Showing 81001 words to 84000 words out of 194715 words

Chapter 28 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1004

inci a guje suna son kamawa su runguma, wasu ma har sun kama sun runguma ɗin sun yar da gaskiya, kayi rayuwa ba tare da cutar da wani ko tauye hakkin wasu ba yafi komai wahala a duniyar yanzu, babu mai tai makon ɗan uwan sa, jama'a da dama sun manta lahira sun rungumi duniya hannu bibbiyu, jama'a da dama sun manta cewa wanda ka bayar shi zaka tarar a lahira wanda kuma kaci a nan duniya zaka barshi, dan Allah barkama ka karawa kan ka karfin gwiwa wajen ganin ka tsaya tsayin daka ka ceto mana kasar mu, muna bukatar adalin shugaba irin ka, kasar mu na bukatar jajirtattun maza irin ka, aikin Allah na da wahala, ba'a shiga aljanna a na kwance a gado, duk wanda Allah keso da Rahma to sai ya jarrabe shi da wani abun, to ka ɗauka duk wan nan barazana da abokan hamayya suke maka jarabawa ce daga Allah, kuma ka dage ka ci jarabawar, san nan ka zauna da kowa zuciya ɗaya" duk wan nan hiran da suke cikin harshen turanci suke yin sa,
dogon numfashi yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya kafin yace "Kin san me?" Girgiza masa kai tayi alamar a'a "Meeting da naje ɗazun sai da nayi dana sanin shiga ta siyasa, saboda a fillin Allah wasu daga cikin manya ke min baraza a kan na janye tun yanzu abun ya tsorata ni, shi yasa nake tsoron kar na jefa rayuwar ku cikin haɗari" kwanciya mum tayi a jikin sa cikin sigar soyayya ta fara magana "Barkama ka sani fa kafin mutun yaji daɗi sai ya sha wahala, musamman ma mutun mai zuciyar gaskiya irin naka to fa sai ka daure ka kawar da kan ka daga kan wasu abubuwan idan ba haka ba bazaka taɓa cin ma nasara ba, a zamanin yanzun nan duk wanda yace zai fito fili ya nuna cewa shi gaskiya yake so tofa makiya ba zasu taɓa bari ya kai labari ba sai ya dage da kai wa Allah kukan sa, yanzu dai ka manta da komai ka ci-gaba da gwagwarmayan ka kana addu'a muma zamu taya ka, In Sha Allah ba dai ɗan adam ba, sai Allah ya cika maka burin ka na ganin ka taimaki talakawa kuma ka raya mana kasar mu ta girma kamar sauran manya manyan kasashe na duniya In Sha Allah" ta kai karshen maganar tana riƙo hannun sa, murmushi ya saki har sai da dimple nashi ya lotsa, cike da so da kauna yace "Shi yasa nake son ki matata duk lokacin da na shiga damuwa kin san yadda zaki yi ki kwantar min da hankali, duk wata natsala ta idan na kawo miki, ba za'a fi 10mins ba kike samo mana mafita, Allah ya miki albarka ki taya ni da addu'a In Sha Allah burin mu zai cika bari naje nayi wanka yanzu na fito sai mu ci-gaba da hirar ko?" Gyaɗa masa kai tayi tana faɗin "Amin ya Allah" ta kai karshen maganar tare da tashi daga jikin sa, miƙewa yayi ya nufi toilet ita kuma ta miƙe ta wuce wajen drawer kayan sa ta ciro masa kayan sawa da duk wani abun da zai buƙata ta dawo ta ajiye masa a bakin gado san nan ta haye saman gadon ta kwanta tana tunanin rayuwa.

After some days

*KADUNA*

A yau Akil yazo yin sallama da Umaisha zai koma makaranta, sanye yake da manyan kaya wato wata dakakkiyar yadi navy blue mai bala'i kyau da tsada, ɗinkin half jomfa, kayan sun masa kyau, yau ma kamar kullun tsaye yake a kofar gida bai shiga ba, ya bawa gidan baya ya kifa kai da jikin mota kamar dai kullun, ya aiki mai gadi da ya kira masa matar sa, ko da mai gadi yaje Abbi baya nan ya tafi company shi kuma Irfan ya wuce Uk tun kwana biyu da suka wuce, gidan ya rage daga Umaisha sai Aafia, koda mai gadi ya sanar da su sakon Akil sai Umaisha tace "Kaje kace masa Abbi yace ya shigo ba zan kara fita ba" tayi maganar cike da tsoron abun da Akil ɗin zai mata sai dai kuma ta sawa ranta ko kashe ta zai yi bazata ki bin umarnin Abbin ta tabi na Akil ɗin ba.

Ko da mai gadi ya isar masa da sakon da Umaisha tace, ko kaɗan Akil bai damu ba, ba musu ya shigo cikin gidan, kallon ɗaya zaka yiwa face nashi kasan yana cikin damuwa yau he look so silent kamar ba shi ba, bakin sa ɗauke da sallama ya shigo palon already Aafia ta bar palon tun tafiyar mai gadi.

Cikin sanyin murya Umaisha ta amsa masa sallamar, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kan sa tare da zama saman sofa, murya kasa kasa kamar mara lafiya yace "Jeki sanya hijabin ki kizo" da sauri tace "Yaya Akil a cikin gida ne fa ba waje ba" tsare ta yayi da ido na yan mintoci kafin yace "Ban isa in ce kiyi abu bane?" Girgiza masa kai tayi tare da miƙewa ta nufi bedroom na su, ajiyar zuciya ya sauke tare da jingina kan sa da jikin sofa,

Jim kaɗan ta dawo cikin hijabi yana ja har kasa ɗan nesa da shi ta zauna tana faɗin "Ina wuni" tayi maganar tana kunbura kumatu, ɗagowa yayi ya zuba mata ido kasa kasa ya fara magana "Dan nace ki sanya hijabi ne kike ɓata rai haka?" Shiru ta masa tana jin haushi a zuciyar ta "Ina son ki sani duk macen da bata ɗauki hijabi a matsayin sutura ba ni a waje na da ita da dabba duk ɗaya ne, bana son mace da bata suturta jikin ta, bana son macen da bata daraja kan ta, hijabi shine darajar ya mace, ina son mace wayayyiya amma ba ballagaza ba, idan nace wayayyiya ina nufin mai wayewa irin ta addinin musulunci, ina matsayin yayan ki, kuma mijin ki, amma a yadda muke ni ban yarda da na rinƙa kallon ki haka ba hijabi ba, kuma ban kawo sadakin ki ba koda kuwa a cikin ɗakin uncle ne ba a palo ba, ina son kullun na ganki da hijabi har kasa idan nazo, yau bana jin daɗi jikina, bana son yawan magana dole ne yasa nazo miki sallama, ina son ki sani wallahi idan na tafi kika karya doka ɗaya daga cikin dokokin dana sanya miki wallahi 6 hours ya isa ya kawo ni in da kike, idan kuma nazo in ran ki yayi dubu sai na ɓata miki, san nan ki faɗa wa Uncle idan na dawo na nitsu zan kawo sadakin ki na ɗauke ki mu koma tare, abu na gaba ki faɗa wa Uncle ya dai na samin wasu dokoki tsakani na dake dan ke ɗin matata ce ko suna so ko basu so, dole ke matata ce, yanzu ma na shigo gidan nan ne ba dan komai ba sai dan bani da lafiya banason yawan hayaniya, amma daga yau ni ba zan sake shigowa ba, shi yasa ma ina dawowa zan kawo sadaki na ɗauke ki dan ba zan iya wan nan abun da uncle ke min nan ba" ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ciro kuɗi daga aljihun sa masu yawa rafar 500 ya ɗaura mata saman hannun sofa ya nufi hanyar fita "Yaya Akil meke damun ka?" Cak ya tsaya tare da juyowa ya zuba mata ido, ganin bai amsa mata ba yasa ta sake mai mai ta tambayar, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Nima ban sani ba kawai bana jin daɗin jiki nane gaba ɗaya na rasa meke min daɗi" miƙewa tsaye tayi ta nufo sa tana faɗin "To kasha magani ne?" Zuba mata ido yayi ya kasa ɗauke idon sa daga kan ta, tun da yake bai taɓa tsayuwa ya kalli face nata da kyau ba sai yau, wow shine ka ɗai abun da yake furtawa a ransa,

har ta iso gaban sa bai sani ba, cikin girmamawa tace "In kawo maka maganin zazzaɓi" girgiza mata kai yayi ala'mar a'a san nan ya juya ya nufi hanyar fita.
Kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin "To shi ne zaka tafi kuma bayan idan ka tafi yau sai bayan kusan shakara kafin na sake ganin ka" mamaki ne ya kama shi, a sukwane ya juyo cikin tsawa yace "Ke ni bana son munafurci yanzu kukan me kike?" Cike da tsoro tace "To ba kai ne zaka tafi ba kuma ni ban gan ka sosai ba idan ka tafi ya zan yi?" A fusace yace "A baya da baki sanni ba ya kike yi?" cak ta tsayar da kukan nata ta zuba masa ido, guntun tsaki yaja tare da wucewa abun sa, ya bar ta nan tayi mutuwar tsaye.


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

TRIPLET'S💞 19





https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo


*THE BEGINNING*



💞*STAR LADY*💞




EPISODE 19



Kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin "To shi ne zaka tafi kuma bayan idan ka tafi yau sai bayan kusan shakara kafin na sake ganin ka" mamaki ne ya kama shi, a sukwane ya juyo cikin tsawa yace "Ke ni bana son munafurci yanzu kukan me kike?" Cike da tsoro tace "To ba kai ne zaka tafi ba kuma ni ban gan ka sosai ba idan ka tafi ya zan yi?" A fusace yace "A baya da baki sanni ba ya kike yi?" cak ta tsayar da kukan nata ta zuba masa ido, guntun tsaki yaja tare da wucewa abun sa, ya bar ta nan tayi mutuwar tsaye.

Kai tsaye motar sa wuce, ko da ya shiga motar ya kasa tafiya ya zauna shiru kamar mai tunani, ba abun da ke masa yawo a kai face muryan Umaisha mu samman in tana masa shagwaɓa yana bala'i son ganin tana zuba masa shagwaɓa sosai, sai dai iyashege irin nasa ya hana ya rinƙa biye mata wai a cewar sa idan ya biye mata zata raina sa hakan yasa baya sake mata fuska.

Almost 1 hour yana zaune cikin motar, ya kasa tafiya ji yake kamar ba zai iya komawa school ya bar ta ba, duk da zasu rinƙa waya hankalin sa bai kwanta ba, gani yake kamar zai yi nisa da bugun zuciyar sa, gani yake kamar idan ya tafi zai rasata, wan nan dalili yasa har zazzaɓi ta kama shi.
Sai da ya kara 30 mins a wajen san nan ya kunna motar sa, da kyar ya iya jan motar ya bar wajen, ya nufi gida.

A ɓangaren ita ma Umaisha sai da tayi tsayuwar 20 mins a wajen san nan ta ja kafar ta jiki ba kwari ta wuce bedroom na su, tana shiga ta kakalo murmushi dole tana faɗa wa Aafia yaya Akil ya koma school, guntun tsaki Aafia taja kafin tace "Allah ya raka taki gona yan damuwa kawai, shi sa yaya Irfan ai ɗaya suke shi ma yaya Irfan har da wani cewa kar mu kuskura mu fita ba hijabi, wlh yanzu ma ina tashi in tafi gidan su Rufaidat in je in mata albishir Abbi yace zai biya mata School fees ta shiga school namu ita ma, kuma wlh babu hijabi babu gyalema zan tafi sai nafa uban da zai sani sawa" ta kai karshen maganar tare miƙewa ta hau shirin zuwa gidan su Rufaidat, ita kuma Umaisha gyara kwanciyar ta tayi a saman gado ta ɗauko wayar ta, ta shiga massage ta fara tsara massage na kalaman soyayya masu daɗi, dan ta turawa Akil, kirjin ta sai dukan uku uku yake tsoro take ji karya zageta ko ya mata faɗa dan ta san halin sa komai ba burgeshi yake ba shi, haka ta daure ta tsara masa kalamai masu daɗi da kwantar da hankalin masoyi, tana kammalawa ta tura masa ta kwanta tana jiran ko zai mata reply.

Lokacin message ɗin ya shigo wayar sa yana tuƙi, da hannu ɗaya ya ɗauki wayar dan ya duba, ganin sakon ta yasa ya fara karanrawa cikin sauri, lokacin guda cool murmushi ya bayyana a kan face nashi har cikin ransa ya ji daɗin sosai, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kai wayar sai tin bakin sa ya mannawa wayar kiss nan take yaji zazzaɓin nasa ta gudu jikin sa ya ɗan warware, a hankali ya mayar da wayar ya ajiye, ya ci-gaba da tukun sa ba tare da ya mata reply ba, ita kuwa tana can tana jiran ko zai yi reply tana fargaban shin yaji daɗin massage ɗin ne ko bai ma karanta ba ne, har barci ya ɗauke ta Akil bai yi reply ba, ita kuma Aafia ta shirya cikin atamfa doguwar riga ɗinkin ya ɗan kama ta haka ta fice babu ko gyale, ta nufi gidan su Rufee, taxi ta shiga dan lokaci basu gama iya motar tasu ba, lokacin suke koya shi yasa ta shiga taxi.


*KANO*

Jiki ba kwari Imran yazo yin sallama da Jelly duk ya damu sosai dan bai son yin nisa da ita, ita kuwa sai murnar ganin sa take, sai faman washe baki take kamar wata zararriya, yaki faɗa mata zai koma ne daddy kawai ya faɗawa ita kuma yace mata kawai yazo ganin tane, sosai tayi murna, sun sha hira sosai, sai 3 na yamma san nan ya musu sallama ya kama hanyar Kaduna kamar zai yi kuka bai son rabuwa da Jelly ɗin sa, haka ba yadda ya iya, ya wuce Kd.

*ABUJA*

Zaune suke a palo dukkan su sai Jehan ita kaɗai ce bata nan, suna zaune suna yar hiran su, yayin da shi kuma daddy yake latsa wayar sa yana kallon yadda mutane ke accepting na shi a media kowa sai faɗi Nawazudden yake, ko ina sunan dake treading a media kenan, sai murmushi daddy yake yana jin daɗin hakan, ita kuwa Rimsha ta tada kai da cinyar mum tana karatun littfin husnul Muslim, ita kuma Gwaggo ta zubawa Tv ido tana kallon Sunnah Tv.

babu ko sallama Jehan ta faɗo palon sai kwaɓe fuska take kamar wadda taga kashi ko wani abun kyamar. "My Jehan lafiya? Daddy ne ya tambaya yana kallon face ɗin ta, zama tayi gefen sa tana faɗin "Daddy ina kewar School ne" shafa kan ta yayi yana faɗin "To ai next week zaku koma ko? Gyaɗa masa kai tayi kafin tace "Daddy yau azumi saura kwana nawa?" Cikin sauri Rimsha tace "Remain 12 days fa" "did I ask you?" Cewar Jehan tayi maganar tana hararar Rimsha ɗin, murmushi Rimsha tayi tana faɗin "Sorry ASP Jehan or DPO or commission" turo baki Jehan tayi tana kokarin yin magana suka ji sallamar mai gadi, miƙewa daddy yayi ta nufi kofar palon yana amsa sallamar, kallon Gwaggo mum tayi kafin tace "Da alama barkama ya san da zuwa mai gadin nan fa" murmushi gwaggo tayi tace "Ni dai ba ruwa na kun fi kusa ai" mum na kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa "Mum i need to see your previous pictures before you got married to my dad nan take face ɗin mum ta sauya, nan take taji ba daɗi taji zuciyar ta na mata ciwo Jehan ta tuna mata baya, shiru tayi bata yi magana ba.

Da sallama daddy ya dawo palon hannun sa ɗauke da carton irin na turo sako daga kasar wajen nan, a tsakiyar palon ya ajiye, da sauri Jehan ta miƙe ta kariso wajen tana faɗin "What is this daddy?" Miƙewa zaune Rimsha tayi ta zubawa daddy dara daran sleeping eyes ɗin nan nata ba tare da ta je wajen ba.

Buɗe kwalin daddy yayi ya fara fito da kayan yana faɗin "Kaya na saya muku daga Dubai" ya kai karshen maganar tare da fitowa da Jehan wasu kayan masu kyau na yan kwallo dan Jehan a koi ta da son kayan yan kwallo sosai, daddy na kokarin yin magana Jehan ta ansa kayan daga hannun sa tana dariya ta wuce ta haye sama ta nufi bedroom na su dan taje ta gwada, girgiza kai kawai daddy yayi ya ci gaba da fito da kayan, ita dai Rimsha ta zuba masa dara daran sleeping eyes nata tana kallon yadda yake fitar da kayan, ɗago kai yayi yace "My siha close your eyes, i want to surprise you" ba musu ta ta rufe idon na ta, wani leda ya ɗauko daga cikin kwalin ya nufe ta, ya zauna gefen yana faɗin "now open your eyes" da sauri ta buɗe idon nata dan ta ƙagu ta ga me daddy zai mata surprise a kai, miƙa mata ledar yayi yana kallon face nata, cikin zumuɗi ta ansa tare da buɗewa

a sukwane ta miƙe tsaye tana faɗin "What? Daddy am I dreaming or not?"

Sosai daddy ke murmushi dan bashi da wani burin da ya wuce yaga farincikin yayan sa, wan nan murmushi dake kan face ɗin Rimsha ya fi masa abubuwa kaso 80 cikin ɗari na rayuwar sa.

Fito da kayan Rimsha tayi tana ta dariya kamar bakin ta ba zai rufu ba, kyakkyawan dimple nata sai motsawa yake ga open teeth nata dake tsakanin fararen hakwaran ta kamar gonar audiga, cikin zumuɗi ta zuje zip ɗin jacket ɗin ta sanya a jikin ta tana faɗin "daddy ai na ka samu irin jacket ɗin GAR dan Allah" "Saya na yi mana, My siha daga Dubai na sai miki saboda son da kike wa guy ɗin shi ne na ga kuma yana yawan sanya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login