Showing 9001 words to 12000 words out of 194715 words
da su Goggo zasu girka da ruwan gidan su kazaman yaran nan" Ta shagala cikin tunani da zancen zuci bata ma san ta iso wajen su sadiq ba sai ji tayi kwallo ya bugeta a kafaɗa da karfi har sai da tayi tangal tangal kamar zata faɗi kasa, a zafafe ta juyo tana kallon matashin da ya bugo kwallon, matashi ne mai jini a jiki yana da ɗan kiba da tsawo wadda akalla zai kai 24 to 25 years.
Kallon banza mata shin mata kafin yace "Ke ki wuce ki bamu waje kinzo kin tsayawa mutane a waje" Bata ma fahinci me ya faɗa ba ta dai fahimci faɗa yake mata, A kule ta fara magana cikin harshen turanci "Kai banza kazami idan ban da kai wawa ne ma taya za'ayi kuzo kuna buga ball a kan hanyar wuce wa jibeka wani katon banza da kai cikin yara duk kafi su girma kazo kana shiga cikin yara ko kunya baka ji" ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki fusata iya fusata matashin nan ya fisata kasan cewar yana jin turanci sosai a fusace ya nufota gadan gadan tana tsaye ko motsi ba tayi ba sai ma kallon rai ni da take masa,.Yana iso wa wajen ta bai yi wata wata ba ya ɗaga hannu zai wanka mata mari cikin sauri Sadiq ya rike hannun sa yana faɗin "Haba Fadil me yayi zafi zaka yi yunkurin marinta" Fadil na ƙoƙarin yin magana muryan Jahan ya katse su cikin harshen turanci tace "Lallai kuwa wani kaza mi da kai ne kake yunkurin taɓani aiko da kayi kuskuren marina da baka sake mafarkin marin wata ba da kayi nadamar zuwan ka duniya" A fusace Fadil ya kwace hannun sa daga rikon da Sadiq ya masa yana kokarin kai mata mari Sadiq ya sake rike sa yana faɗin "Ki tafi in da zaki je kiyi hakuri" kallon banza tayiwa Sadiq kafin tace "I can't go anywhere please ka sake shi ya mare ni idan ba shi da hankali wani wawa kazami da shi sai wari yake" tayi maganar da kwabaɓiyar hausar ta, ta kai karshen maganar tare da tufar da yawu tana yamutse fuska, a fusace Fadil ya ture Sadiq har sai da yayi baya baya ya faɗi kasa cikin zafin nama ya ɗaga hannu zai mare ta
Share fisabilillah 👏
To Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai
💋Star Lady💋
💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞
Mai bukatan karanta book ɗin*TRIPLETS* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please
STAR 🌟 LADY..✍️
*💋The beginning💋*
Episode 3
....cak ta riƙe hannun sa tana tsaye ko alamar tsoro babu a idon ta bare shakkan sa cikin fushi ya sanya kafar sa yana kokarin kwashe kafar ta ta faɗi kasa batayi wata wata ba ta wanke masa fuska da mari cike da izza tace "Da Jehan kake magana first born a wajen...sai kuma tayi shiru tare da wurgi da hannun sa da ta riƙe tana jan tsaki ta wuce ta nufi hanyar shiga gidan su Sadiq mamaki ya hana Fadil motsawa daga in da yake ya dafe kumatun sa yana kallon ta har ta shige gidan su Sadiq shi kan shi Sadiq dake baje a kasa mamaki ya hana shi miƙewa sai zancen zuci yake "ƴar ƙaramar yarinya kamar wan nan har ta iya sa hannu ta mari namiji babba kamar Fadil babu shakka ko tsoro a idon ta wace ce wan nan yarinyar gaskiya ina son sanin wace ce ita dan wannan irin ƙarfin gwiwar da ƙarfin halin nata ba haka kawai ba daman kuma yan unguwar nan suna ta magana a kan su akan basu yi kama da talakawa ba to suwaye su wace ce ita?" haka Sadiq yayi ta jerowa kan sa tambayoyin da bashi da amsar su shi kan shi Fadil tambayar da yake wa kan sa kenan wace ce Jehan da har zata iya marin sa babu ko shakka bare ɗarɗar, gaba ɗaya matasan dake wajen suna buga kwallo sun sha mamakin Jehan ba kaɗan ba kasan cewar sun san halin Fadil bai da wasa yana da zafin rai ga cinzali da mugunta dayawan ƴan unguwa suna tsoran sa yau mace ta mare sa a gaban jama'ar unguwa tab yarinya kin shiga uku sai dai muce Allah ya jikan ki.
A gefen Jehan kuwa tana shiga gidan su Sadiq tayi karo da kanwar Sadiq a bakin kofa zata fito hannun ta rike da murhun da take suyar awara a kofar gida ɗan baya kaɗan yarinyar tayi tana faɗin "Sannun ki da zuwa" ko kallon in da take Jehan bata yi ba ta wuce ta shige cikin gida.
Tana shiga ta tufar da yawu ganin gidan caɓa caɓa da ruwa shiru ta tsaya kusa da rijiyar ta kasa ɗibar ruwan dan bata iya ba kuma taga abun ɗiban ruwan yana da girma shiru tayi tana karewa gidan kallo tana kwaɓe fuska.
Tana tsaye Amaryan baban Sadiq ta fito daga ɗakin ta shirye cikin atamfa doguwar riga tayi kyau ba karya kallon sama da kasa Jehan ta mata kafin tace cikin harshen turanci "Ke zo ki ɗiba min ruwan" waro ido waje Amaryan baban Sadiq tayi ta ɗan juya baya dan taga ko dai ba da ita Jehan take ba akoi wata a bayan ta, ganin ba kowa ne yasa ta dawo da kallon ta kan Jehan kallon banza Jehan ta mata tana faɗin "Ke dake nake ai kizo ki ɗiba min ruwa nace" kallon uku goma amaryan baban Sadiq ta mata kafin tace cikin harshen turanci ita ma tace "Ke kina da hankali kuwa ni kike cewa na ɗiba miki ruwa kin san wace ce ni kuwa?" Dogon tsaki Jehan taja kafin tace "Thank God ashe dai akoi masu ɗan jin English a kauyen nan ke ni ban tambaye ki ke wace ce ba kuma ban nemi sanin ke wace ce ɗin ba, ruwa kawai nace kizo ki ɗeba min ban son hayani ya" a fusace Amaryan baban Sadiq ta nufo Jehan da nufin wanka mata mari dan ta mata rashin kunya zuba mata ido Jehan tayi tana mata kallon mahaukaciya har ta ƙariso wajen, ganin babu alamar tsoro a face ɗin Jehan ne yasa Amarya taja birki tana kallon ta dai dai lokacin Sadiq ya shigo gidan, da sauri ya kariso wajen yana faɗin "Amarya lafiya?" Kallon sama da kasa amarya tayiwa Sadiq ɗin kafin tace "Ban sani ba" san nan ta juya harshen cikin harshen turanci tace da Jehan "Ke ɗauki bokitin ki, ki bar gidan nan kuma daga yau karna sake ganin kafar ki wai da sunan kinzo ɗiban ruwa gidan nan kina jina ko?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "Da ba a son rai na nazo ɗiban ruwan nan ba amma tun da kika ce haka to ki sani daga yau kullun sai nazo ɗiban ruwa in ga uban da ya isa ya hanani" ganin Jehan bazata daku a hannun ta bane yasa ta juya fuuu ta wuce ɗaki tana masifa "Wallahi bari shi ma baban Sadiq ɗin ya dawo dole ya hanaki zuwa gidan nan har kaman ni ina faɗa yau wata tana bani amsa ni da duk gidan nan shakka ta ake nasan maganin ki" kallon Sadiq Jehan tayi kafin tace "Who is she?" "Kin mantane nace miki bana jin turanci" sadiq ya bata amsa guntun tsaki taja kafin tace "waye ne ita" murmushi Sadiq yayi yana faɗin "Cewa zaki yi wace ce ita" kallon sama da kasa ta masa kafin tace "To koma me tun da ka gane nufi na just amsa me kawai" "ita ma maman mu ne" waro dara daran idon ta waje Jehan tayi ta sanya hannu ta tana gwada tsawon Amarya a iska tana faɗin "How? Za ace wan nan yar Small yarinyar ta zama maman ku ba ma sister ku ba" hannu Sadiq yasa ya ɗauki guga ya fara ɗiban mata ruwan yana faɗin "Eh matar baban mu ne itama da ita da maman yarinyar da take waje tana tuyan awaran nan dukka matan baban mu ne" "Why baban ku zai Auri wan nan small girl ɗin I think fa ka girme ta ko?" "Eh na girme ta kawai dan iyayen ta na da kuɗi ne sai tace baban mu take so shi ne aka aura masa ita bana jin yana son ta amma dai ni ban sani ba tun da ba shiga har kan su nake ba" ya kai karshen maganar dai dai lokacin da yake juye mata ruwa gugan karshe a bokitin nata, Shiru Jehan tayi dan ba abun da ta gane a zancen Sadiq bayan cewa Amarya maman su ne matar baban su. Ɗaukan mata ruwan yayi yana faɗin "Muje na kai miki gida" wucewa gaba tayi da sauri ta fice daga gidan tana tufar da yawu bayan ta Sadiq ya bi yana mai farinciki ko ba komai yau Jehan ta masa magana, ko da ta fito duk matasan dake buga kwallo da Sadiq ɗazun basa nan sun watse kowa ya kama kan sa wuce wa tayi abun ta tana hararar masu wucewa a hanya
Babu ko sallama ta faɗa cikin gida yadda ta bar su mum da goggo da maman Sadiq haka ta dawo ta same su saman kujerar da ta tashi ta koma ta zauna tana turɓune fuska "Jehan ina ruwan kuma?" Cewar mum turo baki tayi kamar biro kafin tace "wan can dirty boy ɗin yana kawo wa" ruƙe haɓa goggo tayi zata yi magana Sadiq ya shigo bakin sa ɗauke da sallama da fara'a mum ta amsa masa tana mamaki yanzu daman Sadiq Jehan ke cewa dirty boy oh Allah "Mama ai na zan juye muku ruwan?" Sadiq ya tambaya kakalo murmushi dole Mum tayi kafin tace "Ajiye min a kitchen babana" da azaman sa ya karisa cikin kitchen ɗin ya ajiye ruwan ya fito dai dai lokacin goggo ke tambayar Jehan "Wai babyn dady me ya faru kike ta ɓata rai haka ne?" Murmushin Sadiq yayi yace "Ita da Amarya ce ban dai san me ya haɗa su ba na shigo na samu amarya ta nufo ta zata bugeta" mum na kokarin yin magana goggo ta rigata a kule tace "Wace amarya kuma? Giya ta sha ne da zata ce zata bugi baby Jehan?" Kallon maman sa Sadiq yayi kafin yace "Kiyi hakuri gwaggo" miƙewa gwaggo tayi tana faɗin "Ba wata zancen hakuri sai naji dalili, akan me zata ce zata bugi Jehan" shiru maman Sadiq tayi ita kuwa mum mamaki take wai duk wahalar da suka shiga gwaggo bata sauya ba akan Jehan, cikin sanyin murya mum tace "Aunty A'isha kiyi hakuri mana tun da bata bugetan ba" a fusace gwaggo tace "A'a gaskiya ba zan hakura ba idan na barta gobe ma zata sake yunkurin tabata ne gwara na dakatar da abun tun yanzu kai Sadiq muje in ga wace isashiya ce wan nan" "Matar baban mu ne" Sadiq ya bata amsa yana kallon maman sa "Dan matar baban kune sai ta yi yunkurin taɓa Jehan tana da hankali kuwa?" Shiru suka yi gaba ɗayan su ita dai mum idan da sabo ta saba da halin gwaggo da Jehan dawo da kallon ta kan maman Sadiq gwaggo tayi tana faɗin "Zan hakura ne kawai saboda mutuncin ki da kirkin ki amma ku faɗawa baban Sadiq ya jawa matar sa kunne idan ta kuskura hannun ta ya taɓa jikin Jehan to zata yi danasanin mai girma a rayuwar ta" ta kai karshen maganar tare da komawa ta zauna tana ɗaure fuska "Mum zan iya tafiya ko in karo muku ruwan?" Cewar Sadiq girgiza kai mum tayi tana faɗin "A'a babana ya isa muna godiya sosai Allah ya albarkaci rayuwar ka" "Amin mum amma dan Allah mum idan kuna buƙatar ruwa ku kirani zan ɗebo muku ban son Jehan ta rinƙa zuwa gida dan amarya bata da mutunci ko kaɗan gashi duk gida ba wan da ya isa ya mata magana dan tana takama baba zai iya komai akanta zai iya koran kowa a gidan saboda ita shi yasa take abun da ta ga dama" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya fice daga gidan kallon maman Sadiq da kyau mum tayi damuwa ne karara a bayyane a kan face ɗin ta Allah sarki gata mace mai hakuri da kamala "Maman Sadiq abun da Sadiq ya faɗa haka ne?" Gyaɗawa mum kai maman Sadiq tayi kafin tace "Haka ne" miƙewa Jehan tayi ta wuce ɗaki a ranta tana faɗin "Ko me su gwaggo kuma suke cewa oho" "Maman Sadiq me ya sa hakan to? Ba kece uwar gida ba? Ko dai akoi wata ce kafin ke?" Cewar gwaggo shiru maman Sadiq ta ɗan yi kafin ta fara magana a nitse "Da farko ni ka ɗai ce a wajen baban Sadiq daga baya ya auro maman Hanan lokacin da tazo gidan ba irin cin kashin da bata min ba shi kuma baban Sadiq yana biye mata ranar girkin ta zata yi girki ta hana ni, ni da Sadiq haka ina ji ina gani idan na masa magana sai yace to shi ina ruwan sa na ansa da kai na mana ni ba mace bace kuma yana sane ba iya faɗa da ita zan yi ba dan tafini tsawo da kiɓa wani lokaci Sadiq idan yaga abun da take min yayi yawa sai ya shiga ɗaki yayi ta kuka dan yana tsoron yin magana yasan halin baban sa zai iya korin sa daga gidan shi ba korin sa da za'ayi ne damuwar sa ba a'a tafiya da zai yi ya barni bai san me zai iya faruwa da ni ba gwara masa ya zauna yana kallo na idan wani abun da yafi karfi na yazo sai ya tare min, haka muka ci gaba da rayuwa cikin wahala ga talauci har ta kai ta kawo baban Sadiq ya dai na bani abinci ya dai na shiga ɗaki na ya dai na kulani kwata kwata, saboda haka Sadiq ya ajiye makarantar sa daga class 5 ya fara koyan aiki a garejin bayan layin nan yana aiki idan ya samu kuɗi yana ciyar da ni Allah da ikon sa Allah ya bani ciki na sake haifan Yusuf daga nan ban sake samun Haihuwa ba har yau dan tun daga lokacin har izuwa yanzu baban Sadiq bai sake kusan tata ba, shi ma Yusuf haka ya taso cikin wahala da ukubar maman su Hanan tun yana yaro take bashi wahala har Allah yasa ya girma gwara Sadiq ma ya samu karatu kaɗan zuwa class 5 shi Yusuf ko kaɗan bai samu ba kasan cewar baban sa bai da karfi daman bai da karfi rike mata biyu kawai jaraba ce ni kaɗai ɗin ma da kyar yake iya ciyar da ni sau biyu a rana amma haka ya rufe ido ya kara Aure, Sadiq yana iya bakin kokarin sa wajen ganin ya kula dani da kanin sa muna a haka har maman Hanan ta samu cikin Hanan yarinyar nan dake tuyar awara a kofar gidan mu, ita ma tun daga kan Hanan bata sake Haihuwa ba sai dai abun mamakin ita Hanan tana da hali mai kyau ba kamar maman ta ba, muna cikin wan nan wahalar yazo mana da wata zance wai an bashi mata wata yar mai kuɗi ce ta ganshi tace shi take so dan haka Aure zai kara a lokacin nayi kokarin nuna masa illar hakan yaki yarda dana matsa yace to na tafi gidan mu jin hakan yasa nayi shiru na kyale sa kasan cewar bani da uwa mahaifiyata ta rasu kuma ba zan iya tafiya na bar su sadiq ba, yarinyar da yace zai aura yarinya ce karama bata wuce Sa'a Sadiq ba dan bata wuce 23 years ba Sadiq ma ya ɗan girme ta na nuna masa illar abun amma ya rufe idon sa yaki shi yaga kuɗi daman gidan da muke cikin nan gidan hayane alokacin sanadiyar Auren yarinyar baban ta ya sai masa gidan ya dawo mallakin sa yarinyar nan tun da tazo shikenan baban Sadiq ya tattara mu daga ni har maman Hanan ya watsar daman ni ya dade da watsar da ni ya tattara ya koma ya tare a gindin yarinyar sai abun da tace ya keyi ko waje idan tace karya fita tofa baya taka ko ina daman ba wani sana'a yake ba itace yake sayarwa a ɗan bayan layin mu baban yarinyar ya saya masa kaya dayawa da abubuwan amfani san nan ya gyara ma yarinyar ɗakin ta an mata ciki da palo har da fenti gashi yarinyar tazo da abubun ta dayawa har da su kayan kallo da su gas da kayan abinci na zamani kullun zata girka kaji da shinkafa bata taɓa tsanmana ba sai dai taci ta ragewa baban Sadiq ya fito waje idan ba wuta yana cin ragowar ta yana washe baki ni ko ajiki na dan Sadiq yana iya kokarin sa wani lokaci idan ya samu kuɗi a garejin su sosai har kaza nima yake sawomin gasashe muci da shi da Yasuf mu ɗebawa maman Hanan da Hanan ɗin ta, maman Hanan ma ta kasa jurewa shi ne suka fara sana'ar awara a kofar gida ɗan su ciyar da kan su baban Sadiq ya sallama mu ba ruwan sa da mu baya bamu ci baya bamu sha bare sutura ko idan bamu da lafiya ya nema mana magani kwata kwata ba ruwan sa da mu damu da babu duk ɗaya ne awajen sa daga ni har maman Hanan ya fita sabgar mu, ko mutuwa zamu yi mu mutu shi ba ruwan sa kullun yana wajen amaryan sa gashi yarinyar bata da kunya ga masifar bala'i idan rashin Kunyar ta ya motsa sai Sadiq na min wanki kaya na sai ta kwaso nata ta zuba masa tace ya wanke idan yaki sai ta sa baban shi, shi kuma gudun ta sanya babansa yasa sai ya ansa wankin nata ya wanke mata Yusuf ne dai baya