Showing 57001 words to 60000 words out of 194715 words
picture on my phone" tayi maganar cikin sanyin murya, buɗar bakin daddy sai cewa yayi "kinga kayan da Rimsha ta ɗauka?" Girgiza masa kai tayi alamar a'a tana faɗin "No daddy am busy looking for the picture, my mind wasn't there" jinjina kai daddy yayi kafin yace "okay take a look at that outfit there" yayi maganar yana nuna mata irin rigar Rimsha dake rataye a matsayin sample, zumbur Jehan ta miƙe tana murmushi wanda ya kara fito da kyan ta, "Yeah daddy it's, it looks more beautiful in reality" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi wajen rigar, sosai ta kurawa rigar ido tana kare masa kallo kafin ta juyo tace "Daddy what about the rest of the stuff?" Tayi maganar tana zuba masa dara daran Idon ta "zasu yi maki irin kayan da Rimsha ta zaba ai" Cewar daddy ya kai karshen maganar tare da juyowa ya kalli ɗaya daga cikin ma'aikatan yace "Get her what to write what she wants for you to write for her" ya ƙai karshen maganar yana nuna mata gefen sa akan tazo ta zauna, ba musu ta dawo ta zauna kusa da shi, ma'aikacin ya kawo mata, ita ma tayi nata rubutun tagama ta miƙa masa
Miƙa wa daddy yayi tare da riƙo hannun su yana faɗin "muje mu karasa shopping ɗin kafin suyi packaging ɗin, it's getting late now" miƙewa sukayi suka nufi kofar fita, juyo wa daddy yayi yace "package everything in less than 30 minutes we'll be back in a while" Ya kai ƙarshen maganar tare da fice wa ɗan sandan sa ya rufa masu baya, tun kafin su fice ma'aikatan suka amsa da "Alright Sir" Jiki na rawa suka fara haɗa masu kayan suka yi packaging suka saka a leda suka yi bill ɗin.
A bangaren su Rimsha kuwa direct cikin mall suka nufa suka sassayi kayan da zasu kai na party, ko mai kayan ciye ciye na students, abubuwa sosai suka saya kama daga Capri-son, Happy hour, Munchit, Cocopops sweets kala kala komai seda suka saya daga ƙarshe suka sayi leader ɗin party park, Jehan ta ɗauki na Barbie Rimsha ta ɗauki ta Sofia, the first suna fitowa dara daran idon Rimsha ya sauka akan Ice cream cikin zumuɗi tace "Daddy i want this Ice cream" tayi maganar tana nuna masa Ice cream ɗin "No my Siha sanyi yayi yawa" marairaice masa face tayi kamar zata yi kuka, cikin sauri yace "A'a My Rimsha me abun kuka kuma ɗauki dole ma ai na sai miki kefa Jehan zaki sha?" Turo baki Jehan tayi tana faɗin "Ni Smoothie nake so" jinjina kai daddy yayi Rimsha ta ɗauki ice cream ɗin daddy ya biya suka fice daga wajen
suka koma Boutique aka yi masu Bill na kayan da suka ɗauka, daddy ya bada ATM nashi, suka ansa suka sanya a POS na su san nan suka miƙo masa POS ɗin dan ya saka pin nashi, a tare Jehan da Rimsha kowa ya miƙa hannu suna rige rigen wai su zasu saka kowa yaƙi bari ɗaya yasa, mamaki ne ya kama daddy, a mall da zai biya kuɗin ice cream shi ya sanya pin da hannun sa basu damu ba sai a nan ne zasu ce su zasu sa.
Da dai daddy ya ga basu da niyar bari ɗaya yasa pin ɗin sai ya ansa ya sanya pin ɗin ya raba gardama.
Ɗan sandan su na tsaye yana riƙe da kayan da suka sayo a mall ɗin, zai ɗauki kayan Boutique ɗin ɗaya daga cikin ma'aikatan yayi saurin ɗauka yace "Its my duty lemme take it to the car" haka akayi ya kai masu kaya har mota daddy ya ciro rapper na 500 ya bashi godiya ya rinƙa zubawa har suka bar wajen ya juya ya koma bakin aikin sa.
Ko da suka koma gida su mum na palour suna jiran su. Daddy da Rimsha ne kawai suka yi sallama, Jehan kuwa cinyar Gwaggo ta haye ta fin cike Hijab ɗin kanta tana faɗin "My Goggo am tired am hungry" shafa kanta Gwaggo tayi tace "sorry let's go and have dinner daman ku muke jira" ta ƙai karshen maganar tana kama hannun ta suka nufi dining. Ita kuwa Rimsha gun Mum ta nufa ta zauna a gefen ta ta kwantar da kanta a kafadar ta "let's go and have dinner" mum ta faɗi tare da kama hannun Rimsha takai ta kan dining gun su Gwaggo ta dawo wajen daddy ta masa Sannu da zuwa tace suje su ci abinci tun da yayi wanka kafin su fita in yaci abinci se yayi wankan kwanciya. Jinjina kai yayi san nan suka wace dining ɗin suka fara cin abinci.
After some hours.
RIMSHA & JEHAN
Zaune suke a Palon sama Kowa Cikin kayan bacci.
Sun baza tulin kayan da suka sayo suna aikin sassakawa a leda, se kusan 11 pm Suka kammala sannan kowa ya nufi makwacin sa kamar yadda suka saba sai murna da farinciki suke.
*PRIZE-GIVING* DAY
A yau ne ranar ƙarshe da zasu makaranta zasu yi hutu sunyi shirin su kaman amare komai irin daya Gwaggo ta daura masu ɗankwali kaman gwaggoro suna sanye da danƙara danƙaran gold kaman larabawa, sun fito sun yi kyau over. Daddy na sanye Cikin danƙareriyar getzener ɗinkin babbar riga Fara kal anyi mata Aiki na Manyan Mutane da Blue ɗin zare ya saka Hula ita ma blue takalmi ma blue se kamshi yake zubawa kaman sabon ango.
Bayan sun yi breakfast se wurin 9:30am suka bar gida kasan cewar 10:00am ne partyn Rimsha ta matsa su tafi shiyasa suka tafi da wuri.
Tun daga bakin gate ɗin an tsara komai anyi adon da ballons kalar uniform ɗin makarantar, a cikin Hall ɗin makarantar za'a yi partyn kowa yayi shiga ta alfarma.
Daddy a motor sa ya tsaya yace da ɗan sandan ya rakasu ajujuwan su ya kai masu kayan su, haka akayi tun daga nesa da ajin su ƴan ajin su Rimsha suka rinƙa mata kirari "Our first lady is now our Princess" aji ta shige suka fara gaisuwar rungume rungume juna da students yadda suka saba, Aunty ta fito ta amsa kayan da ɗan sandan ya biyo Rimsha dasu.
Jehan kam tuni ta wuce zuwa class ɗin su tace ma ɗan sandan ya fara kaima Rimsha se ya kawo mata na ta kayan, bayan Aunty ta amsa kayan Rimsha sai ɗan sanda ya nufi ajin su Jehan ya kai mata nata kayan, san nan ya dawo parking space wajen daddy ya tsaya a gefen motor.
10pm
Dukkanin ɗalibai da malamai duk sun hallara a Babban Hall ɗin makarantar wasu parents ma duk sun shigo Jehan da Rimsha se zuba ido suke suga shigowar daddyn su bama su kaɗai ba kowa jira yake yaga shigowar Nawazuddeen amma shiru bai shigoba.
Sai 10:30am ya shigo yana tafiya ta ƙasaita irin na manyan mutane kana ganin shi ko baka san wanene ba zaka san ba ƙaramin mutum bane. Malamai ne cike harda me makarantar duk suka miƙe don girmama shi, ɗalibai ganin Malaman su sun miƙe yasa suma suka miƙe sauran parents ma haka, shi mai makarantar ne ya zo ya taro daddy ya miƙa masa hannu sukai musabaha. San nan ya masa jagoranci zuwa inda aka tanada domin shi, kafin ya zauna ya buƙaci a bashi mike zeyi magana, jiki na rawa MC ya bashi aka kashe kiɗan dake tashi saman sama, Cikin natsuwa da wannan zazzakar voice nashi yayi Sallama dinbin al'umma dake wajen suka amsa masa sannan ya buɗe musu taro da addu'a da turancin, daga ƙarshe ya musu godiya ga karrama shin da suka yi sannan ya buƙaci kowa ya zauna kamin shi ma ya zauna. Duk abinda ke faruwa akan Idon mummy da Gwaggo ne da sauran dubban al'umma waɗan da suka kalla live a TV ciki harda abokan takarar daddy.
Mai makarantar ne ya amsa mike ɗin cikin girmamawa yace "ku tafa masa" gaba ɗaya Hall ɗin ya dauki tafi raf, raf, raf, na kusan tsawon minti biyu,
san nan mai makarantar ya yi Godiya ya gabatar da speech akan makarantar ya gabatar da Malaman makaranta gaba ɗaya sannan daga bisani ya nemi daddy da ya bama students gifts nasu da award nasu. Amsa masa daddy ya yi.
makarantar ya fara kiran students ɗaya bayan ɗaya suna zuwa amsar gift nasu da award nasu, da aka zo kan Rimsha Ita kaɗai Awards Guda huɗu taci Best in Islamic Studies, best in English, Best in Mathematics, se best in home economics. Sannan aka bata wani medal na The person with the Highest points. Daddy sabida murna seda ya mata hawaye a cikin bainar Jama'a, ta ƙara so gabansa ta share masa hawaye tace "Daddy In Sha Allah we'll keep making you proud" murmushi yayi yana kokarin tsaida hawayen sa, Jehan ta ƙara so wajen cikin harshen turanci tace "Daddy please stop crying" ta faɗi kaman zata yi kuka murmushi shi ne ya kubce masa ya haɗe su gaba ɗaya ya rungume yace "Am proud of you my daughters Allah ya yi wa rayuwar ku Albarka" gaba ɗaya Hall ɗin suka amsa da Amin Amin, shi bema san yayi maganar da ƙarfi ba har suka ji.
Miƙewa yayi ya ciro check a aljihunsa wanda already ya rubuta tun a gida ya miƙama me makarantar yace "gashinan Sadaƙatul Jariya school fees ne na Mutane 500 complet har su gama makarantar nan, ku sanar da marasa ƙarfi da suke son ƴaƴan su suyi karatu basu da halin biya musu gashinan na biya" "Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar" Hall ɗin ya dau Kabbara, Mutuwar tsaya da ta zaune manya manyan masu kuɗi da sukazo taron domin ƴaƴan su suka yi, sun sha ruwan mamaki irin kyautan da daddy yake, baya jin kyashi ko kaɗan, shi kuwa daddy bai jira cewar kowa ba yace su Rimsha su ɗauki stuffs ɗin su su wuce gida, haka kuwa a kayi suka ɗauka suka nufi mota sai sauri daddy yake dan bai son jama'a su tsaida shi suce zasu yi hoto.
Yana zuwa parking space ɗan sandan sa ya buɗe kusu mota suka shiga, da sauri ɗan sandan yaja motar suka bar school ɗin.
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai
💞Star Lady💞
*💞 TRIPLET'S💞
https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo
*💞The beginning💞*
*Episode 14*
*KADUNA*
*Unguwar sarki*
Hajiya Umaiya na sume a tsaye, shi kuma Abba yana sume a kwance har sai da Lami ta dawo daga kasuwa, ta isko su a sume, ihu ta fasa tayi kan Hajiya tana kiran sunan ta, tana taɓa Hajiya, Hajiya ta zube kasa wanwar, kara tsorata Lami tayi ta nufi fridge ta ɗauko ruwa jikin ta sai kerma yake ta buɗe ruwan, tsabar kiɗimewa da tayi bata san lokacin da ta juyewa Hajiya ruwan gaba ɗaya a kan taba, Ihu Hajiya ta fasa mai razaba kwakwalwa tare da miƙewa zaune tana zazzare ido kamar an tare ɓera a tarko, waige waige ta fara yi kamar mai neman wani abun, can idon ta ya sauka kan Abba dake sume cikin tsoro tace "Ke Lami me yasami Alhaji? Yaushe ya dawo?" Kara zaro ido waje Lami tayi murya na rawa tace "Nima a nan na dawo na same ku kuna sume" kara waro ido waje Hajiya tayi, tayi shiru tana kokarin tunano me ya faru, amma ta kasa tuna komai, jiki ba kwari ta yunkura tana son miƙewa, sai ji tayi gaba ɗaya jikin ta ya mata nauyi sosai, dafe kan ta dake sara mata kamar zai fashe tayi da kyar ta iya miƙewa tana faɗin "Kawo min ruwa" da sauri Lami ta miƙe ta ɗauko wani ruwa a fridge ta dawo ta miƙewa Hajiya, ansan ruwan Hajiya tayi tare da duƙawa kusa da Abba ta tarfo ruwan a hannun ta ta shafa masa a face nashi, dogon numfashi yaja tare da saukewa a hankali, ya waro idon sa waje ya fara bin saman da kallo kafin ya sauko da idon sa kan face ɗin Hajiya, a hankali ya miƙe zaune yana kallon Hajiya "Alhaji yaushe ka dawo?" Hajiya ta tambaya tana zaro ido, shiru yayi yana bin ta da kallo, "Alhaji kayi magana mana"
da kyar ya iya motsa bakin sa yace "Hajiya yaushe na dawo? Ba ina Abuja ba?" tashin sense shiru Hajiya tayi tana kokarin tunano yaushe Alhaji ya dawo, amma ina ta kasa tuna komai, shima Alhaji shiru yayi yana kokarin tunano yaushe ya dawo bayan shi dai yasan yana Abuja wajen meeting to ya akayi ya dawo gida
Almost 30mins sunyi shiru suna tunani daga karshe suka hakura da kokarin tunano me ya faru da su, haka suka miƙe suka wuce sama ran su cike da tunani fal.
Hayewa saman gadon Abba Hajiya tayi ta kwanta ta dafe kan ta dake tsananin sara mata kamar zai fashe, shi kuma Abba yaja kafar sa a hankali da kyar da kyar ya shiga toilet dan yin wanka,
a ta kaice dai su Hajiya sun manta komai da ya faru sun manta da abun da ya faru da Hajiya Zainab.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*WASHINGTON DC*
*LOT 33*
*06:00am*
Sanye yake da short mai ɗan girma zuwa gwiwar sa sky blue kyakkyawar cinyoyin nan nasa a waje ga kyawawan gashi dark brown kwance a cinyar nasa daga sama har zuwa idon sahu na kafar sa, jikin sa na sanye da farar riga mara nauyi mai karamin hannu, kyau iya kyau Tiger na da shi kyakkyawan Bature ne sosai sai iskanci kala kala, ba kalan da bai iya ba rashin kutunci ne cike fal a kan sa,
A hankali yake takawa har ya haura sama gaba ɗaya, ya tura kofa ya shiga wani waje mai kama da ɗaki, sai dai gaba ɗaya wajen da glass a kayi shi, kasan wajen kuma kyakkyawar grass carpet ne a wajen launin kore, waje ne mai girman plot 1, an kawata wajen sosai ga luntsuma luntsumar kujerun hutawa san nan ga injunan motsa jiki kala kala a wajen, da gani kasan wajen training na su ne, ga in juna da mashuna kala kala masu kyau da tsadar gaske, wajen dai ba'a chewa komai sai dai masha Allah.
A hankali Michael ya kariso cikin wajen, kusa da wani mashin na motsa hannun ya tsaya, yayin da wani matashi ke kwance a wajen yana ɗaga wasu kana kana nan karafuna.
Kallon tsab Michael yayi wa matashin kafin yace "Good morning photo copy" Ajiye karafunan hannun sa guy ɗin yayi tare da miƙe wa zaune, subhanallah tsarki ya tabbata ga Ubangiji dayayi wayan nan halittu, guy nan kamannin sa ɗaya sak da Michael ba abun da ya raba su sai kwayar ido da gashin kai, Michael gashin kan sa dark brown ne, shi kuma guy nan gashin kan sa ya rina ta ya sanya mata color ta dawo light brown mai kama da golden, sai kuma kwayar ido Michael kwayar idon sa light brown ne shi kuma guy ɗin nan nashi idon light ash ne masu kyau, ban da ido da gashi komai nasu ɗaya ne.
Kallon tsab guy ɗin yayi wa Michael kafin yace "how are you doing this morning?" "I'm going well" ya faɗa tare da wucewa ya nufi wajen motsa kafa, har ya kai wajen sai kuma ya juyo yana faɗin "James yaushe Romeo zai dawo?" Komawa James yayi ya kwanta ya ci-gaba da ɗaga karfen da yake yana faɗin "I don't know maybe this week" shiru Michael yayi ba tare da ya sake magana ba, shima James shiru yayi ba tare da ya sake magana ba suka ci gaba da motsa jikin da suke.
07:00am dankareriyar gold watch dake ɗaure a hannun su tayi kara lokacin guda alamar awa ɗaya ta karu a kan lokaci, kallon juna suka yi, kusan a tare suka ajiye karafunan hannun su, kowa ya sanya hannu yana kokarin kashe karar watch ɗin, dankareriyar gold watch ne mai bala'i kyau da tsada iri ɗaya ba abun da ya raba watch ɗin, ko ina zasu je watch ɗin na hannun su basa rabuwa da shi sai dai in zasu yi barci ko zasu yi wanka shi ne suke cirewa,
Tsai da karar watch ɗin sukayi a tare, dai dai lokacin jibga jibgan Bodyguard na su guda huɗu suka shigo wajen hannun su ɗauke da plate masu ɗauke da cup na ruwan lemon wadda masu motsa jiki ya kamata su sha idan sun kammala motsa jikin nasu,
Rabuwa bodyguard ɗin suka yi, biyu suka nufi wajen Michael biyu kuma suka nufi James, cikin girmamawa suka miƙa musu plate ɗin, ba musu kowan nen su yasa hannu ya ɗauki cup ɗin suka kafa a ɗan karamin bakin su.
Cikin ƙan ƙanin lokaci suka shanye lemon ɗin tas, tare da mai da cups ɗin saman plate dake hannun bodyguard ɗin, daman ka idar motsa jikin kenan shan 1 cup na lemon idan an kammala.
Bayan bodyguard ɗin sun fice ne Michel ya kalli James yace "Photo copy zan je na shirya na wuce school yanzu" ba tare da James ya kalle sa ba yace "Ba za dai ka dai na ce min photo copy ba ko?" Miƙewa Michael yayi yana faɗin "To ai kai photo copy ne da gaske dama aikin sojan kawai kai ma ka shiga da ya fima yawon ban zan da kake ɗin nan kullun gaka wajen partyn abokai, ka gama school kana zaune" shiru James yayi ba tare da ya sake magana ba, sai mamaki yake wai Michael ne yake ce masa mai yawon banza to ba gwara shi