Showing 51001 words to 54000 words out of 168002 words

Chapter 18 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

652

hankali ta nufi gadon da matar take, ta zauna a kusa da ita.

"Sannu"

"Yauwa" ta amsawa Nana.

"Shigowata ta uku kenan, ban taSa ganin ki ba" matar ta yi ?urii da ido tana kallon Nana.

Nana ta mi?a mata hannu, da nufin su gaisa.

Tamkar doluwa, matar ta bawa Nana hannu da nufin su yi musabaha.

Su na gaisawa jikin Nana ya hau rawa, ita kuma launin fatar matar, ya ?ara yin jawur, idanunta ya fara zubar da hawaye.

Nana ta ce "Wace ce ke?"
Ayshacool
Bakinta yana rawa ta ce "Ha...ha..Haulat"

"Me yasa ki ka yi mini ?arya? Ki ka zo mini a matsayin mutum? Kuma me ki ke yi a jikin bil'adama?"

"Fansa na Wauka, nan gidan a nan mune rayuwa da 'yan uwana, kawai su ka gina gida, hankalinsu kwance su ka yi zaman su, ba su yi tunanin akwai wata halittar a gurin ba. Da sun gabatar da karatun Alkur'ani ne ma, da mun ha?ura mun tashi, amma kawai suka yi gini suka zauna"

Nana ta numfasa ta ce "Kuma sai ki shiga jikin wanda bai ji ba bai gani ba ki zauna? Kun san ba ma ganin ku, me yasa za ku din ga zaluntar mu, ba za ku yi mana uzuri ba? Yanzu kin kyauta an ce matar nan ba ta ci ba ta sha, sai kuka kin yi adalci kenan?"

"Nima ba a yi mana adalci ba, ramawa muke yi"

Buzu yana zaune a kan benci, ya saka hanyar fitowa daga gidan, yana jiran ya ga ta ina Nana za ta fito, dan tana fita ya ji zaman Wakin ya dame shi.

Kawai ya hango ta, ta fito idanunta a rufe, ta nufo shi. Sai da ta kusa ?arasowa, sannan ya nufe ta yana son tambayarta ko lafiya. Kawai ta tafi za ta faWi ?asa.
Ri?e ta ya yi yana mamakin me ya same ta haka?

?akinsu ya shigar da ita, ya kwantar da ita, yana mamakin yadda jikinta ya yi sanyi ?alau.

Mamaki ne ya cika Nana bayan da ta ganta a tsakiyar daji, da ita da Haula.

"Wace ce ke? Kuma me yasa ki ka yaudare ni ki ka zo mini a matsayin mutum?"

Haula ta yi dariya ta ce "Kamar dai yadda na gaya miki, laifi aka yi mini nake ramawa. Kwatsam kuma ke ma sai na haWu da ke. Yanzu a duniya babu abin da nake ?auna sama da hadimin ki, shi ya sanya ma har na yi yin?urin taimakon ki, dan na samu shiga a gurin ki"

Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Waye Hadimin nawa?"

"?aisar, tun da na buWi ido a duniya ban taSa ganin kyakyawan matashin Aljani mai kyau da cikar zati kamar sa ba"

Galala Nana ta kalle ta, ta ce "?aisar Win? Wannan zan?alelen abin?"

"?warai shi, saboda na burge shi na zo na cinye gubar da aka kawo miki a wainar fulawa, sai dai kash! Ha?a ta ba ta cimma ruwa ba. Ina ro?on ki, ki taimaka mini na samu ?aisar, ni kuma na yi miki al?awarin barin jikin matar can, da taimaka miki da duk abin da ki ke so"

"Tirrr Allah ya yi mini tsari da sake ja wa kaina wata jarabar, ta hanyar haWa kaina da ku, shi ma maraba nake nema da shi, ido rufe, balle na sake rakito ki, ki je can Allah ya daidaita ku. A'uzu bi kalimattilahi tammat" Nana ta furta a zahiri tana hamma. Ta tashi zaune ta ga an rurrufe ko ina na Wakin, an kuna garwashi a Wan kaskon dafa shayinsa.

"Sayyid" ta kira sunansa da Wan ?arfi, amma ta ji shiru.

Ta yi mamakin dalilin da yasa ya rufe ko ina haka. Ta shiga banWaki ta yi alwala, saboda an idar da sallar azahar ma.

Da ya shigo Wakin ya tarar da ita ta idar da salla, bai ce mata komai ba, ta Wora girki tana yi masa hira, saboda ba ta iya tuna komai ba. Jin ya yi shiru ba ya tanka mata, ya sanya ta yin shiru.

*

Yaya Atine ce ta zo gida duba Baba, ta ga yadda yake tafiya da ?yar saboda ciwon ?afa.

Ta jinjina kai ta ce "Wai Isa wannan ?afar taka, ka je asibiti kuwa?"

"Atine da wani kuWin? Kin san auren 'ya na yi kwanan nan ai, mai nasara nake saya da aboniki sai a ji garau da nake haWiya, shi ne nake samun afuwa na yi bacci"

Ta kwaSe baki ta ce "Yanzu kana nufin duk kuWaWen da ka samu, da auren Nanan babu wanda za ka je Asibiti, ni fa zuwa na yi idan zan samu wani abu ma ka Wan bani, gidana ko ?wayar shinkafa babu"

"Haba Yaya Atine, ina su Nazifin da za ki zauna babu abinci?"

"Kai ina Gaddafi, ka ke zaune a haka?"

Baba ya ce "Gaddafi tun auren Nana ya tafi Ikko"

"Ka ga kawai ka fito da kuWi, idan kuma matarka ta saka ka a gaba, ta tatse ka shikenan dama ka saba abin kunya"

Caraf Mama ta ce "Ina zunubin yake balle romonsa? Ina abin yake ni kar a yi mini sharri, ban ci komai ba"

"Idan ma kin cin ai ba za ki ce kin ci ba, ni Wallahi kamata ya yi ka mayar da hankali su ma su Jamila ka aurar da su, ko ka samu ka huta. Ni ina suke nema tun da na shigo ban gan su ba"

"Su na nan sun je gidanmu" Mama ta ba ta amsa tana tsuke fuska, saboda kar ma ta ja zancen.

Ta gama surutanta, ta tashi ta tafi"
Ayshacool
****
Nana kuwa haka su ka ?arasa wunin su, ba tare da wani yana kula wani ba, ya koma mata buzunsa. Sai dai hakan bai damu Nana sosai ba, saboda ya yi mata bayani. Duk da shirun bai yi mata daWi ba, Wan kulatan da yake yi, ba ?aramin daWi take ji ba.

Sai dai tana zaune, tana addu'ar kwanciya bacci, ya shigo ya gama abin da zai yi ya Wane kan katifa. Ya zauna ta ?arasa addu'a ta shafa shi ma ya shafa.

Yana shirin ya ga ta kwanta, amma ta ?i kwanciya.

Ya ce "Mu kwanta"

Ta murguWa baki ta ce "Ni ba bacci zan yi ba"

"To mu zauna"

"Ni kawai sai ka wani din ga yi mini shiru, ni ka daina irin haka ba na so" Zuciyarsa na azalzalarsa ya tambaye ta abin da yake cikin zuciyarta, saboda har wani irin zafi yake ji a ?irjinsa, amma ya kasa furta komai. Ya rasa me ma zai yi gaba Waya.

"Ba zaka kula ni ba ko?"

"Husnahhh" ya furta a kunenta. Zirrr tsigar jikin Nana ta tashi.

"Ki amsa ni"

"Na'am" ta furta a tsorace. "Ni mahaukaci ne, nima ba na gane rayuwar da nake yi, rayuwata ta banbanta da yadda sauran mutane suke ta su. Ni ba?o ne a duniyar nan taku. Ke kaWai ce Ahalina, da ke kaWai nake gane kan wannan rayuwar. Ba zan iya zama yadda ku ke ba gaba Waya, duk da ke ma wasu lokutan kin bambanta da rayuwar sauran mutane. Amma ki yi ha?uri da yadda ki ka same ni"

"Sayyid"

Ya amsa mata da "Ma vie"

"Dan Allah ka gaya mini gaskiya, zan karSe ta a duk yadda take, dan Allah kai wane jinsi ne? Ka na tsorata ni wasu lokutan"

Hannunsa bai daina yawo a jikinta ba ya ce "Na fi yadda ni halitta ne kamar ke, mutum ne ni, amma ban san ya ake yi... Sai kuma ya yi shiru, kuma ya hana Nana sake cewa uffan, ta hanyar jan su zuwa duniyar ma'aurata, mai cike da al'amura masu tsayawa a zukata da wahalar mantawa.

Duk da, da faransanci yake gaya mata wasu kalamai, da ba ta san ma'anarsu ba, amma kai tsaye maganganun nasa suke shiga zuciyarta, tare da haifar mata da wata irin nutsuwa, duk da wahalar da ya bata.

Ta ?ara narkewa a jikinsa, ga bacci na son Waukar ta, amma zuciyarta da ?wa?walwarta, na kan kalaman da ko fassarar su ba ta sani ba, sai dai tsananin daWin da suke yi mata, ya sanya ta ci gaba da sauran su.

Sun shafe lokaci a haka, sannan da ?yar ta tashi ta fara yin wanka, sannan shi ma ya tashi, sai dai kan ya dawo tuni bacci ya yi awon gaba da ita.

*
Tamkar Nana ta taka rawa yau, saboda murnar za su fita yau, ya ce mata tare za su je dubiyar.

"Amma babu matsala ba za su bu?ace ka ba mutanen gidan? Kar mu yi laifi"

"Na gaya musu"

Da wuri ta gama komai, suka shirya suka fita tare.

Ta Waukko dubu goma a kuWin hannunta, ta tsaya ta yi sayayya a hanya, sannan suka tafi.

Asibitin da aka kwantar da Shukura suka fara zuwa.

Haidar ne ya fara gano ta, ya zabura daga jikin mahafinsa ya nufo Nana da wani irin gudu, cikin matsanancin farin ciki.

Caraf Nana ta Waga shi, ta rungume tana juyi da shi a gurin. Kawai ya ?ara ?an?ame ta ya saka kuka.

Ita kanta Nana hawaye ne ya cika mata ido, cikin sanyin murya ta ce "Is ok sweetheart, ya isa haka" ta yi maganar tana shafa kansa cike da ?aunar sa.
Yanayin kamaninsu da ta gani da Sagir, ya sanya ta gane shi ne mahaifin sa.

Ta ?arasa suka gaisa, ta ce masa "Dan Allah a wane Wakin suke?"

"Su na ciki room 2 VIP, sai dai ba sa bari a shiga"

Ta ce "Subhnallah jikin har ya yi tsanani haka, Ubangiji Allah ya ba ta lafiya, Hajiyan na ciki ne?"? A fusace Sayyid ya ja hannunta, zuwa cikin asibitin. Sagir ya mi?e da sauri ya bi bayan su, saboda ga Haidar a gurin Nana, shi kuma ya ja Nana sun yi ciki ba sallama ba komai.

A ?ofar Wakin suka tsaya, Sagir ya ?araso ya ce "Bari na yi wa Mummyn magana" ya shiga cikin Wakin, Nana ta dubi Sayyid ta ce "Daga tsayawa tambaya, sai ka ja hannuna mu tafi ai ba zai ji daWi ba"

Wani mugun kallo ya yi mata, da ya tilasta mata yin shiru da bakin ta.

Hajiya Amina ce ta fito fuskarta Wauke da fara'a tana faWin "Ga 'ya ta, ga 'ya ta" ta rungume Nana. Nana ta dur?usa har ?asa tana gaida Hajiya Amina.

"Lafiya ?alau Nana, kin ga yadda ki ka yi kyau tubarkallah? Haidar yau ga Nana"
Ya yi murmushi yana sake ri?e hannun Nana.
Ayshacool
Hajiya Amina ta ce "Allah sarki, tare da mai gidan ku ke ashe, mu na ta ?in abin nan da ganin an zalunce ki, Allah dai ya ?ulla lamarin. Sannu ka ji ya gidan?" Hannu ya Waga wa Hajjya Amina tare da risunar da kansa ?asa cikin girmamawa, ba tare da ya yi magana ba.

Nana za ta yi magana, mijin Shukura ya le?o ya kalli Nana ya ce "Ta ce ki shigo" mamaki ya kama Nana, amma ta Soye hakan. Ya karSi Haidar saboda kar ta shiga da shi, ya damu Shukura. Nana ta shiga Wakin da sallama, babu haske sosai a Wakin, amma ana iya ganin komai da yake Wakin. Nana ta ?arasa gaban gadon da Shukura take. Sai dai ta Wan tsorata ganin Shukura duk a kumbure.

"Sannu Maman Haidar, ya ?arfin jiki?"

Ta yin?ura da kyar, Nana ta taimaka mata ta jingina da jikin gadon ta ce "Jiki da sau?i Nana, dama za ki zo duba ni?"

"Haba Maman Haidar, me zai hana? Ni ban za ci za ki kawo yanzu ba ki haihu ba ma. Sannu" Ta jinjina kai ta dudduba Wakin ta ga daga ita sai Nana a Wakin. Ta kama hannun Nana ta ce "Na san a zamana da ke, wata?ila na yi miki abubuwa marasa daWi, duk da ina yaba Wawainiyar da ki ke yi da Yarona. Sai dai kowane mutum akwai irin baiwar da Allah ya yi masa, komai kallon ?as?ancin da ka ke yi masa.
Wannan maganganun nawa, ba sa rasa nasaba, da yawan miyagun mafarkin da nake yi da ke"

Gaban Nana ya yi wata irin mummunar faWuwa, ta kalli Shukura ta ce "Da ni kuma?"

Sai kuma Shukura ta rikice, ba ta san ta ina za ta fara yi wa Nana wannan bayanin ba, amma ta dake ta ce "Mafarkai nake yi marasa daWi, kuma ina yawan ganinki kin zo za ki taimaka mini. Ni dai kawai ki saka ni a addu'a a tsorace nake, ji nake yi tamkar zan bar duniya, ba zan rayu ba".

"A'a maman Haidar, kamar ba wayayyi ba, mafarki fa ba gaske ba ne ba, duk da wasu lokutan ishara ne, amma mafarkin annabawa ne yake Wari bisa Wari gaskiya. Sai kuma wasu bayin Allah da a kan yi wa ishara a mafarki. Wasu lokutan shaiWan ne kawai yake wasa da hankulanmu, amma ki kwantar da hankalinki ki saka a ranki babu wani mai yi sai Allah, kuma babu wanda ya isa ya yi miki abin da Allah bai yi miki ba. Sannan in sha Allah zan saka ki a cikin addu'a ba dan ki yarda cewa ganina da ki ke a mafarki a zahiri nice zan taimake ki ba, Ubangiji za mu nufa da bu?atunmu baki Waya, shi zai magance koma mene ne, ki kwantar da hankalinki dan Allah"

Shukura ta jinjina kai ta ce "Haka ne, na gode sosai da sosai Nana, na gode"

"Ba komai Allah ya ?ara afuwa, bari na je, na ji an ce ba a bari a shigo a gan ki"

"To shikenan na gode" ta ji daWin kalaman Nana, mussaman da ta yi ta nanata mata, mafarki ba gaskiya ba ne, wasu lokutan sharrin shaiWan ne kawai.

Nana ta fito daga Wakin, jikinta duk a sanyaye.

Hajiya Amina ta taso tana faWin "Nana kin fito?"

"Eh Hajiya, Ubangiji Allah ya bata ingantacciyar lafiya, Ubangiji Allah ya raba ta da cikin nan lafiya"

"Amin ya Allah Nana"

"A'a Hajiya ina Haidar Win?"

"Babansa ne ya tafi da shi yanzun nan"

Jiki a sanyaye Nana ta ce "Kash, ban gama ganinsa ba Hajiya"

"Ki yi ha?uri, jiransa ake yi, yana tafiya da Haidar ne gurin kakarsa ake kai shi, ni kin ga ga jinya, abin zai yi mini yawa ne. Amma in sha Allah zan saka a kawo miki shi har gida."

"To shikenan, ga wannan a bawa yarona, wannan kuma a saya wa Maman Haidar wani abin, ban san me take so ba"

Hajiya Amina ta ce "Nana har da Wawainiya har haka, dan Allah ki bari kar ki takura kan ki, zuwan ma da ki ka yi na ji daWi sosai da sosai "

Nana ta ce "A'a Hajiya, idan ba ki karSa ba ba zan ji daWi ba, dan Allah ki karSa"

Hajiya Amina fuskarta Wauke da murmushi ta karSa ta ce "To Allah ya saka da alkhairi, ki yi wa mijinki godiya ma ya ba wa Haidar kuWi, Allah ya saka da alkhairi. Na ga haryanzu ba ya magana"

Nana ta Wan saci kallonsa, ta yi murmushi ta ce "Ba komai Hajiya"

Ganin hirar ta ssu ba zata ?are ba, ya sanya shi yin gaba, Nana na ganin ya yi gaba, ta yi wa Hajiya Amina sallama a gurguje, ta nufi hanyar da ya bi.

"Shi ne za ka yi gaba ka bar ni?" Ya waiwayo ya kalle ta ya ci gaba da tafiya.
Ayshacool
Ta tsaya tana yi wa Nurses Win gurin sallama, ya ja ya tsaya tare da waiwayowa yana hararar Nana. Ta yo gaba tana murmushi, tare da mamakin yadda yake so ta ?arfin tsiya sai ya mayar da ita irin sa, na rashin kula mutane.

Yana zuwa bakin ?ofar fita, ya ja ya tsaya, Nana ta ?araso tana ?o?arin duba, abin da ya hana shi fita amma ya tare ta, shi bai shiga ba, kuma ba dawo ba.? Ta le?a ta gefensa, ta ga mene ne ya hana shi wucewa, kawai ta ga Alhaji Zailani, tare da Doctor Sharif, a take gabanta ya yi wata irin mummunar faWuwa, ta ja ta tsaya cike da razani da fargaba.

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
Alhaji Zailani ma gabansa ne ya faWin, cikin fargaba yake bin ?wayar idon Buzun da kallo, tare da mamakin ganinsa a gurin a dai-dai wannan lokacin.

A hankali Sayyid ya ja da baya, taku biyu, ya sanya hannunsa ya ri?o Nana ta bayansa, ya ba su hanya.

Alhaji Zailani ji yayi tamkar an zare masa lakar jikinsa, jikin nasa ya yi wani irin sanyi, wani abu mai kama da tsoro ya shige shi. A hankali ya taka ya shigo, yana ?o?arin kallon Nana da ke tsaye a bayan Sayyid, amma Sayyid Win ya hana hakan, saboda yadda ya ?are babbakewa ya kare ta.
Ita kanta Nana ji ta yi yanayin ta na ?o?arin canzawa, ta saka hannu ta ri?e na Sayyid, tana addu'a a cikin zuciyarta.
Wani irin ba?in ciki ya mamaye zuciyar Alhaji Zailani, ganin yanzu wannan Buzun ne mijinta, da ya aure ta ya san da yanzu bu?atar sa ta biya, wani abin yake hari ba wannan ba, amma Mahaifinta ya yi masa sagegeduwa.
Doctor Sharif ya ce "Alhaji lafiya kuwa?"

"Eh lafiya ?alau" Har Alhaji Zailani ya yi gaba, ya tsaya ya sake waiwayowa, amma ya sake ido huWu da Sayyid, ya kange Nana, ya kare ta babu yadda za a yi ya iya hango Nana yadda yakamata. Sai da Sayyid ya tabattar Alhaji Zailani ya bar gurin, sannan ya waiwayo ya kalli Nana, yadda duk jikinta ya yi sanyi, ya kamo hannunta suka fita waje.

Bai dai ce mata komai ba, ta tare musu abin hawa, ta gaya masa inda zai kai su.

Gaba Waya Nana ta rasa abin da yake yi mata daWi, ta rasa dalilin da ya sanya, gaba Waya ta rasa abin da yake yi mata daWi. Duk da tana zaton hakan baya rasa nasaba da mugun nufin da Alhaji Zailani ya taSa nuna mata, amma ta rasa dalilin da ya sanya gaba Waya take nema ta rikice, ta fita daga hayyacinta.

A hankali ta kwanta a jikin Sayyid. Cikin damuwa ya dube ta, ya dafa ta ya ce? "Ba lafiya ne?"

Ta ce "A'a"

"To Meyafaru?"

"Ba komai" ta furta a hankali kamar mara lafiya.

"Ko mu koma gida ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Sannu" ta jinjina masa kai.

Sai da suka je daf da titin unguwar su, sannan ta tashi daga jikinsa, tana kallon titin nasu.

Suka je gurin da za su sauka, ya ciro kuWi a aljihunsa ya mi?a wa mai Napep Win su ka tafi.

"Sayyid"

Ya waiwayo ya kalle ta.

Sai kuma ta yi shiru, dan rasa me za ta ce masa ta yi.

Tsayawa ya yi yana ?are wa ?ofar gidan su Nana kallo. Ko ina faci ga uwar kwata a layin.

"Bari na shiga na yi musu magana, sai ka shigo"

Ya jinjina mata kai ya ce "Zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login