Showing 87001 words to 90000 words out of 194715 words

Chapter 30 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

974

yayi wa Pasto church ɗin ma sai an yi da gaske yake zuwa kuma baya bawa Pasto ko biyar, idan yaje church ɗin ma baya sauraron komai da suke faɗe, saboda gani yake ba amfani, dan bai da ilimi ba karatu yayi ba shi gani yake ɓata masa lokaci kawai suke da surutun banza, kan sa emty yake duk mate na shi a School wasu sun zama lectures wasu kuma sun kama aikin yi amma shi yana nan sai jagaliyanci ya sa a gaba, wan nan dalilin ne yasa ba abun da ya sani sai kashe kuɗi da zuwa party clubs da abokan sa, hakan yasa yake kallon Pasto a matsayin mahaukaci mara aikin yi, shi kwanta kwata bai yarda da wasu addinai ba a cewar sa duk adinin nan ɓata lokaci ne.

Bari mu leƙa Nigeria mu dawo


*KADUNA*

Har bakin hanya Rufaidat ta rako Aafia sai murna take tana zuba mata godiya, ita kuma Aafia sai fatan alkhari take wa Rufaidat da fatan ta tsaya tayi karatu da kyau, dan karatu shi ne mutun, anguwar nasu shiru ba hayani sosai, shi kan shi bakin hanyar ba jama'a sosai, kafa ta ɗauke saboda ba babban hanya bane, irin kana nan titin nan ne dake ratsawa ta cikin layi

suna tsaye a bakin hanya suna jiran taxi yazo Aafia ta hau ta koma gida, wata dankareriyar mota kirar *Mercedes-Benz* tazo tayi parking a gaban su, a hankali mamallakin motar ya sauke glass ɗin motar sa, babban Alajine mai ɗan yawan shekaru, dan a kalla zai kai, 45 to 47 years, sanye yake cikin manyan kayan hausawa da hula, yayi shiga irin ta kamala da cikar bahaushe, nan take Aafia ta ɗaure fuska kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, ita kuma Rufaidat sai washe baki take an ga mai kuɗi.

"Sannun ku yan mata" Alhajin ya faɗa yana washe baki, cikin sauri Rufee tace "Yauwa Alhaji Sannun ka" ita kuwa Aafia ko kallon in da yake ba tayi ba dan a koi ta da jiji da kai over "Yan mata idan ba damuwa ku shigo na kai ku in da zaku je mana, dan baku yi kalar tsayuwa cikin ranar nan ba" yana magana yana kallon Aafia, kara washe baki Rufee tayi tace "Kawata ce kaɗai zata tafi ita zaka ragewa hanya ni kuma ga gidan mu a nan idan ka dawo" a sukwane Aafia ta juyo tana kallon Rufee da mamaki, wato ita rufe har tallan kan ta take, shi kuwa Alhaji washe baki yayi tare da shafa gemun sa yana faɗin "Daman ai kawar taki ita ta tsai dani" hannu Aafia ta miƙawa Rufee suka gaisa, san nan tace "Sai kin zo gida ko sai mun haɗu ga taxi nan zuwa na wuce"

"Wow gaskiya izzar ki ya kara burgeni ba kaɗan ba, hakan ya sa naji na kara son ki" cewar Alhaji, ita kuwa Aafia wucewa tayi abun ta, ta tari taxi ɗin da yazo ta shiga, cikin sauri Alhaji ya buɗe motar ya fito waje ya nufi wajen taxi ɗin yana faɗin "Dakata malam, haba yan mata, dan Allah ki tsaya mana, minti biyu kawai nake bukata daga gareki" a kule Aafia tace "Kai malam ko in ce baba, kai baka ji kunyar tare yarinya sa'ar yar cikin ka kace kana so ba, to idan kai baka san kunya ba ni na san shi, kai mai taxi muje!!!" Ta kai karshen maganar cikin faɗa,
kunna taxi ɗin mai taxin yayi suka bar wajen sai magana Alhaji yake amma Aafia taki kula shi

Sai da taxi ɗin ya kurewa ganin sa san nan ya juya cikin sauri ya koma cikin motar sa, cikin rangwaɗa Rufee tace "Alhaji ai daman ni nasan ba zata saurare ka ba, saboda bata da mutunci ga girman kai da izzar banza, ga rashin kunya da rashin girmama manya, amma ni ba ruwana ina girmama manya musamman irin ka mai kima da daraja" kakalo murmushi dole Alhajin yayi kafin yace "Nagode" tana kokarin sake magana sai ga yayan ta Yusuf, a sukwane ta wuce ta nufi gida ba dan taso ba, dan tana bala'i tsoron Yusuf, bashi da wasa ko kaɗan

shi kuwa Yusuf cikin fushi ya nufo Alhaji, yayin da Alhajin ke kokarin kunna motar sa yabi bayan Aafia.

"Kai malam wanene kai?" Cewar Yusuf, shiru Alhajin yayiwa Yusuf bai yi magana ba, kasan cewar Yusuf mutun ne mafaɗa ci hakan yasa ya fara faɗa "Wato kune irin Alhazawan dake ɓata yaran talakawan ko? To wlh ƙanwata tafi karfin ka idan ka kuskura na sake ganin kafar ka a layin nan wlh sai ran ka ya ɓaci bar ganin kana da kuɗi, maganin ka zan yi, a kan kanena bani da mutunci" ba karamin ɓatawa Alhajin nan rai Yusuf yayi ba, gashi ya dakatar da shi daga bin Aafia, cikin fushi ya juyo da idon sa kan Yusuf, nan take idon nasa suka sauya launi suka koma light purple mai bala'i haske kamar torchlight, hasken na haska face ɗin Yusuf, Yusuf ya zube kasa a wajen sai gawa, a guje Alhaji ya ja motar sa ya bar layin.

sai da ya ɗan yi nisa san nan ya dakatar da motar tasa tare da canza kalar idon sa ya koma irin na mutane, fari da baki, haɗe da canza kalar face nashi da jikin sa dukka ya zama matashi mai jini a jika wadda ba zai wuci 25 years ba kyakkyawa fari tas da shi kamar balarabe, san nan ya ja motar yabi hanyar da su Aafia suka bi, ko zai gan ta.

*KANO*

Daddyn Jelly ya shiga damuwar da har ta jawo masa rashin lafiya mai tsanani dan shi a gaskiya ba zai iya cin amana ba, gashi yana tsoron video sa ta fita wa duniya, tun jelly bata iya gane daddyn ta na cikin damuwa har tazo ta fara ganewa, duk in ta tambaye sa sai yace mata ba komai, haka ta ci-gaba da hakuri, gashi su biyu suke rayuwar su sai Nana da Zuwaira masu aikin su, yan uwan maman Jelly suna zuwa time to time, iyayen Mahaifiyar Jelly sunyi sunyi a kan daddyn Jelly ya auri kanwar Hajiya Umaima wato mum ɗin Jelly amma yaki yadda yace shi baya so, ba zai iya rayuwa da kowa ce mace ce ba, dan shi gani yake ko kan kanwar Hajiya Umaima ɗin ma ba zata iya kula masa da Jelly ba, yafi son ya kula da kayan sa shi da kan sa, shi yasa ya zaɓi suyi rayuwar su su buyu, ko hutu baya barin Jelly taje wajen family maman ta baya son komai ya raba ta da gida in ba school ba.


*Washington DC*


Tun John na iya gudu har ya kasa dan already dawakan ma sun riga sun jima da wuce sa, shi kuma Romeo ya wuce ya bar wajen tun tuni, yau Tga ne ya hukun ta John, ya hora John iya horar wa, kafin ya kyale sa tare da yi masa kashe di a kan kar ya sake sha wine ya shigo cikin gida a buge, idan zai sha ya nitsu waje guda ya sha kuma ya kwanta a wajen yayi barci har sai ta sake sa, gidan su gidan mutun ci ne a kasar dan haka ya kiyaye shan wine yana yawo a sakar gari kamar mahaukaci kar ya ja musu zagi da zub da mutunci, sosai John ya niku tillis da kyar ma yake magana, sai murna Jay yake an masa magani John yau, da haka suka watse kowa ya nufi part na shi.

*12:30 am*

Duniya duk suna barci shi kuma Romeo a lokacin bodyguard ɗin sa ke serving nasa abinci, kamar wani aljani, while shi kuma James yana kwance saman katafaren gadon sa yana aiki a system na sa, yana shirya ta yadda zai sa mai gidan sa ya janye daga aikin kashe GAR.

Zaune Romeo yake saman table chair na palon kasa ga jibga jibgan Bodyguard guda 24 a kan sa 12 ta gefen nan 12 ta gefen nan, kamar dai yadda suka saba, palon gaba ɗaya gauraye yake da hasken kwayayen lantarki dake manne a saman POP palon, har wutan jikin staircase a kunnen suke, shi yasa palon yayi haske over, hakan ba karamin kara kawata palon yayi ba gwanin kyau da ɗaukan hankali, ga sanyin Ac da kamshi air freshener da ya haɗu da kamshin perfume ɗin Romeo hakan ya bada wata irinyar fitinanniyar kamshin mai kwatar da hankali mai shaƙa

sanye Romeo yake da kayan barci, riga fara kal mai jikin bargo zuwa gwiwar sa mai ma ɗauki a tsakiyar rigar, while gaban rigar a buɗe, ga wani kwantatciyar dark black gashi mai tsantsi da sheki kwance a saman faffaɗar kirjin nasa, soft skin na shin nan sai sheki yake kamar bai taɓa fita waje ba, sai faman lumshe dara daran blue eyes na shi yake kamar mai jin barci, lallausan lips na shin nan sun kara zama red sosai saboda ya ɗan cizasu kamar wadda wani abun ya ɓata wa rai, hakan yasa suka kara ja sosai, lips na shin sun kasan ce kamar audiga saboda laushi shi yasa da ya ɗan ciza su kaɗan sai su kara ja.

Duk wani abun da zai buƙata bodyguard ɗin sun zuba masa a plate kasan cewar sun san koda sun tambaye sa ba amsa musu zai yi ba, hakan yasa daddy ya faɗa musu abubuwan da yafi buƙa ta da yazo dining table su zuba masa, shi yasa da yazo suke serving na shi kawai.

Almost 20 mins yana zaune yana latsa waya sai faman lumshe dara daran ido sa yake yana ɗan cije lallausan lips na shi, ga abinci kuma bodyguard sun zuba masa.

A ɓangaren James kuma bayan ya kammala shirye shiryen sa sai ya kira mum ɗin su a waya, dan su gaisa, duk da ba wani son ta yake ba kuma yana jin haushin ta hakan baya hana shi, duk bayan 1 year ya kirata su gaisa, ba ƙaramin daɗin hakan take ji ba, saboda son da take musu amma shi Romeo da Michael da Tga, da dad, uncle Herry, ko da wasa basu taɓa kiran ta a waya ba ba kuma su taɓa kusan tar in da take ba, Mahaifiyar su baturiyar cikin New York ce, a halin yanzu ma tana zaune a can New York ɗin, tsakanin Washington DC da New York babu wani nisa sosai amma ko da wasa basu taɓa tunanin ma su kai mata ziyara ba, sun tsani ganin ta basa son ta ko kaɗan ta sanadiyar haka ne Michael da Romeo suka tsani dukka mata, dan su sunfi tsanar ta.

Sai daɗi mum take ji da James ya kirata, suna gaisawa ya tambaye ta ko tana buƙatar kuɗi, cikin murna tace masa a'a kiran da ya mata ma yafi mata komai a duniya, yana jin bata bukatar komai ya katse kiran sa, tayi kokarin kiran sa amma ina bata same sa ba, dan in ya kira ta suna gama waya yake sata a blacklist dan ma kar ta sake kiran sa, dan ba wani son ta yake ba kawai tana ɗan bashi tausayi ne shi yasa yake kira yaji ko tana bukatar wani abun ko kuɗi


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞


TRIPLET'S💞 20





https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo


*THE BEGINNING*



💞*STAR LADY*💞




EPISODE 20




Sai daɗi mum take ji da James ya kirata, suna gaisawa ya tambaye ta ko tana buƙatar kuɗi, cikin murna tace masa a'a kiran da ya mata ma yafi mata komai a duniya, yana jin bata bukatar komai ya katse kiran sa, tayi kokarin kiran sa amma ina bata same sa ba, dan in ya kira ta suna gama waya yake sata a blacklist dan ma kar ta sake kiran sa, dan ba wani son ta yake ba kawai tana ɗan bashi tausayi ne shi yasa yake kira yaji ko tana bukatar wani abun ko kuɗi


Ajiye wayar yayi saman bedside drawer ya ɗauki remote ya kashe wutar ɗakin gaba ɗaya, san nan ya kunna lamp na saman bedside drawer, tare da jan bargo zuwa saman kirjin sa ya lumshe ido, amma ya kasa barci sai tunani yake a kan yadda zai ɓullowa ramarin aikin da a ka sa shi na kisan GAR, dan gaskiya zai iya kashe kowa idan suka bashi aikin hakan amma ban da GAR, ba zai iya wan nan aikin ba, ko wani ya gani zai cutar masa da ɗan uwan sa na jini sai in sa karfin sa ya kare bare kuma a ce shi da kan sa kai ina hakan ba zai yiwu ba, gashi kuma baya jin kamar zai iya fita daga kungiyar nan nasu, dan yana son aikin sosai da sosai, Yasan cewa shi ne yake da hanya mafi sauki da zai iya kashe GAR cikin ruwan sanyi ba tare da shan wahala ba, amma ko a mafarki yayi mafarkin hakan to idan ya tashi sai ya hukun ta kan shi, yanzu shi babban damuwar sa a nan shi ne idan shi yaki yarda ya kashe GAR to fa zasu bawa wani aikin, gashi kuma GAR bai damu ya yawo da sojoji ko bodyguard sosai ba kasan yana ganin kamar ba wata damuwa, amma time to time yana fita da sojoji sosai. Haka dai ya rinƙa tunane tunanen sa na neman mafita har barci yayi awon gaba da shi.

A ɓangaren Romeo kuwa, hankali sa kwance yake ɗaukan fruit da bodyguard suka yayyan ka masa suka shake masa plate da su, hankalin kwance cikin nutsuwa yake ɗauka yake kaiwa ɗan ƙaramin bakin sa, a hankali yake motsa laɓɓan sa kamar bai son tauna abu haka yake cin fruits ɗin, da yaci kaɗan bodyguard ɗin jikin su na kerma zasu muƙo masa tissue paper, wani lokaci ya ansa ya goge bakin sa wani zubin kuma yayi kamar bai gan su ba, haka zasu mai da, suna tsai tsaye kamar wasu saƙaguna ko alamar barci babu a idon su, shi kuma yana zaune sai latsa waya yake yana cin fruits a hankali cike da class da izza.

Sai 01:00 am, san nan Romeo ya miƙe cikin nitsuwa ya nufi bedroom na shi, yana tafiya suma bodyguard ɗin suka nufi waje dan suje su kwanta su hutu, kasan cewar dama Romeo shi ne mutun na karshe dake cin abinci kullun, dan wani lokaci ma sai 2 na dare yake cin abinci kamar wani aljani sai dai ba wani abun kirki yake ci da daddaren ba baya wuce fruits ko kuma salmon, to da zarar yaci abincin daren sa ya wuce bedroom suma bodyguard ɗin zasu wuce nasu bedroom ɗin sai kuma da safe idan za'ayi breakfast sai suzo wajen table ɗin dan suyi serving masu cin abinci, sojoji uku ne ke girka musu abincin a gidan, idan sun gama kirkin su Romeo sai su fara girkin nasu bodyguard da sauran sojojin dake gidan, mai shara da mopping a gidan dukka sojiji ne, duk wani aiki na gidan jibga jibgan sojoji masu razanar da zuciyar maza ke yin sa.

Romeo na shiga bedroom na shi ya haye katafaren lallausan gadon sa mai kama da audiga, daman sai lumshe dara daran idon nasa yake alamar yana jin barci, bedroom ɗin gauraye yake da gasken wuta lantarki launin sky blue, hakan ba karamin karawa bedroom ɗin kyau yayi ba, kashe wutar ɗakin gaba ɗaya yayi har da na jikin furniture ɗin da lamp na saman bedside drawer duk ya kashe su dan shi bai son haske idan zai yi barci, nan take ɗakin ya gauraye da duhu, remote ya ɗauka ya kara gudun Ac san nan ya ja lallausan bargon sa mai kama da audiga zuwa saman faffaɗar kirjin sa, ba jimawa barci yayi awon gaba da shi.

*NIGERIA*

*KADUNA*


Matasan unguwa ne suka fito yuka samu Yusuf yashe a kasa ya rasu, sosai suka sha mamaki da jimami abun da ya faru, wasu daga cikin abokan sa sai cewa suke yanzu fa suka rabu da Yusuf lafiyar shi kalau, wasu kuwa cewa suke an ya ba wani abun ne ya samu Yusuf ba, haka dai jama'a sukayi ta ceceku ce.

Sai washegari a kai masa sutura a ka kaishi makwancin sa wato gabarin sa, sosai mahaifiyar su Rufee tashiga damuwa da tashin hankali dan Yusuf shi ne karfin gidan, ita kam Rufee bata wani damu sosai ba kuka iya na yan mintoci tayi daga nan ta dasa daga in da ta tsaya, ba wanda ya iya gane me yayi sanadiyar mutuwar Yusuf, kowa ya bar abun a matsayin karar kwana, alokacin da abun ya faru a koi matasa guda biyu dake zaune kofar gidan su, a kan idon su komai ya faru amma sun manta komai sun kasa tunawa, abun ya wuce musu kamar basu gani ba.

A ɓangaren ita kuwa Aafia kai tsaye unguwar su ta wuce Allah ya taimake ta wan nan Alhaji bai samu damar ganin taba har ta shige gida, shima mai taxi ɗin da ya tashi dawowa sai bai bi hanyar da suka bi suka zo ba, sai ya canza hanya, hakan yasa bai haɗu da Alhajin ba.

Ko da Aafia ta shiga gida Umaisha na sharara barcin ta cikin kwanciyar hankali, tsaki Aafia taja ta wuce toilet dan tayi wan ka.

*ABUJA*

Kwance tashi babu wuya a wajen Allah a yau a ka ɗauki azumi, tun karfe 10 Jehan ke zubawa Gwaggo da mum kukan shagwaɓa wai ba zata iya kai azumin ba, while

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login