa gane kan ta, tun bai fi kwana uku da dawowa ta ba, duk ta canza. Ba ta cin abinci, bacci ma ba ta iya yi. Kullum na farka cikin dare tana zaune, na yi, na yi na tambaye ta mene ne,ta ce mini ba komai, Mummy ai har ke na gaya wa ko za ki tambayeta abin da yake damun ta.

Hajiya Amina ta ce "Rigima ce kawai irin ta Shukura, duk ta Waga hankalinta, wai tana ji a jikinta wannan cikin mutuwa za ta yi. Ina ta rarrashinta ina ba ta ha?uri, amma ta addabi kanta kuma wallahi farkon cikin duk ba haka ta yi ba."

Cikin damuwa Yusuf ya ce "Yanzu doctor mene ne abin yi?"

"Zamu ajiye ta a nan, a samu jinin ya sauka, idan babu matsala za a iya barin cikin ya cika watannin haihuwar fine, idan kuma akwai matsala za a tiyata a cire cikin"

Hajiya Amina ta ce "Allah ya zaSa abin da ya fi alkhairi"

Doctor ya amsa da "Amin, dan Allah a kula, hajiya ke kaWai za ki zauna a gurin ta, babu 'yan dubiya Please, kar a bari kowa ya je inda take, yanzu dai ta samu bacci Alhamdilillah"

"To shikenan in sha Allah, za a kiyaye"

Kiran Alhaji Zailani ne ya shigo wayarsa, dan haka ya bar gurin ya yi gaba ya Waga.

"Sharif"

"Na'am ranka ya daWe"

"Yaya ake ciki, Amina ta gaya mini su na asibitin ku Shukura babu lafiya, haihuwar ce ko yaya?"

"A'a tukuna dai ranka ya daWe, jininta ya yi hawan da ba zai yiwu mu yi tiyata yanzu ba, mu na dai ?o?arin dai-daita jinin nata ne".

"To ko ma dai mene ne, kar ka manta da maganar mu"

"Ban manta ba, ina sane ranka ya daWe"

"Yauwwa ya yi" ya katse wayar.

*

Jamila ce zaune fuskarta duk hawaye, a gaban Hajiya Sa'a. Hajiya sa'a ta ri?o hannunta ta ce "Kar ki damu Jamila, na san kin yi iya ?o?arin ki, za mu canza fasalin aikin namu, Sannan za ki samu lafiya za ki warke gaba Waya ma"

Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba.

"Akwai wata tafiya da nake son na yi Abuja, idan babu damuwa ina son za ki raka ni, amma sammako za mu yi, mu je mu dawo?"

Ta Wan yi shiru sannan ta ce "Mama za ta bar ni, Baba ne babu lallai ya yadda, amma na san za ta saka baki ya bar ni, zan ma iya tahowa bai sani ba"

"Yauwwa Jamsy, kar ki damu ki kwantar da hankalinki, in dai mu na tare, kuma za ki din ga yi mini biyayya babu abin da ba zan yi miki ba, kin ji yarinyar kirki?" Jamila ta jinjina kai tana Wan sakin fuskarta.

Ta numfasa ta ce "Hajiya bari na je gida"

"Ban ce ki daina ce mini Hajiya ba?"

"Yi ha?uri Mummy"

"Good, sai kin dawo yarinyar kirki, ki gaida gida, zan saka miki kuWin, kayan kwalliya a account Win ki"

Ta saki murmushi ta ce "Tom Na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi"

Ta juya ta bar falon, tana jin wani irin nishaWi, duk da wata irin fargaba na ratsa ta, daga ?ar?ashin zuciyarta, da ba ta san ta mece ce ba.

Karo ta yi da wani matashin saurayi, yana ?o?arin shiga gidan.

"Sannu ina wuni?"

"Lafiya ?alau ya ki ke?"

"Lafiya ?alau" ta amsa tana niyyar raSa shi ta wuce.

"Gurin Mummy ki ka zo ne?"

Jamila ta ce "Eh gurinta na zo"

Ya ce "Ok shikenan, ki gaida gida"

"Gida zai ji na gode sosai da sosai" ta nufi gate Win ta fice.

****

Da ?yar Nana ta iya sallar asuba, saboda gajiya ga bacci da take ji, da ta idar da sallar ma, a kan sallaya ta jingina tana gyangyaWi ta kasa azkar Win.

Hannunta ya Wan shafa, ta buWe idonta da kyar ta kalle shi.

"Bacci ne?" Ta Waga masa tana lumshe idonta.

Ya kama hannunta, ya Waga ta tsaye, ya ja ta zuwa kan katifa. Ta tsaya tana ?o?arin cire hijjabin, ya ?arasa cire mata ta kwanta. Ta hau katifa ta buWe bargo ta kwanta, kawai ta ji shi ma ya bankaWo bargon ya shigo. Zumbur ta tashi zaune tana kallon sa. A ranta ta ce "Lallai ji mutum da samun guri" za ta yi magana ta fasa ta tsaya tana kallon sa.
Ayshacool
Shi kuwa ya yi kwanciyarsa, ya lumshe idanunsa, ya bar ta a zaune tana hamma. Sai da bacci ya ci ?arfinta sannan ta kwanta. Sai da ya ji ta kwanta sannan ya buWe idonsa. Ya juya sosai yana kallonta.

Zai iya cewa tun da ya tsinci kansa a cikin wannan duniyar da yake a yanzu, wadda yake kamantawa da duniyar mafarki, bai taSa tsintar kansa cikin nishaWi da farincikin yau ba.

Ya kasance cikin damuwa, da tsananin Sacin ran rashin sanin waye shi, daga ina yake? Ina zai dosa? Rashin sanin amsoshin nan, na dugunzuma hankalinsa da haifar da wani irin nauyi a ?irjinsa, wani irin duhu ya mamaye shi, bai taSa jin daWin komai, ko farinciki da komai ba. Duk da dai-dai gwargwado Habu da sauran wanda suke tare su na ?o?ari a kansa, amma sam babu abin da yake raguwa na duhu da damuwa a tare da shi. Sai bayan da ya fara kasancewa da Nana a Waki guda.

Ganin gilmawarta kawai, yana kallon ta, yana jin daWi. Ya kan ji kamar ya yi mata magana amma sai ya kasa, ya rasa mai zai ce mata. A wannan duniyar da ya yi wa la?abi da duniyar mafarki, ya ga mutane na bawa ahali muhimmanci, amma shi ba shi da su, kuma ba a duba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login