Showing 78001 words to 81000 words out of 194715 words
nan take daddy yaji harshen sa ya masa nauyi over, ya kasa ci gaba da maganar
kallon tsab Romeo ya masa kafin ya kau da kan sa gefe, murya kasa kasa kamar mai raɗa yace "get out!!" cikin sauri daddy ya miƙe ya bar wajen, ya koma cikin gida, jingi na kai da jikin sofar Romeo yayi tare da ɗaga kan sa sama kamar mai tunanin wani abun, zuciyar sa na masa zafi daddy ya tuno masa da babban ciwo dake zuchiyar sa wadda baya son tunawa kwata kwata a rayuwar sa, a wan nan hali wayar sa ta fara ringing, yana ji amma bai ɗago ba ma bare ya ɗauki wayar, har kiran ta katse, kira ta biyu ta shigo, hannun sa ya cusa cikin curly hair ɗin sa, yana ɗan shafawa a hankali tare da sauke ajiyar zuciya, kira na biyu ya yanke na uku ya sake shi gowa, a hankali ya ɗauki wayar kamar bai son taɓa wayar haka ya kawota sai tin face nashi tare da waro blue eyes nashi masu kwalli, zubawa wayar kyawawan eyes nashi yayi, na yan wasu sakan ni, sai da wayar ta kusa katsewa san nan ya sanya kyakkyawar yatsan hannun sa yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnen sa yayi shiru bai yi magana ba, daga ɗayan ɓangaren TGA yace "Hello" shiru Romeo ya ɗan yi kamar ba zai yi magana ba,
A hankali ya furta "What is going on T?" Daga ɗayan ɓangaren TGA yace "tomorrow I will be on my way" jinjina kai kawai Romeo yayi ba tare da ya sake magana ba, shiru shima TGA yayi yana jiran yaji me GAR zai kuma cewa
Har Tga ya cire rai da GAR zai amsa masa sai kuma yaji cikin wan nan sayyar muryan nasa yace "safe journey" ya kai karshen maganar ya ajiye wayar a gefen sa ba tare da ya kashe kiran ba, Tga da yaji shiru sai ya katse kiran, shiru GAR yayi tare da lumshe dara daran kyawawan blue eyes ɗin nan nasa, kamar mai jin barci yayin da hannun sa ke saman wuyar Brady yana shafawa a hankali.
Lokacin da daddy ya koma palo duk sun gama cin abinci sun watse kowa ya wuce bedroom na shi, yana kokarin wucewa ya haura sama, James ya sauƙo, shirye yake cikin wani ɗan iskan crazy jeans baki sai t-shirt fara tas, ya zuba gold chain a wuya, ya sanya wata haɗaɗiyar Booth a kafar sa baƙa kalar wandon sa a kafar sa, daman shi gashin kan sa bai da tsawo sosai, ba ta kai ya tara ya ɗaure ba dan haka sai ya barta zube kawai, tasha gyara sosai, sai kamshi yake zubawa, kai da gani kasan wan nan wani waje mai mahimmanci a gare sa zai je,
"Where are you going James?" daddy ya tambaya yana duba time a jikin agogon hannun sa, 09:30 pm, a ta kai ce James yace "Party" yayi maganar tare da wucewa da sauri, yana kokarin ciro wayar sa daga aljihun wandon sa, hoton da ogan su ya turo masa a waya ta faɗo, dan yaje ya wanke hoton ya mai da ta na cati, ɗaukan hoton daddy yayi ya zubawa hoton ido yana kallon face ɗin Romeo sanye da face mask "what are you going to do with this pic James?" a sukwane James ya juyo tare da dawowa ya ansa hoton ya nufi hanyar fita yana faɗin "is it not my blood brother picture?" Shiru daddy yayi ya haura sama abun sa bai kawo komai a ran sa ba, shi kuma James ya wuce ya fice daga palon ya nufi parking space.
Sauri sauri ya ɗauko motar sa ya fice dan kar Romeo ya tambaye sa ina zai je.
Yana fita kai tsaye *Flash dancing club* (gidan rawa) ya nufa, sai da ya kusa isa wajen san nan ya tsai da motar sa a bakin titi ya cire kayan da ya sako daga gida, ya sanya nasu na yan ta'adda, wato irin kayan mai kama da na yakin nan mai ɗauke da wukaken ko ta kwana a jikin su, haka ya shirya tsab a kan titi ya cire duk wasu chain da ya sanya a wuya da hannun sa, ya bar agogon su kawai, san nan yasa face mask dan kar wanda ya san shi ya gane sa yazo ya faɗa wa daddy da Romeo.
Yana gama shiri ya ja motar sa ya wuce club ɗin, yana parking a parking space na su ya fito ya shige ciki, kai tsaye wani keɓaɓɓen ɗaki ya wuce,
a nan ya isko wasu fafaren Indiyawa suna jiran sa, zama yayi a saman kujerar dake wajen suka fara tattaunawa a kan abun da ya tarasu,
Good 3 hours suka ɗauka suna tattaunawa kafin daga karshe James ya miƙe ya nufi wani ɗan karami kofa dake wajen ya buɗe ya shige, suna zaune suna jiran sa.
Jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da wata jaka yazo ya miƙa musu san nan ya basu hannu sukayi musabaha tare da yin sallama, ya wuce ya fice daga wajen ya nufi motar sa.
A wan nan karon ma yana fita daga club ɗin ya ɗan yi tafiya kaɗan ya tsaya ya sauya kayan jikin sa ya mai da wanda ya fito da su daga gida, ya shirya tsab kamar yadda ya fito daga gida san nan ya wuce ya nufi gida.
Yana shiga gate na biyu tayi scanning na shi san nan ya wuce parking space, lokacin karfe ɗaya sau ra minti 20 na dare.
Ko da yayi parking na motar ya fito sai ya fara lallaɓawa a hankali kamar mara gaskiya, musamman ma da ya shigo palon kasa, a hankali yake sanya kafar sa a floor ɗin dan kar wani yaji takun sahun sa.
Kamar daga sama yaji zazzakar voice an ce "where are you coming from?" A razane ya ɗago kan sa sama, dan ta saman kan sa yaji voice ɗin, ganin Romeo tsaye a saman benen a bakin kofar shi ga part na shi ne yasa James sauke nauyayyar ajiyar zuciya a hankali, cike da tsoro yace "from my friend party" shiru Romeo ya masa tare da tsare sa da dara daran kyawawan blue eyes na shi, sanye yake cikin kayan barci riga da dogon wando farare kal masu laushi da kyau da tsada, kayan sun zauna a jikin sa sun anshe sa sosai kamar dan shi a kayi su, a wan nan karon ma a koi face mask a face na shi, dan shi idan ba barci zai yi ba baya rabuwa da face mask dan bai son jama'a su iya tantance face na shi, bai son su iya gane banbancin sa da TGA, dan kwarai suna kama amma suna da ban ban ci ta abu huɗu kawai, wan nan dalilin yasa bai son cire face mask ɗin, har ya saba abun ya zame masa jiki, ya zamo idan bai sanya face mask ba ma baya jin daɗi.
Da wan nan daddaɗar sexy voice ɗin nasa mai kwantar da hankalin mai sauraro cikin nitsuwa yace "From today i forbide any body in this house going to party anymore" cikin girmamawa da rawan jiki James yace "Okey bro" sai kerma irin na marasa gaskiya jikin sa ke yi, duk a ruɗe yake, sai zufa yake duk da sanyin Ac dake ta shi a palon kirjin sa sai dukan uku uku yake, tsabar tsoro har kan sa na sara masa kamar zai fashe.
Juyawa Romeo yayi cikin nitsuwa ya taka ya koma cikin part na shi, ba tare da ya sake yiwa James magana ba, da sauri James ya haura sama har yana haɗawa da gudu, kallon ɗaya zaka masa a wan nan yanayin da yake ciki kaga asalin mara gaskiya, yana shiga bedroom na shi ya faɗa saman gadon sa ko takalman kafar sa bai cire ba kirjin sa sai dukan uku uku take, yana murna da ya samu ya kubcewa Romeo, dan yasan ba dan dare bane yanzu da sai Romeo ya kama shi sai ya gano shi, saboda Romeo a koi shi da kaifin kwakwalwa da basira, ga saurin gane abu, ba'a banza yake The general of the army gaba ɗaya ba.
Saboda tsorata da James yayi da kyar barci ta ɗauke sa ko takalmin kafar sa bai cire ba bare aje ga zancen wanka da sa kayan barci, ya tsorata sosai dan ya san halin Romeo bai da wasa, kana wargi kaɗan zai kama ka.
*NIGERIA,*
*ABUJA*
Wasa wasa zazzaɓi ne mai zafi ya rufe Rimsha tana rubgume da zanen da tayi na GAR haka mum ta shigo ta same ta, a tsorace ta kira daddy, lokacin already ya dawo yana gida, yana zuwa ya taɓa jikin ta zafi kamar wuta, hannu yasa yana kokarin ansan zanen da ta rungume, cikin magagin barci da zafin zazzaɓi ta fara sambatu ta kankame zanen sosai tana faɗin "Jehan dan Allah ki kyale min zane na daddy ya hanani kallon GAR a Tv yanzu zanen kawai ya rage min duk wani video sa dake wayata zan goge dan ba zan iya kin bin maganar daddy ba, dan Allah ki kyalemin zanena idan kika ansa Allah zan iya mutuwa, ni GAR yana matuƙar burgeni dan Allah ki kyaleni"
Cike da tashin hankali daddy ya ɗago ya kalli mum wadda ita ma shi take kallon, tashin sense ja da baya kaɗan yayi murya kasa kasa yace "Munyi kuskure, mun yi kuskure tun farko da muka bar Rimsha tana kallon wan nan kafurin yanzu saboda na hanata kallon shi ne har zazzaɓi ya kamata, innalillahi wa inna ilaihir rajiun tab ɗi jam a koi matsala" matsowa Mum tayi ta dafa sa tana faɗin "To yanzu me mafita?" Girgiza kai yayi yana faɗin "Mafita shi ne mu kyaleta ta ci-gaba da kallon sa, a hankali mu raba ta da shi, idan muka ce zamu raba ta da kallon sa lokaci guda zata iya cutuwa kin dai ga alama yanzu to, ba zai yiwu mu ce lokacin guda ta dai na kallon sa ba, idan mukayi hakan mun zalunce ta, kuskure dai mun riga mun yi sai dai mu kiyayi gaba ki san yadda zaki yi kina zare mata abun a ranta a hankali hankali har ta rabu da abun dukka, yanzu zai wuce da ita hospital kome yake ciki zamuyi waya" ya kai karshen maganar tare da komawa wajen ya duƙa ya sameta cak a kafaɗar sa suka nufi waje sai sambatu take ga jikin ta zafi kamar wuta
jiki a mace mum tabi bayan su ta wuce bedroom nata, while gwaggo da Jehan kuma suna ɗakin gwaggo basu san meke faruwa ba, ita ma mum tazo dubasu ne ta samu Rimsha cikin wan nan hali.
Kai tsaye hospital daddy ya wuce da ita, suna zuwa a ka anshe ta hannu bibbiyu, a ka fara bata taimakon gaggawa, shi kuma daddy sai yawo yake a bayan A&E yana tunanin mafita.
*KADUNA*
zaune suke gaba ɗayan su suna hira while Imran yana aikin latsar waya yana kallon hotunan Jelly,
cikin natsuwa Abba ya fara magana "Imran yaushe zaka koma school?" Ɗagowa Imran yayi daga kallon wayar nasa da yake cikin girmamawa yace "Next week zan koma" jinjina kai Abba yayi kafin yace "Kai kuma fa Akil?" "Tare zamu wuce da Yaya Imran In Sha Allah sai mu rabu a Germany ya wuce nima na wuce namu School ɗin" Abba na kokarin yin magana Akila ta rigasa cikin shagwaɓa tace "Abba dan Allah nima zan bi yaya Imran, na gaji da karatu a Nigeria" Shafa kan ta Abba yayi tare da jawota jikin sa yana faɗin "Ba komai heartbeat zaki je amma ba yanzu ba sai kin kammala secondary ki san nan kije kiyi jami'a a can" kara lafewa tayi jikin Abba tana mai kaunar iyayen ta da yan uwan ta, Akila kenan heartbeat na kowa dake cikin gidan, har da masu bawa flowers ruwa da mai gadi duk kaunar ta suke, kowa son ta yake, ba iya gidan ba duk wan da ya zauna da ita sai ya so ta saboda kyan halinta da kaunan jama'a ba ruwan ta da rigima ga girmama mutane, tana son zaman lafiya, ga fara'a kowa na tane
Tana kwance jikin Abba ta jiyo wayar ta na ringing a bedroom na ta, da gudu ta miƙe ta haye sama ta nufi bedroom ɗin, wayar na gab da katsewa ta shigo, hannun ta har rawa yake wajen yin picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen ta cike da zumuɗi tace "Bappa ina wuni" daga ɗaya bangaren muryan Jelly ta daki dodon kunnen ta cikin kauɗi tace "Aunty Akila ni ce ba daddy ba" daɗi kamar Akila tayi ihu sai murmushi take bakin ta yaki rufuwa, ta kasa ɓoye murnar ta, cike da kaunar yan uwa ta tace "Jelly na ya kike ina kewar ki sosai yar uwata" a bangaren ita ma Jelly bakin ta ya kasa rufuwa saboda murna da farinciki ji take kamar tayi tsuntsuwa tazo ta kalli Akila, tana matikar son Akila over,
haka suka rinƙa hira Jelly na zuba mata shirme ita kuma tana biye mata, almost 1 hour suka ɗauka suna hira sai murmushin da dariya Akila keyi ji take kamar ta koma gidan su Jelly kawai da zama, sun kasa yin sallama da juna har sai da daddy ya anshe wayar suka gaisa da Akilan san nan ya katse kiran
Yana katsewa Akila ta fara ƙoƙarin neman layin su Umaisha dan su gaisa, sai dai kash a rufe tasamu layin, haka ta hakura ba dan taso ba, tana bala'i kaunar yan uwan ta sosai, rashin samun su Aafia a waya bai mata daɗi ba ko kaɗan amma haka ta hakura ba dan taso ba, ta miƙe jiki ba kwari ta fice ta koma Palo
Ko da ta dawo palon, yaya Imran da Akil duk sun tafi basu a palon sai Ammie da Abba, da suka zubawa Tv ido sosai suna kallon, yanzu sun samu saukin wayan nan dodannin dake zuwa musu kasan cewar su Imran na yawan yi musu karatun al Qur'ani mai girma a gidan, shi yasa tun ranar da suka ɓace basu sake dawowa ba, daman saboda tafiyar su Imran kano ne yasa abubuwan ke zuwa dan ba'a karatu kuma ba'a kunna kira'a, daman Abba da su Imran ke kunnawa, to shi Abba ya dawo ya samu bala'i ne shi yasa bai samu damar karatun ba, dan ita dai Hajiya Umaiya bata wani yin karatu Al Qur'ani sharholiyar ta kawai take, san nan faruwar wan nan abun yasa Hajiya Umaisha ta yi hankali sosai, ta rage wasu abubuwa yanzu duk wani hakkin miji tana kokarin ta sauke sa dan tsoron dodannin, yanzu ta dai na masifa da faɗa ta koma so silent kamar ba ita ba, daman shi kam Abba shiru shiru ne baya shiga har kan kowa abun da ke gaban sa kawai yake, haka suka koma ratuwar farincikin su kamar yadda suka saba.
*ABUJA*
Sosai a ka bawa Rimsha kulawa har sai da suka tabbatar ta dawo dai dai, daddy ya shiga damuwa over ji yake kamar zai yi kuka saboda kaunar da yake wa Rimsha gashi ta jefa kan ta cikin wahala.
Basu bar hospital ba sai da daddy ya tabbatar da tasamu lafiya sosai san nan ya ansa magungu nan ta ya wuce ya suka shiga motar sa suka bar hospital ɗin, Rimsha ta samu sauki dan da kafar ta ta taka zuwa wajen motar daddy.
Suna isa gida, suka isko mum gwaggo da Jehan a Palo zaune cikin damuwa ko wani hali Rimsha ke ciki, mum na ganin su ta miƙe tana faɗin "Ya jikin nata dai?" kallon face ɗin Rimsha daddy yayi kafin yace cikin zolaya "GAR ya bamu magani ai" cool murmushi Rimsha ta saki har sai da dimple nata ya lotsa open teeth nata ya bayyana ga hakoran nata a jere tsab sai kyalli suke kamar gonar audiga, hakan ba karamin kyau ya karawa kyakkyawar face nata ba, duk da cewa ta ɗan rame saboda zazzaɓin, sleeping eyes nata sun kara haske sosai sun kara girma saboda yar ramar da tayi. Riƙo hannun ta gwaggo tayi suka haura sama dan taje ta mata wanka ta huta, wucewa daddy yayi ta nufi bedroom na shi yana faɗin "Ina son magana da ke boɗɗi" cikin sauri mun tabi bayan sa ita kuma Jehan tabi su gwaggo.
Zaune bakin gado ta isko sa yayi shiru kamar mai tunani wani abun, "lafiya daddyn Jehan?" Mum ta tambaya dai dai lokacin da take zama a gefen sa, dogon numfashi yaja tare da sauke wa a hankali ya ɗan juyo suna fiskantar juna "Wallahi ba lafiya ba" zaro ido waje mum tayi tana faɗin "Meke faruwa to?" Riko hannun ta daddy yayi ya fara magana cike da damuwa "kwana ki na ta tafiya zaɓe na ta kara gabatowa ni kuma sai kara samun baraza nake daga abokan ha mayya, baraza ta ko ina nake samu abun ya fara affecting ɗina na fara karaya, dan wasu ma ban san daga ina suke min barazanar ba, ina tsoron kada na jefa rayuwar ku a cikin haɗari bana son abun da zai taɓa min ku bana son tashin hankali ku, ina ganin zan hakura da siyasar nan kawai" cikin sauri mum tace "A'a barkama ni ban yarda da ka hakura da siyasa ba, kasan cewar adalin mutun irin ka mai gaskiya a siyasa babban nasara ne ga yan kasa, kana da tausayi kuma zaka taimakawa talakawa, na sani siyasa babban haɗari ne dan ba kowa yake son cigaba al'umma ba, amma jajirtattun mutane ire iren ka masu son tai makon talakawa bai kamata ku rinƙa karaya kuna sarewa haka ba, kama ta yayi ku rinƙa karawa kan ku kwarin gwiwa, na san cewa rayuwa a matsayin mai gaskiya yafi komai wahala a duniyar da muke ciki yanzu, dan dayawa daga cikin mutane sun ajiye gaskiya sun bi karya da ha