Showing 105001 words to 108000 words out of 194715 words
shi sama yayi wurgi da shi gefe guda, lokacin guda shi ma James ɗin kamannin sa suka sauya, sai huci yake, ba karamin mamaki su uncle Herry suka sha ba dan basu taɓa kallon James ya ɗauki zafi haka ba, duk gidan yafi kowa hakuri shiru shiru yake yana da hakuri sosai sannan yana bala'i son Michael bai son ɓacin ran Michael ko kaɗan, amma yau da hannun sa ya bugi Michael abun da bai taɓa yi ba.
Ihu azaba Michael ya fasa, gadan gadan James ya nufe sa da niyar dukan sa, da sauri Tga ya rike sa yana faɗin "Please James control your anger?" Kokarin fisge kansa James yake dan yaje ya daki Michael, yau Michael ya kai shi makura bai taɓa tunanin tsanar da Michael yayiwa mahaifiyar su ta kai ya iya yunkurin dukan ta ba
Cikin zafin nama ya kwace daga rikon da Tga ya masa tare da hankaɗe Tga ɗin har sai da ya faɗi saman sofa, ba karamin tsorata Tga yayi ba, tambayar kan sa yake daman James na da karfin da zai iya tureni? Kasa miƙewa yayi ya zubawa James ido kawai yana kallon sa da mamaki
Damko wuyar rigar Michael James yayi ya mikar da shi tsaye, sai numfashi sama sama Micheal keyi saboda wahala, dan ya bugu sosai wurgi da shi da James yayi, ya kasa yin wani yunkuri
idon James ya rufe baya ji baya gani bai lura da halin da Michael ke ciki ba ya dunƙule hannu zai kai masa naushi kenan, fitinanniyar kamshin perfume ɗin Romeo ya daki hancin duk wata halitta mai rai dake palon
A tare suka kai kallon su saman benen, yana tsaye saman bene ya goya hannu a kirjin sa ya zuba musu wannan dara daran kyawawan blue eyes ɗin nasa yana kallon su, jikin sa sanye yake da Ripped Jeans da Round neck polo shirt fara kal kamar yanzu ya fito da ita daga kwallin ta, yau dai ya saki dark black curly hair sa bai ɗaure ba ta kwata masa har bayan sa sai sheki take tasha gyara ga wani fitinanniyar kamshin da take zubawa, kyau iya kyau kamar shi yayi kan sa, soft red lips na san nan sai wani sheki suke kamar ya sanya musu lip balm
Ganin sa yasa James ya saki Michael, James na sakin sa ya wuce sai numfashi yake fitarwa da sauri sauri har wani tangal tangal yake, ya taho ya faɗa jikin Romeo yana sauke huci a hankali
kyakkyawan fararen hannun sa Romeo ya ɗago gentle yana ɗan bubbuga bayan Michael ɗin, slowly ya dawo da kallon sa saman face ɗin Michael ɗin, ya ɗan kalle sa sannan ya mai da kallon sa kan su mum, gently in a cool voice yace "What brought this woman in this house?" Shiru suka masa suna zare ido jikin su sai kerma yake, ita ma mum ganin Romeo yasa ta shan jinin jikin ta, duk da ita ta haifesa amma ganin sa ba karamin razana ta yake ba, ganin sa firgitata yake, in da tasan yana gida da bazata zo ba, yanzu ma tsautsayi ya kawota tana burin ganin sune shi yasa ta ansa wayar kawar ta tayi wa James massage ta roki sa a kan ya sanya security su buɗe mata tazo ta gansu kawai ta koma, da kyar ya yarda ya sanya security suka buɗe mata gate amma yace mata komai ya faru da ita shi baruwan sa, saboda son da take musu yasa tace ta yarda.
Jin sunyi shiru yasa Romeo yace in a cool voice "James, TGA who gave the security authority to open the gate for her? I knew one of you most have given the security permission to do that!!!" still shiru suka masa suna zazzare ido kamar an tare ɓera a tarko, dukkan su har shi TGA ɗin kirjin su sai dukan uku uku yake saboda tsoro jikin su sai kerma yake, sun sha ruwan mamaki ma da suka ga Romeo bai ɗau zafi sosai ba yau duk da mum tazo.
"Dad tell her I don't want to see her in this house henceforth, if I sees her footh here again she should fine herself to be blame!!!" Ya kai karshen maganar yana kokarin juyawa kenan, muryan mum ta katse shi, har in ina take wajen furta "I love you my pleasure" tayi maganar cikin tsoro, a fusace ya juyo, har suna haɗa baki da Michael wajen cewa "I hate you!!" Tashin sense shi dai James abun nasu yafi karfin sa, shi dai yasan yana jin haushin mum amma ba irin wannan haushin ba, yana ɗan son ta kaɗan
rai a matukar ɓace Romeo yace in a strong voice "tell her dad i hate her and i don't want to see her close to me, if not I will shoot her with my hand!!!" ya kai karshen maganar tare da sakin Michael yana wani sauke huci kamar mayin wacin zaki sai faman furzar da iska mai zafi yake daga bakin sa, Michael kuwa kamar jira yake, Romeo na sakin sa yayi bedroom ɗin Romeo da sauri,
Jim kaɗan ya dawo hannun sa rike da pistol gun, yana zuwa ya sai ta mum yana faɗin "get out" a sukwane daddy yace "Michael what is this?" Harɗe hannu a kirji Romeo yayi ya zubawa Michael dara daran blue eyes na sa, murya na rawa dad yace da Romeo "Please lion stop him" shiru Romeo yayi kamar bai ji me daddy yace ba, ita kuwa mum tana tsaye ta zuba musu ido yayin da shi kuwa Michael ke kokarin harbin ta, tabbas daddy yasan Michael zai aikata sarai zai iya harbin nata kamar yadda ya faɗa dan Michael yana da zuciya kamar Romeo ba a ban za yake kiran su da Lion and Tiger ba, suna da zafin zuciya over, barin ma Romeo shi na sa zafin zuciyar na daban ne idan ya fusata ba mai iya dakatar da shi
jikin daddy har kerma yake, sai faman rokan Romeo yake da ya dakatar da Michael "Please My lion stop him" wata gigitatchiyar tsawa Romeo ya dakawa daddy wadda ya sanya gaba ɗaya jama'ar palon razana da kiɗi ma "I can't stop him dad, Michael shoot her!!" Mum na jin abun da Romeo yace ta juya a guje ta fice daga palon, dan tasan halin su sarai tsab zasu iya aikata abun da sukayi niyya, dan tun suna yara ba wadda ya isa ya sanya Romeo yayi abu kuma ba wadda ya isa ya hana shi, ganin Romeo da idon ta a lokacin da yake cikin farinciki ma razana ta yake bare kuma ransa ya ɗan ɓaci, dan yau bai ɗau zafi bama, da ya ɗau zafi da ya jima da harɓe ta.
Mum na fita Michael ya faɗa jikin Romeo tare da sakin kuka mai ɗan sauti yana faɗin "she is wicked, she has wrong us, please lion tell me the reason why has she done that to us why?" Ya kai karshen maganar tare da kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, Rungume sa Romeo yayi suma wuce bedroom ɗin Romeo.
A tare su dad suka koma suka zauna, dad ya tsorata sosai, duk da cewa baya son mum bai son a kashe ta, ya fi son dai tayi nisa dasu ne ta bar su su samu peace of mind, shi kuma James a fusace ya haura sama yabi bayan Romeo da Michael...✍️
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪
B 💞Star Lady💞
*ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI TAALA WA BARKATUHU JAMA'A INA MUKU FATAN ALKHARI DA FATAN CIN MA BURI NA ALKHARI, MASU MIN MAGANA A KAN CEWA BAI KAMATA ROMEO YA RINƘA YIWA IYAYEN SA TSAWA HAKAN NAN BA, BAI KAMATA YA RINƘA YIWA MUM ƊIN SA HAKAN NAN BA, INA SON KU SANI FAƊAKARWA NAKE BA KARA ƁATA TARBIYA BA, IDAN KUKA YI HAKURI A HANKALI ZAKU JI MENENE YASA YAKE MUSU HAKAN, KOMAI NADA DALILIN SA A RAYUWAR NAN, SO PLEASE KU KYALENI HAKA NAN, BUGU DA KARI KUMA KARKU MANTA FA SHI ROMEO BATURE NE, KUN SAN TURAWA YADDA SUKE WANI LOKACIN MA ƳAƳA SUKE KOMAWA MASU MULKI A GIDA, IYAYE SU KOMA KARKASHIN SU, SAN NAN KUMA KARKU MANTA SHIFA ROMEO KIRISTAR NE BA MUSULMI BANE, MU MUSULMAI MUNE MUKA SAN DARAJA IYAYE DA GIRMAMA SU, AMMA YAWANCIN KIRISTOCI BASU SAN WANNAN BA FATAN KUN FAHIMTER, KU CI-GABA DA BIBIYA A HANKALI KOMAI ZAI WARWARE MUKU, NAGODE*
💞TRIPLET'S💞
https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo
*THE BEGINNING*
💞STAR LADY💞
WhatsApp me for more information 09162620621
Episode 23
A tare su dad suka koma suka zauna, dad ya tsorata sosai, duk da cewa baya son mum, amma bai son a kashe ta, ya fi son dai tayi nisa dasu ne ta bar su su samu peace of mind, shi kuma James a fusace ya haura sama yabi bayan Romeo da Michael.
Zaune bakin lallausan katafaren gadon Romeo ya isko Michael, sai faman turɓune fuska yake, while shi kuma Romeo yana tsaye gaban mirror, karasawa cikin bedroom ɗin James yayi, tare da zama kusa da Michael ɗin yana faɗin "Sorry My tiger, how are you feeling now?" Yayi maganar cike da kauna da kuma tausayin ɗan uwan nasa, kasan cewar shi Micheal a baya an taɓa masa aiki a ƙwaƙwalwar sa saboda wata matsala da ta taɓa faruwa da shi a baya, shi yasa sometimes idan ya birkice ba mai iya shi sai Romeo, kuma wannan dalili yasa gaba ɗaya gidan sukafi son shi saboda tausaya masa da suke, ko shi James ya bugi Michael ɗin ne cikin fitar hayyaci, baya hayyacin sa lokacin, badan haka ba da ba zai bugesa ɗin ba,
karisa hayewa saman gadon Michael yayi ya gyara kwanciyar sa yana faɗin "Please James i need hot coffee" yayi maganar a shagwaɓe, dukan wasa James ya kai masa a kirji yana faɗin "You make me thinking" lumshe ido Michael yayi ya buɗe tare da kara shagwaɓe murya yace "Thinking for what?" Hararar wasa James ya masa kafin ya miƙe yace "I'm coming let me bring the coffee for you first" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga room ɗin, duk abun da suke Romeo na jin su amma kamar bashi a ɗakin, yana tsaye gaban mirror yana faman latsa waya da alama sako yake turawa mai muhimmanci,
Jim kaɗan James ya dawo hannun sa riƙe da kyakkyawar cup mai ɗauke da hot coffe sai tiriri yake, yana fitar da hayaki, gefen gadon ya zauna yana faɗin "stand up please" kara turɓune fuska irin na shagwaɓa Michael yayi kafin yace "I don't need a coffee again" zaro ido waje James yayi lallai Michael ya raina masa wayyo yaje ya kawo coffee ɗin ne dan iskanci kuma zai ce bai so,
shi kuwa Michael lumshe brown eyes ɗin sa yayi abun sa kamar mai barci, hannu James ya kai kamar zai kai masa duka, sai kuma ya tuna da ya bugesa ɗazun kuma yasan wannan bugun da ya masa ma Romeo ba zai kyale sa ba, sai ya tuhumesa a kan me yasa zai bugi Michael, amma sai in Michael ɗin baya nan, dan Romeo baya yiwa ɗaya daga cikin su faɗa a gaban kowa, duk wanda yayi laifi a cikin *TRIPLET'S* ajiye sa yake shi kaɗai ya masa faɗa, tuna hakan yasa James ya miƙe ya fice da coffee ɗin a hannun sa ya mai da in da ya ɗauko.
Shi kuwa Michael daga lumshe ido yayiwa James barcin wasa sai abun ya zama da gaske barci ya ɗauke sa, ko da Jame ya dawo room ɗin Michael ya riga da yayi barci, kwanciya yayi shima a gefen Michael ɗin yana jiran yaji Romeo yace me yasa zai bugi Michael, shima daga kwanciya ba jimawa barci tayi awon gaba da shi, basu san time da Romeo ya fice daga bedroom ɗin ba sun yi barci, Michael yana barcin ma sai sauke ajiyar zuciya yake cikin barci saboda zafin zuciya irin nasa.
NIGERIA
KADUNA
Kai tsaye gidan sa mutumin nan ya wuce da Jelly, irin gidan nan ne na matasa yan ci rani masu cike da ɗakuna,
kamar matar sa haka yaje ya sanya key ya buɗe bedroom nasa yana faɗin "Shiga mana" make masa kafaɗa tayi a shagwaɓe tace "No daddy na ya hana ni shiga room ɗin kowa, kawai ka ɗauko min bag ɗin ka bani in tafi gidan su yaya Imran" da dai yaga taki shiga ɗakin ta lalama sai ya zare mata ido yace "Ki shiga ko na yanka ki da wuƙa" dariya Jelly tayi kafin tace "Ni rago ne da zaka yanka ni?" Ƙasa yayi da murya baya son yi mata da karfin sauran matasan da suka rage basu fita ba wato yan zaman banzan nan su jisa shi yasa ma bai shigar da ita ta karfin tsiya ba yake bin ta a hankali ya sami ta shiga, tana shiga shikenan sai ya ɗaure ta ya toshe mata baki yayi raping ɗin ta niyar sa kenan, amma ina Jelly taki shiga ta kafe a kan lallai daddyn ta ya hana ta kuma bazata ki bin maganar daddyn taba
Ganin da gaske taki shiga ne yasa ya kara kasa da murya yace "Muje ciki kici abinci" turo baki tayi kafin tace "A'a ka kawo min abincin waje" "Ke ni sa'an kine? Zaki shiga ne ko dai sai na ɗaga ki na shigar da ke" kallon sama da kasa ta masa kafin tace "Tun da ka dage na shiga room nan nasan ba alkhari bane a ciki dan daddy na duk ya koya min irin wannan haka Aunty Zuwaira mai aikin mu ma ta koya min karna yarda da maza, kuma ni ba jahila bace babu in da zanje, I'm 14 years now duk irin wannan abun na sansu ɗan iska kawai katon banza kazami" ta kare maganar tana murguɗa masa baki, duk shagwaɓa irin na Jelly tana da wayyo da kuma ilimi sosai duk abun da take tana sane gata bata barin ko ta kwana ba'a mata ta kyale, kana mata abu tun da zafin sa zata rama.
Damko yar hijabin school nasu dake jikin ta yayi yana kokarin turata ɗakin, ihu ta fasa tare da cire masa hijabin ta kwasa a guje tayi waje ta barsa rike da hijabin a hannu.
gudu take sosai dan a tunamin ta ya biyo bayan ta, bata san lokacin da ta hau saman titi ba saboda tsoro, bata ankaraba wata dankareriyar mota kirar *falcon Supernova* ya kwashe ta, nan take ta baje kasa bata suraba, kan ta ya fashe sai jini ya fara malala kamar kogi, bata numfashi kamar ta mutu, a sukwane ma tukun motar ya taka birki tare da fitowa da sauri, ya buɗe gidan baya na motar, wata babbar mace ce ta fito daga cikin motar, irin hamshaƙan Hajiyoyin nan ne wadda nera ta zauna musu sosai, sanye take da dankareriyar swiss lace pink color mai bala'i kyau da tsada, ɗinki riga da zani kasan cewar ba yarin ya bace ta manyan ta sosai, wuyan ta da hannun ta ta musu kwalliya da gold masu tsada, yayin da idon ta ke manne da farin glass (medicated glass)
Cikin sauri Hajiyar nan ta kariso wajen da Jelly ke kwance cikin jini, kan kace me jama'a sun taru a wajen, kowa sai salati yake, cikin sauri Hajiyar tace "Dan Allah ku taimaka ku samin ita a mota mu wuce asibiti da ita" tayi maganar a ruɗe, da sauri jama'ar wajen suka taimaka a ka sanya Jelly a mota, Hajiya ta koma cikin motar, da gudu driver ma ya koma cikin motar, ya kunna motar ya figeta da wata mahaukaciyar gudu suka nufi hospital.
💞Aafia💞
Zaune suke saman gadon su bayan sun dawo daga school, sai faman latsa wayoyin su suke, yayin da ita Aafia a zuciyar ta take shirya yadda zata ɓullo wa yar aikin da Abbi ya kawo da wuri ta koreta a gidan, Aunty ta fara aiki dan ita ya dace da tayi aiki a cewar su, suyita ɓata mata aikin har Abbi ya gaji ya koreta ya sake ta, sai ayyana hakan Aafia take a ranta tana latsar wayar ta
da sallama mai aikin ta shigo bedroom ɗin nasu hannun ta rike da plate mai shake da fruits, duk cikin su ba wanda ta amsa mata sallamar,
Baiwar Allah bata damu ba ta wuce ta ɗaura musu plate ɗin saman table ɗin dake bedroom ɗin san nan ta dawo gaban gadon ta duƙa cikin sanyin murya tace "Aunty ina wuni" kamar ba dasu take ba sun yi banza da ita kamar basu san da zaman ta a wajen ba, shiru ta ɗan yi, a tunanin ta basu ji ba ne sai ta sake cewa "Aunty ina wuni" tsawa Umaisha ta daka mata "ke mahaukaciyar ina ce? Ki fice mana daga bedroom dan Allah, bamu buƙatar gaisuwar!!!" baiwar Allah jikin ta har kerma yake ta mike ta fice daga bedroom ɗin cikin sauri.
Dogon tsaki Aafia taja kafin tace "I hate that girl kuma dole ta bar gidan nan, Halima ita zata ci-gaba da aiki dan ita ce yar aiki da ta dace da yi mana aiki " "same here" Umaisha ta faɗa tana kwaɓe fuska tana turo baki, dai dai lokacin kiran Akil ya shigo wayar ta
Dogon tsaki taja kafin ta ɗauki kiran tare da kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Hello" daga ɗayan ɓangaren Akil yace "Ina kika yasar da wayar kin tun safe nake kira?" Hararar wayar tayi kamar tana gaban sa, san nan tace "In school ne shiyasa" "A School ba'a picking call ne?" "Kayi hakuri to" shiru ya ɗan yi kafin yace "Umaisha ni sa'an wasan kine? Har zaki ga call na kiki ɗauka" shiru ta masa batayi magana ba sai faman hararar wayar take kamar yana gaban ta "Okey ba zaki