Showing 93001 words to 96000 words out of 194715 words
ta sanya hannu, kallon tsab Jehan ta musu kafin tace "Wace dokace ta baku damar shigowa gidan matan aure kuma har cikin palo ba tare da izinin masu gidan ba kuna kartin maza da ku? San nan wan nan takardun me, ba zan sanya hannu ba sai na san takardun menene" tayi maganar babu alamar tsoro ko kaɗan a face nata, sai lokacin mum tayi nadamar sanya hannu da tayi a takardun, taruɗe sosai shi yasa tayi saurin sanya hannun dan bata kawo komai a ran taba.
Ba tare da sun yi magana ba babban cikin su mai riƙe da takardan ya ciro ID card ya nuna mata, kallon sama da kasa ta masa ko tsoro babu a face nata tana ganin kartin maza har huɗu amma bata ji shakkan su ba tace "ID card ba shine na tambaye ka ba, abun da na tambaye ka wace dokace ta baku damar shigowa cikin gidan matar aure ba tare da izinin su ba, kuna kartin maza da ku, san nan kuma takar dan me kuka kawo mu sanya hannu, ba zan sanya hannu a komai ba sai naji na menene ko kuma ku bani takardan na karanta"
tsare ta da sheggun idon sa wanda ya riƙe takardun yayi, a zuciyar sa yana faɗin "Wan nan idan muka ce zamu bita ta karfi zata iya tona mana asiri amma in ta san wata ai bata san wata ba" ya kai karshen zancen zucin na sa tare da shammatar ta ya zaro takarda guda ɗaya daga cikin takardun ya miƙa mata, amma sai ya zaro takarda na kasa ba na sama da su mum suka sanya hannu ba, kwata kwata Jehan bata lura da hakan ba, ansan kawai tayi ta fara larantawa, ganin an sanya takardan neman bellin daddyn sune yasa cikin sauri tace "Ku bani pen na sanya hannu" ansan paper yayi sai yayi kamar ya ɗaura mata a saman sauran takardun al halin kasan sauran na hannun sa ta tura ya miƙo mata takardun dukka tare da bairo, cikin zumuɗi ta sanya hannu a kan wadda su mum suka sanya hannu ba tare da ta lura ba, tana sanya hannu suka ansa suka juya suka fice daga palon,
rungume mum Jehan tayi tana dariya tana faɗin "Mum daddy zai dawo, yanzu ba zai daɗe ba" nan take dukkan su suka fara murmushi suna jin daɗi, sai godiya ga Ubangiji talikai suke, suka koma suka zazzauna suna tayiwa daddy addu'a.
Misalin karfe 9 na dare duk suna zaune a palo sun yi jugum jugum kamar masu zaman makoki, kowan nan su da abin da yake sakawa a ransa, duk sai tambayar kan su suke ya akayi daddy bai dawo ba bayan kuma sun sanya hannun a kan takardun beli, sai addu'a suke ta masa, ita kam Jehan ta tada kai da cinyar Gwaggo tana aikin hawaye ita kuma Rimsha tana kan dadduma ta buga uban ta gumi tana tunanin wani hali daddyn ta ke ciki.
Sun yi nisa cikin tunanin da suke Uncle Shitu ya faɗo cikin palon babu ko sallama goshin sa a fashe ga jini duk ya wanke masa kayan jikin sa sai nishi yake sama sama ya dafe goshin nasa in da ya fashen ga jinin sai bin hannun sa yake, jiri yake gani sosai amma saboda karfin hali irin nasa sai ya danne yana kame kan sa.
Jehan ta riga kowa miƙewa tsaye, cike da tashin hankali Mum tace "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Shitu lafiya? Accident kayi ne? Girgiza kai uncle Shitu yayi ciki firgici da kyar ya iya buɗe baki murya na rawa sai haɗe kalmomin yake saboda azaban da yake ji "Hajiya ku wuce muje da wuri karku ɓata lokaci" gwaggo ce tace masa "Ina zamu je" juyowa yayi ya kalle ta yana faɗin "Aunty A'isha in mun fita zan faɗa muku ni dai burina mu bar gidan nan, ku ɗauki ɗan abun da zaku buƙata muje baku da lokaci fa" tun da mum taji haka sai ta fahinci a koi babban matsala dan haka sai ta haura sama da gudu ta ɗauki trolley ɗaya babba ta zuba kayan ta da gwala-gwalai ɗin ta, da duk wani abu ta mai tsada ta haɗo da wayar ta da ATM nata, ta sauko kasa ta ajiye trolley ta wuce ta koma ɗakin su Rimsha cikin sauri suma ta ɗauko musu kayan su trolley ɗaya tare da wayoyin su da ATM na Jehan, ko da ta dawo palon gwaggo ta ɗauko nata trolley, a tare suka fice uncle duk da jirin da yake ji hakan bai hana shi ya ɗauka wa mum trolley ɗin ta ba.
Mum ta kara tsorata sosai lokacin da suka fito waje taga motar uncle Shitu duk taɓo da datti yayi caɓa caɓa da alama yayi gudun cetan rai ne
dukkan su gidan baya na motar suka shiga, ko sallama basu yiwa mai gadi ba, kasan cewar daman uncle a waje ya bar motar bai shigo da ita cikin gida ba, haka suka wuce cikin motar.
Da wani mahaukacin gudu uncle ya ja motar, baya ganin gaban sa sosai saboda jirin da yake ji, jinin sa ya zuba sosai abun ya fara affecting na shi, amma haka ya daure yana ambato sunan Allah yana gudu da motar.
Uncle na tafita ba'a fi da minti 20 ba sai ga wasu jibga jibgan sojiji sanye da kaki sun diro gidan, kai tsaye suka wuce cikin gida, ganin babu kowa ne yasa suka dawo bakin gate dan su tambayi mai gadi, nan suka tarar da ba mai gadi shima ya gudu, hakan ba karamin fusata su yayi ba, haka suka kulle gidan ko ina suka sanya kwaɗo da key suka rufe gidan suka fito suka shiga Hilux car ɗin su suka bar estate ɗin da gudun gaske cike da bakin ciki.
Shi kuwa uncle kai tsaye park ya kai su mum, yayi Sa'a motar zuwa Katsina ya samu saura mutun uku a ke buƙata motar ta tashi, haka ya ciro kuɗi daga aljihun sa ya bawa mum ta biya musu kuɗin mota, san nan ya sanar da su a kan su ɓoye kan su karsu kuskura su bari wani wadda ya sansu ya gane face na su, suje Allah na tare da mai gaskiya kuma Allah zai tsare su, mum ta tambaye sa ina daddy, amma sai ce mata yayi suyiwa daddy addu'ar Allah yasa can ta fi masa nan, mum taso sake tambayar sa amma kasan cewar babu lokacin, hakan yasa suka fita suka shiga motar Katsina, shi uncle yaki fita daga motar sa saboda jinin dake jikin sa idan jama'a suka gani zasu iya kin ɗaukan su mum a tashan ko kuma suyi wani abun da zai tonawa su mum asiri, Allah ma yasa dare ne ba'a ganin sosai a koi duhu.
Haka uncle yaja motar sa ciki fitar hayyyaci dan ya fara fita hayyacin sa sosai, haka ya bar park ɗin ya hau titi, duhu yake gani sosai baya ganin komai bai san ina ya nufa ba kawai gudu yake shararawa a kan titi gashi ya kasa dakatar da motar saboda ya galabaita over.
Tafiyar 10mins yayi tsakanin sa da park ɗin ya samu haɗari, yayi karo da wata motar, juyi uku motar sa tayi a saman titi kafin ta kama da wuta, anyi Sa'a a komai mutane a wajen suka fara kawo ɗauki, shi wan can motar da sukayi accident ɗin ma da alama driver shima ya mutu.
Su mum kuwa sai kuka kasa kasa suke a cikin mota Rimsha na zaune saman cinyar mum, ba abun da take sai ambato sunan Allah, yayin da ita kuma Jehan ta fita kanta da jikin kujerar motar tana tunani a kan takardan da ta sa hannu tana yi tana hawaye, while ita ma gwaggo hawayen take sosai da sosai, mum kam ba'a magana nata tashin hankali na daban ne, yafi nasu dukkan su.
01:30 am suka shiga Katsina, kasan cewar dare yayi sosai a tasha suka kwana cikin sauro da zafi, abun da basu taɓa ba, hakan yasa suka kasa barci, Jehan sai kuka take yayin da ita kuma Rimsha tayi shiru tana yiwa daddy addu'a, har wayewan gari.
Tun gari bai yi haske sosai ba suka sayi face mask suka sanya a face nasu, mum tayi kokarin kiran layin daddy, amma a rufe haka tayi kokarin kiran layin uncle Shitu shi ma a kashe, sun rasa ina zasu je dan basu san kowa ba, gwaggo ce tayi ta maza taje ta tambayi wasu maza dake zaune a runfar mai sai da shayin cikin tashan, ta musu sallama bayan sun amsa ta musu sannu san nan tace hotel take so su nuna mata su baƙi ne basu san kowa ba, wani bawan Allah ne ya tashi yace da gwaggo "Mama muje na numiki in da zaki hau abin hawa zuwa hotel ɗin" ba musu gwaggo tayi gaba yabi bayan ta har zuwa wajen su mum, gwaggo ce ta sanar da mum abun da ke faru wan nan mutumin zai nuna musu in da hotel yake su kama ɗaki su zauna, kallo gwaggo da kyau mum tayi sai taga gwaggo fa bata cikin hayyacin ta, hakan yasa mum ta kalli mutunmin cikin sanyin murya tace "Bawan Allah ba hotel muke da buƙata ba karamin gida ɗan dai dai muke so dai dai talaka" washe baki mutumin yayi yana faɗin "Nima ai dillaline, daman a koi gidan na da zan sayar muje ku gani in ya muku sai ku saya" ba musu su mum suka bi shi, ya tari abun hawa suka ɗauki trolleys ɗin su suka hau.
Nan ya kai su wani gida ya nuna musu wai gidan shi ne zai sayar, kasan cewar a kiɗi me suke ba su wani duba gidan sosai ba suka ce ya musu, sukayi ciniki 5 million, haka mum tace ya nuna musu bank, ya nuna musu, ga baɗaya basa cikin hayyacin sosai sun rikice ga tashin hankali ita kam Jehan ko magana ta kasa, Rimsha ce ma mai kuzarin bakin magana itama gwaggo ta kasa magana, haka mum ta ciro kuɗin nan ta bawa mutumin nan ko takardun gidan basu tambaya ba, su dai kawai sun samu gida, suka fara sanya kayan cikin ɗakin suka zauna shiru, shi kuwa mutumi yayi gaba abun sa
A wan nan halin asalin masu gidan ya dawo ya same su, da mamaki ya tambaye su mum wanene su, nan mum ke shaida masa ai sun saya gidan ne, ba karamin mamaki mai gidan ya sha ba, cike da mamaki ya tambayi su mum a wajen wa suka sayi gidan nan
da kyar mum ta iya masa bayanin yadda komai ya gudana, a fusace mutumin yace "Wlh dan faran ku murtala yayi wan nan ba gidan shi bane gida nane, tare muke kwana da shi a ɗakin kawai amma ba gidan shi bane" lokacin guda mum taji duniya na juya mata dafe kan ta tayi ta zauna tana mai da numfashi kwata kwata daman 9 millon ne a account nata sai gwala-gwalai ɗin ta, dukkan su sun kasa magana, waya mutumin ya ciro ya fara kiran layin Murtala amma a kashe, tuni Murtala ya bar garin Katsina abun sa ya samu kuɗi,
sai lokacin gwaggo ta lura da gidan ma da suka saya, ashe gidan ma irin gidan mazan nan ne ɗaki biyu ne a cikin gidan, sosai su mum suka shiga damuwa, gashi ba halin zuwa police station basu da zaɓi dole su hakura, wan nan abokin Murtala ne ya taimaka musu ya nema musu gida a Unguwar farin yaro da kan sa ya musu jagora suka sayi gidan 3 millon suka biya kuɗi, san nan suka ɗauki 500k suka sayi kado da kayan abinci da sauran kayan amfani na talakawa, sauran 500k suka bari a account ɗin mum while ita gwaggo daman bata da account sai account na Jehan mai ɗauke da 1 million a ciki.
Tun da sukazo Unguwar Jehan bata cin abincin da su mum ke girkawa, kuɗin account nata kawai take kashe musu ita da Rimsha, dan ita Rimsha bata da account ita ma Jehan ɗin da kyar bank suka yarda suka buɗe mata account tana da 15 years sai da daddy ya nemi alfarma san nan suka bata account, kullun Jehan ke fita ta sawo musu abinci ita da Rimsha da su mum, ita kuma Rimsha tana gida bata fita, dan ita unguwar ma tsoro yake bata shi yasa bata fita take zaune a gida.
Tun da suka zo sau biyu Rimsha ta fita ranar da ta raka Jehan restaurant, sai ranar da ta fita a ka sace ta shi kenan.
*KADUNA*
A wan nan satin Abbi ya auri amaryan sa Halima wadda wani abokin sa ya haɗa su kasan cewar Halima yarinya ce mai hankali ga addini sai dai yar gidan talakawa ne sosai da sosai, shi kuma Abbi yanzu arziki ba'a magana su Aafia an kara goge wa dama ba daga nan ba.
Wan nan shine takaitacen labarin a kan abun da ya raba su Jehan da daddyn su da kuma abun da ya sanya daddyn Jelly zai aurawa Jelly Muneer, da kuma yadda Abbi ya auri Aunty har su Aafia ke mata rashin mutunci. Yanzu sai mukoma cikin asalin Story.
STORY.....✍️🤪
MUCH KAUNA MASU MIN COMMENTS ALLAH YA BAR ZUMUNCI ALLAH YA BAR KAUNA ❤️💖 KUMA MASU MIN LIKE MUCH KAUNA ❤️ MASU MIN SHARE ALLAH YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNATUL FIRDAUS INA GODIYA BA ZAN MANTA DA KU BA MUCH KAUNA ❤️
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪🤪
B 💞Star Lady💞
TRIPLET'S💞 21
https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo
*THE BEGINNING*
💞*STAR LADY*💞
Mai neman karin bayani yamin magana ta wan nan number 09162620621
EPISODE 21
```*💞BACK TO THE STORY💞*```
______Da iya karfin su wayan nan magicians (Matsafa) suka sanya hannu suka fara tsigewa yaran nan gashin kan su, koda ɗaya daga cikin su ya damko gashin Rimsha ya ja yana kokarin shigewa, ihu ta fasa tare da furta kalmar shahada da karfi, hakan yayi sanadiyar magicians ɗin suka ja da baya da sauri, gudun kar su kone, jin sunan Allah yasa Santilago ɗago kai da sauri yana kallon su, yayin da sauran magicians suka ja baya suna zaro ido gwanin ban tsoro, ita kuwa Rimsha sai sauke ajiyar zuciya take tana ambato sunan Allah ta runtse ido gam.
Gigitatchiyar tsawa Santilago ya daka, tare da fara Yaren tsafin su, da karfi ya ɗaga hannu tsama nan take idon sa suka sauya launi, kan kace me gidan ya turnuke da duhu da hayaki kamar guguwa mai karfi, Rimsha bata cikin hayyacin ta sosai ba zata iya ja da su ba, dan bata san meke faruwa ba, salatin Annabi ka ɗai take iya furtawa sai kalmar shahada dake fita daga bakin ta, shima kuma ba'a dai dai take karan tasu ba saboda ruɗu da tashin hankali, yayin da shi kuma Santilago ke faman kiran abubun tsafin su, kusa da shi Barbushi ya zo ya tsaya, suka haɗa hannu da murya sama suka ci-gaba da ambato sunayen manya manyan jiga jigan magicians ɗin na su, gidan gaba ɗaya sai kara duhu yake kamar dare, ga wani iska mai karfin gaske dake tasowa daga ta saman gidan mai birkita tunanin ɗan adam.
Nan take Rimsha taji an ɗaure mata maƙogwaro da karfi kamar za'a tsinke mata shi, ta kasa magana shiru tayi tare da waro sleeping eyes nata waje, wadda yanzu suka sauya sukayi ja sosai kamar garwashin wuta, Saboda kuka da wahala ga yinwa da barci duk sun haɗe mata waje guda.
Kamar a mafarki taji an ɗaga ta sama ta rabu da kasa haka zalika ta fita daga cikin igiyar da suka ɗaure ta,
sama sosai sukayi da ita, sai da ta kusa kurewa tsayin gidan, a hankali ta kalli kasa, ba karamin tsorata tayi ba lokacin da taga babu wanda ya ɗaga ta haka nan ta tashi sama, runtse ido tayi a ranta tana ambato sunan Allah, dan afilin kam ta kasa faɗa sun shake mata maƙogwaro.
Almost 5mins tana tsaye a saman iska kafin su fara bujijjigata suna wainata kamar fanka, ga wan nan iskar guguwa mai karfi mai haɗe da yashi wato kasa sai shiga mata hanci yake dan ta runtse idon ta kam sosai, da kyar take samu tayi mumfashi nan ma sai ta buɗe bakin ta take samun damar yin numfashin
da karfi suka ja ta da tsafin su suka bugata da jikin wani bango sai da ta fasa ihu mai rikita ƙwaƙwalwa, a cikin ihun nata ne take kiran "wayyo daddy na mummy gwaggo Jehan ina kuke zan mutu kuzo ku taimake ni, wayyo na shiga uku mutuwa zanyi wayyo Jehan kizo ki taimake ni"
ba shiri ta sake fasa wani ihun sakamakon buga mata kai da sukayi da jikin wani karfe dake tsakar gidan, jijjigata da karfi suka sake yi kafin su juyo da ita kan ta na kallon kasa kafafun ta a sama, da karfi sukayo kasa da ita, kamar zasu makata da kasa, sai kuma suka da katar da ita, dark black curly hair tan nan ya curkuɗe saboda wahala yana ja a kasa, yayin da kafafun ta ke saman iska, tana lilo tsakanin kasa da sama, a nan ma kara jujjuya ta sukayi kamar fanka, sai da suka tabbatar ta jijjigu a ganin su tafita hayyacin ta sannan suka juyo da ita suka sauke ta kasa
Suna sauke ta kasa su kuma su barbushi suka dakata da ambaton sunan suwagabannin tsafin na su, suna dakatawa gidan ya washe duhun ya tafi haske ya gauraye ko ina, haka shima kuran ya ɓace ɓat kamar ba'ayi ba.
Shiru Rimsha tayi ta kasa buɗe idon ta saboda wahala,
ta kuma kasa zama waje guda sai juyawa take saboda jijjigata da sukayi suka ta juyata kamar fanka, amma dai har lokacin Allah da ikon