Showing 45001 words to 48000 words out of 168002 words

Chapter 16 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

630

rashin ahalin nasa ba, aka aura mata shi, hakan ya kan saka ya ji tausayinta.

Yanzu a wannan duniyar yana kallon Nana a matsayin ahalinsa. Duk da ba ya son hayaniya, amma muryarta mai sanyi da daWin sauraro, ba kamar su Habu ba, sai yana cikin damuwa ko rashin lafiya, ya din ga jin muryoyin su a sama kamar kwarankwatsa ba.
Ya kan ji babu daWi idan ya ji ta shiru, yana matu?ar son ya ga tana kallon sa, idan su ka haWa ido ta murguWa baki tana magana ?asa-?asa, komai na ta a sanyaye.

Ya ?ura mata ido, yadda ta yi nisa a baccinta, ya sumbaci goshinta, ya mayar da bakinsa wuyanta ya sumbata. Ta buWe ido ta juyo ta kalle shi, idanun na ?o?arin sake rufewa. Ya kwantar da kanta a kan ?irjinsa. Ba ta yi musu ba, sai ma jikinta da ya saki. Murmushi ya yi jin yadda numfashinta yake shiga nasa, ya ji tamkar su dauwwama a haka saboda yadda yanayin ya yi masa daWi.

"Ke ce Ahalina"

Nana ce ta raSe a gefen ?ofa, tana hango ?aisar yana rubutu, sai dai wannan karon ba a cikin Library bane ba, gurin da yake haWa magunguna ne. Ga tarkacen kwalaban magunguna ko ina a cikin gurin.

"Ya dai?" Ya tambaye ta.

"Ba komai" ta faWa a hankali, tana sinne kai.

Ya ce "Na ga kwana biyu kina nema na, ba mu haWu ba, akwai matsala ne, ko kina bu?atar wani abin ne?" Ta girgiza kai tana sinnewa.

"Wai meyafaru ne na ga kin canza yau gaba Waya, kamar ba ke ba? Kin wani nutsu" Still taa yi shiru tana ?ifta ido.

Kawai ta ji ya bushe da wata iriyar dariya, da sai da ta tsorata ta Wan ja da baya, saboda yadda sautin dariyar ya karaWe ilahirin gurin.

Ya tsagaita da dariyar ya ce "Kar ki damu, ki kwantar da hankalinki ban ga komai ba, ba abun da na ganu" ta yi tsuru -tsuru amma ta kasa magana.

Ya ce "Ki maze fa kamar babu abin da ya faru, babu abin da na gani, ai ku na cikin duhu, kuma duk da haka ma, lamari ne mai girman gaske da bai dace na ga ?wa?waf ba. Sai na yi gaba abuna" ya yi maganar yana tashi tsaye.

Ya nufi gurin wasu kwalabe, yana duddubawa "Ki saki ranki fa, sai dai ban sani ba ko kin gano sakamakon binciken naki, na mutum ne ko kuma aljani da ki ka iya amincewa wani abu ya faru tsakanin ku. Abin da mamaki yadda jikin Wan Adam yake iya Waukar zafi kamar an saka shi a cikin wuta, kuma bai mutu ba. Kodayake ai haryanzu ban tabattar ba ko wani abun ya faru ba, tun da a cikin duhu ne, amma tsaya a tsakanin ke da shi waye ya kashe muku fitilar ne? Ko ita ta kashe kanta?" Ya sake bushewa da dariya, ya yi wata irin hajijiya, guguwa ta tashi, ta cikin guguwar muryasa ke tashi ya ce "Kamar dai yadda na gaya miki ne, ban ga komai ba ki daina sinne kai" guguwar ta yi waje ta daina jin muryarsa.

Ta yi ajiyar zuciya tana tunani, ta din ga jin tamkar wadda ta aikata saSo.

Ba saSo ki aikata ba Nana, makomar ki ki ke tunani. Wata zuciyar ta tunatar da ita. Tabbas zancen rashin sanin waye shi, yana damun zuciyarta. Amma ita ma mutum ce ba gini ba, ta yaya za ta iya tsallake dabaibayin da ya yi mata a daren.
Ayshacool
Idaonta ya sauka a kan tarin litattafan da suke gurin da ya zauna, da hanzari ta tashi ta tafi ta hau caje litattafan. Bisa tsananin sa'a ta ci karo da littafin da take ta ?uzun son jin ci gaban sa.

Da hanzari ta buWe, sai dai tana buWewa kawai ya kai ta daidai gurin da ta tsaya.

Ta nutsu ta ajiyar zuciya ta fara karantawa.

Lanti ta yi alwashin ko tilon 'yar ta, za ta rasu ba za ta taSa kai wa sarkin aska yarinyarta ba ya bata magani. Mijinta ya rarrashe ta a kan ta yi ha?uri, su kai yarinyar ko za a dace da maganin.

Cikin damuwa ta ce "Duk da yarinyar nan ce kaWai nake da ita a yanzu, ba kuma ni da tabbacin sake samun wani Wan, amma gara na rasa ta da na je gurin ma?iyina nema mata magani, ni na san abin yi, ka bar ni kawai"

Lanti ta shirya, ta Wauki yarinyarta, ta tafi garin da aka Waukko bokan da ya yi wa sarkin aska girka.

Ko da ta je garin ta iske ya tsufa sosai, ga rashin lafiya yana ta fama da ita.

Ta gaya masa abin da yake tafe da ita.

Ta ce "Ka ga halin da yarinyata take ciki nan, ni kuma ba zan iya kai wa sarkin aska ita ba ya bani magani, saboda a duniya ba ni da ma?iyin da ya fi shi yanzu a duniya. Kuma ina son na dakatar da zaluncin da yake yi wa mutanen ?auyenmu, da sunan Aljanu ne suke saka shi"

Ya yi shiru sannan ya ce "Ni kaina na yi dana sanin girkar da na yi wa sarkin aska, kafin ke wasu da dama sun zo a kan haka, ciki har da mai garin ku, su na neman mafita. Sai dai hatta ni kaina yanzu sarkin aska ya fi ?arfina, da na san haka ne da ban yi masa girkar nan ba".

Cikin damuwa ta ce "Yanzu mene ne abin yi?"

Ya ce "Babu wani abu da zan iya, sai dai ki koma gurin kakanki, mahaifin sarkin baka, ki ce masa ni na turo ki, ni boka Giyaz"

"Kakana kuma? Kakana ne yake da yadda za a yi da Sarkin Aska?"

"Ke dai ki je ki same shi, ki ce masa ni na aiko ki"

Ta jinjina kai ta ce "To shikenan" ya bata magani, bayan kwanaki uku, ta koma garinsu.

Kai tsaye gurin kakanta ta fara zuwa, bayan sun gaisa ya yi mata sannu da zuwa.

"An aiko ni gurinka"

Ya ce "Tun kafin ki dawo aka aiko mini da 'yan aike, suka sanar da ni zuwan mi"

Cikin mamaki ta ce "Su wa kenan?"

Ya yi murmushi ya ce "lokacin da aka zo da ni garin nan, ina Wan ?arami sosai da sosai na san wasu daga cikin gwagwarmaya da dambarwa da aka din ga yi da aljanu kafin mu samu zaman lafiya. Sai dai al?awarin aljani ba shi da tabbas, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da muka yi, sun ?i yarda mu zauna lafiya, su na kawo mana farmaki, lokaci zuwa lokaci. Yanzu dai ki na da burin kawo ?arshen sarkin baka, kuma kina burin ganin 'yar ki ta warke gaba Waya, abu Waya za ki yi sai dai abin da wahala"

Cikin za?uwa ta ce "Ka gaya mini, ko mene ne zan yi, muddin burina zai cika"

"Burinki zai cika, amma sai dai ki amince a yi miki girkar aljanu, ya zamana ke ma ki na da aljanun da ki ke iya sarrafawa, sannan za ki iya ja da shi, har ma garin nan ya zauna lafiya. Amma sai dai ki samu masu ?arfi da za su iya jayayya da na Sarkin Aska."

Ta numfasa ta ce "Kakana na amince ka yi mini girkar aljanu, dole na kawo ?arshen sarkin aska a garin nan"

"Lanti, ki je ki ya shawara tukuna. Girkar Aljanu ba hukunci ne da zaka yanke kai tsaye ba tare da cikakken shiri, da nazari ba"

Ta tari numfashin sa da cewa "Ba na bu?atar yin shawara, na gama yanke hukunci na amince a yi mini girkar Aljanu"

Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, babu laifi za ki je sai nan da sati biyu, zan haWa tsumin da za a yi miki amfani da shi, gurin yin aikin zan shafe kwanaki ina aiki a kai, domin yi miki girkar. Sai dai ina son ja bakinki, ki yi shiru har zuwa lokacin da za a yi aikin"

"To kakana, babu wanda zai ji wannan maganar, daga ni sai kai, amma ya aka yi ka iya wannan abubuwan haka?"

Yayi murmushi ya ce "Kamar yadda na gaya miki, tun ina yaro aka zo da ni garin nan, lokacin ana kan ganiyar rashin zaman lafiya da ainihin aljanun da suke zaune a garin nan. Bayan na Wan tasa na fara yawon farauta, a nan na yi karo da wani matashin saurayin, sa'ana muke shiga tare da shi daji, gurin yin farauta sai dai ya fi ni rashin ji.
Ayshacool
Shi ne ya koya mini farauta, da siddabaru kala-kala da hatsabibanci, ban san gidan su ba, kullum a hanya muke haWuwa mu tafi Daji. Sai daga bisani na fahimci ba mutum ba ne ba. Aljani ne yake shiga jikinsa, muke wannan abotar, shi ne ya koya mini harkokin farauta da magunguna har mahaifinki ya gada. Kuma ba kowa ba ne face wannan bokan da aka kawo shi garin nan ya yi wa sarkin aska girka, wanda ki ka je gurinsa yanzu. Jikinsa aljanin yake shiga, kuma shi ya haWa mu abota da boka Giyaz."

Lanti ta jinjina kai cike da mamaki, dan duk labaran da yake ba ta, bai taSa ba ta wannan labarin ba.

Ta koma gida ta yi shiru da bakinta, ko mijinta ba ta sanarwa ba.
Kakan Lanti ya shirya ya tafi daji, ya shafe makonni biyu, yana tattara saiwowayi, sassa?e da kuma sassan jikin dabbobin da yake bu?ata gurin yi wa jikarsa Lanti girkar aljanu.

"Dattijo ka yi a hankali, za ka yi mini Sarna fa" kakan Lanti ya Wago tare da faWin muryar wa nake ji haka, rai kan ga rai Uban du?usa?"

"?warai kuwa, na zata ka mutu ai"

Kakan Lanti ya bushe da dariya ya ce "Ban mutu ba tukuna, ina nan raye ina ka tafi tsawon wannan lokacin haka? Kuma a ina ka samo gangar jikin da ka shiga haka ka zo mini?"

Kyakyawan farin matashin da yake tsaye a gaban kakan Lanti yayi murmushi ya ce "Labarin dogo ne, na yi balaguro ne zuwa gabashin duniya, na samo labarai daban-daban da zan rubuta"

"Yanzu neman labarin ne, kusan shekaru hamsin babu amonka"

"Shekaru hamsin mu a gurinmu ai babu yawa. Bani labari na ga gari ya zama al?arya abubuwa sun canza sosai da sosai. Saukata kenan da kai na fara karo na ce bari na bayyana na kwashi gaisuwa"

"Tuba nake uban gidana, ai ni yakamata na zo kwasar gaisuwa." Nan kakan Lanti ya bawa uban du?usa labarin abin da ya faru.

Cikin damuwa ya kalli kakan Lanti ya ce "Yanzu duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi, sai da aka saSa ta? Waye ya yi wa sarkin askar girka?"

"Giyaz ne, mutane sai wahala suke yi a garin nan, saboda abin da sarkin aska yake yi. Ya sadaukarwa wasu daga ahalinku jini, ya mayar da su ba?a?en aljanu da sunan zai taimaka musu gurin Waukar fansar abin da mutanen garin nan suka yi muku"

Matashin ya shafi fuskarsa cikin damuwa, ya ce "Yanzu wa za ka yi wa girkar?"

"Jikata ce, da nake kyautata zaton sarkin aska ne ya kashe babanta, saboda yana bayar da magani"

Uban du?usa ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne, shikenan zan je gida, zan huta kafin ranar da za ka yi mata girkar, amma ka tabattar za ta iya Wauka? Ka san idan aka samu akasi, za ta iya haukacewa fa"

"Za ta iya, tana da juriya, kuma tana fatan Waukar fansar abin da aka yi wa mahaifinta"

"To shikenan, zan sake dawowa"

"To shikenan ubangidana, ina godiya da wannan ziyara ta bazata" suka yi sallama.

Kakan Lanti ya koma gida, ya shiga wani Waki a cikin gidansa, ya ha?a rami ya saka wata randa. Ya kawo saiwoyin da ya zo da su ya zuba a ciki, ya kawo tarkacen magunguna kala-kala ya zuba a ciki. Ya kawo ?asusuwa da wasu sassa na jikin dabbobin daji, a zuba a ciki. Ya kawo turare Wan goma, da farin goro duk ya zuba a ciki ya rufe randar, sannan ya mayar da ?asar ya binne.

Sai da aka kwana biyu, daren na uku da zai buWe randar, wanda saura kwana biyu ya yi wa jikarsa Lanti girkar aljanu. Yana cikin bacci, ya ji wata irin ?ara, sanyi yana ratsa shi, ya tashi da nufin neman abin rufa, amma ya gan shi a tsakiyar daji, gurin da suka haWu da uban du?usa.

Cikin mamaki ya ce "Ubangidana lafiya aka kira ni a wannan daren haka? Idan na yi laifi ne ina neman afuwa" uban du?usa ya fito daga bayan bishiyoyi ya ?araso gaban tsohon nan ya ce "Ba ka aikata mini wani laifi ba abokina, Ina mai ba?in cikin sanar da kai mutuwar Giyaz"

"Wayyo, Giyaz ya mutu?"

"?warai Giyaz ya mutu, sannan na yi ba?in cikin abin da na zo na riska, galibin 'yan uwana, sun koma ba?a?en aljanu, kuma sarkin aska yana sarrafa su ta mummunar hanyar da ba ta dace ba. Su na sanya muku miyagun cututtuka. Tabbas idan ku ka yi sake sai sun shafe tarihin mutanen garin nan. Ban ji daWin yadda aka saSa al?awri da yarjejeniyar mu ba.
Ayshacool
Kakan Lanti ya ci gaba da shirye-shiryen yi wa jikarsa girka.
Ya samo ?aramin ?o?o, da 'ya'yan wuri, da tsirkiya ya haWa garaya.

Ya haWa caki, ta hanyar samun butar duma ya fafe ta, ya zuba busassun 'ya'yan tafasa, da zogale a ciki, ya toshe bakin.
Ya tsayar da ranar yi wa Lanti girkar aljanu, ya sanya ranar Lahadi, a matsayin ranar da za a aiwatar da girkar. A sirrance ya aika sa?on gayyata zuwa ga bokayen ma?otan garin, da 'yan bori, a kan su halarci gurin taron bikin yi wa Lanti girkar Aljanu.

Bayan almuru, yaje ya samu ?atuwar Bishiyar kukar da ke can wajen garin, ya je ya samu, ya naWe da farin yadi.

Ya koma gida, ya tono randar nan, ya ajiye ta a tsakar gida, ta kwana tsumin cikinta ya yi sanyi.
Ya koma ya dafa wani magani, ya zuba a cikin kwatanniya. Mutanen garin kuwa, suka din ga mamaki wayewar gari, da suka ga wannan farin yadi a jikin bishiyar kuka, aka din ga surutun mene ne dalilin haka , har labari ya iske mai gari.
Aka yi ta yekuwar wa ya aikata wannan abu, kar a je wata fitinar ce za ta taso.

Kakan Lanti da kansa ya je ya samu Mai gari, bayan sun gaisa ya ce "Ranka ya daWe, ni ne na Waura wannan farin ?yalle, yau da yamma zan yi wa jikata Lanti, girkar aljanu"

Mai gari ya waro ido ya ce "Girkar aljanu kuma? Kar ka janyo mana bala'i bayan wanda muke ciki, kuma ya za mu yi idan sarkin aska ya ji, kar aljanu su fushi da mu fa?"

"Babu abun da zai faru sai alkhairi, ba zamu dauwwama Sarkin aska, yana juya mu yadda yake so ba, ina son ka yi ha?uri ka bani wannan damar"

Da ?yar ya shawo kan mai gari ya amince, aka din ga shela ana gayyatar mutane, gurin yin bikin girka.
Mutane suka din ga al'ajabi, tare da jiran yammacin ranar lahadin, domin ba su taSa sanin yadda ake gudanar da girkar ba. Nana da labari har ma?wabtan garin, aikuwa jama'a suka din ga Sarkowa cikin garin.

Kakan Lanti tun safiyar ranar, ya sanya ta yi lalle dungulmi, hannu da ?afa. Ya bata fararen kaya na sa?i, ta saka ya kawo warki, na fatar kura da aka jeme, aka saka ta a shuni, ta Waura a ?ugunta, sannan ya kawo wuri ya bata shi ma ta sanya a ?ugun nata.
Daga bisani ya kawo wasu irin guraye, ta Waura a damatsenta.

Ya kawo sandar dargaza ya bata, sanda ce da aka yi da itacen tsamiya, aka naWe ta da fatocin dabbobi daban-daban, suka yi beza a jikinta.

Tun daga gidan kakan Lanti, ta samu rakiyar mutane, Wuuuu tamkar ?udaje zuwa filin girka.

Fili ya cika ya tumbatsa, aka shimfiWa sa?i kala-kala a gurin.
Ya bata wani kwalli ta sanya a gurin, ya ba ta goro da fure, ta saka a bakinta ta tauna, laSSanta suka yi jawur. Idanunta su ka yi rabajau da kwalli.
Tuni makaWan borin, da kakan ya gayyato daga wasu garuruwan suka jeru, suka fara kaWa garaya da goge.

Ya bawa Lanti, wannan tsumin na cikin kwatanniya ta sha, ya saka ta zauna a kan shimfiWar nan. Ya din ga Webo ruwan cikin randar nan yana zuba mata, wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, har zabura take yi saboda sanyi.
Ya kawo turare Wan goma ya shashshafa mata, ya kawo wani gwado, ya rufa mata. Sannan aka koma gefe aka kunna haya?i.

Ya koma gefe shi ma ya hau kaWa kacakaurar da ya haWa.

An Wauki dogon lokaci a haka, kafin ta fara mur?ususu a cikin gwadon da aka rufe ta da shi, tana wani irin kakari. Shewa masu kiWan borin suka hau yi, ana murnar aljanun sun fara hawa kanta, dan haka suka ?ara ?aimi gurin ci gaba da kiWan borin.

A hankali ta tashi tsaye, tana wata irin girgiza, bakinta na fitar da kumfa, ta Waga wannan sandar ta dargaza, ta fara tangaWi a gurin.

Mutane suka Wauki sowa, gwargwadon tashin kiWan, gwargwadon tangaWin da take yi, tana girgiza dogon gashin kanta.

Babu tsammani, gari ya yi duhu, wani irin hadari ya haWu, sai dai hadarin na guguwa ne. A take jama'ar gurin, suka tsatstsaya, su na kallon yadda garin ya canza, su na jiran ganin abun da zai faru.

Tukunyar tsumin da aka zo da ita ta tarwatse, wata irin gigitacciyar guguwa ta turnu?e gurin, har wani ba ya iya ganin wani.

Sarkin aska ne ya bayyana tamkar an jefo shi, a hankali kuma ?urar ta fara lafawa.
Ayshacool
Lanti kuwa cak ta tsaya, hannunta ri?e da dargazarta, ta sunkuyar da kanta ?asa. Sarkin aska ya nufo inda Lanti take, cikin azama kakanta ya shiga tsakaninsu, ya tari Sarin Aska, wani irin jifa ya yi da tsohon a gefe. Lanti ta Wago da kanta, suka yi ido huWu da Sarkin Aska. Cak ya tsaya yana kallonta cike da mamaki ya ce "Uban du?usa"

"Ka dur?usa akan gwiyoyinka, ka nemi afuwar uwar gijiyata, kafin raina ya Saci" ta yi maganar cikin wani irin sautin muryar da ba tata ba.

Sarkin aska ya ce "Kai yanzu da kai aka yi wa ma?iyanmu girka? Ka manta zaluncin da bil adama suka yi mana? Ka manta gargaWin da kakaninmu suka yi mana a kansu?".

"Ban manta ba, kuma ina bayan gaskiya har abada, ku kuka fara karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi, dan haka ba zan bi bayan Sarna ba, dan haka ka yi abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login