Showing 90001 words to 93000 words out of 194715 words
ita ma Rimsha tasha kukan ta koshi ne ta hakura
mum tace wa Rimsha ta karya azumin amma taki tace ita kam bazata karya ba zata kai, sai kukan yinwa take amma taki yarda ta karya azumin, ita kuma Jehan sai cewa take zata karya mum ta hana ta saboda a lokacin ta fara kirgan dangi ta kirma tana da 13 to 14 years azumi ya haukan ta dan duk alamomin balaga sun bayyana a jikin ta, amma ta dage ita sai ta karya azumin dan ba zata iya ba, ga Rimsha bai war Allah ita da azumi bai hau kan ta bama ta zage sai ta kai bazata karya ba, sai kukan yinwa take, yayin da shi kuma daddy ya tafi wajen meeting bai dawo ba sai 2 pm.
Ko da ya dawo zama sukayi a palo shi da gwaggo da mum suka fara lissafin abubuwan sadaka da zai sayawa bayin Allah, while lokacin Jehan da Rimsha sunyi barci wahala da yinwa, daddy yaso a tasan masa su dan yaji su kuma ra'ayin me suke da shi a kan abubuwan sadaka da zai saya, amma mum tace ya kyale su dan ba barcin daɗi sukayi ba, hakan yasa ya hakura ya kyale su ba dan yaso ba.
Mum tace ya sai atampopi manyan bundir kamar guda ɗari da shadduji, hijabai, takalma, ya kai wa gajiyayyu da marasa karfi tare da marayu, ita kuma Gwaggo tace ya haɗa da kayan abinci, kama daga shinkafa, taliya, mai, manja, maggi, macaronic, indomie, sugar, madara, da dai sauran kayan abinci suje su rabawa gidajen marayu da kauyukan dake cikin wahala
duk kan su daddy ya karɓi shawarar su, ya kira Uncle Shitu a waya ya sanar masa abubuwan da zasu saya, sukayi lissafi ya tura masa kuɗi, a kan ya saya ya rabawa talakawa da mabukara, sai fatan alkhari Mum da gwaggo ke masa, tare da fatan sumun nasara a siyasar sa, sai murmushi yake yana amsawa da amin, yana mai jin matikar kaunar family sa a ran sa, da haka suka zauna suka rinƙa hiran duniya da abun dake faruwa a cikin ta.
*KANO*
Sosai shima daddyn Jelly ya sai kayan sadaka irin su kayan abinci, da kayan sawa ya rinƙa rabar wa marasa karfi masu buƙata, da niyar Allah ya fitar da shi daga kuncin da yake ciki.
Yana zaune a palo yayi shiru yana tunani, damuwa ta masa yawa ya rasa ina zai sa ransa ya rasa mafita duk ta in da ya tuna sai yaji ba gwara, ya buga uban takumi ga yinwar azumi na damun sa
Da gudu Jelly ta fito daga bedroom nasu hannun ta riƙe da wayar sa tana faɗin "Daddy yaya Imran want to talk to you" ta kai karshen maganar tare da faɗa wa jikin sa tana kokarin miƙa masa wayar, hannu yasa ya ansa wayar tare da karawa a kunnen sa yana faɗin "Assalamu alaikum Imran ya kake?" Daga ɗayan ɓangaren Imran yace "Amin Waalaikumussalam bappa ina wuni" murya a dashe daddyn Jelly ya amsa da "Lafiya lou Alhadulillah ya School" ba tare da Imran ya amsa tambayar ba yace "Bappa Jelly ta faɗa min wani abun da ya tayar min da hankali yanzun nan shin da gaske ne?" Waro ido waje daddy yayi yana faɗin "Me tace maka?" "yanzu kiran da ta min ɗin nan tace min a koi wanda ya kiraka a waya ta ɗauka taji yana faɗin wai ka tura masa 100 millon ko kuma ya saki video ka wa duniya, to ina son sanin wanene wan nan bappa ni ban damu dana san a kan wani video a ke magana ba, kawai ina son in san me matsalar sa da kai" kara waro ido waje daddy yayi lokacin guda yaji jikin sa ya warware tsananin tashin hankali da firgici ne suka bayyana a kan face ɗin sa, kirjin sa sai dukan uku uku yake, nan take zufa ta fara karyo masa faɗi yake ina zan sa kai na ni Maik, a zuciyar sa, yayi shiru ya kasa magana dan yaji gaba ɗaya harshen sa ya masa nauyi,
jin daddy yayi shiru sai wani irin numfashi yake fitar wane yasa Imran ya gane eh gaskiyan Jelly bappan sa na cikin damuwa.
A nitsa yace "Bappa dan Allah ka kafaɗa min kaji ko dai sai nazo ne zaka faɗa min ɗin?" Da kyar daddy ya iya cewa "Aa Imran ba sai kazo ba" yayi maganar kamar zai sa ihu saboda damuwa da suka cunkushe masa waje guda, zuchiyar sa kamar zata fashe saboda zafin raɗaɗin azaban ciwon da take masa.
"Bappa to meke faruwa? Dan girman Allah ka faɗa min ko zan samu sauƙi a rai na" shiru daddy ya ɗanyi kafin ya fara bawa Imran labarin duk abun da yake faruwa na takarar da suke da baban Muneer sai dai ya ɓoye masa batun video, da kuma abun da ya shiga tsakanin su da P.A ya dai cewa Imran baban Muneer na masa baraza na da wani abu wadda ya zama wani sashe na rugujewar rayuwar sa, amma kada Imran ɗin ya tambaye sa menene wan nan dan Allah
shiru Imran yayi na ɗan wani lokaci kafin yace "Bappa nayi nisa amma duk time da na dawo sai na sa anyi maganin mutumin nan, yanzu dai shawarar da zamu yi a nan shi ne ka fito kace ka sayar min da company kawai kaga ba wanda ya sanni a Kano ba wanda ya san ni ɗan yayan kane, san nan yadda zumuncin mu yake nan ba wanda ya san ma kana da yaya, to ina son kafito ka ce masa kasayar min da company idan ta kama ma muyi cinikin boge a gaban sa sai muyi, ka sauya tsare tsaren company ta yadda zai gamsu ka sai da min ɗin, zaka iya mai da takardun ma da sunana na wani ɗan lokacin, in yaso daga baya sai mu gyara komai, yanzu ka zauna a matsayin aiki na baka a company, shikenan dole ya kyale ka ta fannin company kam, tun da ba company ka bane a idon sa, kaga zaka samu ka gudanar da aikin ka yadda ya dace kenan" cool murmushi daddy yasaki wadda rabon sa da yayi ta harya manta, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Kai amma naji daɗi sosai Imran" "Ba komai bappa all the best, yauwa san nan nasan zai na tambayar ka kuɗi tun da yanzu ma kuɗi ya kira ya tambaya Allah yasa wayar na hanun Jelly ta ɗauka taji, to idan ya tambaye ka karka rinƙa bashi kaje ka buɗe wani account ka kwashe kuɗin ka dukka ka zuba a sabon account ɗin sai ka rinƙa nuna masa balance na tsohon account ɗin, kace masa wanda ya saya company ma bai biya kuɗin ba kaɗan ya baka yace sai gaba yanzu baka da kuɗi dan aiki kake a karkashin wani, na lura bashi da ilimi ko kaɗan jahiline, dan mai yiwuwa result ɗin ma ta karfi ya ansa, dan abun da yayin nan mai ilimi ba zai yi shi ba, to dan haka sai mu rai na masa hankali tun da jahiline, kasam dai yadda zakayi kana kauce masa har na dawo, ina dawowa zanyi maganin sa" sosai daddy yaji daɗin maganganu Imran harma ya rinƙa zubawa Imran ɗin godiya da Addua'o'i fatan Alkhari, daga haka suka yi sallama
da fara'a ya miƙe ya ɗauki Jelly cak suka nufi bedroom, yau da kan sa ya mata wanka, sabanin a baya tun da abun nan ya faru su Zuwaira ke mata wanka dan shi lokaci kwata kwata baya tare da mutane yana can duniyar tunanin mafita.
Sosai itama Jelly taji daɗin yau daddy ya mata wanka, har da wanke mata gashi ya kawota gaban mirror ya mata kwalli tare da busar mata da gashin kan ta da hand dryer, ya tara mata gashin ya ɗaure mata, ya sanya mata kana nan kaya na shan iska san nan ya feshe ta da perfume masu kamshi, shima yaje yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya shadda milk color mai kyau da tsada, ya riko hannun ta suka fice daga gidan, kai tsaye suka nufi wajen sai da puppy dog, sai farinciki yake yau ji yake kamar an masa albashr da gidan aljanna, a nan ya saiwa jelly puppy dog kyakkyawa fara kal mai yalwar gashi a jiki, tun a lokacin da a ka sai mata karen ta sa masa suna dolly tun a wajen, tana bala'i kaunar puppy ɗin, haka suka wuce super market yai musu shopping sosai san nan suka dawo gida cike da murna, ita kam Jelly murnan ta yafi na daddy dan ta samu dolly.
Da daddare ba yadda daddy bai yi da ita ba a kan ta kawo dolly a sanya ta cikin keji da a ka sawota da shi, amma Jelly taki yarda ta kafe ita dole da dollyn ta zasu kwana a gadon ta, haka daddy ya hakura ba dan yaso ba.
Washegari haka ta tashi rungume da dolly ɗin ta, dan ko sallama asuba ma dolly na gefen ta tayi, ba yadda daddy bai yi da ita ba a kan ta ajiye dollyn saman gado tayi Sallah amma taki yarda, ba yadda ya iya haka ya kyaleta.
Wunin ranar dai Jellyn rungume da dolly ta wuni har dare, suka sake kwana gado guda, yanzu daddy ya hakura ya dai na shiga zancen ta ita da dolly ɗin ta ya zuba musu ido.
Lokaci ya ja haka James ya rinƙa wasa da tunanin ogan su a kan kashe GAR, yayin da shi kuma daddyn Jelly ya samu saukin takura daga wajen baban Muneer haka zalika shi kuma Abbi dukiya sai haɓaka take yana kara samun kuɗi, Allah ya sawa abun albarka, yayin da shi kuma, daddyn su Rimsha siyasa ta gaba to ko ina sunan sa ke yawo jama'a na son shi sosai, ta ko ina masoya ne, Nawazudden, Nawazudden, ta ko ina, sosai daddy ke murna da farinciki a kan haka, tun wan nan tafiya da su Imran sukayi basu sake samun dama sun zo Nigeria ba, saboda abubuwa da suka sha musu kai, yayin da ita kuma Umaisha ta biyewa Aafia ta dai na sanya hijabi, duk wani abun da Akil yace mata sai da ta watsar ta dai na yi, kasan cewar abubuwa sun sha kan sa sosai baya samun damar bibiyar me take, sai dai bata sanya attachment da eyelashes, sune abun da ya rage a cikin dokan da Akil ya kafa mata bata karya ba, ita kuwa Aafia komai sanya wa take hankalin kwance, shima Irfan tun wan nan tafiya da yayi sau ɗaya yazo hutu, ko da yazo ya tsawatar wa Aafia sosai a kan sanya hijabi da ta daina sanya attachment da eyelashes da sauran su, amma yana komawa ta watsar da duk wani nasiha da tsawatar wan da ya mata ta koma gidan jiya
shi kuwa wan nan mutumin da suka haɗu a kofar gidan su Rufaidat yasha neman ta har ya gaji basu sake haɗuwa ba amma bashi da burin da ya wuce sake ganin ta, Abbi bai cika zama a gida ba shi yasa su Aafia ke yin abun da suka ga dama, sai dai duk wan nan abun da suke sun san ba dai dai suke ba dan Abbi bai barsu haka nan ba sai da ya tabbatar ya basu ilimin addini, so sun san komai sun san ba dai dai suke ba, amma suka take sani.
A ɓangaren su Abba kuwa duk karshen shekara wayan nan dodannin suna zuwa musu, kuma sai sunyi sati suna zane su kafin su tafi, in sun tafi kuma sai bayan shekara suke sake dawuwa, babban damuwar shine da dodannin sun tafi shikenan suma zasu manta komai hakan yasa basu samu dama sun iya sawa a musu saukan Al Qur'ani mai girma ba kasan cewar sun manta komai basa iya tuna komai.
*ABUJA*
Kamar kullun yau ma daddy na gida bai fita ba missalin karfe 3 na yamma, yau suna tare da uncle Shitu, sai hira suke a palo, uncle Shitu na ta hira da Rimsha ita kam Jehan daman ba shiri take da kowa ba, dan Uncle Shitu bai isshe ta kallo ba, a cewar ta duk wanda ke karkashin daddyn ta to a karkashin ta yake dole ya girmama ta,
Jehan yar sanda sosai take bawa kan ta horo tayi ta azabtar da kan ta ta fannin gudu da ɗaga karfe, iya bin kwakkwafi a kan abu, bata da yawan surutu kamar dai ita ma Rimsha ɗin basu da yawan surutu, sai dai Jehan a koi ta da zafin kai, rai na mutane, rashin kunya, tsaurin ido, shagwaɓa, izza da kuma girman kai, amma duk da haka tana da ilimin addini sosai sai dai bata kai Rimsha ba amma tafi Rimsha ilimin boko, dan ita ta ɗauki boko da muhimmanci, ita ma Rimsha tana da ilimin bokon sai dai ko a School daman Jehan tafi Rimsha da class, ita ma Rimsha bata son rai ni amma tana da fara'a ga son mutane ba ruwan ta shiru shiru bata son hayaniya.
Sai hira suke zubawa daddy na cike da farinciki ita kuwa Jehan ta lafe a cinyar Gwaggo sai shagwaɓa take zuba mata, gwaggo na biye mata, mum dad suna hira Uncle shitu na hiran da Rimsha a kan wani hadisi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama in da yake cewa ka kyautatawa Mumini kyakyawan zato, ka zauna da kowa zuciya ɗaya, idan kayi hakan ko da wani yayi niyar cutar da kai Allah ba zai bashi dama ba dan kai baka kullace sa a ranka ba.
Suna tsaka da hirar su mai gadi yayi sallama, da fara'a daddy ya amsa masa, har kasa mai gadi ya duƙa yace "Alhaji kayi baki a waje" kasan cewar daddy ya saba da ansan baki kala kala ko yaushe musamman ma da siyasa ta gaba to hakan yasa bai damu ba ya miƙe ya nufi waje yana faɗin "Ina zuwa baby Jehan" jikin sa sanye da jallabiya baka.
Fitan daddy ba'a da 5mins ba uncle Shitu ya miƙe yana faɗin "Bari na bi bayan Alhaji sai mu dawo tare" da fara'a mum ta amsa masa da to, san nan yayi waje.
Yana fita harabar gidan sai bai ga kowa ba, cikin sauri ya nufi waje, dai dai lokacin wasu jibga jibgan sojoji ke kokarin tura daddy cikin motar su, jibga jibga ne sosai da sosai gashi dukkan su face nasu da face mask zasu kai su takwas, cikin sauri Uncle Shitu yace "Meke faruwa lafiya?" Ɗaya daga cikin sojojin ne ya nunawa uncle Shitu ID card nashi na aiki ba tare da yayi magana ba, kallon daddy uncle Shitu yayi kafin yace "Meke faruwa Alhaji" girgiza kai daddy yayi kamar zai yi kuka yace "Wai wani ɗan kidnaping suka kama yace musu nine mai gidan shi nike basu makamai suke sace mutane, nayi kokarin su barni na kira lawyer amma sun ki yarda, ni ina jin akoi abun da a ka shirya min ne, please Shitu ga amanar family na ka kulamin da su kafin na dawo karka sanar musu abun da ke karuwa san nan ka kira min lawyer mu haɗu da kai a office ɗin na su" innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine kawai abun da uncle Shitu ke iya furtawa, muryan sa har kerma yake wajen cewa "bari na fito da mota sai muje tare" basu jira uncle Shitu ya gama magana ba suka ja motar su a guje suka tafi da daddy kamar zai yi kuka
cikin sauri Uncle ya koma cikin gida ya ɗauko mota, duk abun da ke faruwa mai gadi na kallon su sai salati kawai yake, uncle Shitu na kokarin jan motar mum ta fito, tana faɗin "Lafiya Shitu fita kuma zaku yi ne ba sallama" in brief uncle Shitu ya sanar da ita sojoji sun kama da daddy da kuma abun da ke faruwa amma yanzu zai bi bayan su, su taya su da addu'a komai zai dai dai ta In Sha Allah, sosai mum ta shiga tashin hankali mara misaltuwa har jiri jiri take gani saboda tashin hankali nan take taji kan ta ya mata yauyi ta kasa motsawa daga wajen, har uncle Shitu ya ja motar mai gadi ya buɗe masa gate ya fita da gudun gaske yabi bayan su daddy.
Slowly mum ta juyo da nufin ta koma cikin gida sai ganin Jehan tayi tsaye a bayan ta tana hawaye, da kyar ta iya ɗaga kafafun ta da suka mata nauyi kamar dutse ta karisa wajen Jehan ɗin, ta rungumeta tana goge mata hawaye tare da bata baki, a haka suka koma cikin Palo.
Da gudu Jehan ta faɗa jikin gwaggo tana kuka tana faɗin "Gwaggo uncle yace an kama daddy wai ɗan kidnaping ne" zubur gwaggo ta miƙe tare da dafe girjin ta tana ambaton sunan Allah, ita ma Rimsha miƙewa tayi cike da shin hankali nan take hawaye suka fara wanke mata fuska, mum na kokarin yin magana sukaji sallama daga bayan su, a bakin kofar shigowa palon, a sukwane suka juya, wasu yan sanda ne sanye cikin kayan aikin su hannun su riƙe da wasu mai ɗauke da wasu rubutu, kai tsaye suka shigo cikin palon basu jira wani izini ba kuma
Kai tsaye wajen mum suka nufa suka miƙa mata takardun da bairo a kan ta sanya hannu, ko kaɗan bata damu ba a tunanin ta tun da har suka iya wuce asalin babban gate na estate ɗin suka zo nan to manyan yan sanda ne, kuma kila a kan case ɗin daddy suka zo, dan haka bata tsaya duba takardun ba kawai ta sanya hannu jikin ta sai kerma yake
gwaggo ce tayi ta maza wajen cewa takardun me wan nan, already lokacin mum ta sanya hannun sun miƙawa Rimsha a kan itama ta sanya hannu, ko kallon in da Gwaggo take basu yi ba
cikin kiɗi ma da tashin hankali Rimsha ta sanya hannu jikin ta sai kerma yake, ansan takardun daga hannun Rimsha sukayi suka miƙa wa Jehan ita ma