Showing 27001 words to 30000 words out of 194715 words

Chapter 10 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

953

wai dan ta yarda ɗin ba hasali ma tunanin yadda zata gudu ta koma gidan su Imran take, daga daddy har ita ɗin ba wan da yayi barci ranar haka suka kwana cikin tunani.

Bari mu leƙa Jehan mu dawo

💞💞💞💞💞💞💞💞

KATSINA

Misalin karfe 1 na dare farin wata na nan tas a tsakiyar duniya kasan cewar daren goma sha huɗu ne na wata, wasu kartin maza su biyu suka diro cikin gidan su Jehan kai tsaye suka wuce kufar da zata kai su ɗakin gwaggo kamar sun san hanya ɗaya daga cikin su ya sanya yar makulli safaya key ya buɗe kofar ɗakin, suka kutsa kai cikin ɗakin kasa kasa ɗayan yace "Fadil ina take sai fa mun kunna haske" Fadil na ƙoƙarin yin magana suka ji diran wasu mutanen cikin gidan nan take suka tsorata har suna rige rigen shiga toilet dake ɗakin wadda babu kofa, suka ɓuya wadda su Jehan suka mai da wajen a jiye kayan datti dan basu amfani da toilet ɗin dana waje suke amfani kasan cewar wan nan yayi karami sosai, shiru suka laɓe suka kasa kunne dan jin su wanene suka shigo gidan su Jehan ɗin, takun tafiyar manya sukaji hakan ya tabbatar musu ba kananan mutane bane suka shigo gidan, sunyi shiru suna jan mumfashi a hankali sun kasa kunne, can kasa kasa suka jiyo muryan ɗaya daga cikin wayan da suka shigon yana faɗin "Nasir ai kofar ma abuɗe take" Nasir Fadil ya mai mai ta sunan a ransa yana mamaki, suna tsaye har su Nasir suka shigo cikin ɗakin, sai da suka gama shigowa san nan suka fara magana kasa kasa dan sun san gwaggo da Jehan sun yi barci a irin wan nan lokacin,
jin motsin mutane yasa mum ta farka daga barci da kyar ta iya miƙewa zaune ta ɗauki wayar ta, ta kunna wutar wayar, ta sauko kasa daga gadon, ta ɓuɗe kofar ɗakin ta fito ta nufo ɗakin su gwaggo dan tanan take jiyo motsin ta sha ruwan mamaki ganin ɗakin su Jehan ɗin a buɗe, sosai ta kara haska kofar wajen ganin germ lock ɗin dan dama daki su Jehan da germ lock suke rufewa ba sakata a ɗakin, cikin tsoro ta ɗaga haske wayan nata ta haske cikin ɗakin sai kan face ɗin ɗaya daga cikin abokan Nasir dake tsaye ta bakin kofa, ga idon nashi jawur kamar jini manya manyan kai da gani kasan wan nan yana shaye shaye over ganin shi ba karamin tsorata mum tayi ba nan take numfashi ta ya ɗauke ta zuɓe kasa sumammiya

Tashin sense masu karatu mu koma mu leƙo daddy da jelly ya suka tashi sai mu dawo

💞💞💞💞💞💞💞💞

KANO

Washegari da safe daddy ya sha ruwan mamaki ganin yau jelly ita da kan ta tayi wanka tun kafin ya dawo sallar asuba ta tashi ta yi wanka ta shirya cikin uniform nata riga fari da wando ash da ɗan karamin farin hijabi zuwa kirji, hakan ba karamin mamaki ya ba wa daddy ba dan bata taɓa kwatatan ta hakan ba, amma sai ya ɓoye mamakin sa ya yaba mata sosai sai dariya take fararen hakoran tannan sai kyalli suke, wucewa shi ma yayi ya je yayi wanka, ko da ya fito bata ɗakin ta fice palo sauri sauri ya shirya cikin suit sannan ya ɗauki jakar computer sa da wayar sa ya duba time 7:02 sauri sauri ya fito zaune ya iskota saman sofa tana ta murmushi kamar ba ita ba a wan nan karon daddy ya kasa ɓoye mamakin sa yace "My baby what is happening ne?" Miƙewa tayi ta rungume sa tana faɗin "My daddy I want you to be happy everyday that's why" rungume ta yayi kawai amma bai yarda da maganar ta ba dan yasan halinta sarai, kafin ya sake ta yana faɗin "Muje muyi breakfast mu tafi kar lokaci ya kure" ba musu ta bishi suka zauna saman kujerar table, Nana tazo tayi serving na su sauri sauri suka yi breakfast, bayan sun gama daddy ya riko hannun ta suka nufi waje, suka je suka shiga mota gidan baya idi driver ya shiga gidan gaba ma zaunin driver yayiwa motar key suka bar gidan, a bakin gate na school na su suka tsai da motar daddy ya juyo ya kalle ta yace "Yau ba zamu shigar da ke ciki ba nayi late sauka ki shi ga school ina kallon ki" ba musu ta sauka daga motar da murmushi tace "Daddy na, ina kaunar ka sosai ka kula min da kan ka sannan kayi min alkawari ba zaka sake kuka ba komai zai faru da ni" daddy bai kawo komai a ransa ba yace "Na miki alkawari my baby ba zan sake kuka ba" sako kan ta tayi ta glass ɗin motar ta manna masa kiss a kumatu bata jira reply na shi ba ta wuce da sauri saboda hawaye da ya gangaro mata, zuba mata ido daddy yayi yana kallon ta, ya sha ruwan mamaki ganin yau bata juyo ta masa bye bye ba saɓanin kullun da take juyowa wani lokaci ma tafiyar baya baya take tana kallon sa, ganin su daddy basu tada mota bane yasa ta fahimci daddy na kallon ta dan haka sai ta kara sauri ta shige cikin school, tana shiga school Idi driver ya tada motar suka bar wajen sai mamaki daddy yake nan take yaji jikin sa ya mutu gaban sa na faɗuwa, haka ya daure dan bai kawo komai a ran sa ba har suka isa office na shi,

Ita kuwa jelly tana laɓe a wajen gate sai da taji motar su daddy ya bar wajen tayi Sa'a mai gadin ya zaga bayan gida su daddy na tafiya ta fito da sauri ta kariso bakin hanya ta tari abun hawa ta hau tana sauke ajiyar zuciya "Ina zan kai ki?" Mai mashin ɗin ya tambaye ta cikin sauri tace masa "In da ake hawa mota" ɗan juyowa yayi ya kalle ta kafin yace "Motar zuwa ina?" Sai lokacin ta tuna ita bata ma san a wani gari gidan su yaya Imran yake ba shiru tayi tana tunanin hiran da suka yi a baya da Imran "Motar zuwa ina nace?" Mai mashin ɗin ya sake gefo mata tambaya nan ta tuna last zuwan yaya Imran yace mata daga Kaduna ya fito da ta tambaye sa daga ina ya fito tuna haka yasa cikin sauri tace wa mai mashin ɗin "Motar zuwa Kaduna" ba tare da ya sake magana ba ya buga mashin ɗin sa suka nufi park sai sauke ajiyar zuciya take,
Ko da suka isa bai sauke ta ba sai da ya kai ta har wajen motocin Kaduna tayi Sa'a kuwa motar saura mutun ɗaya ya tashi, mai mashin ɗin yace "Kawo kuɗi na biya miki kuɗin mota" ba musu ta sauke jakar school dake bayan ta, ta zaro dollar dubu ɗaya tana faɗin "Nawane kuɗin?" Waro ido waje mai mashin yayi yana kallon kuɗin dake hannun ta nan take jikin sa ya fara rawa kasa kasa yayi da murya yace "Ki mai da kuɗin nan idan kina da kuɗin Nigeria ki kawo" miƙa masa dollar tayi tana faɗin "To kai riƙe na baka dan kana da kirki ina da kuɗin Nigeria" ta kai karshen maganar tare da sanya dayan hannun ta ta zaro dubu dubu guda biyar ba musu mai mashin ɗin ya ansa dollar da ta bashi ya mata godiya san nan ya ansa 5k da ta ciro ya sauka ya biya mata kuɗin motar zuwa Kaduna ya mata sallama tare da bata canjin ta ya wuce, shi kan sa driver ya sha ruwan mamaki ganin yarinya kamar jelly tazo hawa mota hakan yasa ya tambaye ta ina zata je dan ya tabbatar tana cikin hayyacin ta yarinya 14 years, cikin sauri ta sanar da shi Kaduna zata je da mamaki a face na shi na jin tana cikin hayyacin ta haka a ka loda kayan passengers a bayan mota, driver ya shiga kowani passenger ya shiga mazaunin sa jelly ta zauna kusa da wata tsohuwa mota ta tashi zuwa Kaduna.

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💋Star Lady💋

*💞TRIPLET'S💞*


💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞





STAR 🌟 LADY..✍️


*💋The beginning💋*


Episode 7

💞💞💞💞💞💞💞💞

*3 years back*

*Abuja*

*7:10 am*

Wata haɗaɗiyar Hajiya ce zaune saman sofa mai zaman mutun 2 cikin wani katafaren palo, palo ne mai girman gaske mai ɗauke da sofa set manya manyan set biyu kowani set da kalan sa sai makekiyar Tv plasma dake manne a bango, daga gefe kusa da kyakkyawar staircase ɗin haurawa sama table ɗin cin abinci ne awajen mai bala'i kyau mai kujeru 8 daga wajen table ɗin kofar kitchen mai girma gaske mai ɗauke da duk wani abun da mace ke bukata a kitchen, ga manya manyan gas cooker guda biyu.
Sanye matar nan take cikin dan kareriyar Swiss lace pink color da ratsin baƙi, ɗin kin bubu gown ta sha kwalliya sosai, wuyar ta da hannun ta sanye da dankara dankaran gold tayi kyau sosai ta yi ɗaurin Zahra Buhari a kan ta da ganin ta kasan naira ta zauna mata sosai jikin ta jikin hutu yayi luwai luwai da shi gata fara tas kyakkyawa a jin farko, shiru ta zauna tana kallon News a makeken Tv plasma dake manne a bango, hankalin ta yayi nisa a kallon da take wani kyakkyawan Alajine ya sauko daga saman bene fari tas da shi kamar balarabe yana shirye cikin wata dakakkiyar shadda ash color kyakkyawa ne sosai yana da kwantatciyar saje da gemu bakin kirin ga gashin kan sa na fulani har wani curly yake yana nannaɗewa ya gangaro masa har gaban goshi ga wata kyakkyawar gashi da ta kewaye ɗan bakin sa tayi masa kamar raun ba karamin kyau hakan ta karawa face na shi ba, a hankali ya tako ya kariso cikin palon ya sanya hannu ta baya ya rufe idon hajiyar dake zaune sofa, cool murmushi ta sake har sai da fararen hakwaran ta suka bayyana ga wani siririyar wushirya a tsakanin hakwaran nata gwanin ban sha'awa cikin shagwaɓa tace "Barkama (sunan girmamawa ne na fulani) kayi latti ai to" murmushi ya saki wadda yasa dimple na shi lotsawa slowly ya zame hannun sa daga kan face nata tare da zagayowa ta gaban ta yana faɗin "bongel am (kyakkyawa ta) barka da tashi" murmushi tayi tana kokarin yin magana wata kyakkyawar yarinya chocolate color ta sauko daga saman benen da gudu, kyakkyawace ajin farko doguwa tana da dogon hanci har baka ga dara daran ido kamar ball farare tas kamar auduga idon nata design of fish ne san nan kuma sleeping eyes gare ta wadda idan ka ganta zakayi tunanin barci take ji amma ba barci bane gasu da girma idon kamar ball bakin ta ɗan karami launin pink lip nata na sama design of heart ne kanta ba ɗankwali curly hair ta ya nannaɗe kamar indomie ga gashin nata dark black sai kyalli yake kai kace an tsomashi cikin baby oil ne saboda curly da kyalli da yake gashin nata har gadon bayan ta duk da yana nannaɗe hakan bai hana shi kai mata tsaliyar bayan ta ba tana da dogayen gashin ido sosai kamar tasa eyelashes ga saje mai kyau dark black kwance a gefe da gefen kumatun ta tana sanye cikin wando skin tight baƙi da white T-shirt mai dauke da bajel ɗin makaranta kyakkyawan kafofin ta ba ta kalma, hannu ta na riƙe da wani katuwar teddy kamar jaririn mutun a shekaru ba zata wuce 10 years ba,
Da gudu ta sauko bene tana faɗin "Daddy kace wa Jehan ta kyaleni" tayi maganar cikin harshen shuwa arab ta kai karshen maganar tare da rungume sa, shafa curly hair ta yayi kafin yace "My Rimsha My siha where is your Abaya? Ko so kike muyi latti ne?" Girgiza masa kai tayi tana faɗin "Daddy this teddy is it not my own?" Tayi maganar sai da dimple nata irin na shi ta lotsa sosai, ta kai karshen maganar tare da ɗago masa teddy'n dake hannun ta tana nuna masa, yana kokarin yin magana Jehan ta sauko da gudu tana faɗin "I'm I playing with you? I'm I your mate?" A lokacin Jehan tana da 12 years, tana sanye cikin uniform riga me dogon hannu light blue se doguwar riga a saman ta dark blue mai hannu a kafada rigar ta tsaya a dai dai gwiwar ta se wandon uniform dark blue ƙafar ta sanye da Black socks ba takalmi a ƙafarta da gudu tayo kan daddy tana kokarin fisgo Rimsha, ihu Rimsha ta fasa tare da kanka me daddy tana faɗin "Daddy save me" fararen hannun sa yasa ya riƙo hannun Jehan yana faɗin "Haba Jehan yau fa Graduation ɗin My siha mai kuma ya haɗa ku faɗa a kan teddy kullun baku da aiki sai faɗa kan teddy ba kalan teddy da ban sawo na kawo gidan nan ba ni narasa meke damun ku" bai kai ga rufe baki ba mum ta miƙe ta amshe teddy tana faɗin "This teddy is for Rimsha whare is your own Jehan?" Turo baki Jehan tayi tana faɗin "Mum This is mine, is not for Rimsha" kallon mum daddy yayi san nan yace "bongel ɗauko min sauran kayan su yau ba ma zamu yi breakfast ba haka zamu wuce dan munyi latti, sayi breakfast ɗin a school ɗin na su ko idan mun dawo" ya kai karshen maganar tare da ruƙo hannun Rimsha ɗaya na Jehan ɗaya suka zauna saman sofa mai zaman mutun 3 yana kallon face na Rimsha, har cikin ransa yake bala'i son yaran nan nashi gashi Jehan ita ce mai kama da shi sai dai bata da dimple irin nashi ita kuma Rimsha da mum take kama sai kuma ta ɗauko dimple ɗin dad wushiryan mum, miƙewa mum tayi ta haye sama sauri sauri dan ɗauko musu sauran kayansu

Kallon daddy Rimsha tayi cikin harshen shuwa arab tace "Daddy ni zanzo first class In Sha Allah" murmushi daddy yayi ya sanya hannu yana tara mata curly hair ta da baya kitsuwa idan a ka mata kitso sai ya warware ga gashin nata da tsowo sosai a nannaɗe kamar indomie duk da naɗuwar sa kuma bai hana tsowon gashin nata bayyana ba dan a nannaɗen ma ya kai mata har tsakiyan baya "In Sha Allah my siha ke zaki zama first class" ya kai karshen maganar tare da ɗaure mata gashin nata da kyar dan sai ya kamo sai su zame shi yasa ma bata cika ɗaurewa ba dan ko ta sanya rebon fita yake shima daddy yanzu kulle mata yayi kamar igiya da gashin ya kullu, ita dai Jehan ko a jikin ta hankalin ta na kan Tv,

a tare mum da gwaggo suka sauko hannun mum riƙe da Abayar Rimsha Black colour da Hijab fari da takalmin ta da Black socks ita kuma Gwaggo na shirye cikin Abaya fari tas ta yafa gyalen abayar a kan ta idon ta sanye da glass ɗan siriri mai matukar kyau da tsada, hannun ta rike da Hijab ɗin Jehan light blue Dan Karami kalar T-shirt ɗin uniform ɗin, mum ta shirya Rimsha Gwaggo ta shirya Jehan

bayan mum ta gama shirya Rimsha ne ta ɗago ta kalli daddy tace "Yanzu Barkama da gaske kake ba zan biku ba?" Dogon hancin ta yaja yana faɗin "Duk abun da zai faru a School ɗin daga farkon har karshen zaki gani ki kunna TV kuma in muka dawo nayi alkawari zan biya" hararar wasa ta masa tana musu addu'a, riƙo hannun Rimsha yayi gwaggo kuma ta rinƙo hannun Jehan suka nufi hanyar fita daga palon "eyeeee My siha yau ba zuwa da jaka kenan" mum tafaɗa tana dariya, dariya ita ma Rimsha tayi kafin tace "Mum yau hutu za'ayi ai" komawa mum tayi ta zauna saman sofa tana faɗin "Allah ya bada Sa'a kuzo min da first class" a tare gwaggo da daddy suka amsa da Amin dai dai lokacin suka fice daga palon suka nufi parking space na gidan, da gudu wani ɗan sanda ya nufo su ya buɗe wa daddy da gwaggo kofar motar daddy kirar Roll-Royce boat Tail a tare suka shiga gidan baya daddy ya ɗaura Rimsha saman cinyar sa ita ma gwaggo ta ɗaura Jehan saman cinyar ta, ɗan sandan ya shiga ya tada motar yaja suka nufi gate, tun basu kariso wajen gate ɗin ba iliya mai gadi ya wangale musu tampatsetsen gate ɗin cikin kwarewa da iya tuki ɗan sandan nan ya danna hancin motar waje suka miƙi titi,

Cikin kankanin lokaci suka isa bakin katafaren gate ɗin Great Heights Academy horn ɗaya ɗan sanda yayi mai gadin ya wangale musu gate ɗin, ɗan sandan ya kutsa motar sa cikin school ɗin.

Makarantar cike take makil da jama'a ga manya manya baki da manya manyan yan siyasa da sarakuna sunzo taya yaran su murna masu kammala primary da jss 3 da ss 3 Rimsha na cikin wayan da za su kammala primary 6 na su tana cikin wayan da suka zana common entrance while Jehan na jss 2 yanzu, sai murna Rimsha take ita ma zata shiga secondary zata kamo Jehan.

Ɗan sanda na parking a parking space na school ɗin ya fito ya buɗewa daddy da gwaggo suka fito nan take manya manyan alhazawan dake tsaye a wajen suna jiran fitowar daddy suka kariso cikin murna da fara'a suka fara bashi hannu a kan su gaisa, kasan cewar shine babban bako a wajen hakan yasa director makarantar da sauran malamai suka kariso wajen da sauri dan tarban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login