Showing 33001 words to 36000 words out of 168002 words

Chapter 12 - Buzu Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

633

yadda ya yi mata kwarjini, saboda ya kafe ta da ido. Kamo hannunta ya yi ya Wora a kan kankanar ya ce "Ci"? kamar mara gaskiya ta Wauka ta kai bakinta.

Duk da gefe guda hankalinta na kan kazar nan, har da haWiyar yawu, saboda sai tururi take yi ga ?amshi.

Ya tashi ya Wauki kofi, ya tsiyayo shayi, a cikin butar shayinsa, ya zo ya ajiye a gefen sa.

"Ki ci" ya kuma maganar yana zaro mata ido.

Ba shiri ta tattarata nutsuwarta, duk santa da kazar, kasa sakin jiki ta yi ta ci, saboda tsoron yadda ya tsare ta da ido, sai dai tana iya hango tausayi da damuwa a cikin idanun nasa.

"Na ?oshi" ta faWa a Wan tsorace.

Ya Wauki Wan ?aramin kofin da ya zuba shayi, ya mi?a mata, a zaton ta shayi ne, sai dai tana sha, ta ji tamkar ta haWiyi wuta. A take yanayinta ya sauya ta ji duniyar ta fara juya mata!

Ayshercool
08081012143
Ayshacool
https://chat.whatsapp.com/FMI9ln54k8E3VhCaqgRAZq


Page 32


Gani ya yi ta rintse idanunta, jikinta ya fara karkarwa, mamaki ne ya kama shi, ya duba cikin kofin ya ga shayi ne a ciki. Ya kai bakinsa ya sha, shi bai ji komai ba.

Mur?ususu take yi, a galabaice tana jin tamkar ana yayyanka kayan cikinta, ta yi wani yin?uri sai ta fara aman jini mai yau?i. Ta Wauki lokaci tana yi. Ta Waga kai da ?yar, ta ga Buzu a tsaye a kanta, kafin daga bisani ya rikiWe mata zuwa wannan tsohon. A razane ta fara ja da baya. Ya ja da baya ya buWe bakinsa, zai fara feso mata wuta, ?aisar ya bayyana yana wani irin huci.

Tsohon ya buWe bakinsa yana dariya mai razanarwa, haya?i na fitowa daga bakinsa, ya ce "Na sani, na san za a rina, ta wannan hanyar ce kaWai zan hukunta ka ?aisar"

Cikin tsawa ?aisar ya ce "Kuskure mafi girma da zaka aikata, shi ne cutar da yarinyar nan, cutar da uwar gijiyata tamkar cutar da ni ne, dan haka ni da kai muke wannan rigimar babu ruwanta, domin babu ta yadda za a yi ta biya bashin da ba ita ta ci shi ba"

"?arya ne, sai ta biya shi, ita ce za ta biya ka sanya wannan a ranka. Ka fi kowa sanin ba ma yafiya, ba ma yafe bashin gaba, sai ta biya wannan bashin" ya Waga sandarsa ya nuna Nana da ita, amma cikin zafin nama, ta ji an yi sama da ita an watsar a guri Waya.

A hankali ta ja jikinta tana tari, ?aisar ya bayyana a gabanta, cikin Sacin rai ya ce "Ki sanya a ranki ba a yi komai ba, ?alubale da tarkuna marasa adadi mun din ga faWa musu kenan, idan mun tsallake wani, wani sai mun faWa masa"

Nana ta Wago kanta a galabaice ta kalli ?aisar ta ce "Wai dan Allah waye wannan tsohon? Me na yi masa, Ko shi ne na aura a suffar mutum ne?"

"Sanin waye shi, ba shi da wani amfani a gare ki. Ki yi ta kanki da rayuwar ki kawai. Ko dai ki bar wannan auren mu tsira baki Waya, ko kuma yanzu mu ka fara wahala".

Nana ta girgiza kai ta ce "Sanin waye shi yana da amfani a gare ni, waye shi? Meye ala?a ta da shi da yake tsorata ni, laifin me na aikata masa yake i?irarin sai na biya? Da wace hujjar zan kashe auren nan? Ko har ka manta irin ?alubalen da na keto?"

Shiru ?aisar ya yi mata yana karkaWe rigarsa, har ta buWa baki za ta yi magana, ta jiyo sautin wata ?ara a bayan wata ?ofa, kuma ta ji tamkar ta san muryar da ta yi ?arar.

"Ihun me nake ji haka?"

"Je ki duba mana" ya bata amsa yana yin gaba, ya nufi kofar da sautin ?arar yake. Yana shiga Nana ta rufa masa baya, sai dai ta yi turus da ta ga Jamila a Waure a jikin wani itace, jikinta babu kaya, fatarta tamkar ta ?one, ga wasu zarurruka da aka saka, aka WaWWaure ta da su.

Hankali tashe Nana ta ce "Kai Jamila, me ta yi maka? Meya same ta haka?"

?aisar ya ce "Me ta yi mini ki ke tambaya? Me ya faru bayan kin ci abincin da ta kawo miki? Idan Alhaji Zailani zai kassara yaran da ya haifa a cikin sa, saboda duniya ke me yasa ki ke tunanin dan kun haWa uba Waya da ita ba za ta cuce ki ba? Dole ta karSi hukuncin abin da ta aikata, ko da kuwa ya kama na kashe ta ne.

Nana za ta yi magana ta ji ana taSa fulon da take kai.

Ta buWe idonta ta ga wani irin matsanancin duhu, babu alamar haske ta ko ina. Ta yin?ura ta tashi zaune, tana faWin hasbunallahu wani'imal wakil.

Ta mi?e tsaye tana laluben hanya, ganin duhun na ?ara tsananta. Wal?iya aka yi mai tsananin haske, da ya gauraye Wakin, ya bayyana tsaye da sandarsa yana kallon Nana. Rikicewa ta yi ta saka ihu. ta zabura za ta kasa da gudu. Tun da ta tashi tsaye a kan katifarta yake kallonta. Sai da ta yi ihun nan, ta nufi hanyar waje, ya mi?e da azama ya ri?e ta.

Fizge-fizge ta hau yi cikin matsanancin tsoro da razani.

"Me ya faru ne?" Ya yi magana cikin nutsuwa da kamala.

Fashewa ta yi da kuka, cikin rawar murya ta ce "Tsoro nake ji, dan Allah ka daina tsorata ni"

"Me na yi miki?" Ya yi maganar fuskarsa Wauke da damuwa.

Ta Waga kai ta kalli kamilalliyar fuskar sa, ya lumshe idanunsa ya buWe a kanta. Ta sunkuyar da kanta tana jin yadda sanyi yake ratsa ta, zuciyarta take bugawa, jikinta sai tsuma yake yi.
Ayshacool
*
Da safe babu kowa a Waki sai Nana, ta shiga banWaki ta yi wanka, ta gama ta buWe ?ofar ta fito, ta ganshi yana gyara mata shimfiWarta, ya karkaWe mata. Ya Wauki tsintsiya ya fara share Wakin.
Ya Wago suka haWa ido, ya kawar da kansa ya ci gaba da shararsa. Saboda daga ita sai zanin wankanta ta fito, dan ba ta san yana Wakin ba.

Nana ta ?araso ta ce "Ka bari, zan share Wakin, bari na shirya"

"Ba komai, ki huta ba kya jin daWi" ta Wan ware ido, jin ya yi magana.

Ta numfasa ta ce "Ina kwana"

"Wane kwanan?"

"Gaishe ka na yi fa" ya Wago ya kalle ta ya mayar da kansa ya cigaba da shararsa, ya gama ya kwashe ya je ya zubar.

Ta shirya yana gefe yana aikin shan shayi, yana haWawa da dabino yana ci.

Ta bubbuWe kazar da Habu ya kawo, ta Wumama, ta Wibi miya ta haWa su ta ?ara dafawa, ta zuba ta ajiye a gabansa.

Ya girgiza kai ya ce "Naki ne, ki ci"

Ta ce "Ai na ci, kai ba ka ci ba"

Ya girgiza kai ya ce "Na ?oshi"

Nana ta sake tura masa kwanon ta ce "A'a ba ka ?oshi ba, dan Allah ka ci" ta yi maganar tana saka masa cokali a kan kwanon.
Ya kama cokalin, ya Wan yagi kaWan zai kai bakinsa ya ce "Bismillah" Nana ta Waga kai ta kalle shi da mamaki.

Jiki a sanyaye ta ce "Na san wata?ila ina yin wasu abubuwa, da za ka kasa gane kaina, kamar ba ni da hankali wasu lokutan. Na san babu lallai an yi maka bayani, ina fama da rashin lafiya ne" ta yi maganar tana wasa da yatsun hannunta.

Ya ce "Aa yau ba ki yi rashin lafiya ba, kin warke ai tun jiya" sai ta ga kamar bai fuskanci abin da take nufi ba.

Ta tsura masa ido, tabbas ma sha Allah, kyakyawan ne, fari ne mai dogon hanci sosai da Wan siririn sajen sa, kuma a nutse yake. Babu babban abin da yake Waukar hankalinta game da shi, bayan nutsuwar sa, sai wannan kyakyawan dogon gashin da yake da shi, tamkar mace. Duk da ta kasa tantance abubuwa da dama a kansa, amma zuciyarta na Wauke da tarin tambayoyin da take fatan bakinta ya furta.








Ya Wago shi ma ya tsare ta da nasa idanun, yana tauna a hankali. Ta sauke nata idanun ta ce "Amm ban san sunanka ba haryanzu ba fa"

Kamar ba zai yi magana ba ya ce "Zan sha ruwa" tana mamakin dalilin da ya sanya yake kaucewa wannan tambayar har sau biyu, sai ta ?yale shi, ta Waukko ruwan ta ba shi.

"To ka bani wayata, na yi kallo"

"A'a" ya furta yana tashi tsaye. ya tafi gaban mudubi, ya fara shiri. Yana tsaka taje gashin nasa, ya hango Nana ta cikin mudubin, tana kallonsa. Ya Waukko comb Win ya nufo Nana, da sauri ta sunkuyar da kai.

Ya zo gabanta ya mi?a mata comb Win, ta tsaya tana kallon sa, ya ?ara mi?a mata. Ta saka hannu ta karSa, ya gyara zamansa ya juya mata baya, ya Wan yo baya da kansa. Ta yi shiru tana kallon kan nasa.
"Ki taSa, na ga ki na so" wata irin kunya ta kama Nana, haushin kanta ya kama ta, yadda ta bari har ya iya gane gashin kansa yana burge ta.

Ta dafa kafaWarsa, da nufin ta tashi, kawai ta gansu a wani ?asaitaccen Waki na alfarma, maimakon Wakin su.
Ta kalli jikinta, ta ganta sanye da wasu kayan na daban. Hannunta dai ri?e da comb Win. Duk yadda ta yi ?o?arin yin magana ta kasa.
Ta saka hannu, ta fara taje lallausan gashin nasa, ta gama ta tufke masa kamar yadda yake yi. Ya mi?e tsaye ya juyo ya kalle ta, ya kama hannunta ya sumbata ya ce "Allah ya yi miki albarka"

Kamar wadda aka jonawa shocking ta zabura, ta ga Wakin ba kowa, ga dai kwanukan da ya ci abinci, ya wanke ya ajiye mata. Ta tashi tsam ta je ta le?a ta taga, ta hango shi a zaune a kan kujera, a gefen gate ya kara radio a kunnensa, gefe ga butar shayin sa.
Ta dafa bango ta jingina a hankali, hawaye ya fara ziraro mata, a hankali ta ce "Ka yi nasara ?aisar, ka burkita mini ?wa?walwata fiye da baya. Na fara hauka, ba na iya tantance zahiri, tunani da mafarki. Ka cutar da ni" ta ?arasa maganar tana sheshshe?ar kuka.

Muryar ?aisar ta ji tana amsa kuwwa a Wakin. "Ba ni ba ne, ko zan saka ki hauka ba yanzu ba, da sauran lokaci, ina ?ara baki lokaci ne. Abin da na yi ta yi miki gargaWi a kai ne"

"Allah yana tare da ni, ba zan bayar da magani ba ?aisar, ba na bu?ata ka ?yale ni na yi rayuwata dan Allah" ta ?arasa maganar wani kukan yana kufce mata.
Ayshacool
"Nana" ta ji muryarsa a bazata. Da sauri ya sauke rawaninsa a kiWime ya ce "Meya faru?" Kasa magana ta yi, ta ci gaba da kuka.
Cikin damuwa yake kallonta, ya rasa abin da zai ce mata, ga shi da gaske kukan take mai tsuma zuciya.

"Na yi wani abu ne?" Ya furta yana kallonta. Ta girgiza masa kai alamar a'a.

Ya sake cewa "Ba lafiya ne?"

Ta sake girgiza masa kai. Ya saka hannu ya dafa kafaWarta, a take wani irin sanyi ya shige ta, har ?afafuwanta.

Babu tsammani ya haWa ta da ?irjinsa, duk da tana jin yadda zuciyarta take harabawa da sauri, amma ta yi shiru ba ta motsa ba, ba ta tunanin a rayuwarta, akwai wanda ya taSa ba ta wannan damar. Maimakon ta daina kukan, sai ta sake fashewa da sabon kuka, sababbi da tsofaffin damuwoyinta duk suka taso mata. A hankali ta ji ya zura hannunsa a cikin nata ya ri?e.

Duk da a ?asan zuciyarta, tana jin mafarki ne, amma ta ji daWin samun damar zubar da hawayen nan da ta samu.

*

Tamkar zai tashi sama, haka yake bala'i yana kumfar baki.

"Ai dama na sani, wallahi haryanzu tana son tsohon mijinta, kuma tana magana da shi ta waya, ina da cikakkiyar shaida a kan hakan"

Wata babbar mace da fuskarta ke Wauke da damuwa ta ce "A'a Iliyasu, ba na tunanin Mai jidda za ta yi haka"

"Au goya mata baya za ayi ma kenan? Ina da cikakkiyar shaida, ba na son mutuncinta ya zube ne kawai saboda 'ya'yana"

"A'a ba goya mata baya zan yi ba, amma ka yi ha?uri dan Allah"

"A'a a yi magana a buWe, idan tsohon mijinta take so, to ta koma gurinsa ba dole"

Maijidda na gefe tana ta sharSar kuka, tamkar ranta zai fita, ya gama bambamin masifarsa ya fice daga gidan.

Matar ta dawo da hankalinta kan Maijidda ta ce "Wai maijidda abin da Iliyasu ya faWa gaskiya ne? Ana idar da sallar asuba fa ya kira ni a waya ya ce lallai na zo na ji abin da ki ka aikata"

Cikin kuka ta ce "Wallahi Adda ba a yi haka ba, ro?onsa kawai na yi ya bani dama na je na ga halin da yarinyata take ciki, an ce mini an yi aurenta, amma ban sani ba, ko ba komai Nana da Imaran su ma yarana ne, na rasa irin wannan abu ?iri-?iri an raba ni da yarana"

Adda ta ce "To ke mai jidda ban da abinki, ba a gurin babansu suke ba? Ko a kan yara biyu sai ki salwantar da aurenki, da yaran nan shida saboda guda biyu ne?"

Ta Wago jajayen idanunta ta ce "Adda su ma biyun ni na haife su, ba su da kama ta, su na bu?ata ta, shekara goma sha ina tattalin wannan auren, duk da ?iyayyar da yake nuna wa 'ya'yana amma wallahi zuciyata na Kano tare da Nana da Wan uwanta"

"Aikuwa sai ki yi ha?uri, Allah ya ?addara abin da zai riga ya faru. Yanzu ki bari zan shirya da kaina, ki kawo abin da ki ke da shi da ki ka ajiye saboda aurenta, mu haWa a kai mata ke dai ki yi ha?uri da zuwa, zuwa lokacin da zai saukko. Bari na kira shi a waya"

Adda ta kira Iliyasu, sai da ta ta tsinke ta sake kira, sannan ya Waga.

"Dan Allah malam Iliya ka yi ha?uri, ita ma ta ce a baka ha?uri, ba za ta sake ba"

"A'a ai na daWe ina fuskantar take-takenta ne, kuma wallahi ba za ta sake ri?e waya ba, kuma wallahi ta sake ta taka zuwa ?afarta zuwa garin Kano, ta fake da yaranta ta haWu da tsohon mijinta, a bakin aurenta tun da ni na Wan iska ba ne"

"Ai ba ma za ta sake ba, ta tuba ta daina ka yi ha?uri ka yafe mata" ya gama bala'insa, Maijidda na jin sa ba abin da take yi sai kuka.

"Maijidda ki yi ha?uri, idan ki ka kashe auren nan saboda yara biyu ya za ki yi da na gaban ki? Duk abu gidan nan akwai ci akwai sha. Idan ki ka koma gidan Gwaggo ma, ita ba cikakkiyar lafiya ba, ga babu guri gara ki yi ha?uri. Ita yanzu tun da ta yi aure ta samu ta zo inda ki ke" Adda ta gama maganganunta, Maijidda ba ta sake tofawa ba.

****
Habu ne a tsaye a ?ofar Wakin, yana kwaWa sallama, ya amsa masa.
Ya Waga labulen ya shiga, kawai ya tarar da su a zaune a gefen katifa, Buzu yana fifita mata shayi a kofi, gabanta kuma ga ledar ?osai ga kankana. Tana tauna ?osan a hankali, fuskarta duk busasshen hawaye.
Ayshacool
Cikin damuwa ya ce "Amarya, meya faru ne? Ya kira ni hankali a tashe ya ce kina kuka, ko wani abin ya yi miki ne da ba kya so?" Ta Waga kai ta kalle shi, sai kuma ta ji tausayin sa ya kama ta, daga shi har Habun.

Ta ce "Ba abin da ya yi mini fa"

Habu ya ce "Kar ki ji komai, gaya mini idan wani abun ya yi miki ma?"

"Bai yi mini komai ba"

"Subhnallah, amma hankalinsa ya tashi sosai da sosai fa ya kira ni ya gaya mini, ki na kuka bai san meyafaru ba. Ko ba kya son sa ne?"

Nana ta Waga kai ta kalle shi, aikuwa ya tsare ta da ido, da alama jiran amsar sa take yi. Ta kawar da kanta gefe tana murguWa baki.

Habu ya yi shiru yana murmushi, buzu ya mi?a mata kofin shayin, ta karSa, sai dai ta tuna wancan karon da ya ba ta abu ta sha, hankalinta gushewa ya yi, dan haka ta ci gaba da ri?e kofin a hannunta.

Ganin babu wata matsala ya sanya Habu ya ce "To ni bari na tafi, amma dan Allah a daina yi masa rigima, ni bari na tafi"

Suka yi magana da french, Habu ya yi musu sallama, ya tafi.

Yana tafe a hanya, hana murmushi yana yi musu fatan alkhairi, domin ya ji daWin yadda ya gan su.

"To kai ma ka ci ?osan mana" ta yi magana tana Waukkowa ta mi?a masa.

Ya saka hannu ya karSa, ya saka a bakinsa.

Nana ta numfasa ta ce "Daga yanzu idan ina yin kuka, ko bani da lafiya, ka daina gaya musu, ka ga an saka shi yana ta zuwa, kuma da nisa daga can zuwa nan"

Ya dube ta ya ce "To ki daina"

"To, amma dama wai ka na magana haka, amma sai ka din ga yi mini shiru? Ba na jin daWin hakan gaskiya" ya Wan yi murmushi ya ce "?aukewa take yi"

"Me?"

"Maganar " ya bata amsa.

Cikin mamaki ta ce "To ta yaya maganar mutum take Waukewa, kamar wutar nepa?"

Ya ce "Ban sani ba, wataran ma yaren naku, Waukewa yake yi, na manta duka"

Kawai ta Wauki kalaman nasa, a matsayin zolaya, sai ma suka bata dariya.

"To ni dai ka gaya mini sunanka"

"Buzu".

Ta ce "Ai Buzu ba suna bane ba, sunanka na gaskiya"

"Shi na faWa"

"To ai Buzu ba suna ba ne ba, kamar sunan ?abila ne"

Horn Win mota suka ji, a bakin gate, dan haka ya tashi ya fita ya je ya buWe, bayan ya buWe, ya ?i dawowa Wakin ya yi zamansa a waje.

Sai bayan sallar isha'i ya dawo, ya ci abinci ya nemi guri ya Waukko wayarta, ya kunna film Win Indiya fassarar hausa yana kallo.

Ta ?ura masa ido, duba yadda ya tattara nutsuwar sa a kan screen Win wayar.

"Wai zuwa yaushe za ka bani wayata ne? Ina son kiran su Anty Ummi, tun da suka tafi ban kira na ji yaya suka je gida ba" ya yi mata shiru, ya ci gaba da kallon.

Zaman shirun ya dame ta, ga wayarta a hannunsa, ga babu abokin hira. Ta kwanta bacci da wuri ko za ta yi bacci, amma ta kasa.

Da ?yar bacci ya Wauke ta.

Daf da kiran sallar asuba ta tashi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login