Showing 51001 words to 54000 words out of 194715 words
jikina waye yace musu bani da lafiya? Ko kece? Na dai am sa musu da to basu kariso bane?" Sai lokacin Hajiya Umaiya ta tuna da zancen Hajiya Zainab dake baje a Kitchen, ihu ta fasa tare da nufar waje da gudu, a razane Abba yabi bayan ta yana faɗin "Umaiya lafiya?" kai tsaye kitchen ta nufa tana salati, Abba na shigowa ya ja birki cike da tashin hankalin suke kallon Hakiya Zainab dake kwance a kasa an kwakwale mata ido dukka biyu ga jini nata malala kamar kogi, san nan an yanke mata nono dukka biyu an cire hancin ta, mutuwar tsaye sukayi shi Abba tsabar tsorata ya kasa karisa shigowa cikin kitchen ɗin, suna tsaye sunyi tsuru tsuru ita kam Hajiya Umaiya ma suman tsaye tayi a wajen,
wani guhuwa me mai karfin gaske ne ya shigo cikin kitchen bakin kirin da shi yana bada sautin kamar wakar shaiɗanu aljanu, sun razana ainun sun kasa gaba sun kasa baya ita dai Hajiya Umaiya suman tsaye tayi shi kuma Abba yana ganin meke faruwa amma ya kasa motsawa, yana ganin guguwar nan tazo ta mamaye Hajiya Zainab ta rufe ta ruf na wasu yan mintoci kafin daga bisani guguwar ya mulmule ya zama kamar ball san nan ya fice ta window da ya shigo, guguwar na fita Abba ya duba babu Hajiya Zainab babu labarin ta guguwar ya tafi da ita ko alamar ta babu a wajen jinin ta daya zube ma babu shi a wajen, wajen ya koma clean, tashin hankali ba'a saka maka date yanke jiki Abba yayi ya sume a wajen ita dai Hajiya Umaiya a tsaye ta sume.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Gidan Abbi*
Sosai Abbi ya shiga damuwa gani yake Irfan ba zai samu aiki ba kasan cewar yadda kasar ta zama yanzu, jiki a mace ya ɗauki waya ya kira dillalan da suka taya company 7 millon a kan suzo su saya kawai su bashi kuɗin ya fara wani business kafin su Irfan su dawo dan yasan idan Irfan na nan ba zai bari ya sayar ba shi yasa ya sallama musu shi tun kafin Irfan ya dawo an gama komai.
Cikin kankanin lokaci dillalan suka zo kofar gidan Abbi, cike da rashin jin daɗi Abbi yace su shigo, ba musu suka shigo su biyu hannun su riƙe da jaka baka mai yar girma kaɗan, kai tsaye palo Abbi ya wuce da su, bayan sun zauna, har da ruwa Abbi ya kawo musu suka amsa suka sha san nan suka gaisa,
bayan sun gama gaisawa ne Abbi yake sanar da su a kan su kawo 7 millon ɗin ya sallama musu company, ɗaya daga cikin sune yace "Alhaji ae yanzu ba zamu iya sayan wan nan kangon 7m ba aa ya mana tsada 5m shine last abun da zamu iya saye idan ka sayar mana" shiru Abbi yayi ya kasa magana saboda ɓacin rai, ɗaya daga cikin dillalan ne ya sake cewa "Alhaji ka sayar ne ko baka sayar mana ba mu tashi muyi tafiyar mu" kamar daga sama a bakin kofar shigowa suka ji an ce ba'a sayar ba kuma ba za'a sayar ba ku tashi ku fice daga gidan nan" a sukwane suka juyo ciki har da Abbi dan ganin wanene,
wani matashi ne tsaye a bakin kofar shigowar hannun sa riƙe da katuwar jaka jikin sa na sanye da riga baki da wandon jeans blue ya daura rigar sanyi mai hula ya kuma sanya hular rigar a hansa baka iya ganin face nashi sosai, a yanayin jikin sa dai ba zai wuci 25 years ba,
Ganin dillalan basu tashi bane yasa ya daka musu tsawa yana faɗin "Bazaku tashi bane?" Cikin sauri ɗaya daga cikin su yace "Alhaji mun saya 7 millon ɗin ga kuɗin bamu takardun mu tafi da shi" a fusace matashin nan yace "Wan nan fillin bazaa sayar ba ku fice daga gidan nan tun kan ranku ya ɓaci" jiki ba kwari suka wuce sumui sumui suka fice daga palon suka bar gidan
Bayan dillalan sun tafi ne matashin ya kariso cikin palon ya zauna saman sofa dake fuskantar na Abbi san nan ya buɗe jakar da ya zo da ita "Bawan Allah waye kai? Me ya kawo ka gidana" cewar Abbi, shiru saurayin yayi bai tanka Abbi ba har ya gama buɗe jakar ya ciro wasu takardu guda biyu ya miƙawa Abbi yana faɗin "Irfan ya shirya next week zai wuce London *UNITED KINGDOM* karatun master's nashi su kuma Aafia da Umaima ance na canza musu makaranta, kuma na canza ɗayan takardan nasu ne na canza musu school, san nan wan nan kuɗin 100 million ne akace na kawo maka ka tayar da company ka san nan idan kana da wata buƙata a kace ka faɗa min" ya kai karshen maganar tare da ɗago kai ya zubawa Abbi ido yana jiran yaji ko Abbi na da wata buƙata "bawan Allah waye ya aiko ka?" Abbi yayi maganar cikin sanyin murya "No Alhaji wan nan bai shafeka ba kawai dai kafaɗamin idan kana da wata damuwar dan zan wuce aiki na ya kare" shiru Abbi ya ɗanyi kafin yace "Bani da ita amma zan so sanin wanda ya aiko ka da kuma kuɗin zuwa kwanana nawa ko sati nawa zan biya" rufe jakar saurayin yayi tare da ɗauka ya ajiye kusa da Abbi saman sofa, ya juya ya nufi hanyar fita yana faɗin "Bawan Allah ne ya baka kuma ba ya baka dan ka mayar bane no kyauta ne daga Allah sauran bayani a kan karatun Irfan a Uk yana cikin aljihun jakar nabarka lafiya" ya kai karshen maganar tare ficewa daga palon ya bar gidan gaba ɗaya,
shi dai Abbi a tsorace yake jiki na rawa ya buɗe aljihun jakar dan yaga sauran takardun Irfan ɗin, nan ya ci karo da wata farar takarda mai ɗauke da sako later warware takardan yayi ya fara karantawa kamar haka "Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu ɗan uwana barka dai fatan kana lafiya ina maka fatan alkhari da fatan gamawa da duniya lafiya, nasan zakaji tsoron an san kuɗin nan shi yasa na haɗa maka da wan nan takardan, karkaji tsoro ka ansa kuɗin mallakin kane na baka har abada idan ma kana baƙatan kari zai iya karoma, yasu Aafia na canza musu school Masha Allah naga result na Aafia tayi kokari jamb ɗin ta yayi kyau tana da ilimi sosai ni ta ɗauko ashe, ita ma Umaisha ba laifi tana kokari ranar Monday Irfan zai iya wucewa Uk an gama shirya masa komai yaje yayi master degree ɗin sa ka gaida min da yarana idan sun dawo kasa musu Albarka, sako daga Hussain" zubur Abbi ya miƙe yana faɗin "Hussain daman Hussain yana raye? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun haba ɗan uwana me yasa zaka mana haka zuciya bata da amfani in dai har zaka iya sanin halin da nake ciki ka kawomin ɗauki to nasan zaka iya jin abun da nake faɗa yanzu ma dan Allah Hussain ka dawo garemu shakara 18 fa kenan rabon mu da kai zuciya bata da amfani karka biyewa zuciya kadawo mu haɗe kan mu, mu ci-gaba da yiwa iyayen mu addu'a, saboda ni da Maik zaka dawo ba dan yaya ba karka duba abun da yaya ya maka a baya ka ki dawowa dan Allah ka dawo mu muna son ka ai" ya kai karshen maganar tare da komawa ya zauna ya fara fitar da abubuwan cikin jakar wai ko zai samu address ɗin Hussain,
har ya kammala fito da komai na jakar babu komai sai wayan nan kuɗin da takardun sai kwalayen wayoyi kirar I phone 13 guda uku ko wani waya an rubuta sunan mai shi a jikin kwalin Umaisha Aafia Irfan, haka Abbi ya tattara komai ya mai da cikin jakar, yayi farinciki sosai ya kuma yi bakin ciki sosai yana bala'i son ganin Hussain amma ba dama tunda bai san in da zai same su ba,
kwashe komai yayi ya mai da ya ɗauki jakar kuɗin ya fito dan ya tafi banki, nan ya ci karo da sabbin masu gadi ga wasu matasa tsaye a harabar gidan yasha mamaki sosai a tuanin sa ɓarayi ne har yafara kiran sunan Allah daya karesa,
ɗaya daga cikin matasan ne ya kariso in da yake cikin girmamawa ya gaida shi san nan ya ɗaura da ciwa an ce suzo su rushe wasu ɓangarori daga gidan nan su gyara ginin san nan su kara gina abubuwan da babu, cikin sauri Abbi yace "Waye ya turoku?" A tunanin sa kila sun san address ɗin wadda ya aiko su, amma sai yaji akasin haka domin kuwa suma a waya a ka kirasu a ka basu wan nan aikin basu san daga in da a ka kira su ba, wucewa Abbi ya yi rai a ɗan ɓace ya nufi yar motar Irfan yana faɗin "Kuyi aikin ku" cikin sauri suka fara aikin su shi kuma Abbi ya shiga motar Irfan ya tayar ya nufi gate, tun bai kariso ba wani jibgegen mai gadin da aka kawo masa sabo yazo ya buɗe masa gate ɗin ya kutsa motar waje ya nufi bank su kuma masu aiki suka fara aikin su.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*KANO*
Zaune daddyn Jelly yake cikin katafaren office na shi na Engineer dake company nin sa filman Nigeria limited sai murmushi yake yana murna a kan aikin nan da suka samu dan ba karamin aiki bane contract ne na billions of Naira,
da sallama P.A ɗin sa ta shigo hannun ta ɗauƙe da kyakkyawan plate mai ɗauke da Tea da snacks, har kasa ta duƙa ta gaida shi sai murmushi yake ya amsa mata gaisuwar san nan ta miƙe ta ajiye masa plate ɗin a saman table ɗin ta fice daga office ɗin tana yaba kyan hali irin na daddy, cikin nitsuwa daddy ya ɗauka tea ɗin ya fara sha ya ture snacks ɗin gefe dan bai jin yinwa sosai kawai ma dan ya saba shan tea ɗin ne idan yazo office amma ban da haka yau baya jin yinwa dan yayi breakfast dasu Irfan kafin su fito tare shi ya wuto office su kuma suka tafi ganin gari a kan da yamma zasu biyo masa su koma gida tare, bai karisa shan tea ɗin ba barci ya ɗauke sa a wajen yana zaune.
After some hours
Da kyar daddy ya iya buɗe manya manyan idanun sa da suka masa nauyi, da kyar ya iya waro su waje ya sauke su saman katafaren agogon bangon dake manne a bangon ɗakin sa dake cikin office ɗin, zubur ya miƙe tare da goge idon sa yana kallon time ɗin da kyau 4:45 pm, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shi abun da kawai yake iya furtawa mamaki yake yaushe yayi barci haka shi da yake zaune yake shan tea lokacin kuma 10:00 am me ya faru da shi haka? Haka ya zauna yana jerowa kan sa tambayoyin da bashi da amsar su
jiki ba kwari ya yunkura zai miƙe a sukwane ya koma ya zauna ganin jikin sa babu kaya innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya faɗa tare da kara waro idon sa waje sai yanzu ma ya lura ashe a cikin bedroom na shi na cikin office ɗin yake, yasha ruwan mamakin waye ya cire masa kaya gaba ɗaya haka, wai mekeke faruwa ne ya kai karshen maganar tare da miƙewa a fusace ya fara sanya kayan sa dan yaje ya tambayi P.A dan ba wadda ya isa ya shigo office na shi ba tare da sanin ta ba,
Bayan ya gama sanya kayan sa tsab da tunani fal ransa ya nufi waje yana jan kafa da kyar da kyar dan gaba ɗaya jikin sa ya masa nauyi,
Haka ya fito daga office ɗin gaba ɗaya ya nufi wajen P.A, turus ya tsaya ganin office nata wayan babu komai har desktop computer ta babu a wajen, ta kwashe komai ta tafi, ganin haka yasa daddy ya fahimci a koi wani abu a kasa akoi makarkashi ya, cikin sauri ya juya ya koma cikin office na shi ya ɗauko wayar sa dan ya kira P.A ɗin,
nan yaci karo da saƙo guda biyu ɗaya na P.A ɗaya kuma na Baban Muneer wato Alhaji Auwal abokin takarar sa sun turo masa, jikin sa har kerma yake wajen buɗe sakon baban Muneer,
yana shiga sai yaga video ne cikin tsumuwa ya buɗe video, wata iriyar mahaukaciyar yarazana yayi lokacin da idon sa ya sauka kan Video, har sai da wayar tasa ta faɗin ƙasa a wajen, kasa motsawa yayi ya kurawa wayar ido yana kallon ta dan koda wayar ma ta faɗi kasa bata ɗauke ba video nayi, tashin hankali kwance daddy yake saman gado sa na cikin bedroom ɗin office ɗin kwance yake jikin sa ba kaya shi da P.A, abun da ya kara rikitashi shi ne gashi kuma ba barci yake ba a video idon sa biyu suke sheke ayar su sai dai shi ya kasa tuna lokacin da a kayi hakan a video dai gashi nan ita P.A tana nuna bata so shi kuma yana tilasta mata, dogon salati yasa muryan sa har rawa take ya durkushe kasa a wajen nan take hawaye wani na bin wani suka fara bin kuncin sa, ganin abun yake tamkar a mafarki, a hankali ya buɗe bakin sa muryan sa na kerma yana kuka yace "Ina saurayi matashi ma ban yi zina ba sai yanzu why why P.A zaki min haka Alhaji Auwal kacuci rayuwata ka gama da ni Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" yana cikin surutan da yake, kiran Alhaji Auwal ya shigo wayar nasa, cikin sauri jikin sa har ɓari yake wajen ɗaukan wayar tare da yin picking na call ɗin,
Daga ɗayan ɓangaren Alhaji Auwal ya bushe da dariyar mugun ta yana faɗin "Ka gama kukan ne ko baka gama ba, dan ina da tabbacin ka gama kallon video yadda kaci amarcin ka a karo na biyu dan kaci na farko kam da marigayya matar ka, amma fa gaskiya na jinjina maka ashe kai ma jarumin namiji ne ba rago ba ashe kai ma ɗan hanune ji yadda ka farwa yar mutane daman yinwar abun kake kawai dannewa kake kakiyin aure, to ni dai ba zan iya ganin abokina cikin yin wan nan ba shi yasa na bugar da kai dan ka biya bukatar ka nasan yanzu zam zam kake jin ka ko? Tun ɗazun nake ta kallon video nan naka ina koyar wasu style nima" ya kai karshen maganar tare da kara bushewa da dariya, shi dai daddy hawaye kawai yake yana tuanin mafita dan dai yasan hujjar sa ɗaya shine camera dake cikin office ɗin to amma yasan Alhaji Auwal bazai bar camera a kunne ba, ba zai bar wata hujjaba "Kasan me nake so da kai?" Cewar Alhaji Auwal cikin sauri daddy ya girgiza kai yana faɗin "A'a" da sarkakkiyar murya "Good yaron kirki, kayi kuskuren shiga gonata da kayi yanzu duk ba ma wan nan ba, zan ajiye video nan a waje na ni kaɗai bazan tura ko ina ba amma da sharaɗi, sharaɗin sune kamar haka idan ka kuskura ka sanar da wani abun da ke faruwa wallahi zaka tsinci video nan a duniya, abu na biyu wan nan contract ɗin ya zama dole kasan yadda zakayi ka sallamawa company na, abu na uku kuma duk abun da nake so shi zaka gudanar a company ka, abu na huɗu zan faɗa maka gaba idan ka gudanar da wayan da na faɗa maka yanzu a kan tsari ba tare da kuskure ba, san nan ina son ka sani kuskure kaɗan zakayi na saki video ka ga duniya jama'a su kalli chaskalewan Engineer Abdul Malik maik nasu, zanga har lokacin ma zasu ci gaba da yabon kane ko dai ya abun zai kasan ce amma kuma akoi dayawa da zasu ɗauki style fa dan kai ɗin ba na wasa bane duk da cewa na kara maka karfi da kwaya" ya kai karshen maganar tare da shekewa da dariyar shakiyanci, shi dai daddy ban da hawaye ba abun da yake,
sake bushewa da dariyar iya shege Alhaji Auwal yayi kafin yace "Bari na barka kaɗan huta zuwa anjima sai muyi magana ko? Dan na lura yanzu a zauce kake" yana kai karshen maganar ɗiff ya kashe wayar, kuka sosai daddy yake yana tuanin ta ina zai fara sallamawa Alhaji Auwal contract ɗin nan sai dai ya zauna da gomnati ya sanar da ita company sa ta samu matsala ba zai iya aikin ba kenan, innalillahi wa inna ilaihir rajiun kara rushewa yayi da kuka mai ɗan sauti, daman shi daddyn Jelly yana da sauri hawaye.
To muleko su Rimsha mu gani
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*ABUJA*
zaune a saman katafaren gadon ta dake cikin bedroom nata gwaggo take tana zaune tana latsawar ta jikin ta sanye da gown mai kama da abaya black color ta sanya turban cap mai kyau fari a kan ta,
baki ɗauke da sallama Rimsha ta shigo ɗakin jikin ta sanye da wando zuwa gwiwa black color da riga mai karamar hannu pink color ta zubo dark black curly hair ta daya sha gyara sai sheki yake gwanin ban sha'awa, gashi a nannaɗe kamar indomie ta sake shi har tsakiyar bayan ta, sai faman lumshe dara daran fareren sleeping eyes nata take tana buɗe wa kamar wadda barci bai ishe ta ba fuskar ta fayau ba kwalliya amma sai sheki fatar ta keyi kamar fatar jariri, lallausan pink lips na tan nan kamar ta sanya lipstick pink,
hayewa saman gadon tayi tare da kwatar da kan ta saman cinyar gwaggo cikin shagwaɓa tace "My gwaggo Jehan tace min wai Uncle Shitu ba kanin daddy bane da gaske ne?" kallon kyakkyawar face nata gwaggo tayi cike da so da kaunan tace "My siha da kikayi wan nan maganar kin tunamin da wani abu, bari na ɗauko in nuna miki amma gaskiya ne Alhaji