Showing 54001 words to 57000 words out of 194715 words
Shitu ba ɗan uwan mu bane kawai zumunci ne ya haɗa" ta kai karshen maganar tare da miƙe wa ta sauƙo kasa daga kan gadon ta nufi drawer san ya kayan ta, Rimsha na kwance tana kallon ta
Wata yar karamar akwati ta ɗauko ta dawo saman gadon tana kokarin buɗe wa Jehan ya shigo ɗakin tana faɗin "Ke Rimsha tun ɗazun nake neman ki, ki wuce kije ki shirya mu tafi Shopping daddy na jiran mu, san nan na gama mana list ɗin abubuwan da zamu saya" ta kai karshen maganar tare da zama gefen Gwaggo tana kwaɓe fuska
Buɗe ɗan akwatin gwaggo tayi ta ciro wasu abubuwan hannu guda biyu masu bala'i kyau, da alama na tarihine dan an yi su da kauri irin na da kuma da gani na azurfa ne, sai kallon abun Jehan da Rimsha suke ba karamin kyau abun ya musu ba, ajiye abun gwaggo tayi san nan ta fito da wasu neck chain sirara suma guda biyu sai kyalli suke da alama na gold ne, ajiye ɗaya tayi kusa da abubuwan hannu, ta buɗe ɗayar ta sanyawa Rimsha a wuya tana faɗin "Lokacin da nake yammata ne nake kwalliya da su" ta kai karshen maganar tare da ɗauko ɗayan ta sanyawa Jehan tana faɗin "Ko da yake har yanzu ni yanmata ne" murmushi Jehan tayi kafin tace "Gwaggo kece yan matan? Bayan kin girma zaki kai 50 years fa" gwaggo na kokarin magana Rimsha ta rigata da cewa "Ai kuwa gwaggo ba tsohuwa bace dan mum ta faɗa min gwaggo bata taɓa yin Aure ba kinga kuma wanda bai taɓa yin aure ba ai bazai tsufa ba" tsaki Jehan taja kafin tace "Ke dalla idan masu ido da kwalli suna magana ki dai na sako idon ki duk kwantsa dan mutun bai taɓa yin aure ba sai a ka ce miki ba zai tsufa ba gwaggo fa ta girmi daddy Auntyn daddy ce su biyu maman su ta haifa daga gwaggo sai daddy to daddy ma yanzu ya kai 40 to 45 years haka bare gwaggo, to bari kiji gwaggo kam ta tsufe ta yagalgale dan kawai tana gyara jikin tane badon haka ba da yanzu da sanda take tafiya" ta kai karshen maganar tare da jan tsaki ta miƙe zata fice daga ɗakin, hannun ta gwaggo ta riƙo ta sanya mata abun hannun ko a jikin ta bata damu ba dan in da sabo ta saba da iyashegen Jehan, ita dai Rimsha shiru tayi bata sake magana ba
Gwaggo na gama sa musu abun hannun suka miƙe har suna rige rigen fita gwaggo nace musu "karfa ku cire abun hannun nan da sarkan dukka, ku barshi a jikin ku har ku haifi yara kuma ku basu dan nima wajen maman mu na gado" ina ai tun kan gwaggo ta faɗin word ɗaya ma sun yi waje basu ji me tace bama sun tafi shirin zuwa shopping.
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai
💞Star Lady💞
*💞 TRIPLET'S💞
*💞The beginning💞*
*Episode 13*
*KANO*
Da murna da farinciki su Irfan suka shigo office ɗin daddy, jin shigowar su yasa daddy saurin goge hawayen face nashi ya miƙe ya shiga toilet ɗin cikin bedroom ɗin, sauri sauri ya wanke face nashi ya ɗan gyara jikin sa ya fito, zaune ya same su saman kujerar da yake zama, Irfan na zaune saman kujerar, Imran na zaune saman visitor chair,
suna ganin daddy ya fito suka kara faɗaɗa murmushin su Imran na faɗin "Bappa bamu zo da wuri bako?" Kakalo murmushi dole daddy yayi wadda ake cewa tafi kuka ciwo, yana kokarin yin magana Irfan sarkin basira ya rigashi da cewa "Bappa me ya sameka meke damun ka?" Cikin sauri daddy yace "babu komai Just I'm feeling headache ne" cikin sauri Imran yace "Bappa muje hospital mana to" girgiza kai daddy yayi ya nufi hanyar fita yana faɗin "No muje gida kawai naji sauki" kallon Irfan Imran yayi, yayin da shima Irfan ɗin shi yake kallo, shiru sukayi sai da daddy ya fice san Imran yace "Irfan me ka fahimtar game da Bappa dan ni ina ganin kamar a koi wani damuwa bappa bai taɓa yimin haka ba ka duba fa ka gani yau office nashi muka zo amma ya fice ya barmu a ciki, ni da wani lokaci ma idan nazo garin nan wallahi saboda son da yake min ajiye aiki yake a ranar ya ɗau hutu dan muyi hira koda kuwa bai da lafiya baya taɓa kyaleni na zauna shiru amma yau har ya fita ya barmu a office na shi kai a koi matsala" jinjina kai Irfan yayi kafin yace "kayi gaskiya Imran duk da ban san halin bappa sosai ba amma tabbas yana cikin wata damuwar yanzu dai tashi muje, ma karasa maganar a gida" miƙewa Imran yayi ba tare da ya sake magana ba, shima Irfan ya miƙe suka gera suka fice waje, yau daddy ko system na shi bai ɗauka ba haka suka wuce gida.
AKIL
Tsaye yake a tsakiyar palon daddyn Jelly, sanye yake da wando jeans baki da riga fari tas ta ɗaura cardigan mai hula a saman kayan nasa, ya sako hulan a kan sa, tsaye yake yana fuskantar makekiyar Tv plasma dake manne a bango ya bawa bene baya, ya duƙar da kai kasa ya zura hannu a aljihun sa da alama wani abun yake jira.
Da sallama Akila Aafia da Umaisha suka sauƙo daga sama suka shigo palon, wucewa Akila tayi taje ta rungume sa ta baya cikin shagwaɓa take faɗin "I missed you yaya Akil" juyowa yayi ya rungumeta yana faɗin "Missed you too heartbeat" yayi maganar dai dai lokacin da idon sa ya sauƙa kan Umaisha da Aafia dake tsaye kusa da centre table, nan taƙe ya ɗaure fuska tare da sakin Akila cikin tsawa yace "Waya baki izinin fita? Ina kuma kuka je nazo gidan nan ɗazun baku nan?" Ba Umaisha kawai ba har Akila sai da ta tsorata da yadda yayi maganar, nan take Umaisha jikin ta ya fara ɓari dan tana da tsoro sosai kirjin ta ya fara dukan uku uku
tsawa ya kuma daka mata "Ke bada ke nake bane?" Murya na rawa tace "Kayi hakuri mun bi su yaya Imran ganin gari ne shine yanzu suka dawo damu suka wuce office ɗin daddy" "Zo nan!!" Ya faɗa yana kare mata kallo, cikin tsoro ta kariso gaban sa zata tsugunna ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata baya buƙata da hannun sa,
hannu yasa ya riƙo kunnan ta ya murɗe da ɗan karfi, cike da bada umarni ya fara magana "Daga yau sai yau idan kika kuskura kika sake fita ba tare da ni na baki izinin ba Allah ba zan yi kaffara ba daga ranar zaki dawo ɗaki na da zama kuma karki yi tunanin idan kin dawo ɗaki na ɗin daɗi zaki ji, no rufeki zan rinƙa yi ko palo ba zaki leƙa ba kin ji na gaya miki" hawaye Umaisha ta fara yi saboda murɗe mata kunne da yayi yana mata zafi sosai,
ganin tana hawaye ne yasa ya saki kunnen nata tare da ciro handkerchief daga aljihun sa ya goge mata hawayen yana faɗin "Idan kika sake bari hawayen ki suka zuba ranki zai ɓaci ban son ganin su in ma na farinciki ko na bakin ciki dukka bana son gani" shiru tayi ta sunkuyar kanta kasa ita kunyar sa ma take ji
tsawa ya daga mata "Ke ɗago ido ki kalle ni ban son munafurci sai kuyi ta wani sunkuyar da kai idan mutun na muku magana a waje amma da zarar anyi aure duk sai ku riƙiɗe ku zama tantiran yan iska masu lasisi sai ka rasa ina sunkuyar da kai lokacin da ba'a yi auren ba yake, sai ku watsar da komai ku ɗauko rayuwar dabanci da hauka to ni bana son munafurci komai na a fili nake dan haka na san komai game da halin mata karki fara min munafurcin kun nan tun yanzu, ki nunamin true color ki kawai a wuce wajen!!" ikon Allah ita dai Aafia zubawa Akil ido kawai tayi babu ko kyabtawa ita kuwa Akila in da sabo ta saba da halin sa,
cike da jin kunya Umaisha ta ɗago kai tana ɗan kallon sa kasa kasa "Ke nace ban son munafurci ko, ki kalli cikin ido na kawai tun yanzu yafi min a kan kiyi ta ɓoye fuska sai munyi aure kizo kina tsayamin a kai kina min wallahi tallahi kina kallo na cikin ido, shi abokina ma da yayi rashin Sa'a har ce masa ake idan ya isa yace tak al halin lokacin da yake neman auren ta tsabar kunya da biyayya irin nata itace Amyra a islamiyar su, amma daga yin auren su ta dawo rikakkiyar yar daban cikin gida to ni ban yarda da wan nan iskanci idan mace ta min abu dukan mutuwa zan mata" Allah Sarki Umaisha bai war Allah ko kala bata ce masa ba tayi shiru tana jin surfan da yake
"Zan wuce Kaduna yanzu ina son ki faɗa min me kike da buƙata" cikin sauri ta girgiza kai tana faɗin "Bana buƙatar komai" tayi maganar cikin sanyin murya, guntun tsaki yaja tare da sanya hannu ya ɗauko ledar da ya ajiye sama hannun sofa tun shigowar sa, ya miƙa mata yana faɗin "Na miki setting na komai na wayar karki kuskura naga number wani a wayar nan naki idan ba na family ki ba, san nan zan kara ja miki kunne a kan maganar fita ko nan da kofar gida ban yarda ki taka ba, bayan haka ban yarda ki rinƙa yawan magana ba kina hira da mutane ban yarda da wan nan ba banso" ya kai karshen maganar tare da ciro wrafer sabbin ɗari biyar biyar daga aljihun wandon sa wadda a kalla zasu kai 50k ya miƙa mata yana faɗin "Ki sai kati idan na cikin wayar ta kare san nan zan sa azo a ɗauke ki aje a buɗe miki Account dan nasan baki da shi" girgiza kai tayi cikin sanyin Murya tace "A'a yaya Akil ka bar kuɗin ka nagode wayar ta isa" a fusace ya ɗaga hannu zai wanka mata mari Akila tayi saurin riƙe hannun sa tana faɗin "Ansa kuɗin Umaisha ki tafi ɗaki idan kinje ki tashi Jelly daga barcin ya isa haka yamma yayi sosai" jiki na kerma Umaisha ta ansa kuɗin da gudu ta haura sama Aafia tabi bayan ta.
Kallon face ɗin Akila yayi cike da so da kauna yace "Heartbeat me yasa kika riƙeni?" Murmushi ta saki tana faɗin "Yaya Akil bakaga yarinya bace? Kamar ni fa take shi is 15 years fa, yanzu zaka iya dukana?" Girgiza mata kai yayi alamar a'a kafin yasa hannu yana shafar kan ta a hankali yace "Heartbeat ai ba wanda ya isa ya taɓa ki a kasar nan ya kwana lafiya babu shi wallahi" faɗawa tayi saman kirjin sa tana dariya tana faɗin "that's why I love you my lovely brother" duƙo da kan sa yayi ya manna mata kiss a goshi ta tare da raba jikin su ya nufi hanyar fita yana faɗin "Sai kun dawo ni na wuce Kd ki kula min da kan ki san nan ki faɗa wa yarinyar nan karta kuskura na sake bata abu taki ansa, zan iya karyata a kan hakan kin san bana son hakan" kafin Akila tayi wata magana ma ya fice daga palo, bin sa kawai tayi da ido tana mamakin irin halin sa.
Akil yana kutsa motar sa waje gate ɗin, su kuma su daddy suna kutso motar su cikin gida, ko kallon in da su daddy suke bai yi ba yaja motar sa ya bar layin gaba ɗaya ya miƙi hanyar airport.
Daddy kuwa yana kashe motar sa a parking space ya fito ya nufi cikin gida, kai tsaye bedroom nashi ya wuce ya rufo kofar ya sanya key,
Ko da su Irfan suka shigo palon, babu kowa shiru palon ganin haka sai suka kara sanin ba lafiya ba dan haka sai suka wuce masaukin su dan suje suyi wanka anjima suzo su tambayi daddy ko zai faɗa musu meke damun sa.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*ABUJA*
Shiryawa sukayi Rimsha cikin Abaya doguwar riga blue color, kayan sun ansa jikin ta, kyanta ya kara bayyana, da kyar mum ta iya ɗaure mata dark black curly hair tan nan saboda tsantsin gashin, tayi light make up a face nata, kamar ka sace ta ka gudu saboda kyau da tayi, ga dara daran fararen sleeping eyes nata nan sun sha kwalli sai kyan su ya kara bayyana sai ɗaukan hankali suke, su gwaggo dukkan su sai da suka yi magana a kan kyan idon Rimsha, idon nata a koi ɗaukan hankali da kyau sosai, idan ka kalleta in the first place zaka yi tunanin barci take ji koda kuwa daga barci ta taso sabo idon nata kamar zata lumshe su haka suke, gasu dara dara fafare tas kamar auduga kwayar idon nata kuma dark brown ne mai ɗaukan hankali gwanin ban sha'awa, sai faman lumshe su take tana buɗe wa, mum na fama da ɗaure mata kai.
Ita kuma Jehan sanye take da wandon jeans Ash color da top fari tas, ta tara gashin kanta tayi parking har baya, Mum na ce mata ta sanya hijabi sai faman turo baki take tace "mummy I told you I don't like hijab" shiru mum tayi bata sake magana ba dan tasan daddy ba zai ɗauke ta haka nan ba hijabi su fita ba
Tsab suka kammala shirin su ita dai Rimsha ta sanya mayafin rigar ta a kan ta, sun yi kyau over musamman Rimsha dake da wata iriyar jiki wadda ko wani kaya ta sanya sai ya zauna a jikin ta kamar dan ita a ka yi shi sai ya lafe yabi shape ɗin coca colar ta ya lafe kamar dan ita a kayi su, koda kuwa kayan Jehan tasa sai yabi shape ɗin coca colar ta ya zauna dai dai kamar nata ne while Jehan kuma tafita ƙiba kaɗan
Zaune a palo suka isko daddy yana jiran su, da sauri Rimsha ta tafi ta rungume sa tare da manna masa kiss a kumatu tana faɗin "Sorry dad for keeping you waiting" manna mata kiss shima tayi a goshi yana faɗin "No don't worry about that, have you done?" Gyaɗa masa kai tayi alamar eh sun gama, ɗago kai yayi ya kalli Jehan dake tsaye tana latse latsen wayar ta, "Where is your hijab Jehan?" Daddy ya tambaya yana kokarin miƙewa, turo baki tayi kamar biro cikin shagwaɓa tace "Allah daddy i don't like the hijab at all" kallon Rimsha yayi kafin yace "Kawo min Hijabin ta" da sauri Rimsha ta wuce ta nufi sama,
Jim kaɗan ta dawo hannun ta ɗauke da Malaysian hijab mai kyau fari tas yasha kwalliya da stone masu kyalli, ansa daddy yayi da kan sa ya sanya mata hijabin san nan ya riƙo hannun su suka fice mum na ta musu addu'ar dawowa lafiya da Allah ya tsare hanya
Sai faman kwaɓe fuska Jehan take haka suka wuce parking space, da sauri ɗan sandan dake tuƙa daddy yazo ya buɗe musu kofar motar suka shiga gidan baya, daddy ya zauna a tsakiyar su,
Ba tare da ɓata lokaci ba ɗan sandan ya shiga mazaunin driver yayiwa motar key suka bar gidan.
Direct *Jabi Lake Mall* suka nufa a parking space ɗan sandan yayi parking ya fito ya buɗe masu motor, suka fito suka nufi cikin Mall ɗin suka shiga suka wuce Boutique (wajen sayar da kayan sawa)
Rimsha ta gwada wan nan ta cire wan nan, ta gwada kaya yafi a ƙirga duk wanda tasa se tayi complain a kan bai mata ba.
Se daga baya tayi final choice akan wata wedding dress (kayan Amare) doguwar riga ce fara kal me high neck ga ƙasan ta ya buɗe sosai yana jan ƙasa daga saman kuma fitted da dogon hannu ne Amman net ne hannun, rigar ta zaɓa tare da ɗauko high heel black color sai crown sima black color, Sai ɗankwali wanda zata daura shi ma black.
Wani ma'aika ci ne ya nufa Rimsha da irin abun da Amare ke sawa wanda ake rubuta Bride To Be, cikin natsuwa ya fara magana "Me zan rubuta maki anan" yayi maganar cikin harshen turanci yana nuna mata abun, da murmushi ɗauke a face nata tace abata inda zata rubuta.
shi dai daddy ya zuba mata ido duk matsin ta akan idonsa, Jehan kuma kamar ba ta a wajen tayi shiru hankalin ta na a kan wayar ta tana latsawa,
Miƙa mata Memo aka yi da pen, ta ansa tayi rubutu ta miƙa masa, 5mins ya dawo da abun black anyi rubuta da farin zare an rubuta ta gaban * Happy graduation First lady Rimsha* ta baya kuma aka rubuta *Finally done with primary school*. Amsa tayi ta nufi daddy tace "look daddy how does it look?" Tayi maganar tana miƙa masa,
zaunar da ita yayi a saman cinyar sa sannan ya amsa abun cike da so da kauna yace "It looks beautiful" murmushi tayi tana kwantawa a ƙirjin sa karaf dara daran sleeping eyes nata suka sauka akan Jehan dake zaune tana latsa waya kaman ba ita a gurin "Jehan aren't you buying the clothe" Rimsha ta faɗi cikin kulawa tayi maganar tare miƙewa daga cinyar daddy ta nufi Jehan ɗin ta zauna a gefen ta, tana kallon face nata
Miƙa wa shima daddy yayi ya nufo su yana faɗin "My Jehan what's wrong bazaki sayi kayan bane?" Ya faɗi cike da kulawa yana ƙaraso wa wajen nasu, tsaki tayi tace "Daddy kayan da nake son saya I can't find the