Showing 183001 words to 186000 words out of 194715 words
juya subi wancan motar.
Ba musu driver ya juya duk da bai san waye ya ɗauko a cikin taxi ɗin nasa ba, sosai wancan motar ke tsala gudu a kan hanya duk da girman ta, hakan yasa Romeo ya kara zargin motar sosai da sosai.
Dai dai wani check point na kan hanya wasu yan sanda dake tsayawa a wajen suka dakatar da motar, shima Romeo dakatar da mai taxi ɗin sa yayi ya fito yace wa mai taxi ɗin "I'm coming" ya nufi wajen motar can, dai dai lokacin driver motar ya bawa ɗan sandan cin hanci, ba tare da yan sandan sun binciki motar ba sukace motar ta wuce dan sun karɓi cin hanci.
Driver ya koma cikin motar yana kokarin tada motar Romeo bai yi wata wata ba ya fisgo driver motar yayi wurgi da shi waje, cikin sauri sauran dake cikin gaban motar suka fito, su biyu ne, da ka gansu kaga rikakkun yan daba, ga jikin sunan duk tabon shatin yan kan wuka,
Saboda jacket da ya sa ya kuma saka hular a hansa ga face mask da glass a fiskar sa gashi dare ne hakan yasa har yan sandan dake wajen basu gane shi ba.
A guje wayan nan yan daba biyun sukayi kan sa da nufin dukan sa, duk kan su duka ɗai'ɗai ya musu suka zube kasa kamar wasu kayan wanki
Abun ku da rashin gaskiya irin na duniyar yanzu, sai yan sandan dake wajen suka ciro bindigu suka saita Romeo da shi wai ya ɗaga hannu sama ko su harbesa a kan me zai daki wayan nan mutane, saboda sun basu cin hanci yasa suke wannan hargagin, hakan da yan sandan sukawa Romeo yasa ya kara zargin su ya kara sawa a ransa kenan kullun motar tana wuce suna bata hanya kenan.
Bai ɗaga hannun sa ba sai ya juyo yana kallon yan sandan, sun dage zasu harbe sa idan bai ɗaga hannu ba, a hankali ya ɗago kafar sa ya fara tinkarar su, sai kokarin harbin sa suke amma bindigar taki harbi saboda tsorata da sukayi jikin su nata kerma sun kasa danna kunamar bindigar da kyau, ɗaya daga cikin sune ya kira wayar over over akan a karo musu yan sanda ga ɗan ta'adda sun kama yana kokarin yi musu illah.
Wannan danganta Romeo da ɗan ta'adda da sukayi hakan ya ɓata masa rai a fusace ya kwace bindugun hannun su, ya musu dukan tsiya, wadda ya sasu sumewa a wajen, da farko bai yi niyar dukan su ba, a matsayin su na jami'an tsaron yaso ya sa a cire musu kakin sune ma'ana a kore su daga aiki sannan a basu hukunci dan sune ɓata garin tun da su suke karɓan cin hanci su bar masu laifi su gudu, amma danganta shi da ɗan ta'adda da sukayi yasa ransa ya ɓaci ya musu dukan kawo wuka duk ya fashe musu fuska, shi kuwa driver taxi daya kawo Romeo tuni ya juya kan motar sa ya gudu, yaga Romeo na dukan yan daban nan kar ya shafesa dan shima bai san wa ya ɗauko a taxi ɗin nasa ba, shima cewa yake ko dai ɗan ta'adda ya ɗauko ne.
Daman yan sanda uku ne a wajen lilis Romeo ya musu da duka, sannan ya ɗauki bindigar ɗaya daga cikin su yana kokarin har bin kwaɗon da aka rufe kwantenan bayan motar dan yaga me suka ɗauko suke wannan gudu haka
bai kai ga harbin kwantenan ba sai yaji diran motoncin yan sanda, wanda wancan ɗan sandan ya kira office nasu a kan a turo yan sanda ga ɗan ta'adda sun kama.
Zubawa motoncin yan sandan ido yayi ta cikin black glass nasa yana kallon su, motoci uku ne, suna iso wajen sukayi parking suka diro kasa suka kewaye sa da bindigun su, suna faɗin "you are under arrest keep this gun and raise up your hand" ka ajiye bindigar nan ka ɗaga hannun ka sama"
shiru ya musu kamar bai ji me suka ce ba, abun ma haushi ya bashi, hannu yasa a aljihun sa, a sukwane yan sandan suka ja baya a tunanin su boom ko wani makamin zai ciro, haushi ma yaji kamar ya harbe yan sandan duka su mut dan a cewar sa basu da ammafa suna yan sanda suna da wannan tsoro haka, daga sa hannu a aljihun sa sun ja baya
Wayar sa ya ciro suna ta ce masa ya ajiye wayar nan amma kamar ba da shi suke ba, latsa wayar nasa yayi na ɗan lokaci kafin ya mai da aljihun sa ya juya ya saita kwaɗon dake jikin kwantenan zai harba kenan ɗaya daga cikin yan sandan ya harbe bindigar hannun sa, bindigar ta faɗi kasa shi kuma bullet ɗin ta ɗan kuskure hannun sa, a fusace ya juyo yana kallon wanda yayi harbin
Kwata kwata baya jin duka mutane yau kuma baya jin yin kisa, amma suna kure sa,
tsawa yan sandan suka daga masa wai ya zube a kan gwiwowin sa, ran sa ya fara ɓaci yanzu, yana kokarin takawa ya tinkare su dan ya musu dukan mutuwa kenan sai wajen gaba ɗaya ya karaɗe da jiniyan jiga jigan motoncin sojoji masu numfashi kai daga jin jiniyar ma kasan ba sojojin wasa ne ke tunkarar wajen ba, dakata wa yayi dan shi ya kirasu a kan suzo su tafi da gaba ɗaya yan sandan nan, dan yana da aiki a kan James sosai so baya son ransa ya ɓaci yau, yana son cikin nitsuwa idan James ya dawo suyi magana shiyasa ya kira sojojin.
A ɓangaren yan sandan kuwa sai murna suke wai an turo musu sojoji kila manyan su sun samu labarin babban ɗan ta'adda ne suka kama shiyasa suka haɗa musu da sojoji, sai dai abun da ya ɗaure musu kai, wannan jiniyar na motar jiga jigan sojojin kasan ne, kenan manya manyan sojoji kamar wayan nan zasu iya kawo wa kananan yan sanda kamar su ɗauki, abun ya basu mamaki amma dai sun zuba ido suna jiran suga me ke shirin faruwa.
Jibga jibgan motoncin masu numfashi shabiyu ne suka iso wajen, wasu jibga jibgan sojojin masu jini a jika, fararen American tas da su, gasu da kirar karfi sun samu horo mai kyau, fuskokin nan nasu kamar hadari babu wasa a ɗaure take tamau ba su san menene dariya ba, ganin wayan nan sojojin kawai ya isa ya sa rundunar mutane zuciyar su ya buga su mutu saboda tsoro.
Ji kake dip dip, suna dirowa kasa daga bayan motocin su, da gudu wasu suka kewaye Romeo dake tsaye, wasu kuma suka kewaye wannan motar yan ta'addan wasu kuma suka kewaye gaba ɗaya kan titi daga ta in da suke, hannun su na rike da jiga jigan bindigogi wayan da suka amsa sunan su bindiga, wadda baya saɓa saiti in da ka aikashi nan zan wuce kai tsaye, ba irin makaman kananan yan sanda da sojoji bane.
Ɗaya daga cikin yan sandan ne yace da sojojin "Yauwa wannan shine ɗan ta'addan ku kama shi, ɗan tada kayan baya ne, yazo ya fara dukan jami'an tsaron mu ya.... Bai kai karshen maganar ba sojan ɗaya ya daka masa wani gigitacen tsawa wadda ya sanya gaba ɗaya yan sandan dake wajen zubewa kasa a kan gwiwowin su, tsabar tsoro jikin su sai kerma yake
A hankali Romeo ya zame hular kan sa tare da karɓan bindigar ɗaya daga cikin sojojin sa, ya sai ta kwaɗon jikin kwantenan motar yan ta'addan can, ya harbe kwaɗo, kofar ta buɗe
Ji kake dip dip da gudu sojoji biyu suka zo suka buɗe masa kofar contenan, yan mata ne cike a ciki duk basa cikin hayyacin su an musu allura fita daga hayyacin su, kallo ɗaya Romeo ya musu ya kawar da kan sa gefe ya juya tare da cire hand gloves dake hannun sa ya nufi mota ɗaya daga cikin motocin da sojojin sa sukazo yanzu.
Lokacin da Romeo ya cire hulan kan sa kamannin sa suka bayyana tsoro yasa yan sandan dake wajen sume saboda babu wani ɗan adam dake cikin birnin Washington DC da baya tsoron Romeo bare kuma su da suka masa laifi har da harbin bindigar hannun sa tab, sun gama sadaukarwa yau mutuwa zasu yi, shiyasa suka fara da suma tun ma basu ji hukuncin da zai yanke musu ba.
Shi kuwa bai bi ta kan su ba ma dan yana da abun yi, motar sojojin sa ya nufa, da gudu jibga jibgan sojoji biyu suka nufe sa, suka buɗe masa kofar motar gidan gaba, shiga yayi ya zauna sannan gently yace su kai masa wayan nan yan ta'addan gida zai yi aiki a kan su da kan shi, motar yan ta'addan kuma su kai headquarter su ajiye zuwa da safe yan sandan nan kuma su kira president su sanar da shi ya soke aikin su, dan dukkan su basu san aikin da suke ba.
Ɗaya daga cikin sojojin sane ya shiga motar ya mata key yaja sa zuwa gida, har cikin gida ya shiga da Romeo, yana yin parking ya fito ya buɗe masa kofar motar, gently Romeo ya sako kafar sa waje kafin ya fito gaba ɗaya ya nufi cikin gida, shikuma sojan ya juya kan motar ya koma wajen sauran sojojin can dan suyi aikin da lion ya saka su.
Lokacin da Romeo ya shiga bedroom nasa, Micheal na kwance masa saman katafaren gadon sa idon sa a lumshe da alama barci yake, wuce sa Romeo yayi yaje ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kayan barci masu kyau da tsada launin sky blue riga da dogon wando mara sa nauyi.
Sai tashin fitinannen kamshi yake ya saki dark black curly hair sa har baya, ya haye saman bed nasa kusa da Michael ya jawo laptop nasa ya fara aikin bincike a kan James.
Number wayar James ya shigar cikin laptop ɗin nasa ya fara kokarin bin diddigin in da James ɗin yake, yasha mamaki ganin number James yana shararin sama niya, kenan jirgi James ya hau zuwa ina to? Shiru Romeo yayi yana mamakin ina James zai je bai sanar da shi ba, kuma dole yasan tafiya zata fita cikin Washington DC, har James zai iya fita cikin garin nan ba tare da sani na ba? Sai jerowa kan sa tambayoyi wadda bashi da amsar su yake, "gaskiya nayi sake na biye musu ina musu abun da suke so, daman dan suje suyi ta tsula tsiyar su a waje ne yasa sukace basa son bodyguards ko sojoji surinƙa binsu idan zasu fita, nayi kuskuren yarda da hakan da nayi" sosai Romeo yake tunani a zuciyar, daga karshe dai sai ya fara binciken wace jirgi James ya hau kuma ina zai je, me ya fitar da shi cikin Washington DC da daddaren nan kuma da jirgin kasuwa abun da basu taɓa yi ba, koda yawon shakatawa su James zasu je wata kasa jet ɗin sa yake badawa a kai su duk in da zasu je dan tsaro, amma yau James ya saci hanya ya hau jirgin kasuwa why.
Duk wani binciken da yayi a wannan daren dan gane ina James ya dosa bai samu damar gane wa ba, dole dai sai da safe yasa sojojin sa su bincika masa a wani airport James ya hau girji dan suji ina zai je, daga nan ya ajiye bincike a kan James ya shiga bincike cikin sauran criminals da basu samu damar halactar taron su James ba dan ya gano ina suke,
Bayan ya kammala wannan binciken ne kuma ya shigar da number motar da ya kama ɗazun mai ɗauke da yanmata nan, nan ma yayi bincike a kan motar, daga ina motar ta fito ina kuma ta nufa, dan ya san dai ba iya wayan nan yanmatan ne kawai ba, tun da motar ta kwaso wayan nan tofa tabbas ta saba kwasan yanmata ne dole ya san ina ake wannan badakala a cikin garin sa,
Da binciken nasa yayi bincike a wajen bibiyar ɗaya daga cikin driver masu safaran yanmata da suka kama, nan yaci karo da driver'n yana yiwa wani babban likita aiki, ganin yana aiki da likitan yasa Romeo ya fara bincike a kan likitan da kuma asibitin, nan yaga abun da ya tayar masa da hankali, domin kuwa a wannan asibitin ana kawo maza da dama ana cire musu kodar su, da wasu sassa jikin su irin su ido gaban su da dai sauran, ana sanyawa manyan masu kuɗi na duniya, yasha mamakin ganin duk wannan badaƙala da sheɗan ci ace a cikin garin da yake ake yin su, abun ya ɓata masa rai sosai, ji yake kamar ya tashi ya tafi wannan asibitin yanzu, sai dai dare yayi, kashe laptop ɗin yayi ya ajiye saman bedside drawer ya ɗan yi shiru na yan mintoci kamar mai tunanin wani abu, sannan ya kwanta ya ja musu bargo shida Michael yau ko abinci ma bai jin ci saboda tunanin da ya masa yawa meke shirin faruwa da su ne, ina James ya tafi wayan nan abubuwa sun dame sa, hakan yasa yaji baya jin yinwa kwata kwata.
Ko da ya kwata ya kasa barci tunanin James kawai yake, ya rasa dalilin da yasa yake ji a ransa tamkar zai rabu da James, slowly ya waro dara daran idon sa, ya zubawa Michael kallo, sai barcin sa yake bawan Allah hankalin sa kwance bashi da wata matsala, shafa kan sa Romeo yayi sannan ya mai da idon sa ya lumshe yana tunanin ya zasu yi idan akace yau babu James a tare da su, dan tabbas idan abun da yake zargi a kan James ya tabbata shi da kan sa zai harbe James ɗin da bindiga, dan ya kamanta adalci, to ya zasu yi yau idan akace ya harbe James da bindiga ya mutu, tare suka taso kullun suna tare, duk da baya shiga har kan su, yana matuƙar kaunar su fiye da tunanin mai tunani
A wannan dare dai da kyar barci ya ɗauki Romeo zuciyar sa cike da tunanin ɗan uwan sa.
Asuba ta gari
Mu leƙo Nigeria mu dawo jama'a
# 💞NIGERIA💞
💞KADUNA - GIDAN ABBO💞
Almost 30mins Hajiya ta ɗauka kwance tana mai da numfashi kafin ta ɗago ta kalli Jelly, a hankali ta zuro kafafun ta kasa sannan ta miƙe ta riƙo hannun Jellyn suka nufi bedroom nata tana faɗin "Me yasa kikayi wannan kwaɓen a fuskar ki?" Toro baki Jelly tayi kafin tace "Nifa wanka da kwalliya nayi" shiru Hajiya tayi dan tasan halin Jelly yanzu idan tace zata mata wani magana ko ta mata faɗa idan ta fara kuka sai ta kai dare bata yi shiru ba, gashi bata jin rarrashi ko kaɗan, dan haka Hajiya sai ta rufa wa kan ta asiri tayi shiru taja hannun ta kawai suka wuce toilet
Suna shiga toilet a sukwane Hajiya ta zaro ido ganin lalatan da jelly tayi da sabulai dake cikin toilet ɗin
Bokitin dake cikin toilet ɗin Jelly ta ɗauka ta ɗaura shi saman baf ɗin wanka ya ɗebo duk wani shower gel da su toothpaste da su sabulai su man kamshin baki shaving powder duk ta haɗe su cikin bokitin nan ta gauraye su waje guda, da farko Hajiya ta kasa gane menene ma a cikin bokitin sai daga baya data kalli robobin su shower gel ɗin a gefe ne yasa ta gane menene a cikin bokitin, salati tayi ta sanar da Ubangiji yau ga abun da ya fi karfin tunanin ta, tana tsoron yiwa Jelly wata magana, dan in ta kuskura tawa Jelly maganar da bai mata daɗi ba, idan ta fara yi mata ihu har dare bazata yi shiru ba, sai Abbo ya dawo ya rarrashe ta yayi ta yiwa Hajiya faɗa a kan me zata ɓata mata rai.
Ɗaukan bokitin Hajiya tayi ta fitar waje, dan wayan abubuwa da Jelly ta haɗa sai zubarwa, dan har da su makilin na goge baki ta musu asarar makudan kaya masu tsada.
Jelly na tsaye a cikin toilet ɗin har hajiya taje ta zubar da kwaɓen da tayi ta dawo hannun ta riƙe da wani carton na sabulu mai kyau da tsada, ajiye bokitin tayi ta haɗa ruwan wanka sannan ta cirewa Jelly kaya ta fara yi mata wanka
Ba karamin wahala ta shaba wajen wanke fuskar Jelly, dan mai data damɓara kan sabulu ga foundation da kwalli abun ba'a magana, ita kan ta Jellyn sai da tayi kuka wajen wanke mata fuskar nata.
Bayan Hajiya ta gama mata wanka tsab ne ta ɗaura mata towel suka fito suka nufi bedroom ɗin Jelly ɗin, sosai Hajiya baiwar Allah ta mata kwalliya mai kyau ta sanya mata kaya dogon riga abaya wanda yaya Nawid ɗin ta ya sayo mata, sannan ta feshe ta da turare mai kamshi, tsab ta koma kamar ba ita ba, ta dawo asalin Jellyn daddy, riƙo hannun ta Hajiya tayi suka fito palo.
Saman sofa ta zaunar da ita tace "Ki zauna kiyi kallo bari nayiwa Abbon ku girki kinga yau a part namu yake kuma yamma yayi" make kafaɗa Jelly tayi ta turo baki tana faɗin "Ni a'a zan biki kitchen na taya ki aikin nima" Hajiya zatayi magana Nawid da ya fito yanzu yace "Ai gara duk wani aiki da zaki nayi Ummi ki rinƙa yi tare da ita ko zata koyi wani abun arziki tun da kinga mace ce kuma ba yarinya bace nan gaba kaɗan sai aure" jin abun da Nawid yace yasa Hajiya tace eh yana da gaskiya dan haka sai ta kama hannun Jelly suka wuce kitchen tare
Aiki Hajiya ta fara yi, tana yi tana nunawa Jelly komai dalla dalla, sai gyaɗa mata kai Jelly keyi kamar mai gane duk abun da Hajiya ke faɗe, alhalin ba abun da ke shiga kan ta, miyar steew sukayi ko in ce Hajiya tayi dan Jelly kam tana tsaye a gefe tana ganin duk abun da Hajiya ke sakawa a cikin miyar, ta zuba ido tana kallon yadda Hajiya ke saka su carry kaɗan kaɗan a cikin miyar, ji take kamar taje ta karɓa robar carry ɗin ta bulbula dukka cikin miyar dan ita bata son harka da karanta so take taga ana bulbula komai yaji sosai
Bayan Hajiya ta tabbatar miyan yayi ne sai ta