Showing 69001 words to 72000 words out of 194715 words
da ya kawo shi toilet ɗin mai gadi amma abun yaci tura dan ya kasa tuna komai, shiru sukayi suna ta mamaki, ita dai Hajiya duk da ta kasa tuna komai hakan bai hana tasa su Imran su mata saukan Al Qur'ani mai girma ba dan tana ji a jikin a koi matsala,
haka ko a kayi Hajiya da Abba suka shirya suka tafi yiwa yan uwan Alhaji Mustapha jajen ɓatan Alhaji Mustapha da Hajiya Zainab, su kuma su Imran suka zauna shi da Akil da Akila suka fara karatun Al Qur'ani mai girma dan su sanu saukin matsalar su.
Bari mu leƙa KANO mu dawo kila kafin nan sun gama karatun.
_______________________________
*KANO*
Daddy na zaune saman sofa shi da Jelly ɗin sa sai buga game suke a Palo, Jelly sai winning na sa take tana ta dariya, shi daman bai san ma me yake taɓa wa ba, saboda damuwa da suka masa yawa
Yayi nisa cikin tunanin da yake wayar sa ta fara kara alamar shigowar kira, da sauri Jelly ta miƙe ta ɗauko masa wayar ta dawo ta miƙa masa, gabyin Engineer Muhammad ne yasa yayi saurin ɗaukar kiran tare da kara wayar a kunnen sa, da kyar ya iya furta "Assalamu alaikum" daga ɗayan ɓangaren Engr yace "Waalaikumussalam barka da safiya sir" "barka Engr ya aikin? Ya office ɗin?" Yayi maganar da murya irin na marasa lafiya, cikin zumuɗi Engr yace "Sir gomnati tayi rejected na later da muka tura a kan rejected na contract ɗin nan da muka yi, to suma sun yi rejected sun ki ansa san nan sun haɗo mana da nasu later"
zubur daddy ya miƙe tsaye tare da zaro ido waje yana faɗin "Me suka ce a later?" "Sir ban buɗe later ba ai" tsabar sauri har daddyn Jelly na haɗe words wajen cewa "Ɗauko later ka buɗe ka karanta muji" da sauri Engr ya ɗauko later ya buɗe ya fara karantawa kamar haka "Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu ɗan uwana fatan ka na lafiya, ya kake ya yata Jalila? Ina fatan komai normal Allah yasa haka, ban san dalilin ka na yin rejected na contract nan ba amma koma ne bazakayi rejected ba korafin ka ba zai ansuba dan na sha wahala sosai kafin na samun maka contract nan dan haka dole kayi aikin nan, ka kula kayi aiki da amana kamar tadda na sanka, ban da ha inci na barka lafiya sako daga Hussain" "What? Sako daga wane" daddyn Jelly ya faɗa a razane "Sako daga Hussain" Engr ya mai mai ta masa, "Husaini daman kana raye ina kake? me yasa ka guje mu please ka dawo gare mu muna son ganin ka kaman ta da abubuwan da suka faru a baya dan Allah" "Sorry sir" Engr ya faɗa cikin girmamawa, a sukwane daddy yace "daga ina sakon ya fito?" "Kamar fa daga Dubai ne sir dan ga tambarin kasar a jikin later" cikin sauri daddy yace "a jiye min later da kyau gani nan zuwa yanzu" ya kai karshen maganar tare da katse kiran sauri sauri yace "Jelly ɗauki system ɗin ki shiga bedroom bari naje office ina dawowa yanzu kinji?" Gyaɗa masa kai kawai tayi san nan ta miƙe ta haye saman kujera ta kara tsayi ta manna masa kiss a kumatu, shima ya manna mata a goshi san nan ta sauƙo ta ɗauki system ɗin ta wuce bedroom, shi kuma ya fice daga palon daga shi sai jallabiya amma haka ya fice saboda sauri ba zai iya tsayuwa ya shirya ba, haka ya shiga mota ya bar gidan ya nufi office.
_________________________________
*WASHINGTON DC*
*03:00 pm*
Agogon Washington ta buga, wasu dankara dankaran motoncin 6 ne masu numfashi wadda suka amsa sunan su motoci, a jere motocin nan su danno hancin zuwa cikin gidan su Michael, sai da suka wuce gate 1 gate 2 tayi scanning na su tsab san nan suka wuce suka nufi parking space na gidan,
koda suka je bakin gate ɗin parking space ɗin, sai da suka tsaya a nan ma wan nan na'uran ta gama kiran numbers ɗin motoncin san nan gate na parking space ɗin ya buɗe suka shiga
suna kashe motocin wasu jibga jibgan sojoji suka fito da yar gudun su, suka kewaye ɗaya daga cikin moton cin wadda ke a tsakiya, sojoji ne masu jiki a jika jibga jibga da su, sun samu horo mai kyau fuskokin nan nasu masu firgitar da zuciyar maza babu alamar wasa ko kaɗan a tattare da su, jeruwa sukayi a bakin wata dankareriyar mota kirar *Bugatti La voiture noira* wani jebgegen soja ne ya fito daga nashi motar, jibgege da shi mai kiran basawa shima fuskar nan tasa babu alamar wasa, sai sara masa wayan nan sojojin suke, bai kula suba ya wuce ya nufi wan nan motar *Bugatti La voiture noira* ya sanye hannun sa dake cikin hand gloves baka ya buɗe kofar motar tare da komawa bayan kofar motar ya tsaya ya ɗaga hannun sa ɗaya sama ya ɗaura saman goshin sa alamar respect, cikin nitsuwa mamallakin motar ya zuro kafafun sa dake sanye cikin bakaken Booth waje, kafin daga bisani ya fito a hankali
yana fitowa sojojin nan suka buga kafa a tare har sai da kasa ya amsa da dum san nan suka ɗaga hannun suka sara wa matashin da ya fito daga cikin motar, sanye matashin nan yake cikin wandon jeans blue da t-shirt ya ɗaura kyakkywan jacket mai ɗan girma zuwa gwiwar hakan yasa t-shirt nasa na cikin bai samu damar bayyana ba, ya ɗaura wani abu mai kama da rawani mai kauri a wuyar sa, san nan ya sanya black face mask a face nasa tare da black glass a idon sa, hannun sa na cikin hand gloves baki, a ta kaice dai baka iya ganin komai na shi sai dark black curly hair sa mai tsawo sosai, ya tara curly hair ɗin ya kulle a bayan wuyar sa ya nannaɗe jelar da kyau ta yadda ba zata masa yawo a bayan sa ba, duk da yana cikin jacket mai girma hakan ba zai hana ka gane cikakken jarumin Namiji bane, yana da tsawo sosai, dan yafi duk sojijin dake wajen tsawo san nan yana da ɗan giɓa kaɗan yana da murɗaɗen jiki sosai, wadda da gani kasan cikekken jarumin sojane.
Zura hannun sa yayi cikin manya manyan aljihun dake jikin jacket ɗin cikin takun ƙasaita irin na jaruman maza ya nufi hanyar fita daga parking space ɗin, a sukwane wayan nan jibga jibgan sojojin suka take masa baya, wow abun gwanin ban sha'awa, taku yake suna take masa baya, duk in da ya saka kafa ɗaya sai suma sun saka, duk wani sojan da suka zo wucewa kusa da shi sai ya sara musu cikin rawan jiki,
su Michael suna tsaye a bakin kofar shiga palo suna jiran sa, suna ganin sa tun daga ɗan nesa, nan take suka kara nitsuwa shi kam John jikin sa har kerma yake saboda tsoro, duk cikin su Jay da James ne masu ɗan kwari sune tsoron su bai tsanan ta sosai ba.
Har wajen da su Michael ke tsaye sojojin nan suka rako matashin nan san nan suka tsaitsaya a wajen yayin sa shi kuma matashin ya nufi cikin palo kamar bai ga su Michael ba, murya na rawa har suna haɗe baki wajen cewa "Welcome lion" kai kawai ya ɗaga musu ba tare da yayi magana ba ya wuce cikin palon, da sauri suka bi bayan sa, su kuma sojojin suka tsaya a wajen kamar wasu saƙaguna.
Koda suka shigo palon lion baya nan ya wuce bedroom na shi dan a gajiye yake, kallon juna sukayi kafin daddy da Uncle Herry su wuce bedroom nasu
"What is wrong with you John?" James ya tambaya dan yaga yadda jikin John ke rawa kamar mazari, tsaki Jay yaja kafin yace "An fara Exam a school kuma basu yi ba mana shi yasa ya fara kuka tun yanzu tun lion bai damke saba" shi dai Michael ko a jikin sa dan yasan ya riga da yasa uncle na su ya rubuta masa Exam ɗin, shi kuma John ba ɗaya kanin biyu
wucewa James yayi ya nufi bedroom nashi yana faɗin "Johnn you are in big trouble I pity you" tsaki Michael yaja kafin shi ma ya wuce bedroom na shi, kallon sama da kasa Jay yayiwa John kafin ya wuce shina ya nufi bedroom na shi yana faɗin "ina fatan lion in ya damke ka ya maka hukunci da sai ka gwammaci mutuwa tun da kunce ku bakuji" durkushewa kasa a wajen John yayi ya dafe kan sa yayi shiru kamar bashi a wajen, ya shiga damuwa sosai mafita.
After some hours
08:00 pm
zaune suke saman katafaren table ɗin cin abincin su dake cikin Katafaren palon su, gaba ɗayan su suna wajen kama daga Uncle Herry, daddy Michael, James, John, Jay, sai jibga jibgan Bodyguard masu basu tsaro tsaye a kan su suna aikin su wato basu tsaro da kula da abubuwan da zasu ci da kuma in suna bukatar wani abun sai su kawo musu, kamar irin su tissue paper idan zasu goge hannu ko baki, sai idan suna bukatar shan ruwa ko wine sai su zuba musu, wan nan shi ne aikin wayan nan jibga jibgan Bodyguard ɗin masu lafiya da jini a jika, masu fuska kamar wasu zakuna.
"Where is Romeo?" Cewar daddy shiru palon yayi ba wanda ya amsa sai John ne yace "he is inside his room" kallon Michael daddy yayi kafin yace "Michael go and call him, yazo muci abinci mana" "I can't go anywhere dad because I'm tied" ba ƙaramin tsorata duk wani halitta mai rai dake cikin palon suka yi ba jin daddy ya ambaci a kira Romeo, nan take wayan nan jibga jibgan bodyguard ɗin suka kara nutsuwa tsit kamar basu a wajen
daddy na kokarin yiwa Michael magana Jay ya miƙe yana faɗin "let me call him dad" jinjina kai daddy yayi ba tare da ya sake magana ba yana mamakin halin yaran sa kwata kwata basa girmama shi ko kaɗan abun da suka ga dama kawai suke, ɗan gara James ma shine mai ɗan tausayi da saukin kai a cikin su, Michael kam sai dai Allah ya shirya, lion kuma ba'a magana dan nashi yafi na kowa shi karshe ne
wucewa Jay yayi ya haura sama ya nufi wata katafaren kofa launin golden color mai bala'i kyau wadda kamar da gold aka yi ta.
A hankali cikin tsoro Jay ya tura kofar ya shiga, wani katafaren palo ne gari guda, girman palon nan ya kai 1 plot da ɗori, tampatsa tampatsan kujeru ne masu mumfashi set uku a cikin palon launin sky blue, fari, da kuma milk, ko wani set na gefe guda,
ga wani haɗaɗiyar sofa table mai bala'i kyau a tsakiyar kowani sofa set, manya manyan fridge uku ne a palon masu shaƙe da kayan drinks da sauran abubuwa, daga gefe kuma ga wani makeken Tv plasma zaune saman Tv stand, shi kan shi Tv stand ɗin abun kallo ne, dan ya tsaru iya tsaruwa, gaba ɗaya palon gauraye yake da haske kwayayen wuta dake manne a saman POP palon, ba abun da ke tashi a palon sai sanyin Ac da wani fitinannen kamshi mai bala'i daɗi da ratsa zuciya, gaba ɗaya curtains na palon farare ne kal kamar hannun bai taɓa taɓa su ba, saboda haske ma kamar yanzu a ka fitar da su daga cikin ledar su, san nan su kan su curtains ɗin abun kallo ne, dan sun tsaru kai da gani kasan ba wajen wasa kazo ba, kowani sofa set a koi Chinese carpets mai bala'i laushi kamar audiga a tsakiyar su, kowani sofa set Chinese carpet kalan sofar a ka sanya masa, tiles na kasan palon da kuma na jikin bango dukka farare ne kal a ka sanya, tsayawa zayyana muku haɗuwar palon nan lokaci guda ba zai yiwu ba sai dai a rinƙa sako abubuwan a hankali, dan wan nan palon ya wuce tunanin mai tunani, wan na palon shi a ke wa laƙabi da aljannar duniya,
a hankali Jay ke taka kasar palon kamar mai tsoron wani abu haka ya tura wani katafaren kofa ya shiga yana faɗin "excuse" Wow Aljanar duniya part 2 bedroom ne mai girman plot 1, ga wani makeken gado mai girman gaske, tsawon saman kayin kadon nan ya kai 2.1m (miter) kusan girman gini, dan ma dai ginin suna da tsawon 3m ne shi yasa, shi kan sa kayin gadon abun kallo ne, an kawata shi da kwalliya golden color kamar gold ga wasu hasken fitullu masu bada wuta launin sky blue a jikin kayin gadon, kayin gadon round ne (arp) while jikin gadon kuma 4 kwana, daga farkon kayin gadon har karshen sa duk kyawawan fitillun ne masu kyan gaske ke bada wuta sky blue, wan nan katafaren gadon shin fiɗe yake da lausasan bedside da kuma bargo masu laushi kamar audiga, daga bed sheet ɗin har bargon farare ne kal kamar hasken audiga, gaba ɗaya kyawawan bedside drawer, nan wasu kyawawan lamp ne ɗaure a saman su, mirror dake cikin ɗakin nan ma kawai ya isa mutun yayi kauyanci a wajen, kwalliyar saman mirror iri ɗaya ne da kwalliyar kayin gadon wato kamar kwalliyar gadon manya manyan sarakuna ta duniya, haka aka kawata wan nan bed ɗin da artists na shi, saman mirror shaƙe yake da lotions da perfumes kala kala masu kamshi da tsada, ga combs for combing hair and hair cream kala kala shake a wajen kai da gani kasan tsabtar mamalakin bedroom nan ya wuci tunanin mai tunani, mutun ne mai son gyara dan ko ta ina kayan gyara jiki ne saman mirror. Gefe da gefen mirror wasu haɗaɗun show glass ne a wajen ma su ɗan tsawo, ɗaya cike yake da air freshener da perfume na ɗaki kala kala masu daɗin kamshi, ɗayan kuma shake yake da takar su irin su Christian Bible, da dai sauran takardun su, floor tiles na ɗakin farine kal, kamar kafa bai taɓa taka tiles ɗin ba saboda hasken sa, da gani kasan mamallakin ɗakin nan yana son white color sosai dan kusan komai nasa na ɗakin fari ne, kusa da katafaren gadon nan wani hamshakin Chinese carpets ne mai bala'i lausi ga gashi a jikin sa kamar gashin mage wadda kana takawa kafar ka na nitsawa cikin gashin saboda laushi, tsadaddun curtains na ɗakin launin white color ne suma masu bala'i kyau da tsada, a koi ƙofofi guda uku a cikin bedroom ɗin, dukkan su kuma ƙofofin glass ne, ɗaya na toilet ɗaya kuma na balcony, while ɗayan kuma na dressing room ne, bedroom nan ya kawatu iya kawatu wa,
ga wani sky blue haske da fitillun jikin furniture ɗin ke badawa hakan ba karamin kara kawata ɗakin yayi ba, kwayayen fitillun dake manne a POP bedroom ɗin ma dukka hasken wuta launin sky blue suke badawa, hakan ba karamin karawa ɗakin kyau da ɗaukan hankali yayi ba, ko ina a gyare tsab kamar sabon waje, sai daddaɗar kamshi da sanyin Ac mai ratsa zuciya ke tashi a cikin bedroom ɗin gwanin dadi da ɗaukan hankali.
Kallon saman katafaren gadon Jay yayi, lion na kwance ya rufe jikin sa har izuwa wuyar sa da lallausan bargon sa mai kama da audiga saboda laushi, while long dark black curly hair sa ya barbazu ya rufe masa kyakkyawan face nashi, baka iya ganin komai na jikin sa, sai wan nan dark black curly hair ɗin nasa da ta rufe masa face, da alama barci yake, ya lafe luf a lallausan gadon, yabi lafiyar gadon, ganin haka yasa Jay ja da baya a hankali, kamar mara gaskiya ya fice daga bedroom ɗin ya koma Palon kasa wajen su daddy.
Yana komawa ya zauna saman kujerar table ɗin yana sauke ajiyar zuciya ba tare da yayi magana ba, tun da daddy yaga haka sai bai tambaye sa ina Romeo ɗin ba, yayi shiru suka ci-gaba da cin abincin su.
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai
💞Star Lady💞
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai
💞Star Lady💞
💞 TRIPLET'S💞 17
*💞TRIPLET'S💞*
https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo
*THE BEGINNING*
💞*STAR LADY*💞
EPISODE 17
*KANO*
_______Daddyn jelly na zuwa office jikin sa har rawa yake wajen amsan later ya fara dubawa ko zai samu address ɗin Hussain a jiki, sai dai kash bai samu ba, ba karamin haushin hakan ya ji ba, jiki ba kwari ya juya ya koma gida cike da dana sanin abubuwan da suka faru a baya, sun yasar da ɗan uwan su gashi shi kuma bai yasar da su ba yana bibiyar al amuran su yana taimaka masu, gaskiya basu kyau taba, da wan nan tunani ya koma gida.
Zaune tsakiyar gado ya isko jelly tayi ɗai ɗai abun ta ta sanya system a tsakanin kafafun ta sai buga game nata take bata san me duniya ke ciki ba.
Zama yayi gefen gadon yana faɗin "My Jelly har yanzu baki gaji da buga game ɗin bane?" A sukwane ta ɗago kai da alama bata san da shigowar sa ba, ture system ɗin tayi gefe guda ta rarrafo ta faɗa jikin sa tana dariya, shafa kan ta yayi cike da so da kaunar ta, yana kokarin yin magana wayar sa ta fara kara
Cikin sa ya ciro wayar daga aljihu sa, dum dum gaban sa ya