Showing 75001 words to 78000 words out of 194715 words

Chapter 26 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

982

Kullun sai na faɗa miki ki dai na cewa kina kyamar talakawa amma baki ji ko kaɗan ko? Ya miki kyau to ba yar kowa bace yar talakawa ce, kuma a haka nace nake so ko akoi wadda ya isa ya hanani auren zaɓin rai na ne?" Murya har sarkewa yake tace "Kayi hakuri yaya Akil tuba nake" dogon tsaki yaja tare da katse kiran, shiru Umaisha tayi tana tunani "Ashe daman yaya Akil yana da hankali, ashe kawai zafin rai gare sa ba wai rashin hankali ba Allah sarki, Allah ya sassauta masa zafin kan nan da zuciyar nan tasa"

shiru sukayi dukkan su, ba wanda ya sake magana har suka isa kofar gida, ya kashe motar sa ya fito ya ɗauka mata ledojin dan yasan ba zata iya ɗauka ba

suna shiga harabar gida a nan suka isko Abbi da Irfan da Aafia, suna tsaye cirko cirko saboda da sukaji Umaisha shiru bata dawo ba shi sukazo su leka ko tana wajen ganin bata nan shine suka tsaya suna tattaunawa ta ina Irfan zai je neman ta

ganin su yasa Umaisha ta tafi da sauri ta faɗa jikin yaya Irfan tana ɓoye fuska dan ita a koi ta da kunya sosai, har gaban su Abbi yazo ya ajiye mata ledojin cikin girmamawa yace "Sannu ku ina wuni uncle" da fara'a Abbi yace "Lafiya lou Alhadulillah ina kuka je ne na fito ban same ku ba?" Juyawa Akil yayi ya bawa Irfan hannu yana faɗin "Yanzu dan na fita da matata sai na faɗa wa wani in da na kai ta, wan nan sirrin mune ai" tashin sense kallon Irfan Abbi yayi kafin yace "Ni kam Irfan ko dai ka aurar da Umaisha ban sani bane?" Wuce Akil yayi abun sa ya nufi gate yana faɗin "My wife sai mun yi waya" kallon sa Irfan yayi har sai da ya fice san nan yace "Umaisha ku kwashe kayan kuje ciki" cikin sauri suka kwashe kayan da sauri suka wuce ciki Aafia tana ta kallon Umaisha tana jiran suje ɗaki ta tambaye ta ina Akil ya kai ta

Gyara tsayuwa Irfan yayi cikin nitsuwa ta fara magana "Abbi kayi hakuri haka halin Akil yake muna masa fatan yayi hankali ta dalilin Umaisha mun yi magana da Imran a kan hakan san nan kuma Abbi idan ka lura yaro ne fa 22 years yake da shi" cikin fushi Abbi yace "A'a wlh bai isa ba wan nan iskanci ba zan ɗauka ba, bai isa yazo ya min wan nan iskanci a gida ba ya ɗauki yata lokacin da yake so ya fita da ita san nan ya dawo da ita lokacin da yake so in masa magana yace min shi da matar sa to a yau she ta zama matar sa? Wlh idan yamin tsiya sai na haramta masa auren Umaisha in ga wanda ya isa ya sa na bashi ita, ya koma ya tambayi yaya cikin kannen sa waye mai zafi ma faɗa ci zai faɗa masa, daga yau ka sanar ma sa idan ba zai shigo cikin Palo yayi hira da Umaisha ba to ya bari bana bukata daman bance masa tana neman mijiba kwata kwata ma nawa tace 15 years fa gare ta zai fara koya mata wasu ɗabiun ya sauke min ya daga tarbiyar dana ɗorata to bai isa ba yaya ma yayi kaɗan a kan wan nan zance bare shi, kuma nayi cancelled fita da Umaisha suje wani wajen, idan wani abun yake son nuna mata ko ya saya mata to sai dai yaje shi kaɗai ya dawo ya kawo mata nan!!!" Shiru Irfan yayi dan yasan halin Abbi yana da saukin kai da fara'a amma idan a ka taɓosa yana da zafi sosai, yana da faɗa kuma wan nan karon a kan gaskiya yake faɗar sa dole su nunawa Akil Umaisha na da daraja dole su saya mata kima

Wucewa Abbi yayi ya shige cikin palo ransa a matukar ɓace, jiki ba kwari Irfan yabi bayan sa, ko da ya shiga palon Abbi ya wuce bedroom na shi, shi ma sai ya wuce bedroom na shi jiki a mace.

A ɓangaren su Aafia kuwa, suna shiga bedroom na su da murna Aafia ta fara watsa kayan tana fitarwa, ganin manya manyan hijabai ne yasa taja dogon tsaki ta ture ledojin, ta jawo wan da ya sawo daga super market tana faɗin "Lallai Umaisha kina da babban aiki a gaban ki wan nan hijabai dukka lallai kina ruwa" da sauri Umaisha tace "A'a Aunty Afi muna dai ruwa, dan hijabai ɗin ba nawa ni kaɗai bane, nawa 12 naki 12 ne ai" zaro ido waje Aafia tayi kafin tace "Sannu Uban na wlh bai isa yace zai sani sanya hijabi ba, ina ruwan sa ma dani tab aiko gyalen ma sai na ga daman sawa in ga uban da ya isa ya sani sawa, shegen idon sa kamar na duji" dariya Umaisha tayi tana faɗin "Ni fa da yace naje na sanya hijabi har karya na masa nace bani da su, na ɗauka zai kyaleni yace na ci-gaba da sa gyalen, amma sai na ga akasin haka ya tasani a gaba mukaje kasuwa ya kwaso min wan nan abubuwan dukka dan iskanci" ta kai karshen maganar tare da kwanciya saman gadon, tsaki Aafia taja tana fitar da abubuwan cikin ledojin super market ɗin, chocolate ne kala kala dasu hollandia milk su biscuits sweet da sauran kayan kwalama, nan Aafia ta ware wanda zata ci lokacin ta tattara sauran ta zuba su cikin bedside drawer, ta tasa wadda ta ware a gefe kuma tana ci suna yar hiran duniya.

__________________________________

*WASHINGTON DC*


Jay

Yana komawa ya zauna saman kujerar table ɗin yana sauke ajiyar zuciya ba tare da yayi magana ba, tun da daddy yaga haka sai bai tambaye sa ina Romeo ɗin ba, yayi shiru suka ci-gaba da cin abincin su.

Kallon Micheal James yayi cikin kulawa yace "My bro bana son ka rinƙa yin irin abubuwan nan da kake yana da kyau kayiwa sauran mata adalci, mum daban suma sauran mata daban, ba dukka suka taru suka zama ɗaya ba, ba wai ina faɗa maka haka bane dan ka kula mata ko wani abu no nima bani da lokacin kula mace kwata kwata a rayuwa ta, ba kuma ina faɗa maka hakan bane ko dan ka yarda da mace ko kuma mum batayi laifi ba, no mum tayi babban laifi, wadda ta cancanci mu tsaneta kuma dole mu kasa yarda da mata saboda abun da mun tayi ta cutar da zuciyar mu ta sa mana tabon da ba zai goge ba, amma yana da kyau ka cire tsanar su a ranka, dan wani lokaci suna da amfani, kuma ina son kayi hakuri ka shirya muje New York mu gaida mum gobe, please na san bata da burin da ya wuce ta gan mu, ba wai dan wani abu zamu je gaishe ta ba sai dan sada zumunci, ba wai dan muna son ta ko zamu yafe mata ba a'a kawai yana da kyau ne muje ɗin, shekara 18 kenan rabon mu da mugan ta fa tun da tazo sau ɗaya daddy ya koreta bata sake zuwa ba why mu ba zamu je ba?" Miƙewa Michael yayi tare da buga table ɗin cikin fushi yace "I told you to stop talking about that human for me!! I said I don't like, wai a na dole ne? Nace bana son jin zancen wata mata ni bani da uwa daddy shi ne kawai duniya ta, karka sake cewa muje wajen wata mummy idan kuma ka sake wlh barin muku gidan zanyi!!!" a fusace Shima daddy ya miƙe rai a matukar ɓace ya fara magana "be careful James, idan ka sake mana maganar wata shashashar mata a nan sai ranka ya ɓaci, bamu son ta kuma babu in da zaku je, idan ma ka sake maganar ta to sai dai ka nemi wani uban ba ni ba" ya kai karshen maganar tare da rungume Micheal yana rarrashin sa yana ɗan bubbuga masa baya



Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞


💞 TRIPLET'S💞 18





https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo


*THE BEGINNING*



💞*STAR LADY*💞




EPISODE 18


*Washington DC*


a fusace Shima daddy ya miƙe rai a matukar ɓace ya fara magana "be careful James, idan ka sake mana maganar wata shashashar mata a nan sai ranka ya ɓaci, bamu son ta kuma babu in da zaku je, idan ma ka sake maganar ta to sai dai ka nemi wani uban ba ni ba" ya kai karshen maganar tare da rungume Micheal yana rarrashin sa yana ɗan bubbuga masa baya, girgizar kai James yayi kafin ya miƙe tsaye cikin fushi ya bar palon, yana jin haushin abun da mum ta musu da kuma irin tsanar da Romeo, daddy, Michael, Tga, uncle herry, suka mata.

A gefen su Michael kuwa komawa daddy yayi ya zauna shi ma Michael ya koma ya zauna,

"Micheal where is your exam card?" cewar Jay yayi maganar yana tsare Michael da ido, a kule Michael yace "Wai Jay meye ruwan ka da ni ne? A koi wani business ne tsakanin mu?" Dariya Jay yayi yana faɗin "Michael baka da gaskiya" a fusace Michael ya buga table ɗin ya fara sunfa uwar masifa ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba sai dannan sa su daddy suke,
cikin wasa John yace "Kai Micheal is it not our brother? kake masa tsawa haka" cikin fushi Micheal ya danko wuyar rigar John yana kokarin yin magana sukaji takun tafi daga bayan su, wadda ko basu juya ba sun san mai wan nan takun, a sukwane Michael ya saki wuyar rigar John ɗin tare da tattara nitsuwar sa waje guda, gaba ɗaya palon yayi tsit, duk wani halitta mai rai a palon sai da ta nitsu tsit kamar ba kowa.

A hankali yake sako kafar sa yana taka staircase ɗin kamar bai san taka kasa matashi ne mai jini a jiki farine tas farin Bature dogo ne sosai mai faffaɗar kirjin kamar wani zaki yana da murɗadɗen jiki wadda kallo ɗaya zaka masa kasan yasamu training mai kyau ya koshi da training, ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fashe saboda horon da ya ke bawa kan sa, sanye yake da wando guntu 3 cutar hakan ne ya bawa kyawawan kafofin sa bayyana ga wasu gashi dark black mai tsantsi da laushi kwance a kyawawan fararen kafofin nasa har izuwa idon sahu na kafar sa hakan ba karamin kyau ya kara masa ba, yana sanye da riga mai ƙaramin hannu hakan ya bawa tuma tuman ɗamtsen hannun sa damar bayya kamar zasu fashe saboda horo, ga wasu kyawawan gashi dark black sai sheki suke kwance a hannun na sa har izuwa idon sahu na hannun sa, kasan cewar a komai face mask a face nashi baka ganin face na shin sai dai dara daran light blue eyes na shi masu bala'i kyau da ɗaukan hankali gwanin burgewa, yana da dogayen gashin ido kamar ya sa eyelashes, gashin geran sa kuwa a cike suke kamar zasu haɗe saboda cika gasu a kwance luf kamar an zana masa sai sheki da kyalli suke, sai faman lumshe dara daran light blue eyes na shi yake kamar mai jin barci, lallausan dark black curly hair sa da ya sha gyaran nan kuwa ya ɗaure a bayan sa, kaɗan ya zubo masa ta gaban goshin sa, hakan ba karamin kyau ya kara wa face nasa ba, ya kara kawata kyan sa sosai ya fito da face ɗin gwanin ban sha'awa da burgewa, soft skin nasa nan kamar ka taɓa jini ta fito saboda kwanciya da laushin da yayi yaji hutu kamar bai taɓa fita waje ba, kyawawan fararen kafofin sa na sanye cikin wani haɗaɗiyar bedroom slippers mai bala'i kyau da laushi jikin takalman duk gashi kamar gashin jikin mage, san nan yana da dogayen yatsun kafa da na hannu farare tas mai ɗauke da kumba (farce) farare tas kamar audiga yatsun nashi a koi lallausan bakin gashi mai tsantsi kwance a kan su haka zalika yatsun hannun sa dogaye ne sosai suna da ɗan kauri kaɗan masu ɗauke da kumba (farce) farare tas kamar audiga, yana da kwantatciyar lallausan bakin saje a gefen kumatun sa har izuwa gemun, sai dai bai bar gemu ba,
a hankali yake takowa kan sa na duƙe kan wayar sa kirar *falcon Supernova IPhone 6 pink diamond* wadda a kalla kuɗin ta ya kai ($48.5 million) a hankali yake latsa wayar kamar baya son taɓa screen ɗin wayar, hannun sa na ɗaure da dangareriyar gold watch irin na hannun su Michael sak. Duk in da ya sanya kafar sa, sai wani kyakkyawan ƙaton karen sa dake gefen sa mai suna Brady ya sa na shi kafar.
Brady irin manya manyan karen nan ne masu gashi ajiki sosai wadda yake har kasa duk in da Romeo yayi taku ɗaya sai Brady ma yayi taku ɗaya, tun bai karisa shigowa palon ba wan nan daddaɗar fitinanniyar kamshin perfume na shin ta kauraye ko wani lungu da sako na cikin palon, sai shakan kamshin bodyguard nasu ke yi suna lumshe ido, dan kamshin perfume na shi number ɗaya ne a duniya wajen daɗi

```````ROMEO```````
Cikakken namijine mai Jini ajika, lafiyayye kuma kakkarfan jarumi., kaifi ɗaya ne ba mai iya tan kwara shi idan ya faɗi abu tofa ya faɗa ne kome za'ayi baya sauya magana miskiline na karshe baya shiga harkan kowa baya son magana, idan ma yana waje tofa kome zai faru shiru ake ba wadda ya isa yayi magana har sai ya tashi a wajen dan bai san hayani ya, idan baka san shi ba sai kace kurma ne, bai son kallon mace a Area da yake saboda Mahaifiyar sa ya tsani kalmar mace a rayuwar sa kamar yadda ya tsani jin sunan mahaifiyar sa, Allah ya masa farinjinin da mata da maza ke haukan son shi, daga kasashe daban daban yayan manya manyan masu kuɗi na duniya na son shi, ta ko ina mata son shi suke suna burin ko sau ɗaya ne suga face na shi, sai dai kuma babu macen da ta isa tayo area da yake, saboda ba shi da sauki basu ga alamar face ɗin wasa a tattare da shi ba, baya dariya kullun face nashi a ɗaure take tamau kamar hadari kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, ganin face na shi kawai yana sa hantar manyan maza ta kaɗa bare ku ma mata, ganin face na shi kawai tana jirjiza daula, yaci sunan sa da daddy ke kiran sa wato lion, lion ɗin ne da gaske,

...Taku yake cikin nitsuwa da kwanciyar hankali Brady na gefen sa suna saukowa tare. Nan take su Johnson suka kara shiga hankalin su, suka nitsu ba su Johnson kawai ba har su daddy uncle Herry duk sun nitsu numfashi ma a hankali suke fitar wa dan gudun kar wani sauti da zai sa Romeo ɗago kan sa daga kan wayar sa ya fita. Saukowa yayi yazo ya wuce su bai ko kalli in da suke ba kamar bai san da zaman mutane awajen ba ya fice ya nufi waje, Brady na biye da shi a gefen sa.

Yana fita suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya a tare, miƙewa Johnson yayi ya ɗan leƙa kofar palon dan yaga Romeo yayi nisa ne ko bai yi ba, ganin babu alamar sa awajen ne yasa ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali ya dawo ya zauna, kasa kasa ya dubi Michael cikin harshen turanci yace "We're finally saved Michael it seems like kana da rabon yin tsere da doki kwanan nan" harara Micheal ya watsa masa kafin ya miƙe ya bar palon yana huci kamar wani zaki shi a dole an ɓata masa rai,

miƙewa daddy yayi ya nufi waje yabi bayan Romeo, a ransa yana faɗin "na sanya maka sunan Romeo da murnana, a tunani na zaka girma kamar Romeo sai kuma nayi rashin Sa'a ka girma kamar lion kwata kwata baka san wani abu wai shi felling ba ba ruwan ka da wani abu wai shi kaunar yan uwa da iyaye kai dai umarni kawai ka iya badawa gaskiya sunan Romeo bai dace da kai ba da tun kana yaro na fahimci haka da na jima da canza maka suna, amma yanzu time ya kura wayyo ni William sai na gama kamar sabon rashin mutunci ya karo tafiyar san nan to ko dai an sake ɓata masa wani aikin ne ya dawo ya sauya gaba ɗaya" da tunani cike fal ransa ya nufi in da yake zaton zai samu Romeo, wato garden

Haka ko a kayi Romeo na zaune a wajen yana latsa wayar sa ya ɗaura hannun sa ɗaya a saman wuyar Brady yana shafa lallausan gashin Brady ɗin, hasken fitullun dake wajen masu bada wuta launin sky blue ba karamin karawa face ɗin Romeo kyau suka yi ba, wutar tayi dai dai da kalar idon sa, hakan gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali, ga wajen ya kawatu iya kawatu, gwanin kyau.


Kusa da shi daddy yazo ya zauna cikin nitsuwa yace "Welcome My lion" shiru ya ɗan yi kafin yace "Tnks" yayi maganar ba tare da ya kalli daddyn ɗin ba, "My lion, i want us to discuss something" shiru yayi tare da ajiye wayar dake hannun sa a gefen sa alamar yana sauraron daddy kenan, cikin ɗari ɗari daddy ya fara magana "About your mum i want you to.... Bai kai karshen maganar ba ya dakata saboda juyowa da Romeo yayi a sukwane har sai da kwayar idon sa suka kara shining saboda ya waro su waje sosai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login