Showing 15001 words to 18000 words out of 194715 words
ji mai rikita ƙwaƙwalwa yace "Kai Santilago ka kwashe su ka kai su ɗaki daban daban zuwa gobe da safe idan gimbiya ta fito sai muji me zata ce" Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya nufi hanyar komawa cikin gidan yana taku ƙasa na bada dum dum har ya shige ta wata ƙatuwar kofa mai ɗauke da tambarin wata mata tsaye ba kaya a jikin ta, ga malalen jini nan kwance cikin idon matar ga idon nata sun yi ja bakin nonon ta duk jini ke zuba aka zana ta,
shi kuma Santilago ya sanya hannu ya ɗauko Rimsha dake sume da hannu ɗaya ya ɗauko ɗaya daga cikin yaran ma da hannu ɗaya ya saɓa su a kafaɗar sa san nan ya ɗauko saura biyun yariko kafofin su kan su na lilo na kallon ƙasa haka ya wuce da su ta wata faffaɗar hanya dake ɗan gefe da kofar da Barbushi yabi yana tafiya kasa na amsawa nan ya rinƙa wuce ɗakuna masu burglaries kamar gidan fursina ba abun da ke tashi daga ɗaku nan face bala'i warin jini wani ɗakin kuma kaga akoi yara a ciki wani kuma sai dai kaga kashi ko wani sassa na jikin mutane, dai dai wata katafaren gate dake wajen ya tsaya, da gudu wani mutun wadda da ka gan shi kasan cikakken bil adama ne, yazo da gudu ya ɓuɗewa Santilago gate ya wuce da su Rimsha ciki, yana shiga wasu kantin mutane kusan kamar sa suka rufa masa baya su uku, ko wacce ɗaki daban ya kai ta Rimsha itace ta karshe suka kai ta wata ɗaki dake karshen ginin suna kokarin buɗe kofar ta farfaɗo daga doguwar sumar da ta faɗa kafin tayi wani yun kurin Santilago yayi wurgi da ita cikin ɗakin suka jawo kofar dafaffiyar karfe mai karfin gaske suka kulle suka sa key suka juya suka bar waje.
Ɗaki ne mai matikar duhu baka iya ganin komai a ciki ko yatsun hannun ki baki iya gani, ga bala'i wari jini mai sa tashin hankali da tashin zuciya dake fitowa daga cikin ɗakin.
Da kyar ta iya miƙewa zaune jiri na ɗibar ta sabida bala'i yinwa da take ji a sukwane ta toshe hanci lokacin da ta fara dawowa hayyacin ta waro dara daran fararen idon ta waje tayi ko zata samu daman ganin wani abu sai gwale idon take tana bin ɗakin da kallo tana toshe da hanci da hannu ɗaya ko tsillin tsinke idon ta ya kasa iya gane mata a ɗakin saboda tsananin duhu, motsin ta fara ji daga ɗan nesa da ita, a sukwane ta takure jikin ta waje guda saboda tsoro ta runtse dara daran idon ta tana ambaton sunan Allah ji tayi an ɗan taɓa ta a bayan ta hankali tashe ta yi saurin waro idon ta waje tare da juyawa a sukwane tana faɗin "wanene? akoi wani a nan ne?" ji tayi an kwashe da wata mahaukaciyar dariya da wata murya mara daɗin ji kamar na aljanu,
daga ɗan gefe kuwa wata iriyar siririn murya mai kama dana baby's taji ana kuka da shessheka kasa kasa, a razane tamike tsaye tana ja da baya tana faɗin "Dan girman Allah idan akoi mutane a ɗakin nan kumin magan kar ku haukatani ku dai na kukan nan mu rungumi Allah, Allah zaiji kukan mu zai kawo mana ɗauki" tayi maganar cikin harshen turanci ihu aka kurma da wata katuwar voice irin na yan shaye shaye, a sukwane ta toshe kunnuwan ta da hannayen ta dan ihun mai rikita ƙwaƙwalwa ne ba zata iya ji ba kan ta zai fashe nan take ta fara hawayen tsoro.
kamar daga sama taji an cire hannayen nata daga kunnuwan ta ana mata kukan mage a kunne, ihu ta fasa tare da bazama cikin duhun kamar mahaukaciya.
muryoyi uku uku ne suka fara fita lokaci guda ɗaya na dariya ɗaya na kuka ɗaya na wani irin abu kamar wakar shaiɗanu aljanu daga gefe guda kuwa kukan mage ne mai sautin gaske ke tashi, idan ta toshe kunne sai a buɗe mata idan tayi ihu suma abubuwan su kara sautin nasu ihun idan ta zauna shiru taji ana taɓata ga ɗakin duhu baka ganin komai.
Hawaye ta fara yi sosai wani na bin wani tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta daga ciki har da addu'ar san ya sabon kaya wato
اَلحَمدُ لِلهِ الَّذِي كَسَانِي هَذَ (الثَّوْبَ) وَرَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَولٍ مِنِّي وَ لَا قُوَّةٍ
Haka ta rinka gero Addua'o'i sai ta kama wan nan bata kai karshen ba ta sake ta kama wani ga hawaye wani na bin wani a kuncin ta ga bala'i yinwa da take ji lokaci guda ta fita hayyacin ta ta zama kamar zautatciya, tun tana iya jero addua'o'i har ta fara jin duniya na juya mata harshen ta yayi mata nauyi saboda yinwa a hankali ta sulale kasa warga jam ta baje bata ko motsi, tana faɗuwa suma abubun sukayi shiru tsit kamar babu su a ɗakin.
Aafia
Zaune take saman kujerar table dake cikin E,library dake cikin Greenfield university kaduna tayi shiru, kan ta na kan wani book da take karan tawa ga wayar ta da key motar ta a gefen ta jakar ta kuma yana ɗayan gefen nata, cikin takun ƙasaita wasu haɗaɗun yanmata su uku suka shigo cikin Library'n dukkan nin su suna sanye cikin wandon jeans da t-shirt sun zubo gashin dokin nan har baya kamar nasu, kai tsaye wajen Aafia suka nufa suka zauzzauna saman sauran kujerun dake table ɗin da Aafia ke zaune kallon su ta kasan ido Aafia tayi kafin ta ɗago kai tare da cire katon glass ɗin dake face nata tana faɗin "Yan mata ya kuke?" Ɗaya daga cikin sune tace "Yar Alaji ko in ce hajiya da kan ta tun ɗazun muke neman ki bamu gan ki ba can muka haɗu da Umaisha wajen Masallaci shi ne take faɗa mana kina nan" guntun tsaki Aafia taja kafin tace "Ku dai bari ina da Exam on Wednesday ne that's why nake karantun" ɗaya daga cikin sune tace "Ke dalla Rufee ba wan nan ba mu yanzu Afi baby ki faɗa mana ya kika yi da wan nan shegiyar kwailar Amaryan Abbin ku nan?" Turɓune fuska Aafia tayi tana turo baki kamar biro tace "Rabu da shegiya wai ni zata wa iskan ci jiya har da wani zuwa bedroom na dan munafurci tana wani cemin wai mu haɗa kai mu zama abu guda mu zama friend hmm zata yi bayani ne Allah sai ta bar gidan nan because I don't like her at all I hate this woman over wallahi shi kuma Abbi har da wani cewa zai kawo wasu masu aiki dan yau na zuba mata gishiri a abinci Allah ba wata house girl da zan bari ta zauna a gida duk wadda aka kawo sai na san yadda zan yi na koreta ita Amaryan ita zata yi girki kuma mu rinƙa bata girkin duk wani aikin da tayi sai na ɓata a haka har Abbi ya gaji ya sake ta mu huta Allah ba wata mai aikin da zata sake zuwa gida tayi aiki ita zata rinƙa aiki dan daman gidan su ai ba bu house girl" ta kai karshen maganar tare da zan dogon tsaki bushewa da dariya Rufee Anisa Amal suka yi suna tafa hannu "Wallahi Aafia karki bata wani dama karki kuskura ki bari ta samu sake a gidan ku idan ba haka ba zata samu ciki ta haihu da Abbi kuma hakan babban abun kunya ne a gare ku a ce kamar Abbi mutun mai manya manyan companoni wadda ake ji da shi a kasar nan ya auri yar talakawa kuma har sun haihu tab kofa ina zaku je in faɗa miki sai an rinƙa dan ganta ku da yaron da zata haifa wani lokaci ma sai kiga ana kwatan cen ku da gidan su amaryan ba da gidan Abbi ba" cewar Rufaidat buga table da karfi Aafia tayi tare da miƙa wa tana faɗin "it can't happen Rufaidat dole Halima ta bar gidan mu ko tana so ko bata so" Amal na kokarin yin magana Umaisha ta shigo da gudu tana faɗin "Aunty Afi, today your famous had accepted the invitation and he spoke on the Tv _CNBC Tv 18 Robin Roberts_ for almost one minute" ta kai karshen maganar tana nunawa Aafia wayar ta dake hannun ta a sukwane Aafia ta ansa wayar tana faɗin "What are you saying Umaisha do you mean yau TGA yayi magana har tsawon minti ɗaya bai tsaya ba" tayi maganar tana zaro ido gyaɗa mata kai Umaisha tayi tana faɗin "Duba ki gani yanzu nima na kunna data na gani sai sharing na video mutane suke yau TGA ya amsa tambaya har tsawon 1min yana magana" waro ido waje Aafia tayi tana kallon video kyakkyawan baturen dake magana cikin kyakkyawar turanci yana sanye da facemark a face na shi "Wow" Aafia ta furta tare da mayar da video daga farko ta sake gani a sukwane Anisa da Rufaida suka mike suka dawo kusa da Aafia suna kallon video taɓe baki Amal tayi tana makakin yadda su Aafia ke mutuwar son wan nan mutumin da wata kila ma bai san da zaman su ba a duniya kullun basu da wani zance sai zancen sa, ganin Aafia bata da niyar dai na mai da video daga farko tana sake kallo ne yasa Amal tace "Wai Aafia ni kam wanene TGA nan ne kullun sai kin dame mu da zan cen sa" cikin sauri Anisa tace "A'a sai ta dame ki dai dan ni ina ga ba wan da ya kai ni son ganin TGA wallahi kome nake idan lokacin kallon News akan Tga yayi sai na bari nazo na kalla ina bala'i son kallon face na guy ɗin nan sai dai kullun idan yan jarida na ɗaukan sa zakiga hoton ko video yana sanye da facemark ban taɓa kallon real face na shi ba sai dai dara daran idon sa light ash masu ɗaukan hankali masu kama da glass dan in ya waro idon na shi ko ya ɗago su ya kalli abu sai kiga kamar glass yana walkiya suma fa idon na shi wani lokaci yana sanya bakin glass ya rufe su, kai amma guy nan lamba ɗaya ne ya haɗu ta ko ina ba abun da yafi burgeni da shi ma irin sai yan jarida sun tasa shi a gaba sun sanya masa camera suna tambayar sa sai sufi 20mins suna jero masa tambayoyi suna jiran jawabi sai ya tattara gaba ɗaya tambayoyin nasu ya basu amsa ɗaya da batafi maganar 5 second ba shi ma sai ya ja musu aji sai yafi 2 mins kafin su samu amsan duk wanda zai ce miki ga kalan voice na guy ɗin nan a Nigeria kai bama a Nigeria ba har kasashen waje to ya miki karya dan ko magana yake ciki ciki yake magana kuma ga face mark a face na shi maganar tasa bata fita sosai kuma ni ban taɓa ganin in da yayi magana na tsawon 1min ba idan ba yau ba yanzu haka ki shiga media kiga yadda jama'a zasu yi ta rushing na kallon video yau yayi magana har na tsawon minti ɗaya" taɓe baki Amal tayi tace "To wan nan kam a wani gari yake? Abuja ko? Kuma ɗan waye a kasan nan? Mawaki ne ko ɗan film? Ni fa tun da kuke wan nan hauka ban taɓa sanin akan waye ma kuke ba kuma ni ba mai kallon News bace ni ko kallon film ma bana yi bare wani News" ta kai karshen maganar tare da gyara zaman ta, girgiza kai Aafia tayi tare da komawa ta zauna tana faɗin "Amal ni zan baki wan nan amsan ni zan faɗa miƙi who is TGA kina jin labarin *The General of the Army* ko baki ji shi ma?" guntun tsaki Amal taja tana faɗin "To ni ina ruwana da army's nifa ba abun da na sani kawai ki bani labari idan zaki bani amma ni bani da wata masaniya game da army's" gyara zama Aafia tayi kafin ta fara magana "TGA The General of the Army kenan namijin da ni banga kamar sa ba a duniya cikkaken gwarzo jarumin maza kaifi ɗaya ne shi ba mai iya tankwara shi Bature ne ɗan ƙasar *UNITED STATE OF AMERICA* a babban birnin*WASHINGTON DC* babban sojane da babu kamar sa duk wani sojoji da kike gani a *Usa* to a karkashin sa suke bafa wani babba bane, bai da shekaru sosai, kawai baiwa ce daga Allah ya ba shi he is 28 years amma akoi shi da farin jini ga kuɗi mulki tarin masoya Allah ya bashi amma fa Kirista ne ba musulmi ba gashi da bala'i izza kafin yayi magana sai ya ɗau wasu mintoci ina ganin kamar shi kaɗai ne wajen mum da dad ɗin sa, dan ɗan gata ne sosai kafin manya manyan gidan Tv su samu damar yin hira da shi suna shan wahala, wan nan gidan Tv da sukayi hira da shi yau ɗin nan ma a ka ce miki sau biyar suna tura masa takardan gayyatar nan, da kyar suka samu yayi accepted na gayyatar ta su yanzu ki shiga media kiga yadda media ta ɗauka an yi hira da TGA, kuma yayi magana har na tsawon 1min amma time to time yan jarida suna ɗaukan sa hoto wani lokaci a church ɗin su wani lokaci kuma a Airport haka idan yayi tafiya ya dawo" Aafia na kokarin ci gaba da magana Amal tace "Shirmen banza to ai na ku kuma kuka san shi iyayen gayyan soɗi ae, na kuka san shi da har kuke mutuwar kaunar sa haka? Mutumin da ba bahaushe ba, Bature kuma Kirista fa wata kilama bai san wata kasa Nigeria ba ku kuna nan kuna haukan banza bai san da ku ba" Cikin sauri Aafia tace "Ni dai a gidan Tv na fara ganin sa sai kuma a wani News da muke kallo ranar an ɗauke sa hoto yana saukowa daga jirgi ni ba ma abun dake burgeni da shi irin idan yana tafiya kiga jibga jibgan Bodyguards suna take masa baya ga wasu jibga jibgan sojoji a gefen sa wow ai na a jiye wan nan video nasa kullun sai na kalla na kasa goge ta kuma na faɗa miki wani lokaci yan jarida na ɗaukan sa a church na su wan nan hirar da kikaga anyi da shi ma kusan sau biyar a kace gidan Tv na tura masa takardan gayyata amma bai yi accept ba sai yau yayi musu bazata ko in ce ya mana bazata amma fa akoi wani guy a tik tok dake posting na video sa time to time har gidan Tv na ɗauka su ɗaura idan zasu yi labarai a kan sa sai su ɗaura wannan short ɗin video nasa karki ga jama'ar dake followed na Account na guy ɗin dake posting na shi a tik tok ɗin nan sunan sa Johnson yana da followas sama da 10 millon duk kuma saboda posting na TGA da yake yi kuma karki ɗauka kullun yake posting na shi a'a wani lokaci yana yin sati bai yi posting na TGA ɗin ba da zarar yayi kan kice me zaki ga viewers sama da 1 million kamar jira suke hmmm wan nan ma ba kowa ya taɓa kallon face ɗin TGA ba kina leƙa comments section na Johnson zaki ga jama'a suna faɗin handsome of the world ba mata kaɗai ba har maza faɗe suke kuma fa ba fuskar sa suka gani ba dan na faɗa miki kullun da facemark yake yawo ba abun da zaki gani sai idon sa light ash ɗin nan mai kyalli kamar madubi shima idon time to time yake zama ba glass amma a haka jama'a ke mutuwar son sa musamman hausawan mu sai kiji suna faɗin wan nan anya ba aljani ba kuwa dan kyan sa ya wuci ɗan adam tun ma basu karisa kallon ainihin kyan face nashi ba" shiru Amal tayi ta zubawa Aafia ido har ta kai karshen maganar san nan tace mata "Dan Allah Aafia nuna min wan nan The general of the army nan in ganshi dai yau kam cikin sauri Aafia ta ɗauko wayar ta, ta shiga gallery sauri sauri ta fito da video Tga jikin ta har rawa yake tace zo ki kallesa a gidan Tv a na hira da shi duk da ya sanya face mark zo kiga asalin kyau shi fa ko a cikin turawa ma number 1 yake" ta kai karshen maganar tare da miƙa wa Amal wayar ta da sauri Amal ta ansa wayar ta fara kallon kyakkyawa Bature ne zaune saman wata haɗaɗiyar kujera mai matukar kyau da laushi face na shi sanye da face mark baki sai dara daran idanun sa kamar ball masu kyalli kamar glass kasan cewar kwayar idon nasa light ash ne, zubawa surar jikin sa ido Amal tayi yana da murɗaɗen jiki sosai ga faffaɗar kirjin kamar wani zaki duk da yana sanye cikin kaya ya ɗaura jaket mai matukar kyau da tsada a saman kayan na shi hakan bai hana faffaɗar kirjin sa bayyana ba, sau uku Amal na mai da video daga farko tana sake kalla ganin Amal bata da niyar dai na kallon TGA ne ya sanya Aafia ta anshe wayar ta tana faɗin "Ke ni bani karkije kiyi mafarkin sa" waro ido waje Amal tayi tana faɗin "Dan girman Allah Afi ki turamin duk wani videos nasa da kike da shi kuma ki faɗa min sunan account da ake posting na shi a tik tok da kuma gidan Tv dake News a kan sa time to time ɗin kinji?" Ta kai karshen maganar cikkin sigar rarrashi ba musu Aafia ta tura mata video TGA da take da shi dukka ta WhatsApp san nan ta an sa wayar ta tayi searching account ɗin Johnson tayi followed na sa sai murna Amal take da farinciki da haka sukayi sallama dan time ya tafi sosai