Showing 150001 words to 153000 words out of 194715 words
Afnan kira, da sauri mahaifiyar Afnan da yaya ta da ita kan ta Afnan ɗin suka fito suna tambayar ko lafiya Hajiya ta shigo tana ihu hakan, rai a matukar ɓace Hajiya tace "Ke Afnan wlh summa wlh ki fita harkan baby, babu ruwan ki da ita, na rantse miki da Allah idan kikayi gigin taɓa hannun yarinyar nan zan nuna miki yadda ake bariki, karkiga kina yin duk abun da kikaga dama a gidan nan muna zuba kiki ido, wlh ba wai kinfi karfi na bane, dan dai kawai bani da lokacin kine, amma a kan baby ina da lokacin ki daga nan har illah masha Allah, ke in takaice miki zance wlh zan iya komai a kan baby" kallon sama da kasa Afnan tayiwa Hajiya zatayi magana mahaifiyar ta ta rigata da cewa "Ke Hajiya Turai bafa tsoron ki muke ji ba zaki zo ki wani tayar mana da hankali a kan wancan shegiya tsintaciyar magen, daman ina cike dake a kan yarinyar, dan Alhaji yazo jiya yana wani ce mana kin kawo yarinya dan Allah kar yan gidan nan su takura mata, to yarinyar yar kanwar uwar ki ce? Ko ma yar kanwar uwar ki ce idan bata mana ba sai munci uban ta a gidan nan bare kuma naji Alhaji yace wai tsintar ta kikayi, to wlh tsintaciyar mage bata isa ta zo tace zata takurawa yan gida ta hana su jin daɗi ba kinji na faɗa miƙi, Afnan kuma koma me tayiwa yarinyar dedene, Afnan ki ci uban ta dan ba gidan uban ta bane, na uban kine" ita maman Afnan a tunanin ta rigima ake dan Afnan ta daki Jelly bata san kan magana ba
Aliyu yayan Afnan ne yace "Ummi kiyi hakuri kije, dan Allah komai ta wuce haka kinji?" Ita kuwa Hajiya jin abun da maman Afnan tace yasa tayi tunanin kenan da sanin maman Afnan, Afnan ke yin lesbian? Ta tambayi kan ta tambayar da babu amsa, amma a zahirin gaskiya maman Afnan bata san Afnan na wanna aika aikan ba, shikan shi yayan nata bai sani ba, su suna tunanin duk wannan masifar da Hajiya keyi tanayi ne dan Afnan ta daki Jelly, basu san dawar garin ba, shi yasa maman Afnan ta zage dantse dan tarewa yarta faɗa, shi kuma yaya Afnan kasan cewar baya son hayani sai yayi ta basu hakuri.
Da kyar ya samu Hajiya ta hakura ta wuce ta koma part nata, tana shiga palon ta ta samu Jelly zaune tana kallon Tv, da Jelly ta fito ne zata bi Hajiya, sai taga ana nuna cartoon a Tv sai ta zauna kallo.
Hannun ta Hajiya ta ja suka bar palon zuwa nasu part ɗin. A palon part nasu Hajiya ta zauna ta zaunar da Jelly gefen ta, cikin nitsuwa tace "Baby daga yau karki sake fita babban palo bana so, kiyi zaman ki a nan, ga Tv nan zan rinƙa kunna miki, kuma idan wani ya sake cewa ki zo a gidan nan karki yarda ki je, ba ruwan ki da kowa karki sake yiwa kowa magana daga ni sai Abbo sai yaya Nawid, mu kaɗai zaki rinƙa yiwa magana, kuma mu kaɗai ne idan munce kiyi abu zaki yi kin ji ko?" Kai Jelly ta gyaɗawa Hajiya alamar taji.
Cab lalai Hajiya kin kashe maciji baki sare kai ba, dake da Abbo da Nawid ne kawai zaku mata magana tayi abun hmmm, muje zuwa.
Wunin ranar dai Jelly bata sake leƙa babban palon ba tun safe da abun ya faru, a nan tayi zaman ta har dare, idan ta gaji da zama ta kwanta, idan ta gaji da kwanciya ta shiga bedroom ɗin Hajiya su ɗan yi hira, Hajiya na koya mata karatu, amma fa ba abun da take gane wa.
Da daddare suna cin abinci ne Nawid ke sanar da Ummi zai yi tafiya zuwa Katsina next week, kasan cewar Hajiya Turai ya ce ga sarkin matsina, Nawid jikane ka sarkin, hakan yasa yake yawan kaiwa kakan nin sa ziyara
Da fara'a Hajiya ta amsa masa da to dan tana son daman zumuncin ta da yan uwan ta maza da ƴaƴan su ya kara karfi sosai yafi haka,
Yanzu Nawid na daina hantarar Jelly dan ya fahimci haka take, kuma abun ya haɗu mata da ciwo, shi yasa baya damuwa idan tana wani shagwaɓar nata, yanzu in tace masa yaya yana amsawa har ya biye mata, dan Hajiya ta masa kanwar dole, kuma haka ya karɓa ba yadda zai yi, wani lokaci ma idan Jelly ta tayar da ballin ba zata ci abinci da hannun ta ba, shi yake bata a baki da kan sa, ko Abbo.
Bayan sun kammala cin abin ne kowa ya miƙe ya nufi bedroom nasa, ita kuma Hajiya ta riƙo hannun Jelly suka tafi bedroom nata, dan sun saba sai Jelly tayi barci Ummi ke mai data bedroom nata, dan bata yarda tayi barci ita ka ɗai, wani lokaci kuma a bedroom ɗin nata suke zuwa su kwanta har sai tayi barci, sai su salallaɓa su fice su koma nasu bedroom ɗin.
Yau Hajiya ta gaji sosai, suna kwanciya ba jimawa barci ya ɗauke ta, saura Abbo da Jelly, daman Jelly na ta gefen Hajiya, ma'ana Hajiya ce a tsakiyar su.
Miƙewa Abbo yayi, yayi kwanciyar rigingine yana fiskantar Jelly, ya zuba mata ido yana ta kallon ta daga sama har kasa, yana son taɓa ta yana kuma tsoron kada ta masa ihu ko ta tashi Hajiya daga bacci, dan yasan halin Jelly sarai ba'a mata abu tayi shiru, kana mata abu da ɗumi ɗumin sa zata faɗa wa Hajiya ba ɓata lokaci, tunani ya fara yi ya zai yi, dan shi gaskiya yana matikar son Jelly, sai kallon ta yake ita kuma tana kwance ta rintse ido amma ba tayi barci ba, dan ga idon nata nan sai motsi suke, wutar ɗakin a kunne yake dan Jelly bata zama a ɗaki sai da wuta a kunne, tana tsoron duhu, wani lokaci sai tayi barci hajiya ke zuwa ta kashe mata wutar, amma fa idan ta tashi cikin dare, to akoi dirama dan ihu take kamar zatai hauka, da kyar ake lallaɓa ta ta mai da barci, ta hanyar kunna mata wutar ɗakin.
Ahankali ya kai hannun sa zai taɓa ta, sai kerma hannun nasa keyi kamar mazari, ya kasa taɓa ta, yana son taɓa kuma yana tsoron tsiwarta, sai dai abun da bai sani ba, yanzu Hajiya tace duk abun da Abbo da Nawid suka ce mata tayi to tayi shi, kuma ita Jelly duk abun da Hajiya tace tana yin sa ba ɓata lokaci, sannan in dai Hajiya tace tayiwa wani biyayya tofa kome zai mata ba lallai ta faɗa wa Hajiya ba, tun da Hajiyar ce tace tayi.
Haka Abbo yayi ta kokarin taɓa Jelly yana tsoro, har barci ya ɗauke Jelly, haka ya zauna ya zuba mata ido yana ta kallon ta, yana kara jin haunar ta a ransa.
Sai wajen 1 na dare sannan barci ya ɗauke sa, yau kasan cewar Hajiya ta rigasu yin barci, sai Abbo bai ce ta tashi ta kai Jelly bedroom nata ba, dan shima hakan yake so Jelly ta rinƙa kwanciya kusa da su, shi yasa ma baya wani damuwa wajen sa Hajiya ta koya mata kwana ita kaɗai a ɗaki, shine ma mai kara injiza abun, da Jelly ta fara cewa bata so, sai ya wani ce a'a a barta tun da bata so kar a wani takura mata, shi ya fara kawo shawarar tun da tana tsoron kwanciya ita kaɗai to su rinƙa kwanciya da ita sai tayi barci su ɗauke ta su mai da ta bedroom nata, insert of ya sanya Hajiya ta koya mata kwana ita ɗaya, sai ya kara dagula komai dan shima yana ra'ayin hakan. A ranar dai a ɗakin su Jelly ta kwana.
Mu leƙo Rimsha mu dawo
👹DAULAR MUTUWA👹
Yanzu dai ba laifi shakuwa ta shiga tsakanin Rimsha da duna, sai dai ita Rimsha tana biye masa ne kawai bisa umarnin baba na cewa ta biye masa har Allah yasa ya musulunta imani ya ratsa shi ya daina shan jini da sauran su, wannan dalilin yasa take biye masa, yanzu har zama take suyi ta hira, yana mata tambayoyi a kan addinin Musulunci tana bashi amma with her confidence, dan ita ma tana burin ya shiryu ya musulunta ya dai na duk wani abun da yake ya koma ga Allah, sai dai kullun in zata bashi amsa a kan addini, sai Queen ta shaƙe ta, tayi ta fama har sai duna ya taimaka mata, kasan cewar shi ma irin sune, da jikin sa ya haɗu da nata kaɗan, tofa dole su sake ta.
Yauma kamar kullun suna zaune saman bencin duna suna hira, shi kuma yana zaune daga ɗan gefe da su, saman wata kujera da ya bayyanar da ita da tsafin sa, yanzu baya zama kusa da su sosai a ɗan gefe yake zama, saboda sun faɗa masa a addinin musulunci ba'a yin haka, saboda son da yake wa Rimsha yasa yake girmama addinin ta da kuma dokokin addinin nata.
Sai hira suke ita da su Ayla cikin nishaɗi, yau basu je wajen baba ba, sun zauna wajen, zuba musu ido kawai duna yayi yana kallon yadda Rimsha ke ta murmushi kyakkyawan dimple nata yana lotsawa gwanin ban sha'awa hakan ba karamin kyau yake karawa face nata ba, daman abu huɗu zuwa biyar ne a face ɗin Rimsha da yafi ɗaukan hankali duk wanda yayi ido huɗu da ita, na farko wayan nan kyawawan dara daran sleeping eyes ɗin nata farare kal kamar audiga, ba karamin tafiya da imanin ɗan adam suke ba, kasan cewar idon nata yayi daban, sai ka tara mutane sama da dubu baka samu biyu masu irin wanna idon ba, shine babban abun da yafi jan hankali mutane a face nata, na biyu kyakkyawan dimple nata, idan tana murmushi ko tana magana, ko baka son ta sai ka tsaya ka kalleta, saboda dimple ɗin nan, ba karamin kyau yake kara mata ba, ɗan siririn open teeth, dake tsakanin hakwaran ta da suke farare kal a baya amma yanzu saboda da hannu take brush babu brush hakan yasa hakwaran nata suka rage haske, amma still suna da hasken sai dai ba kamar lokacin da suke tare da daddyn su ba, abu na huɗu ɗan bakin ta, wow idan tana magana abun sai wanda ya gani, laɓɓan ta na sama design of heart ne ga bakin nata ɗan karamin dashi launin pink color kamar wadda ta sanya lipstick, hancin nan nata har baka ɗan siriri kamar karas Masha Allah, ga bakin saje kwance a gefen kumatun ta.
Sai hiran su suke duna ya tsare su da ido, can kome ya tunan ya miƙe yazo ya tsugunna a gaban ta, tare da zuba mata ido a hankali yace "Me yasa idan kuna magana kuke yawan sanya Annabi Muhammad? Waye shi?" Dawo da kallon ta kan face nashi tayi cikin nitsuwa tace "Shi ne Babban abun soyuwa a gare mu, kuma shine annabin karshen da baba ya faɗa maka ranar, duk wani cikakken musulmi yana son Annabi Muhammad" "eh nasan kuna son shi kam dan baku magana ɗaya biyu baku kira shi ba" yar murmushi Rimsha tayi kafin tace "Saboda son da muke masa ne yasa har a zamanin baya kafin yazo duniya ya samu takwara dayawa, sosai jama'ar zamanin da kafin yazo suka masa takwara" zaro ido duna yayi kafin yace "To bai zo ba kuma ya akayi suka san shi har suka masa ta kwara? Waye ya faɗa musu sunan shi da har zasu masa takwara? Bayan ni nasan sai an haifi yaro ake sanin sunan da za'a sa masa" ɗan kawar da idon ta tayi daga kallon sa kafin tace "Annabi Muhammad (SAW) an san shi ne tun kafin a ganshi, kuma an sanshi ne tun kafin a haife sa, domin yazo a littafai da dama, sunan sa ya bayyana a littafai irin su attaura, injila, zabura, so already wayan nan littafai sun bayyana zuwan sa da sunan sa da yanayin da zai zo, da kuma in da zai bayyana, waye shi da sauran su, shi yasa jama'a suka rinƙa masa takwara saboda son da suke masa, muma yan zamanin yanzu muna kaunar sa fiye da rayuwar mu, ni kullun cewa ma nake da azamanin sa a ka haifeni dana more" shiru duna ya ɗan yi kafin yace "Kwarai kuwa na san kuna son shi, nima shaidane dan kuwa akoi wata mata dana taɓa shanyewa jini a kasuwa, lokacin na riƙeɗe na dawo kamar yadda kika ganni yanzun nan, na shiga cikin mutane, a kasuwa na ga matar tana sai da kaya, kawai naji ina son shanye jinin ta, to lokacin akoi wata waƙa da ta kunna suna faɗin annabi kwarai kasan gaibu, na kasa manta wannan wakar ita kan ta matar na kasa mantawa da ita, ban san ya akayi ba ita ce mutun na farko dana taɓa shan jinin ta dana kasa mantawa, bayan na sha jinin nata sai naji ban ji daɗi ba, har yanzu na kasa mance ta" jinjina kai Rimsha tayi har idon ta ya kawo ruwa saboda tausayin matar a hankali tace "Baka kyau ta ba, amma dai karka ɗauka abun da suke faɗe a wakar gaskiya ce, domin Annabi bai san gaibu ba, dalili kuwa shi da bakin sa yace bai san gaibu ba, a lokacin da sayyidina Abubakar ya tambaye sa yaushe za'a tashi kiyama, sai yace wa sayyidina Abubakar sanin gaibu sai lillahi shi bai sani ba, Allah ne kaɗai ya san ranar tashin Al kiyama, kaga kenan idan da annabi yasan gaibu da muma mun san lokacin da za'a tashi kiyama dan da zai faɗa wa sayyidina Abubakar, shi kuma zai ruwaito mana hadisai, abu ɗaya ne yasa mutane ke ganin kamar annabi yasan gaibu, shine mafi yawancin lokaci Allah yana masa wahayi mala'ika Jibril yazo ya faɗa masa Allah ya bawa wanna sahabi aljanna, ko kuma Allah ya saukarwa wannan sahabi wata ni'imar, to idan mala'ika ya isar masa da wanna wahayi, shi kuma sai ya sanar da Sahabban sa, hakan yasa mutanen mu na yanzu suke ganin kamar annabi yasan gaibu tun da yana faɗin abubuwan da basu kai ga faruwa ba, kamar dai yadda ya bayyana Allah ya baiwa su sayyidina Abubakar aljannan tun suna raye, shi yasa rashin fahimter ce kawai da mutane ke samu, mafi yawancin mutane suna kan dai dai bisa nasu fahimter, basu kauce hanya ba kawai basu fahinci abun dai dai bane"
hannu ya kai zai shafi kumatun ta, sai kuma ya fasa, cike da kaunar ta yace "To ni dai gaskiya addinin ku yana burgeni, ta in da kuma yake burgeni in da akace matar ka kai kaɗai zaka taɓa ta ba wanda zai taɓa maka ita, wannan abun yamin daɗi sosai, addinin akoi tsabta sosai, kinga a baya zamu kwanta da duk macen da muke so, kuma ina da tabbacin kafin mu wasu sun kwanta da ita, hakan tsam ba tsari, ace mace ɗaya maza dayawa suyi ta kwanciya da ita abun ba ɗaɗi, amma addinin ku yayi hani da wanna gaskiya naji daɗi kuma na jinjinawa addnin nan naku" cool murmushi ta saki taji daɗi duna ya fara yaba addinin musulunci, da alama ya fara hawa kan hanya ma dai'dai ciya hakan ba karamin farinciki ya sanya su ba, dukkan su har da su Ayla.
A wanna yanayi Mustapha yazo ya same su, dan yanzu yana zuwa suyi ta hira da duna sun zama kamar friend, yana zama Rimsha ta miƙe tana faɗin "Ina zuwa Ayla bari na je ɗaki na ɗauko apple na najiya" to kawai suka amsa mata da shi, sannan ta wuce ta bar wajen, su kuma suka ci-gaba da hiran su.
Tazo zata shiga ɗakin nasu, sai taga yar siririyar hanya daga ɗan gefen ɗakin nasu, Rimsha da karambani tace bari ta leƙo taga menene a wajen, ɗan karamin hanya ne, ga wani fitinanniyar wari bala'i dake fitowa daga wajen, haka ta kutsa ta wajen tare da toshe hanci ta tana lallaɓawa saɗaf saɗaf kamar wata ɓarauniya har ta kai karshen hanyar, ba tare da su duna sun ankara da ita ba, suna ta hiran su
ko da taje karshen hanyar sai taga ba wani abu a wajen sai wani katanga mai ɗan tsawo daya musu katanga, ma'ana ya raba su da wan can part ɗin.
Kamar a kafarki taji kafar ta ya tsunduma cikin wani abun, cikin tsoro a hankali ta kai kallonta kasa, nan taga wani irin jini mai bala'i kauri da yauki, cikin jinin duk guda gudan naman jikin mutun, ta wani gefen ma har da kashi ɗan adam, ɗago idon ta tayi a razane ta kalli gefe gefen wajen da kyau, gaba ɗaya kashin kwarangal na mutane ne, ga kuma naman jikin mutun wadda bai gama murmushe wa ba, kasan wajen wani daskararren jini ne mai balai wari, ga kuma wani sabon jini na malala a saman wannan daskararren, da alama yanzu ake zubar da wannan jinin, wani mugun tsoro ne ya dira mata a ranta lokaci guda, nan take jikin ta ya fara ɓari, wani irin wahalallan yawu ta haɗiye da kyar, nan take idon ta ya rena fata, wani gumin wahala ya fara karyo mata.
Amma saboda fitina irin na Rimsha sai da ta kama katangar nan har da yar tsallen ta, ta leƙo, dan ta dage sai taga daga ina jinin nan ke fitowa.
Nan fa idon ta suka gane mata abun da kwakwalwa ba zai ɗauka ba, wani mahaukacin ihu ta fasa tare da sakin katangar, kamar zararriya haka ta bazama ta fito daga wajen, a guje su duna sokayo kan ta, saboda ihun ta da sukaji
Tun da yaga ta in da ta fito yace shikenan kuma mawuyacin abune yau Rimsha ta rayu a gidan nan, ita kuwa sai ihu take kamar wata zararriya, tunani duna ya shigayi ya zai yi ya kuɓutar da Rimsha daga sharrin su Gujungu, dan yasan definitely wayan nan magicians dake wajen zasu biyo bayan ta dan sun jiyo ihun ta, kuma tabbas bazasu barta da rai ba,