Showing 189001 words to 192000 words out of 194715 words
sosai yana mayar da hankali.
Sai karfe 11 na dare sannan su Sadiq suka yiwa maman su da Jehan sallama suka fito, har bakin kofar ɗakin maman Hanan suka raka Hanan sannan suka wuce ɗakin su shida Yusuf Sha'aban kuma baya nan yaje garin maman sa duba ta
Su Sadiq suna fita Jehan ta tashi taje tayi wanka Allah sarki yanzu har ta saba da wanka da ruwan sanyi, bayan tayi wanka ta fito ta dawo ɗakin maman Sadiq, already maman Sadiq ta jima da yin barci abun ta, kayan barcin ta ta ɗauko riga mai laushi da dogon wando ta saka a jikin ta ta ɗauki mayafin lulluɓa da maman Sadiq ta bata ta kwanta ta lulluɓe jikin ta, sai bayan ta kwanta sai ta tuna kamar basu yi Sallah ba, tana kokarin miƙewa sai kuma ta tuna ashe sunyi a asibiti, addu'ar barci kawai tayi ta kwanta, ta lumshe ido tana tunanin Rimsha tana hawaye kamar kullun har barci yayi awon gaba da ita.
Asuba ta gari. Mu leƙo Washington DC mu dawo
# 💞WASHINGTON DC💞
80:00am
Slowly ya waro dara daran blue eyes nasa masu ɗauke da barci, kasan cewar idon nasa akoi alamar barci bai isshe shi ba, sai idon nasa ya kara kyau dan yayi yanayi da sleeping eyes, wani azaban duka kirjin sa tayi lokaci guda wadda yasa yaji barcin ta watsake ta sake sa, miƙewa yayi zaune a tsakiyar gadon ya dafe saitin faffaɗar kirjin sa, da sanyayyar murya mai bala'i daɗi da kwatar da hankali mai sauraro yace "Meke shirin faruwa da nine" dan bai taɓa jin makaman cin wannan bugun zuciya ba a tattare da shi, shiru ya ɗan yi na ɗan lokacin kafin ya yaye bargon jikin sa a hankali ya zuro zara zaran kyawawan fararen kafafunsa kasan bed ɗin sannan ya miƙe ya nufi toilet.
Wanka yayi ya fito ya shirya cikin wani haɗaɗen jeans mai bala'i kyau da tsada launin baki da High neck sleeve shirt launin blue kasan cewar rigar ta kama jikin sa sosai, hakan ya bayyanar da kakkafar suran kirjin sa, faffaɗar kirjin nan nasa abuɗe take sosai cikan damatsan hannun sa yasa faffaɗar kirjin nasa ta kara buɗe wa sosai, har wannan bul bul ɗin breast nasa kana iya hangowa saboda kama shi da rigan tayi, ba karamin kyau kayan suka masa ba, kamar dan shi akayi su, Winter Sports Hat ya sanya a kan sa, bayan ya ɗaure dark black curly hair sa, ya fito yayi kyau over ita ma hulan ta masa kyau sosai, sai dai ya bar wannan ɗan guntun gashin gaban goshin nasa a waje bai shigar da ita cikin hulan ba, fuskar nan nasa a ɗaure take kamau kamar kullun sai dai na yau ma tafi na kullun, dan ina ga yau idan sukayi ido huɗu da mai karamain zuciya nan take zuciyar zata buga ya mutu awajen saboda tsoron yadda fuskar lion tayi yau abun ba'a magana ya wuci tunanin duk wani mai tunani, sai tashin fitinannen kamshi yake, hannun sa na ɗaure da diamond watch nasu na Triplets, kyawawan kafafun sa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal wadda a kalla kuɗin sa ya kai $76000, kasan cewar takalmin launin baki ne sai yayiwa farar kafar sa bala'i kyau, wayar sa da kuma laptop na sa ya ɗauka ya nufo waje, yana taku irin na manyan jarumai, ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa kasan cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma lafiyayye kakkafa ne ke tinkaro ka.
Lokacin da ya fara sako kafar sa a benen sauƙowa palon kasa, ji kake tsit duk wani halitta mai rai dake cikin palon ya nitsu tsit sun sha jinin jikin su, wasu daga cikin bodyguards kam jikin su har kerma yake saboda tsoron sa,
John, Jay, uncle Herry, Tga, gaba ɗaya suna palon kasan, sun zauna kamar masu jiran wani abun kowannen su yana ta faman latsawa waya cikin kwanciyar hankali, lokacin da kamshin perfume na lion ya kai musu karo a hancine yasa sukayi saurin ajiye wayoyin nasu suka nitsu suna satar kallon sa ta kasan ido dan shi baya son yawan kallo, sai yaga kamar wani abu kake kallo a jikin sa hakan yasa idan ya kama ka kana kallon sa sai ya maka hukunci mai tsanani.
wucewa yayi ko kallon in da su John suke bai yi ba ya nufi hanyar ficewa daga palon, har suna haɗa baki wajen rige rigen ɗaga masa gaisuwa, bai amsa gaisuwar ko ɗaya daga cikin suba dan dama ba amsawa yake ba sai dai ya ɗaga musu hannu dan magana na masa wuya, to yau kam ma ko hannun basu samu arzin ya ɗaga musu ba dan hankalin sa kusan baya tare da shi.
Dai dai zai fita palon yajiyo muryan dad da Michael har suna haɗa baki wajen tambayar sa ina zai je, juyowa yayi yazo ya rungumi daddy tare da mannawa daddy kiss a kumatu kasa kasa yace "I need your prayer my dad" daddy sarki saurin razana ya ɗauka yaki Romeo zai tafi nan take jikin sa ya fara kerma cike ta tsoro yace "Where are you going my lion?" Kasan cewar sun san halin dad sai bai faɗa masa abun dake faruwa ba ya basar da maganar ta hanyar cewa zai je wajen friend na sa ne dad karya damu kawai ya yi musu addu'a, ajiyar zuciya dad ya sauke kafin yace zai faɗawa pastor ya musu addu'a, wucewa Romeo yayi zai tafi, sai kuma ya sake juyowa ya shafa kan Micheal dake tsaye yana kallon su, shi dai Michael duk da ba ilimi gare saba yasan ba lafiya ba, dan yana ji hakan a jikin sa, daman kuma ko ciwon kai ɗaya daga cikin triplets yake tofa sauran sai sunji a jikin su, hakan yasa yau tun da suka tashi barci zuciyar Romeo ke bugawa da karfi karfi, shi kuma Michael yana fama da faɗuwar gaba da kasala wadda ta haifar masa da ciwon kai, sai Allah kaɗai ya san shi kuma James me yake ji.
Wucewa Romeo yayi cikin sauri ya fice daga palon, yana fita rundunar jinga jibgan sojojin sa suka fara sara masa, sunyi layi a bakin kofar palon da alama jiran fitowar sa suke.
Wuce su yayi ba tare da yayi wani alama ma da zata nuna ya gansu a wajen ba, kai tsaye wajen shirga shirgan motoncin da aka jera musu ya nufa, motoncin manya manyan masu numfashi, na sojoji guda 8 sai wata dan kareriyar motar fara tas har wani kyalli take kirar Bugatti La voiture wadda a kalla kuɗin ta ya kai $18.7 million, jikin motar kawai abun kallo ne dan ta tsaru iya tsaruwa, idan ka shiga cikin motar nan sai ka rantse da Allah a cikin manya manyan haɗaɗun palo irin na manyan shuwagabannin kasa kake, saboda haɗuwa irin na cikin ta, kujerun motar irin manya manyan kujerun nan ne masu mumfashi wadda suka amsa sunan su kujeru, har wani lotsawa ciki suke idan ka zauna a kan su, sai wani fitinannen kamshi mai bala'i daɗi ke tashi daga cikin motar nan, saboda ansan mamalakin motar ma'abocin son tsabta da kamshi ne shiyasa komai nasa yake kasan cewa mai kamshi da tsabta.
Da taku irin na jarumai sadaukan yaki ya nufi motar, yayin da jibga jibgan sojojin sa ke take masa baya
Wani jibgegen katon Baturen soja fari tas da shine yayi gudu ya sha gaban lion ya buɗe masa gidan baya na wannan farar Bugatti La voiture noira, gently lion ya shiga cikin motar ya zauna, dan shi komai nasa a nitse yake yin sa, daki daki yake bin komai
Sai da wannan sojan ya ɗaga hannu ya sara masa sannan ya rufe kofar motar
Ji kake dip dip sojojin sa suka nufi motoncin su da gudu suka haye saman bayan motoncin nasu, wannan sojan daya buɗe wa lion kofar mota ya shiga, shi ya ja motar lion ɗin.
A tare motoncin suka tashi suka nufi gate ɗin fita gidan, duk in da suka wuce sara musu sojojin dake tsakar gidan suke.
Suna fita wajen gidan suka saki jiniya kamar yaki zasu tafi, abun da ya sa basu saki jini tun a cikin gida ba, saboda daddy, yana jin jiniya zai ruɗe yace yaki Romeo zai je ko wani wajen, shiyasa suka bari sai da suka fita waje sannan suka saki jiniyar.
Duk wata mota ko abun hawa dake hanya kaucewa suke su bawa tawagar jerin kwanon motocin The general of the army hanya, wasu ma jiniyar kawai suke ji tun daga nesa, tun bai iso su ba suke sauka daga kan titi da abun hawan su su bada hanya
Ko da tawagar motocin suka zo wajen fitillar bada hannu, a sukwane mai kula da fitillar wajen ya basu hanya dan su wuce dan yasan ma ko bai basu hanya ba ba tsayuwa zasu yi ba, dan in tawagar motocin The general of the army suka tinkaro waje tofa sai dai ku ku hakura sai sun wuce.
Cikin kwanciyar hankali yake danna laptop nasa ga sanyin Ac na ratsa shi, sai faman cizan lallausan laɓɓan sa yake, ga lips ɗin nasa ya kara yin jawur kamar yasa lipstick saboda ciza su da yake, duk wannan latsa laplop da yake hankalin sa na can duniyar tunani ina James yaje, dan shi har yanzu yaki yardan wa zuciyar James criminal ne, duk lokacin kuma daya tuna James sai yaji zuciyar sa ta bada dum dum ya rasa me matsalar, kokarin sake bin diddigin layin James yayi abun mamaki sai yaga layin a kashe bayan a kashe ma an soketa daga hanyar sadarwa gaba ɗaya, cike da tashin hankali ya ciro wayar sa ya fara kiran layin, kwata kwata layin an suke ta, zaro idon sa waje yayi yana tunanin meke shirin faruwa ne, taya za'ayi ace an soke layin James gaba ɗaya bayan jiya da daddare lafiya lou layin take, to me ya faru da James ɗin?.
Yana cikin tunani bai san lokacin da suka isa *Dulles International airport* ba sai da yaga jibga jibgan sojojin sa sun kewaye motar sa da manyan bindigun su, sannan ya farga, sojan daya tuƙo sane ya fita ya buɗe masa kofar motar suka tsaya cirko cirko suna jiran fitowar sa
Ko da aka buɗe masa kofar motar ya ɗauki tsawon good 30mins zaune acikin motar kafin ya zuro kafafun sa waje a nitse ya fito ya wuce gaba, jiga jigan sojoji masu ji da lafiya wadda da ka haɗu da irin su gara ka haɗu da zaki koba komai shi zaki cinyewar lokaci ɗaya zai maka, sukuma fargana da faɗuwar gaban ganin sune zai yi ta sumar da kai kana farfaɗowa har ka mutu, wayan nan jiga jigan sojoji su 8 suka take wa lion baya zuwa ciki,
Abun mamaki duk wayan nan sojojin mutuwar tsoron lion suke, suna razana jama'a a gari sukuma fuskar lion na razanar dasu yana sanya hantan cikin su kaɗawa.
Bincike lion yaje yayi a kan wani jirgi James ya hau, ba karamin mamaki lion yayi ba jin cewa jirgin Europeans country ya hau, a Europeans ɗin ma jirgin kasar Spain ya hau, Spain lion ya mai maita a ransa
Shiru yayi yana tunani abubuwan sun haɗu sun cakushe masa yanzu ba binciken a kan James criminal ne ko ba criminal bane ya kama shi, bincike a kan ina James yake me yasa aka soke layin sa daga hanyar sadarwa wani hali yake ciki, shine abun da yake gaban lion yanzu, abun da ya sawa ran sa dai tabbas James yana cikin tashin hankali da damuwa a duk in da yake, kuma yana bukatar taimakon gaggawa, dan baya cikin koshin lafiya ba abanza kirjin lion ke yawan dukan uku uku time to time ba, sannan ga Michael can a gida yana cikin faɗuwar gaba hakan har ta hadda sa masa ciwon kai da kasala.
Juyowa lion yayi suka koma cikin motocin su suka musu key suka bar airport ɗin zuwa gida, yanzu babban damuwar ma shine ya rasa ta ina zai fara bincike a kan James domin bashi da wata maka ko guda ɗaya da zai ce ga wannan zai riƙe ya zama masa makami da zai yi bincike ya gano in da James yake.
Kamar yadda jerin gwanon motocin suka fita gida haka suka koma sukayi parking a in da suka taso, sojan daya tuka shi, shiya fito ya buɗe masa kofar mota, a wannan karon da sauri lion ya fita zuwa cikin Palo, kai tsaye part nasa ya nufa
Yazo zai hau bene dai dai lokacin Tga zai sauko, a guje Tga ya koma baya ya bashi hanya, dan dama already sun sani idan lion na saman staircase ba mai hawa har sai ya sauka ya tafi
Yana shiga bedroom nasa ya fara aiki gadan gadan dan sanin ina ɗan uwan sa jinin jikin sa yake wani hali kuma yake ciki, ya manta ma da batun zuciyar sa na zargin James ya dukufa aikin neman sa kawai.
Misalin karfe sha ɗaya na rana zaune suke a palon kasa gaba ɗayan su ban da lion dan shi ba'a sa shi ma a lissafin su saboda kwata kwata baya shiga cikin su, idan yazo waje ma saboda tsoron sa lallaɓawa suke su gudu, kuma ba dukan su yake ba ba zagin su yake ba, wannan fusataccen fuskar nasa suke mutuwar tsoro da kuma kwarjinin da Allah ya masa,
Wani sojane ya shigo cikin palon pastor na biye da shi a baya, ma'ana sojan yayiwa pastor jagora zuwa cikin palon kenan
Da murna dad ya miƙe yaje ya taro pastor sai dariya yake, ɗaure fuska Michael yayi yana hararar pastor kamar yaje ya shaƙe sa yake ji, shikuwa pastor sai washe baki yake, wai ya biyo sahu yaji ko lafiya two weeks basu zo church ba, daddy ya yi imani da wannan pastor nasu sosai jikin sa sai kerma yake ya shiga bawa pastor hakuri, cike da isa pastor yace to ba damuwa yanzu dai su shirya su wuce church ɗin tare da shi tun da yau Friday akoi Church, nan fa Michael yace pastor bai isa ba shi babu in da zai je kuma daga yau ma ba zai sake zuwa church ba har ya mutu, nan fa rigima ta kauri, pastor yace zai tsinewa Michael daddy jikin sa sai kerma yake yana hawaye yana rokan pastor yayi hakuri karya tsinewa Michael, shi kuwa Romeo yana part nasa ya dukufa wajen neman ina ɗan uwan sa ya shiga.
Ganin pastor ya saka daddy kuka hawaye sharɓa sharɓa ne yasa Michael ransa ya ɓaci ya sakarwa pastor wayan nan mayun kwarin nasu na Triplets, ihu pastor ya fara yi yana birgima a kasa, saboda tsanar da Michael yayiwa pastor har da kara masa da ƙudan zuma yayi, Tga, John, Jay suna ganin Michael ya sako kwarin nan sukayi ta kan su dan sun ɗanɗana a baya basu ji ta daɗi ba, uncle Herry ma ba'a barshi a baya ba wajen gudu, kafa me naci ban baka ba, ai a miliyan kowa yayi part nasa, bayan sun shiga part nasu ma sai da suka kara da danna wa kofofin key dan karma kwarin su biyo su.
Iya pastor kawai kwarin suka farma, daddy ya tsorata sosai Allah sarki shi damuwan sa kada pastor ya tsinewa Michael rayuwar sa ta lalace shi yake wa kuka, amma dan iskanci irin na Michael ana neman masa sauki wajen pastor ya kara laifi kan laifi ya sakar wa Pastor wannan bala'i mai kama da tashin duniya.
Daddy na kuka gwanin ban tausayi ɗan tsohon nan, haka ya haura sama da gudun ya nufi part ɗin Romeo dan ya kira shi yazo ya dakatar da kwarin nan karsu kashe pastor, dan yayi ta rokan Michael, Michael yace ba zai dakatar da su ba sai dai su kashe pastor ɗin.
Ganin daddy na kuka ba karamin ɗagawa lion hankali yayi ba, a sukawane ya miƙe ya taro daddy yana tambayar sa lafiya, cikin kuka daddy ya sanar da shi abun da Michael ya aikata, rai a matukar ɓace ya zaunar da dad saman bed nasa sannan ya nufi Palo, daman ga damuwa sun masa yawa ga batun James ga bincike a kan asibiti masu sai da koda da sassan jikin maza, ga bincike a kan kontenan mai ɗauke da mata daya kama jiya, abun ya haɗe masa lokaci guda
Yana sauƙa palo rai a matukar ɓace ya ɗauke Michael da wani gigitacen mari wadda yasa Michael zubewa kasa a kan gwiwowin sa yana ganin wasu taurari masu hasken gaske suna gilmawa ta cikin idon sa, saboda azaban zafin marin ma ya kasa kuka, daman hausawa na cewa duk ciwon da akewa kuka bai kai ciwo bane, idan ya kai ciwo neman kukan ake a rasa, to wannan ma hakane Michael dai ya nemi kukan sa ya rasa
Romeo kuwa bai kara bi ta kan ba dan sauri yake aiki na gaban sa, dakatar da kwarin yayi sannan ya koma sama da sauri, dad kuma yana zaune in da Romeo ya zaunar da shi.
Allah sarki pastor ya jama kan sa bala'i duk fuskar nan tasa ta sunduma luhu luhu kamar an hura palo palo, abun ka da fatar Bature jikin sa yayi jajir kamar jini da kyar da kyar yake fitar da numfashi.
A ɓangaren Michael kuwa good 40mins ya ɗauka a wajen zube a kan gwiwowin sa kafin ya samu marin Romeo ya sake sa, sai lokacin da marin ya sake sa ne ya samu damar fitar da zafafan hawaye daga idon sa, da kyar ya miƙe ya fice daga palon, bai ɗauki mota ba ya fice daga gidan da kafar sa, yana tafiya yana hawaye yana tunanin yau shi Romeo yayiwa wannan marin gaskiya dole ya bar musu duniyar baki ɗaya tun da basa son shi, da wannan tunani ya hau babban hanya wadda manya manyan motocin ke wucewa wai shi zai mutu, yana tafiya yana hawaye, duk motar da tazo da kyar take iya kauce masa, sai zagin sa wasu drivers ɗin suke idan suka kauce masa da kyar, shi kuma ko ajikin sa dan yace mutuwa zai yi kawai tun da ba mai son shi, Allah sarki bawan Allah matsalar daga kwakwalwan sane ba daga shi bane
Wata