Showing 174001 words to 177000 words out of 194715 words
ta katse shi da cewa "Ko dai ka manta baka kama hotel ɗin bane? Au sorry na manta fa ashe gidan ka zamu je ba hotel ba, amma ina son sani wani abu ɗaya kafin mu tafi, a gidan naka babu kowa ko, ma'ana iyayen ka ba a nan suke ba ko? Dan ban cika son hayani ya ba" tashin hankali, wani irin dukan uku uku gaban Alhajin nan yayi, tunani ya kara shiga "Anya wannan yarinyar mutunce kuwa? Ita da kan ta ta kawo kan ta, to gaskiya ba lafiya take ba, kila tana da wani ciwon dai, dan mace mai lafiya kuma cikakkiyar mace kamar wannan ba zata miƙa kan ta haka ba, gata da ka ganta kaga cikakkiyar mace mai addini to meke shirin faruwa ne"
Su Sadiq dai yau suna ganin ikon Allah
Ganin yayi shiru yasa Jehan ta kara matsowa kusa da shi, kasa kasa tace "Farooq Salahuddeen Abubakar, right?" Zaro ido waje yayi yana kallon ta da mamaki ai ina ta san shi
Bai gama tunanin sa ba muryan ta ta katse shi da cewa "Me yasa kayi shiru? Ka tsorata ne? To karkaji komai, amma dai ya kamata kasan wani abu guda, duk abubuwan da kayiwa Hanan jiya da daddare munyi audio recorded na voice naka, sannan duk wasu maganganu da kake mata a nan duk munyi recorded, dan kullun idan ka zo tana kunna karamar wayar ta tayi ta recording, so ina son ka sani idan ka sake dawowa cikin garin Katsina wlh sai na baza wannan recorded ɗin wa duniya kowa yaji, kasan dai ba wanda bai san muryan ka ba ko? Dan kullun kuna hawa kaban mike kuyi ta shirgawa mutane karya, kowa ya sheda wannan ɗan iskan muryan naka kamar na karuwar akuya, ka baro Abuja kana bin kauyuka kana lalata ƴaƴan mutane, dan bakin iyaye na bin ka ko? To mu nan munfi karfin yaro sai dai baban yaro wato Salahuddeen Abubakar ina ga shine dai dai mu, wato yanzu kun dai na neman mata a manyan birane saboda gudun cututtuka, sai ku shiga kauye ku yau dari ƴaƴan talakawa da sunan aure ku lalata musu rayuwa ku gudu ku barsu, wasu ma da ciki zaku gudu ku barsu, ayi ta haifan ƴaƴan da basu da uba suna tashi cikin wahala da kuncin rayuwa, ba ilimin boko bare Arabic, da sun girma su zama yan shaye shaye dan ba ilimi, saboda ire iren ku zan zama yar sanda, duk sai naci Kutumar uban ku, na tarwatsa muku tunani yan iska banza" duk wannan magana tayi shine cikin harshen turanci
Tun da ta fara magana Farooq ya tsare ta da ido yake ta faman haɗiyar wahalallen yawu, sai zazzaro ido waje yake kamar wani ƙasurgumin munafuki, tunani yake wace ce Jehan, ai na kuma ta san shi farin sani haka, wayan nan tambayoyin duk ita ya dace yayiwa sai dai ba dama, dan cikin sa ya ɗuri ruwa, musamman da yaji sun yi recorded abubuwan da yayi ta faɗe a matsayin sa na kanin babban ɗan siyasa, idan wannan abun ya fita yake nan, gashi kuma ba wanda bai san voice na saba, wasu ma a media har tsokanar muryan nasa suke, saboda yana magana da sauri sauri kuma muryan tasa kamar na yar baby, irin munafukan muryoyin nan gare sa.
A ɓangaren su Sadiq da sauran yan anguwa kuwa, sun zubawa Jehan da Farooq ido, sun kasa kunne suna son jin me Jehan take faɗawa Farooq, sai dai basu samu damar ji ba, dan ƙasa ƙasa Jehan tayi maganar saboda ita da kan ta bata son fitina, bata son kowa ya gane wace ce ita, kuma da turanci tayi maganar.
A ruɗe Farooq ya shiga motar sa ya kunna, har lokacin yana kallon cikin idon Jehan yayin da itama take kallon cikin idon sa, sai dai Farooq ya kasa gane wace ce saboda fake face dake fiskar ta yasa bai gane wace ce ba, amma bashi da wani burin da ya wuce ya gane wace ce Jehan ai na kuma ta san shi, dan shi bai cika wani fitowa gidan Tv ba, sai dai ya taya yayan sa kanfen da muryan sa kawa, amma dai dayawan mutane sun san shi, sai dai ba kowa ya damu da fuskar tasa ba dan ba shi ne mai neman takarar ba yayan sane, tunani ɗaya yake, ko ma wace ce Jehan makusanciya ce a gare shi dan wannan sanin da ta masa ba sanin wasa bane farin sani ta mi shi.
Ko uppan ya kasa cewa Jehan ya ja motar sa ya bar wajen yana tunanin ko dai kashe Jehan zai sa ayine, dan in wanna voice ɗin nasa ta fita shikenan ya gama yawo yayan sa ma ba zai bar shi ba, da tuni fal ransa na ya zai yi da Jehan, ya zai yi ya kwace Audio sa dake hannun ta haka ya bar layin gaba ɗaya tunani cike da ran sa, sai dai abun da bai sani ba ba wani recording da Jehan ta masa, kawai ta shirga masa karya ne dan ta ceci Hanan.
Bayan ya tafi ne Sadiq ya matso wajen Jehan, dan tana tsaye tana bin motar Alhajin da kallo har ya bar layin nasu.
"Jehan me kika ce masa haka, naga ya tafi da sauri kuma yana cikin tashin hankali har haka?" Cewar Sadiq, kamar jira Jehan take a mata magana ta juya da sauri ta wuce cikin gidan.
A zaure ta wuce su maman Sadiq sunyi cirko cirko suna leƙo abun dake faruwa, kai tsaye ɗakin maman Sadiq ta wuce, ta faɗa saman yar katifar maman Sadiq ta hau kuka kamar karamar yarinya.
Tashin hankali yau ga DPO Jehan tana kuka meke faruwa muje zuwa.
A tare Sadiq da maman sa suka biyo bayan ta, kusa da ita maman Sadiq ta zauna yayin da shi kuma Sadiq ya zauna ta bakin kofa, in da ya saba zama.
A hankali maman Sadiq ta shafa kan ta tana faɗin "Lafiya Jehan meke faruwa? Me ya saki kuka" ɗago wa tayi cikin kuka tace "Daddy na na tuna, Farooq ya tunamin da daddy na" ka san cewar su maman Sadiq sun san wace ce ita sai bata ɓoye musu waye Farooq ba da kuma abun da yake tsakanin su.
"Yayan Farooq yana ɗaya daga cikin abokan takarar daddy na, ya taɓa zuwa har gidan mu, sannan kuma akoi hotunan su a wayar daddy na sosai, na san Farooq nasan halin sa, duk yan gidan su na san su, da Farooq da yayan sa sun taɓa zuwa har gidan mu wajen daddy na" ta kai karshen maganar tare da sake fashe wa da kuka, sosai maman Sadiq da Sadiq suka shiga bata baki suna rarrashin ta, da kyar suka samu tayi shiru ta hakura.
Da sallama Hanan ta faɗo ɗakin da sauri taje ta rungumi Jehan, duk da zata girmi Jehan a shekaru amma sai tace "Aunty Nagode" shafa kan ta Jehan tayi murya a dashe tace "Ba komai Hanan" maman Sadiq ce ta tambaye su wai meke faruwa ne tsakanin Hanan da Alhajin nan, basu ɓoyewa maman Sadiq komai ba suka sanar da ita, sosai ta musu addu'ar kariya daga sharrin zina sai amsawa da amin suke.
Sannan Jehan da Sadiq suka fito suka nufi asibiti, dan maman Sadiq tace musu anyiwa mum aiki cikin nasara, amma har yanzu bata farfaɗo ba likitoci sunce zuwa gobe da safe zata farfaɗo, tun safe maman Sadiq na asibitin sai shabiyun rana ta dawo gida.
A tsakar gida suka wuce baban Sadiq da amarya, baban Sadiq yana zaune saman kujera yana tsinkewa amarya ganyen alayyaho zatayi musu miya, sosai Jehan ke jin haushin baban Sadiq kamar ta shake sa ya mutu kowa ya huta, wani kato da shi sai ya rinƙa biyewa yar amaryan nan tana sashi abubuwa kamar ƙaramin yaro.
Amarya da baban Sadiq ɗin har suna haɗa baki wajen cewa "Sannun ku" ko kallon su Jehan bata yi ba ta wuce, shi kam Sadiq mamaki ne yake hana shi amsa sannun nasu, Allah sarki Sadiq bawan Allah bai saba ba, sai yaga abun kamar a mafarki.
Sunyi Sa'a suna fita suka sami taxin suka hau zuwa asibiti.
Mu koma muje mu leƙa su Umaisha wato gidan Abbi mu dawo sai muga ya jikin mum.
💞KADUNA💞
Sai karfe 4 na yamma sannan su Umaisha suka dawo gidan, ba laifi Aunty ta samu sauki sosai da sosai, taji kwarin jikin ta saboda ruwan da aka kara mata
suna shiga Palo Umaisha ta wuce bedroom nasu, ita ma Aunty nata bedroom ɗin ta wuce, tana mai godiya ga Allah sanan tana yiwa Umaisha addu'ar fatan alkhari da fatan Allah ya tsare ta da tsarewar sa.
Umaisha na shiga bedroom nasu wayar ta ya fara kara, dogon tsaki taja kafin ta kalli Aafia dake baje saman gado tayi ɗai ɗai tana barci, a ƙule ta ɗauki wayar kamar zata sa ihu dan haushi.
Shiru tayi bata yi magana ba, shima Akil ɗin shiru yayi bai yi magana ba, almost 5mins suna manne da waya a kunne ba wanda yace da ɗan uwan sa uppan, da dai taga bashi da niyar yin magana sai tace "Hello" shiru yayi kamar ba zai amasa ba "Hello ina jin ka, kayi maganar da zakayi pls" ta sake faɗa tana hararar ɗakin nasu kamar Akil ɗin take gani a zahiri
Cike da wannan izzar nasa yace "Lallai dole na koya miki hankali har ni zaki cewa kina jina nayi magana na ba, tom ki shirya gobe zan yiwa Nigeria diran mikiya, da safiya ina garin Kaduna, kuma ina sauka ki sani gidan mijin ki zaki wuce" shiru tayi kamar bata ji me yace ba, yana sane tana jin sa sarai amma taki yin magana, katse kiran yayi zuchiyar sa na tafasa ji yake tamkar ya ganshi a gaban ta yanzu, ya karya ta ya zauna kuma yayi jinyar kayan sa, yana bala'i kaunar ta sosai, sai dai baya ɗaukan raini ko kaɗan, shiyasa duk wani maganar da zai mata da umarni yake maganar.
Ita kuwa yana katse kiran tayi wurgi da wayar saman gado tana faɗin "Dan wahala kawai, Allah ya kai mu goben in ga karshen rashin kunyar taka, yaro man kaza, gobe zan diro Nigeria ina zuwa zan ɗauke ki, eyee to sannu Sulman dan ba zance Abbi ba sai dai ince sannu baban Abbi" ta kai karshen surutan rashin kunyar nata tare da wucewa toilet dan tayi wanka, tun safe bata yi wanka ba, tana fama da Aunty a asibiti ti.
A ɓangaren Abbi da daddyn Jelly kuwa, ko da Abbi yaje yaji abun dake faruwa, sosai hankalin sa yayi mugun tashi, ya shiga damuwa fiye da tunanin mai tunanin, bai yi kasa a gwiwa ba, ya ɗauko daddy dan su dawo Kaduna tare har sai angane in da Jelly take, idan ba haka ba barin daddy shi kaɗai babban haɗari, sannan Abbi ya sake hurawa jami'an tsaron Kano wuta akan su kara kokari wajen neman Jelly, shiyasa ma basu baro Kano da wuri ba sai karfe 4 na yamma, dan sunyi ta zarya tsakanin police station da gida, duk da daddy bai da lafiya amma sai da ya dage yayi ta bin Abbi, tare sukayi ta zarya, daga karshe suka kama hanyar Kd, Abbi yana jin kamar zai yi kuka, yaso faɗa wa su Imran amma daddy ya hana shi, yace ya bar su su rubuta Exam nasu cikin kwanciyar hankali da nitsuwa, to Abbi yace sannan ya hakura da zancen faɗa wa su Imran ɗin har sai sun dawo.
A ɓangaren Jelly kuwa, yau dai anyi Sa'a da kan ta tayi jika jikan ta wato wanka bata fita ba sam, duk jikin ta sabulu da kumpa, Hajiya Turai tana palon bata ma san Jelly ta shiga wanka ba, yau ra'ayin kanta kawai tayi, da kan ta tayi wankan.
Tana fitowa daga toilet ɗaure da towel ta nufi gaban mirror kamar yadda taga hajiya na mata, ita da kan ta sai sosa jikin ta wajen bayan wuyar ta take, saboda ta lapka sabulu a wajen kuma bata wanke ba, sai sosa wajen tare.
Tana zuwa gaban mirror ta hau labta mai a kan sabulu da kumfa, gashi mai ɗin ma har da na gashi ta tabka dayawa dayawa, a takaice dai duk wani mai dake Wajen mirror sai da ta labka a fiskar ta zuwa jikin ta, sai kwailin take, har wani kyalli fatar ta keyi, fuskar ta taji mai har yana ɗiga
Akan mai ɗin ta ɗauko Foundation da beauty blending ta fara labkawa shima, bayan ta gama ta ɗauki kwalli ta saka a kasan idon ta, kamar wata dodo haka ta zama, bata sa lipstick ba dan yau taji bata ra'ayi, fiskar nan nata yayi wani faw kamar jan kosai ko in ce kamar an ɗaye fatar biri, ga wajen idon ta yayi bakin kirin da kwalli, baka ganin komai a fiskar ta sai idon ta farare tas, idan ka haɗu da ita da daddare sai ka suma saboda tsoro, ta labka mai a saman labkakken sabulu da kumfa ga Foundation abun ba'a cewa komai.
Bayan ta gama lafke lafken kwalliyar ta sai ta wuce wajen drawer kayan sawar Hajiya, dan duk wannan tsiya a bedroom ɗin Hajiya akayi shi, sai faman haɗa zufa take saboda uban mai da ta labka wa jikin ta.
Tun bata karisa wajen drawer ba ta cire towel ɗin jikin ta tayi wurgi da shi saman bed, taje ta buɗe drawer kayan Hajiya, abuna farko da ta fara cin karo da su shine breziya da pant, ɗauko pant ɗin Hajiya tayi, ta ɗago shi sama tana kallo, kara zaro ido tayi, a sukwane ta kalli waist nata wato kugun ta, taga pant ɗin Hajiya wargajeje gari guda, irin ta biyar sai su shige cikin pant ɗin, sai jujjuya pant ɗin take wai ko zata samu wajen rage masa girma
Da dai taga ba wajen rage masa girma, sai ta dura shi haka nan, dukka kafofin ta a site ɗaya ta haɗe su, wato a kafan pant ɗaya, sauran jikin pant ɗin da ya mata yawa kuma sai ta tattara ta ɗaure kamar mai ɗaure alale, ta cusa cikin ta saman kugun ta, sannan ta ɗauko breast, tayi shiru tana tunanin ya ake sawa, dan tabbas tana ganin shi a jikin Hajiya, sai dai koko ɗaya na breziyar Hajiya dai'dai yake da ya ɗauke breast nata dukka biyu, tashin sense, haka ta saka abun ta, koko ɗaya a breast nata ɗayan kuma a cikin ta, abun gwanin ban dariya, ga fuskar kamar an ɗaye fatar biri sai turo baki take.
Sake sanya hannun ta tayi cikin drawer ta ɗauko wani shaddan Hajiya fari tas, yaji aiki sosai ɗinkin half gown da zani, rigar kawai ta sanya wadda yazo mata har idon sahu na kafar ta, dan Hajiya Turai irin hamshaƙan matan nan ne, ga tsawo ga kiɓa, ta ko ina masha Allah, a gefen faɗi kuwa, Jelly kamar tsinke ta zama cikin rigar Hajiya, abun gwanin ban dariya, kayi dariya har cikin ka yayi ciwo.
Bayan ta gama duk wannan shirye shiryen nata, ta fito ta nufi palo da zumuɗin ta zata je ta nunawa Hajiya yau tayi abun arziki da kan ta.
Hajiya na zaune a palo tana shan black tea ɗin ta, Kamar daga sama Jelly ta faɗo mata babu ko sallama, duk kiba irin na Hajiya ganin Jelly bai hana ta tashi a ɗari kamar siririyar mace ba, idan ana zancen cetan rai wake ta wani zancen kiba, to wannan ma hakane domin a tunanin Hajiya aljana ce, sai faɗin innahu min sulaimanu wa innahu Bismillahirrahamanin rahim, a guje Hajiya fa ta zura tayi babban palon kasa tana ihu yau ga aljana a palon ta,
Ganin Hajiya ta zura a guje tayi waje ne yasa Jelly tayi tunanin kila wani abun tsoro Hajiya ta gani, ita ma ai sai ta kwasa a kuje tabi bayan Hajiya tana ihu dan kar abun tsoron da Hajiya ta gani ya kama ta, bata san itace abun tsoron ba
Hajiya kuma ganin Jelly na bin ta da gudu sai tayi tunanin Aljanar ke binta, dan haka sai ta kara karfin ihun ta dan jama'ar gidan su kawo mata ɗauki, ga firskar Jelly yasha daɓa daɓa da kayan make up sannan gashi ta sanya farar shadda, kuma burgujeje ya mata yawa, tana yawo a cikin kayan, ya kuke ganin abun zai kasance?.
Da gudun gaske Hajiya Turai ta faɗa ɓangaren su Afnan, tana gudu tana ihu, a palon part ɗin su ta isko Afnan da Maman ta suna zaune, ganin Hajiya Turai a guje yasa suka miƙe suna faɗin "Ke Hajiya Turai me hakan, zaki shigo mana ba sallama, bamu san... Basu kai ga karisa maganar ba Jelly ta faɗo cikin palon da gudu, Subhanallah zokaga yadda ake gudun cetar rai, Afnan uwar rashin kunya, tuni ta watsa a guje tayi cikin ɗakin ta ta banko kofa,
karo na farko a rayuwar Afnan da ta fara kiran sunan Allah data ga bone, ita kuwa maman Afnan ɗin, tsabar tsorata rungume Hajiya Turai tayi tana faɗin "Na shiga uku na lalace ki taimake ni Hajiya Turai, karki bari Aljanar nan ta kama ni" ita kan ta Hajiya Turai neman tsira take maman Afnan zata wani ce ta taimake ta, ture maman Afnan tayi ta bi bayan Afnan da dugu ta shige ɗaki, aiko itama maman Afnan bata yi kasa a gwiwa ba ta rufa musu baya, ita ma Jelly bin su da gudu tayi dan a tunanin ta wani abun tsoron suke gudun wa.
Jelly na shiga ɗakin Afnan, suka fasa ihu a guje suka sake bazama waje, still itama Jelly tabi bayan su tana kuka.
A takaice dai yau Jelly tasa gaba ɗaya familyn Abbo sun haɗu waje guda, wayan da basa shiri basa ko ga maciji yau sun haɗe waje guda saboda Jelly, dan ba wani part a cikin gidan dasu Hajiya turai basu faɗa da gudu suna ihu ba, duk kuma in da suka shiga sai yan part ɗin sun rufa musu baya suyi ta gudun cetan rai tare.
Daga karshe dai tsakar gida suka koma suna yar tsere da Jelly, suna gudun ta, ita kuma tana gudun abun da suke gudu, domin a ɗaukan ta wani abun suke