Showing 6001 words to 9000 words out of 194715 words

Chapter 3 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

948

da itama Dolly ita take kallo "Why Dolly kika wahalar da ni me na miki?" Tsalle Dolly tayi ta faɗo jikin ta hannu yarinyar ta sa tana shafa jikin dolly ɗin tana kallon face nata. Dai dai lokacin wani babban Alaji ya iso wajen kai da ganin sa kasan Naira ta zauna masa kyakkyawa ne sosai fari tas da shi kamar balarabe ga kyakkyawar saje da gemu dogo da ka ganshi kaga Ustadz yaji hutu fatar jikin nan nashi ta kwanta luwai luwai da shi, yana sanye da jallabiya Brown a jikin sa ya kariso wajen yana faɗin "Baby jelly kizo muje kiyi breakfast a gaba na kafin na fita" make kafaɗa jelly tayi cikin shagwaɓa da murya kamar mai kuka tace "Dady ni ba zan iya cin komai ba dan dolly na tun jiya taki cin abinci fushi take da ni fa dady" ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka rungumota dady yayi tare da dollyn nata yana ɗan bubbuga bayan ta cikin sigar rarrashi yace "Haba babyn dady muje ki ci abinci zan kira doctor Sadiq ya duba dolly ɗin sai muga meke damun ta yasa taki cin abinci" make kafaɗa tayi tana faɗin "Ni dady idan baka kira dr yazo ya fara dubata ba bazan iya cin komai ba" "Okey muje na ɗauki waya ta na kira dr ɗin ko dan ki samu kici abinci nima na samu na fita ana ta kirana a office tun ɗazun kuma nasan inna tafi ba cin abinci zaki yi ba" to tace masa ya kama hannun ta tana rungume da dollyn ta suka wuce cikin palon. Katafaren palo ne mai girman gaske mai ɗauke da manyan sofa set, set 2 launin Milk da Brown sai wani kyakkyawan table ɗin cin abinci mai ɗauke da kujeru 6 daga gefe ga wani makeken Tv plasma manne a bangon. Palon yaji komai da ake buƙata.
Saman kyakkyawar table ɗin dady ya wuce rike da hannu jelly sai faman turo baki take table ɗin cike yake da kayan abinci kala kala zama yayi tare da zaunar da ita saman kujerar kusa da shi ya ɗauko wayar sa dake saman table ɗin ta gefe ya shiga contact ya laluɓo wata number da a ka yi saving da Dr ya fara kira.
Bugu ɗaya dr ya ɗaga cike da cikin nitsuwa dady yace "Assalamu alaikum" daga ɗayan ɓangaren Dr yace "Waalaikumussalam Alhaji Ya gajiya?" "Lafiya lou dr daman nace idan kana kusa ka zo ka duba mana dolly taki cin abinci tun jiya" "To alhaji gani nan zuwa" "Ok sai ka zo" ya kai karshen maganar tare da katse kiran ya mai da wayar ya ajiye a gefen sa ya ɗauki spoon da ya fara cin abincin sa da shi kafin ya fita kiran jelly ya ɗibo abincin ya kai sai tin ɗan bakin jelly yana faɗin "Ci ko my baby" turo baki tayi tana faɗin "No dady ni ba zan ci ba gaskiya sai Dolly na taci" "Haba my baby kinji fa dr yace zai zo ya duba ta, to ki ci naki ke ma kafin dr yazo ya dubata kinji? Yauwa babyn dadyn ta" a hankali ta buɗe ɗan bakin nata ya zuba mata ta fara tauna a hankali hankali tana turo baki a haka har ta haɗiye ya sake ɗebowa ya kai mata bakin ta, ta ansa ta fara ci haka ya rinƙa lallaɓata har taci ta koshi san nan shi ma yaci ya koshi kafin ya miƙe ya riƙo hannun ta suka haye sama tana rungume da dollyn ta suka shige wani haɗaɗe bedroom mai ɗauke da katafaren gadon kwanciya dake shinfiɗe da white bed sheet na alfarma sai makeken drawer sanya kayan su,
Sai da suka isa tsakiyar ɗakin ya saki hannun ta ya nufi toilet yana faɗin "Let me bath my baby ki zauna idan kinji dr ya shigo sai ki kai masa dolly ya fara dubata kafin nazo, wucewa tayi ta haye saman katafaren gadon su ba tare da tayi magana ba shi ma ya wuce ya shiga toilet

Da zaman ta ba'afi 10mins ba dr yazo jin dr yazo yasa ta fito da gudu tazo ta miƙa masa Dolly tana faɗin "Uncle ka dubata taki cin abinci kwata kwata" tayi maganar kamar zata yi kuka tun daga nesa dr ya kura mata ido yana kallon ta har ta kariso gaban sa tana miƙa masa Dolly hankalin sa na kan kyakkyawar face na ta bai ma san tana miƙa masa wani abu ba sai magana take masa amma bai ji taba hankalin sa yayi nisa kallon face nata kawai yake, tana kokarin sa masa kuka dady ya fito yana faɗin "dr Sadiq har ka iso?" Yar firgigit dr yayi kafin yace "Eh na iso" yayi maganar tare da ansan dolly da jelly ke miƙa masa cikin sauri ya fara dubata da gudu jelly ta wuce ta rungumi dady tana faɗin "Dady bana son a yiwa Dolly ta allura" rungumeta dady yayi suka koma saman kujera mai zaman mutun 2 suka zauna shi ku ma dr yana aiki yana satar kallon jelly
`````Dr`````
Babban mutun ne wadda a kalla zai kai 35 year a duniya yana da kyan sa dai dai gwargwado ɗane ga abokin dady suna shiri da dady sosai.
Miƙewa dady yayi yana faɗin "My baby zauna ki kalli Dolly ki dr na duba ta bari na yi shirin zuwa office ko" jinjina masa kai tayi tana faɗin "To dady" wucewa dady yayi yana faɗin "Sadiq dan Allah ka duba mana dollyn nan da kyau muji ainihin meke damun ta yasa bata cin abin ci kaga kwana ki ma haka ta mana to dan Allah wan nan karon kam ina son sanin asalin a bun da ke damun ta" ya kai karshen maganar tare da hayewa saman ya shiga bedroom na shi dan shirin zuwa office.

Dady na tafiya dr Sadiq ya dubi jelly da ta buga takumi ta tsare sa da manya manyan idon ta tana kallon yadda yake duba dollyn nata ɗaga ido yayi ya kalli sama ganin cameran palon a kunne ne yasa ya ɗan ɓata rai tare da mai da kan sa kan dolly ya ci gaba da yan dube duben sa ita dai jelly ta zuba masa ido tana kallon sa.

Wacece jelly

Jalila kenan ya ɗaya tilo ga Alhaji Abdul Malik Salman Sultan tun jelly na da shekara biyu mahaifiyar ta ta rasu dadyn ta kuma yaki kara yin wani auren ya ci gaba da zama da yarsa su biyu suke rayuwa cikin wan nan Katafaren gidan sai masu musu girki Nana da Zuwaira Alhaji Abdul Malik bai cika zama sosai a gida ba wan nan dalili yasa ya sanya camerori a gaba ɗaya longu da sako na gidan sa dan ya rinƙa ganin halin da yar sa ɗaya tilo take ciki yana bala'i son jelly sosai fiye da ran sa, duk abun da take so shi ma shi yake so yana son farincikin ta kasan cewar ita ka ɗai ke garesa yan uwan maman ta sunyi sunyi ya bari su ɗauke ta su rike ta a wajen su amma yaki san nan anyi anyi da shi ya kara wani Auren nan ma yaki karawa dan gani yake duk wadda zai auro ba zata rike masa jelly yadda ya dace ba shi yasa yayi zaman sa daga shi sai ita sai masu aiki.
Wan nan shine ta kai taccen wacece jelly.

Shirye cikin wata dakakkiyar shadda sky blue dady ya fito ya sanya hula da takalma farare sai kamshi yake zubawa yayi kyau sosai, in da ya bar jelly nan ya dawo ya same ta ta buga tagumi tana kallon dollyn ta kusa da ita dady ya dawo ya zauna yana faɗin "My baby kar ki damu dolly zata samu lafiya ta dawo normal" kwantar da kan ta tayi saman cinyar sa tana faɗin "Dady ina jin kamar zan yi kuka" kallon dr dady yayi kafin yace "Dr Sadiq ya ake ciki meke damun dolly ɗin namu" satar kallon jelly dr yayi kafin ya fara magana "Alhaji zaka fitane?" Gyaɗa masa kai dady yayi "To muje tare sai na sawo mata magungu nan da suka dace ko? Dan gaskiya dolly bata da lafiya tana da matsala a zuciya amma In Sha Allah tana shan maganin nan zata samu sauki" "Okey to muje mana amma ni zan wuce Office idan ka sawo maganin sai kazo ka bata" "Miƙewa dr yayi yana faɗin "Ba damuwa zan dawo na bata maganin jelly a kula da dolly sai na dawo yanzu zan zo na bata magani ta warke taci abinci kin ji ko? Da fara'a ta amsa da "To uncle sai kun dawo" . A tare dady da dr suka fice daga palon kowa ya shiga motar sa driver yaja dady shi kuma dr ya ja kan sa suka fice daga gidan suka bar jelly rungume da dolly tana jiran dr.

KATSINA

washegari haka su mum suka tashi cikin kunci da jimami a kwana biyu da ɓatan Rimsha har mum tayi mugun rama saboda tunani.
Yauma kamar kullun zaune suke tsakar gida saman tabar ma sunyi jugum jugum kamar wayan da aka aikowa da sakon mutuwa Jehan na zaune daga ɗan gefen su saman yar ƙaramar kujera tana rike da wayar ta tana kokarin yin posting na hoton Rimsha a shafin ta Facebook. Tana gab da ɗora hoton sai maganar mum na jiya ta faɗo mata a rai in da take cewa Aunty A'isha kin san dai Alhaji Shitu ya gargaɗe mu kan zuwa police station ko, tuna hakan yasa gudun karta jawo wata matsala yasa ta ɗago ta kalli mum murya cike da damuwa tace "Mum ina son in shearing hoton Rimsha ya shiga duniya ko Allah zai sa in samu wan da ya gan ta" waro ido waje mum tayi kafin tace "Ki dai tona mana asiri ina ga Jehan kin gaji da zaman duniya ne shi yasa" cikin sauri goggo tace "Karki kuskura kiyi wan nan ganganci yanzu duk wani old account naki na media ma ki sauke sa ki buɗe sabo kuma karki kuskura kiyi posting na face na ki dan kin san dai ba wan da bai san face naku ba a kasar nan" jiki ba kwari Jehan ta sauke hoton Rimsha ta fasa ɗaurawa tayi shiru tare da buga takumi tana tunanin yar uwar ta "Jehan ki tashi ki ɗauki bokiti kije gidan su Sadiq ki ɗebo mana ruwa mu ɗaura girki dan yau duk gidan nan ba mai cash ko biyar" cewar goggo, a sukwane Jahan ya ɗago kai tana kallon goggo mamaki ma ya hana ta magana sai tambayar kan ta take a cikin ran ta "Wai shin mafarki nake ne ko da gaske ne ni Jahan zanje ɗebo ruwa ya Allah idan mafarki nake kasa nayi gaggawar farkawa" ganin tayi shiru ne yasa goggo tace "Jehan dake fa nake ki tashi mana" a kule tace "Wai goggo mafarki kike yi ne? Ni Jahan ɗin ne zanje ɗebo ruwa kina jin me kike faɗe kuwa goggo?" Tayi maganar cikin harshen turanci Kallon ta da kyau goggo tayi kafin tace "Kiyi hakuri Jehan kinga kuɗin hannun mu ya kare ne yau duk gidan nan ba wanda ta tashi da ko sisi" "To goggo ba akoi kuɗi a Account ba? Ai bani ATM zaku yi naje na ciro muku" "A'a Jehan yanzu kuɗin da suka rage manan nan lallaɓasu zamuyi ɗan su ɗan rike mu na wani ɗan lokacin kafin muga me Allah zai yi yanzu duk abun da bai zama dole ba ba zamu rinƙa fitar da kuɗi dan sayan sa ba" Cewar mum "Maryam wai nawa ne ma ya rage a account nakin?" Cewar goggo "Aunty A'isha kuɗin ba yawa kinga mun saya gidan nan mun sayi gado da sauran kayan buƙata bai fi 300k bane ya saura a ciki kinga idan muka ce komai saya zamu yi a yadda zamanin nan ya zama komai ta ninka kuɗin sa wallahi kafin nan da next week kuɗin zai kare" "Hakane Maryam shi yasa nace tun da akoi rijiya gidan su yaron nan Sadiq sai Jehan ta rinƙa ɗebo mana ruwan aiki ko?" Gyaɗa kai mum tayi tana faɗin "Haka ne Aunty A'isha kuma ruwan rijiyar tasu ba laifi wallahi maman Sadiq na da tsabta sosai" mum na rufe baki Maman Sadiq ta shigo da sallama ɗauke a bakin ta a tare mum da goggo suka haɗa baki wajen amsa mata sallama, ita dai Jehan ta buga tagumi tana tunanin yar uwar Rimsha duk wan nan zancen da su mum suke baya shiga kunnen ta, saman tabarmar da suke Maman Sadiq ta zauna suka gaisa cikin girmama juna san nan tayiwa mum jaje tare da fatan Allah ya bayyana Rumsha "Jahan ɗin dady ki tashi ki je mana" cewar goggo kallon sama da kasa Jehan tayiwa goggo kafin tace "Wai ke meyasa goggo baki son zaman lafiya ne? Wai da gaske kike ni zan je ɗiban ruwa?" Tayi maganar cikin harshen turanci goggo na kokarin yin magana mum ta riga ta da cewa "To shike nan Jehan tun da ba zaki je ba bari ni na tashi naje da kai na" ta kai karshen maganar tare da miƙa wa ta nufi kitchen ta ɗauko wata yar bokiti baki na roba ta fito ta ɗauko mayafi a ɗaki, ta na kokarin nufan hanyar fita Jehan tayi saurin miƙewa ta rike bokitin tana faɗin "are you serious mum? yanzu daman da gaske sai kije ɗiban ruwa da kan ki? Haba mum wai me yasa kuke yin hakane okay let me go and withdraw money from my account sai na sawo ruwan ko?" Kallon ta da kyau mum tayi tana mugun tausayawa yaran nata rayuwar da baka saba da ita ba rana ɗaya ka tsinci kan ka a ciki akoi wahalar ɗauka cike da tausayi mum ta fara magana cikin harshen turanci "Jahan bana son ki sake taɓa kuɗin Account na kin nan kinji? Kinga bamu san in da dadyn ku ya ke ba kuma kin san muna cikin haɗari a gaban ki Alhaji Shitu ya faɗimana komai kin san komai kin san meke faruwa kina dai ji Alhaji Shitu cewa yayi mu ɓoye kan mu karmu bari a san in da muke idan muka kashe kuɗin hannun mu waye kike tunanin zai bamu a wan nan wahalar rayuwa da ake ciki ko so kike mu fita nema har a ganmu a kashe mu ne eh? Ina son ki zama mai godiya ga Allah a duk halin da kika tsinci kan ki kin ji ko? Wan nan rayuwa da muke yanzu ma wata aya Allah ya nuna mana da muna zaune cikin daular dukiya da jin daɗi bamu taɓa sanin halin da yan kasan nan suke ciki ba amma kin yanzu ko ba komai mun samu karuwa munga halin da talakawa suke ciki idan Allah ya bayyana dadyn ku kuma Allah ya cika masa burin sa ya ci zaɓe kinga ai zamu faɗa masa halin da talakawa ke ciki ba sai na kusa da shi sun rinƙa masa karya ba" shiru Jehan ta ɗan yi hawaye na bin kuncin ta da kyar ta iya buɗe baki ta fara magana cikin harshen turanci "Mum yanzu shike nan dady ba zai dawo ba wai ma ina yaje ne mum kinga kafin ya fita fa yace min yana zuwa zai dawo da wuri kuma naji da uncle yazo yana ce miki bayi da tabbacin dady zai iya kuɓuta mu dai mu gudu Please mum ki faɗa min meke faruwa menene gaskiya abun da ya faru da dady na ko dai dady ya rasu ne?" "No Jehan ban san in da dadyn ku yake ba amma koma me ina da tabbacin bai mutu ba kuma ina sa ran zai dawo gare mu zai nememu ina jin hakan a jiki na" ta kai karshen maganar tare da sanya hannun ta ta gogewa Jahan hawayen dake bin kumatun ta tana faɗin "Ya isa kukan haka kiyiwa dadyn ku da Rimsha addu'a kin ji ko? In sha Allah zasu dawo gare mu komai zai wuce" rungume mum tayi tana faɗin "Mum ba zan iya dai na kuka ba sai dai na tsagaita" ɗan bubbuga bayan ta mum tayi tana faɗin "Hakane Jehan na san ba zaki iya dai na kuka ba dan uba da yar uwa ba wasa ba amma addu'a shine best thing da zaki rinƙa yi musu yanzu dai ansa bokiti kije ki ɗebo mana ruwa muyi abinci kin ji" ba musu ta ansa bokitin ta saki mum tana goge hawaye ta nufi hanyar fita "Jehan ki dawo ki ɗauki hijabi kin ji ko?" Cewar mum ɗin girgiza kai Jahan tayi kafin tace "No mum ni ban son hijabin nan gaskiya" "Jehan nan fa ba Abuja bane" Cewar goggo shiru Jahan tayi kamar bata ji me suka ce ba ta fice daga gidan kan ta ba hijabi sai wani ɗan karamin ɗankwali mai kama da handkerchief ta ɗaura a kan ta haka ta fice. Sai da ta fita san nan tace "bismillahi tawakkaltu alallah wala haula wala kuwata illa billah"
بِسْمِ اللهِ، تَوَكَّلْتُ عَلَى اللهِ، وَلاَحَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ

kallon goggo mum tayi kafin ta dawo kusa da maman Sadiq ta zauna tana faɗin "Jahan kenan" murmushi maman Sadiq tayi tace "Ai yara sarakuna ne" da yake cikin harshen turanci mum da Jahan suka yi magana hakan yasa maman Sadiq bata ji me suka ce ba girgiza kai kawai mum tayi bata sake magana ba shiru wajen yayi kamar ba mutane dukkan su sun shiga duniyar tunanin.

```Jahan```
Tana tafiya tana yamutse fuska tana kallon dattin unguwar kasan cewar Anguwar talakawa ne sosai akoi datti ta ko ina kallon banza ta fara yiwa mutane dake wucewa a harabar unguwar duk in da ta wuce sai ta tufar da yawu ko ta toshe hanci.
Tun daga ɗan nesa ta hango su Sadiq da wasu samari saannin sa suna buga kwallo dogon tsaki taja kafin tace "Dirty people" ta kai karshen maganar tare ta tufar da yawu a ranta tana faɗin "Allah ya kiyaye naci abincin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login