Showing 111001 words to 114000 words out of 194715 words

Chapter 38 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

983

nata har na Rimsha, kasan cewar sauri take yasa bata wani tsaya neman wayoyin ba ta wuce ta nufi bedroom na mum dan ta ɗauko ATM card na mum ta haɗa da nata ko da kuɗin account nata ba zai isa ba, dan ba wani kuɗin kirki ya rage a account ɗin nata ba.

Nan taga ikon Allah dan watsa ɗakin mum da a kayi yafi yadda a ka watsa nasu, haka ta tsallake kayan ta wuce ta duba ATM card na mum ta ɗauko ta fice daga ɗakin cikin sauri.

Sadiq na tsaye a harabar gidan yana jiran ta bai san meke faruwa ba kuma itama bata sanar da shi ba, tana fitowa suka fice daga gidan tare da rufe ko ina na gidan, suka nufi bakin hanya

Suna tafiya ne Sadiq yace mata "da kika sanya face ɗin nan kin canza ba wanda zai ce kece" bata gane me ya faɗa ba sai dai kawai tace masa "Okey" shiru ya mata har sukaje wajen mai POS ta miƙa ATM nata tace ya bata 20k cikin sauri mai POS ya ciro mata kuɗi kasan cewar yaga kamar suna sauri, ansan kuɗin tayi tare da ATM nata suka wuce suka hau a daidaita sahu suka koma asibiti.

Kamar yadda suka bar su mum haka suka dawo suka same su, sauri sauri Jehan taje wajen sai da kati ta miƙa 1k nan suka haɗa mata kati Sadiq na tsaye a gefen ta, suka miƙo mata kati da canji, kati kawai ta ansa bata ansa canji ba tace bata buƙata, hannu Sadiq yasa ya ansa mata canjin 800, ya miƙa mata a wulakance tace bata buƙata ta bashi, bai damu ba ya zura kuɗin cikin aljihun sa suka wuce suka koma wajen su mum dan su samu damar ganin likita.

A takaice dai sun ga nurse sannan an basu gado a kan mum ta kwanta likita zai zo ya dubata, Jehan ce ta biya kuɗin gadon suka shiga da mum ciki, kwalla Jehan ta fara yi ta zauna kusa da mum ta riƙo hannun ta tana karan to mata duk addu'ar da yazo bakin ta, while su kuma maman Sadiq da gwaggo suna zaune daga ɗan gefen gadon ta kafan mum sunyi tagumi jugum jugum gwaggo na hawaye ta sunkuyar da kan ta kasa, shi kam Sadiq bakin window ɗakin yaje ya tsaya ya dafe kan sa suna jiran dr yazo ya duba mum suji meke damun ta gashi dai ko motsi bata yi kamar ta mutu.

To bari mu leƙa Rimsha kafin dr yazo muji meke damun mum

👹DAULAR MUTUWA👹

Zaune a wajen Rimsha ta kwana, ko motsi bata iyayi saboda matsanancin yinwa da kishin ruwa da take ji, yau kwanan ta na huɗu kenan ba abinci ba ruwan sha, duk da cewa kwana biyu daga ciki a sume tayi su, sosai Ayla ta tausayawa Rimsha duk da cewa bata san labarin taba bata san daga ina Rimsha ɗin ta fito ba, amma dai tana ji a jikin ta tabbas Rimsha bata saba da rayuwar wahala ba, ba yar gidan malam Shehu bace, daga ganin fatar jikin ta da yar gidan hamshakin mai arziki tayi kama ko dai yar gidan sarauta ko yar gidan wani shugaba, haka Ayla ta rinƙa ayyana Rimsha yar gidan wanene a ranta, har rana ya ɗaga, kwata kwata Rimsha bata iya magana ko motsa bakin ta bata iya yi.

Sai da rana ya ɗago sosai ne sannan magicians ɗin suka zo suka buɗe wa su Rimsha kofar ɗakin nasu suka turo musu abinci, sannan suka fice suka bar kofar a buɗe, da sauri Ayla ta jawo kayan abincin ta ɗauki jug ɗin ruwan da suka kawo masu da sauri ta kafawa Rimsha a bakin ta, da kyar Rimsha take iya haɗiyar ruwan saboda wahala da ta sha

Ka ɗan ta sha ruwan ta fara kwarara amai tana tari, da sauri Ayla ta riƙe ta tana ɗan bubbuga mata baya, sosai Rimsha tayi aman ruwan da tasha kafin ta koma ta jingunu da jikin bangon, sakin ta Ayla tayi ta matso kusa da Kausar dake kwance rai a hannun Allah itama saboda yinwa, haka Ayla ta ɗago kan ta ta fara bata ruwan, itama Kausar kamar Rimsha kaɗan ta sha ruwan ta fara amai.

Sai bayan sun ɗan huta sannan Ayla ta sake basu ruwan kaɗan kaɗan, a wannan karon basu yi amai ba..


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

B 💞Star Lady💞



TRIPLET'S💞




*THE BEGINNING*



💞STAR LADY💞







WhatsApp me for more information 09162620621


Episode 24





Sai bayan sun ɗan huta sannan Ayla ta sake basu ruwan kaɗan kaɗan, a wannan karon basu yi amai ba, yau dai Ayla bata ci abincin ba ta kyale musu a kan su suci tun da ita taci jiya kasan cewar abincin ba yawa, kallon abincin da kyau Rimsha tayi kafin ta ɗago ta kalli Ayla cikin raunanniyar murya tace "Ayla wannan miyar ai kamar naman mutun ne a ciki" gyaɗa mata kai Ayla tayi kafin tace "Eh naman mutun ne a ciki, nima kullun iya shinkafar kawai nake ci bana sa miyar, sai kuma fruits ɗin nan shima ina cinyewa" shiru Rimsha tayi tana mamakin a ran ta tana faɗin "Wa ina zubillah ya Allah ka kawo mana ɗauki, ya Allah dan karfin mulkin ka, dan karfin izzan ka da girman ka ya Allah ka tarkatsa wannan gida na azzalumai cikin gaggawa, ya Allah ka kawawo bayin ka musulmi ɗauki, Allah kayiwa wa'yannan azzaluman hukunci mai tsanani tun a duniya, ya Allah kai ka ɗai kasan adadin rayukan bayin ka da ya salwanta a nan" zuba mata ido Ayla da Kausar sukayi suna kallon yadda ta zubawa abincin dara daran sleeping eyes tana tana zancen zuci.

Ganin ta ki dai na kallon abuncin ne yasa Ayla ta ɗan taɓa ta, ɗago dara daran sleeping eyes nata tayi ta kalli Ayla ɗin "Kuci shinkafar mana, baiwar Allah ni gashi baki faɗa mana sunan ki ba ma" cewar Ayla, lunshe ido Rimsha tayi tare da mayar da kan ta ta jingina da jikin bangon ɗakin tana sauke ajiyar zuciya a hankali.

Cikin sanyin murya tace "Sunana Rimsha kuma ni ba zan iya cin wannan shikafar ba, dana ci namar mutun gara yinwa ta kashe ni" girgiza kai Ayla tayi kafin tace "A'a ni bance kici namar ba miyar ma gaba ɗaya bance ku ciba iya shikafar kawai nace kuci sai kuci fruits ɗin, shi kuma miyar ku kyale musu abunsu zasu zo su ɗauka anjima, kuci da wuri mu fita waje mu sha iska, muyi hira da sauran yan gidan zuwa yamma za'a rufemu" kanta na jingine da jikin bangon ba tare da ta ɗago ba ta waro dara daran sleeping eyes nata a kan face ɗin Ayla kasa kasa tace "Ni ba zanci shinƙafar bama, dan ko nace zan ci amai kawai zanyi dan haka kawai kuci" tayi maganar cikin harshen turanci, kallon kausar Ayla tayi kafin tace "Matso kici kinji?" ba musu Kausar ta matso ta fara cin gayan shinkafa babu miya

Ɗaukan Apple Ayla tayi ta sanyawa Rimsha a hannu tana faɗin "kiyi hakuri kici wannan kinji?" rike apple ɗin Rimsha tayi tana matsar kwalla haka ta kai apple ɗin ɗan bakin ta, ta ɗan ciza tana matsalar kwalla.

Haka Rimsha wannan apple ɗin kawai taci yayin da ita kuma Kausar taci shikafa fari ba miya sannan suka haɗa da fruits ɗin ita da Ayla su kaci.

Bayan sun gama ne Ayla tace suzo su fita waje, make kafaɗa Rimsha tayi tana faɗin "No i can't go anywhere" "Kiyi hakuri muje mu ɗan kalli hasken waje kinji ko" Ayla tayi maganar a raunane

Da kyar Rimsha ta iya dafa bango ta miƙe suka nufi waje sai dafa bango take suka fito tsakar gidan, nan fa Rimsha taga duniya ga yara nan har da manya mafiyawancin su suna zaune ne a bakin kofar ɗakin su, dukkan su suna bushe kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin yinwa da wahala.

Saman wata yar benci Ayla ta wuce taje ta zauna ta zubawa yan gidan ido wadda ko wace ke zaune a kofar ɗakin ta, duk yinwa ya cinye su, sun rame sun bushe sun zama kamar kashi da rai, ko maganar kirki basa iyayi, saboda yinwa mafi yawancin su basa cin abincin gidan kasan cewar da naman mutun ake miyar sai dai suci fruits wasu suci da gayar shinkafa wasu kuma suci fruits zalla amma basa taɓa shan miyar,

kusa da Ayla Rimsha ta zauna tana bin gidan da kallo tana mamaki a ranta.

Can idon ta ya hango mata wani mutun dake zaune ya haɗa kai da gwiwa yayi shiru, zuba masa ido Rimsha tayi na yan mintoci kafin ta miƙe da kyar ta nufesa
a tsorace Ayla tace "Meesha karkije wajen mutumin nan fa zai iya marinki dan bai da mutunci ko kaɗan" a ta kai ce Rimsha tace "Sunana Rimsha ba Meesha ba" da sauri Ayla tace "Irin sunan wata friend na a islamiyar mu ne gare ki kuma ita Meesha muke ce mata shiyasa na kiraki hakan amma kiyi hakuri yanzu dai ki dawo karki je wajen sa" shiru Rimsha tayi kamar bata ji me Ayla ke faɗe ba ta wuce abun ta ta nufi mutumin tana jan kafa da kyar.

A gaban sa ta tsugunna cikin sanyin murya tace "sannu" shiru yayi bai mata magana ba kuma bai ɗago ba, sake mai mai ta maganar nata tayi nan ma bai ɗago ba, sai a karo na uku ne ya ɗago a zafafe yana zaro ido ya ɗaga hannu zai mareta kenan, a sukwane ta rimtse idon ta a hankali ta furta Wayyo Allah na, zaro ido sukayi dukkan su lokaci guda jin Rimsha ta iya furta sunan Allah, cikin sauri shi ma mutunmin ya kwatanta ko zai iya kiran sunan Allah amma ina ya kasa, ita ma Rimsha tayi kokarin sake kira amma ina sunan yaki fitowa, haka ta hakura ba dan taso ba

Zuba mata ido mutumin yayi kafin yace "Ya sunan ki" cikin nitsuwa tace masa "Rimsha" a hankali ya mai mai ta sunan, ba karamin mamaki su Ayla suka shaba ganin Rimsha na hira da mutumin nan, "Kai fa ya sunan ka?" Ta tambaya tana tsare sa da dara daran sleeping eyes nata, kasa kasa yace "Mustapha" shiru suka ɗan yi na yan mintoci kafin yace "Ya akayi kika zo daular mutuwa gidan da ba'a shiga a fita, duk wanda ya shiga to kai tsaye zai tafi in da ba'a dawowa?" Hawaye Rimsha ta fara yi ta fara bashi labarin yadda a kayi ta tsinci kan ta a daular mutuwa, sosai ya tausaya mata, sai dai abun mamaki shi da ta tambaye sa ya akayi yazo nan, ya kasa faɗa mata dan ya kasa tuna komai, yayi mamaki sosai ma jin ita ta iya tuna yadda a kayi ta shigo gidan, shiru yayi ya zuba mata ido yayin da ita kuma take ta kokarin tuna wani abu mai muhimmanci daga cikin rayuwar ta, amma ina ta kasa tunawa, haka suka yita hira da Mustapha har rana ya ɗago sakiyar duniya, ma'ana azahar tayi kenan, lokacin azahar na cika Rimsha ta fara jin gaban ta na faɗuwa, dan har da Sallah sun mantar da ita sai dai da yake abun na jikin ta da time yayi zata ji jikin ta har kerma yake sai dai ta kasa gane hakan.

Bayan sun yi sallama da Mustapha ta koma wajen su Ayla ta zauna saman bencin in da ta tashi, cike da mamaki Ayla ta tambaye ta a kan hirar me sukayi da mutumin nan, nan ta basu labari sama sama, sun sha mamaki sosai dan Mustapha ba ya yiwa kowa magana a gidan kullun yana zaune shiru kamar kurma.

Suna zaune a wajen har mamallakin bencin yazo wato mai gadi su mai kula da su a part ɗin nasu, gidan Part by part ne kowani Part su barbushi suna ajiye mutun ɗaya mai kula da yan wannan part ɗin

kallo ɗaya Rimsha ta masa taji ta tsani mutumin nan, bata son kallon sa, wani mummuna da shi mai kiran samudawa sai dai da alama cikakken mutun ne ba aljani bane, matsa masa gefe Ayla tayi a kan ya zauna, washe baki yayi yana faɗin "Kiyi zaman ki bari na zauna a kasa dan naga yau da baki kika zo da alama munyi sabbin baki kenan" dariya Ayla tayi ka san cewar sun saba da mutumin tace "Kai dai duna bari yau na haɗu da yan uwana ne" kara washe baki yayi kafin yace "Suma musulmai ne kenan?" Jin ya ambaci sunan musulunci yasa Rimsha ta ɗago a sukwane tana kallon sa yayin da ita kuma Ayla tace "Me kuma musulmai" kallon tsab yayiwa Ayla kafin yace "Kema an juya miki tunani kenan?" Shiru Ayla ta yi dan kwata kwata ta dai na fahimtar abun da yake faɗa, ita kuwa Rimsha da Allah yasa tunanin nata bai gama tafiya dukka ba abun yana mata kamar gizo ne yazo ya koma, wani lokaci har sunan Allah tana iya kira wani lokaci kuma tayi kokarin kira amma sai ta kasa, hakan ku ya samo asali ne saboda addua'o'i da mum ta biya kuɗi a ke ta mata ga saukan Al Qur'ani mai girma da ake ta mata hakan yasa ita kaɗai ta saura a gidan mai iya kiran sunan Allah time to time, kuma time to time tana iya tuna wasu abubuwa masu muhimmanci da ko wani musulmi ya kamata ya kasance yana aikata su wato askar.

Jin mai gadin nasu ya ambaci sunan musulunci ne yasa Rimsha ta miƙe ta karisa gaban sa ta tsugunna tana faɗin "Kai kasan musulci ne?" Gyaɗa mata kai yayi kafin ya fara mata bayani "Lokacin da a ka kawo Ayla gidan nan tana yawan faɗa min ita musulmace daga baya suka juya mata tunanin kasan cewar basa son wannan addinin ko kaɗan shiyasa duk mai irin addini in suka kawo shi sai sun mantar da shi komai" cikin sauri Rimsha tace "Amma to kai me yasa baka manta komai ba" zaro mata idon sa kamar na mujiya yayi har sai da ta tsorata ganin idon nasa sun sauya sun koma green color, yar dariya yayi kafin yace "Kin ji tsoro ne?" Gyaɗa masa kai tayi ta kasa magana "To karkiji tsoro, kawai na ɗan nuna miki dalilin da yasa ni basu juyamin tunani na bane" "Ban gane ba" ta faɗa a tsorace, kara kwashe baki yayi kafin yace "To ina nufin da ni da su duk ɗaya ne, nima magicians ne sai dai ni ban cika cin namar mutane sosai ba, kaɗan kaɗan nake ci time to time kuma ban na shan jini sosai sai in naji kewa" mamaki ne ya kamata ta kasa magana ta yi jugum ta zauna shiru tana tunanin to me yasa shi yake dariya har da wasa da Ayla su barbushi kuma basa yin hakan.

Kyasta mata munanan yatsu hannun sa yayi a kan face ɗin ta kafin yace "Kin tsoratane?" Gyaɗa masa kai tayi "To karkiji tsoro ke ba zan cinye ki ba, because you look so beautiful, your face look like moon, ba zai yi kyau ba a ce ancin ye yarinya mai kyau kamar ke" sai lokacin ta tuna tambayar da take son yi masa, cikin sauri tace "Kai musulmi ne?" Zaro mata wannan idon nasa mai kama dana mujiya waje yayi nan take idon nasa suka sauya color zuwa purple color, kan kace me kamannin sa sun sauya ya fara huci da gurnani mai razana kwakwalwa ɗan adam, ihu ta fasa tana kokarin niƙewa yayi saurin riƙo rigar ta, cikin fishi tace "Karka sake taɓa ni dan ba haka aka koya min a gida ba" janyota yayi yayi wurgi da ita ta faɗi kasa tare da sakin ihun azaba,

gaba ɗaya wayan da suke wajen sai da suka miƙe tsaye har da Mustapha ka san cewar sun san halin mai gadin yana da dariya da mutane, dan duk gidan ma shi kaɗai ke dariya amma kuma yana da fushi sosai, kuma duk yadda kuka saba da shi idan ka masa ba dai dai ba nan take yake kashe mutun, yana da wasa da dariya amma bai da mutunci idan ka taɓo sa, a fusace yace "Yau dole amin fefesunki a gidan nan idan ba haka ba ba zaman lafiya" da sauri Ayla ta zube kasa tana masa kirari tana rokan sa a kan yayi hakuri Rimsha bakuwa ce bata san komai ba, sai wani huci yake yana gurnani kamar wani basamude

Ban da kuka ba abun da Rimsha keyi dan wurgi da ita da yayi ta bugu da kasa sosai taji zafi.
Sosai gaba ɗaya wayan dake wajen suka duƙa suna rokan duna a kan yayi hakuri ya kyale Rimsha,
da kyar ya yarda zai hakura amma sai Rimsha ta taso da kan ta, ta dafa kafafun sa ta bashi hakuri, cikin sauri Ayla taje ta taimakawa Rimsha ta miƙe suka dawo gaban shi suka duƙa, cikin kuka Rimsha ta bashi hakuri, lokaci guda taji tsanar mutumin ya kara ninkuwa a ranta, mummunar katon kafar sa yasa ya hanɓare ta sai da tayi baya ta faɗin ta buga kan ta a kasa, sannan yayi wucewar sa yabi ta wata kofa ya bar wajen, sai kuka Rimsha take da kyar Ayla da Kausar suka ɗaga ta, ganin duna ya tafi yasa Mustapha ya kariso wajen su dan ya ja wa Rimsha kunne a kan tabi a hankali karta kuskura ta sake bari tayi wani gangancin, sosai Rimsha ta ji shawarar Mustapha dan ta ji wahala wurgi da ita da duna yayi, kuma tayi danasanin shiga sabgar sa da tayi, da haka Rimsha tace ita ɗaki zata koma ba zata sake fitowa waje ba har ta mutu, Ayla da Kausar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login