Showing 138001 words to 141000 words out of 194715 words
Islam perspective from him" sosai Musharraf yayi mamaki tare da ɗaukan kudirin in dai ko hakane suna da masani a kan addinin musulunci kuma sun san wasu daga cikin littafan musulunci to ba zai bargidan ba har sai ya tabbatar ya musuluntar da su, bai gama tunanin da yake ba ya jiyo muryan James yana faɗin "Don't allow uncle, dad, and the rest to know you are a Muslim, because All of these people that your seeing in this house they don't like Muslim, they hate Islam, especially dad, uncle Herry, but lion has a Muslim friend" sosai Musharraf yaji daɗin bayanan James dan ya kara samun makama da zai musuluntar da su, a iya ɗan zaman sa a gidan ya fahimci kowa na gidan yana tsoron lion da suke kira kuma suna shakkan sa, duk da bai taɓa ganin wannan lion ɗin ba, yasan dai yadda suke maganar sannan shine mai power a gidan, da alama shike juya kowa, amma Alhamdulila tun da shima lion ɗin yana da aboki musulmi hakan yazo masa da sauki, dan yana da tabbacin shima lion ɗin ba zai rasa sanin wasu abubuwa dangane da addinin musulunci ba, through wannan abokin nasa.
Ganin Musharraf yayi shiru ne yasa James yayi tunanin ko dai yaji tsoron dan nace masa yan gidan nan basa son musulmai ne, karfa ya shiga damuwa gashi kuma bashi da lafiya, tuna haka yasa James yace bari ya masa wata dabara dan karya sa kansa cikin damuwa yazo ya kara ciwo kan ciwo "No uncle don't worry, me a really like Muslim people, I'm thinking about there religion, sometime they are doing something good, I read some Muslim books, most of the things that I saw in the books are true, that's means they are not laying, which is why I believed in the books, I'm thinking about the religion, this is the reason why i hate our pasto, he is lying to us everyday, he is always talking about something that is not coming to pass" jin hakan ma ya sanya Musharraf ya kara jin daɗi, da tunanin James ba zai yi wuyar shiga musulunci ba, saboda shi ya fara gane gaskiya, zai yi saurin amsan kalmar shahada, shi kuwa James sai kokarin tattaro kalaman da zai kwantar wa da Musharraf hankali yake, dan bai son ganin Musharraf ya shiga damuwa saboda rashin lafiya da yake ciki.
"I want to see this lion" cewar Musharraf, girgiza kai James yayi kafin yace "give thank to god da a baya baka taɓa kallon lion ba, kuma ka roki Allah yasa kada kayi ido biyu da shi" "why?" Musharraf ya tambaya yana tsare James da ido, jinjina kai James yayi yana faɗin "kawai" "No James ni gaskiya ina son ganin sa" shiru James ya ɗan yi kafin yace "Anywhere yanzu dai i think yana wajen dad, yau ɗaya ga wata lokaci shan drugs na dad yayi, yana can yana bashi magani" cikin sauri Musharraf yace "meke da mun dad ɗin?" "Wine da yake shane before yayi affecting nasa over, yayi spoil na wasu abubuwa daga halittar sa, shiyasa something zakaga yana da saurin rikicewa, yana abu kamar like bashi da sense, kuma zakaga idan abu kaɗan ya faru zai birkice jikin sa ya fara kerma, baka ganin ko magana mukayi sometimes zaka ga jikin sa ya fara kerma kamar mai tsoron mu?" Shiru Musharraf ya ɗan yi kafin yace "to me yasa baku hana shi shan wine ɗin ba?" "We already stop him since before now, kuma yana shan drugs, by the God grace ya kusa samun lafiya ya koma kamar da" addu'a sosai Musharraf ya masa, James yana amsawa da Amin, sannan James ya sauƙo da kwanon ya je toilet ya zubar da ruwan ya dawo ya gyarawa Musharraf zama ta yadda zai ji daɗin yin sallar sa.
A wanna yanayin Micheal ya shigo ya same su, ɗaure fuska yayi kafin yace "who is this James?" Yayi maganar yana kallon Musharraf, "is my uncle my friend also" James ya bashi amsa, yayin da Musharraf kuma ya tada kabbara ya fara sallah a rigingine, juyawa Michael yayi ya nufi hanyar fita yana faɗin "Lion want to see us, in his room now" kallon Musharraf James yayi yace "Uncle I'm coming" kasan cewar Musharraf yana sallah sai bai amsa wa James ɗin ba, shima James bai damu Musharraf ya amsa masa ba saboda ya san idan ana sallah ba'a magana, ya san haka a wajen friend nasa.
A tare suka jera shi da Michael zuwa part ɗin Romeo.
Bakin su ɗauke da excuse suka shiga bedroom ɗin Romeo, yana tsaye ya bawa kofar shigowa baya, ya goya hannun sa a saman kirjin sa, tun da sukaga haka suka gane ba lafiya ba, dan haka jiki ba kwari suka zauna a bakin katafaren bed ɗin Romeo.
Shiru Romeo ya musu, suma shiru suka zauna almost 30mins kafin Romeo ya juyo a hankali, fuskar nan tasa kamar hadari, dara daran blue eyes nasan nan, sun sauya launi zuwa ja, lausasan laɓaɓɓan san nan har wani kwalli suke kamar yasa lips balm saboda ya ɗan ciza su kafin ya juyo, ganin shi a haka ba karamin razana su James yayi ba, nan take suka sha jinin jikin su.
Rai a matukar ɓace, first time da Romeo ya fara ɗaga murya yayi magana, cikin zafin rai yace "I was thinking you are responsible, but you people are not, your misbehaves has jump from our uncle now to our daddy!! I most give you specifies punishment, daddy didn't deserve that miscresant from you, have you forgotten wen he was up and down for us, it's time to repay him, to provide happiness for him and draw him close to us, met me at my place!!!" yana kai karshen maganar ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin, dukkan su sun fahimci kuskuren su na haɗawa da dad da suka yi tun ma Romeo bai fara basu horo ba, tabbas suna son daddyn su, amma basu san me yasa suke ɗaukan dad ɗin kamar su Uncle Herry ba.
Ganin Romeo ya fice ne, kuma baya son African time yasa suka miƙe da sauri suka bi bayan sa.
Kai tsaye wajen wannan filli na dawakan suka nufa, Romeo yasan babban kuskure ne ya bawa Michael wannan hukunci saboda ciwon sa, to amma bashi da zaɓi dole ya hukun tasu, saboda gobe kada su kara yiwa daddy abun da suka masa, sunyi babban kuskure, kuma sun san dad bai da lafiya amma haka suka rufe ido suka haɗe sa da su Uncle suka masa wannan tsiya, ya zama dole su karɓu hukunci dan gaba.
Zama saman ɗaya daga cikin manya manyan kujeru masu numfashi dake wajen Romeo yayi, sannan ya bada Umarni da a fito masa da dawakan sa, dan suyi tsre da Michael da James, abun da basu taɓa kwatantawa ba, yau zasu yi.
Haka kuwa akayi, suka fara tsare da wayan nan manya manyan dawakan masu jini a jika da ji da lafiya da karfi.
Sai dai abun mamaki, dawakan sun kasa wuce James, shi kam Michael tun ba'ayi nisa ba suka wuce sa, James ne ya sha fama da su har zuwa karshen wajen, kuma suka dawo dawakan basu wuce saba, ko kaɗan Romeo bai yi mamaki ba, ya danganta hakan da cewa dan jinin sane yasa dawakan basu wuce James ba, shi kuma Michael saboda laluran sa yasa suka wuce sa, so bai wani damu ba.
Ɗaukan su yayi suka tafi mataki na biyu, shi dai Michael har kuka ya fara yiwa Romeo dan ba zai iya jurewa ba, bashi da lafiya bashi da kwarin jure hakan, amma haka dole ya jure suka shiga mataki na biyu
Manya manyan karafuna Romeo ya sanya su ɗagawa masu bala'i nauyi, haka ya sanya jibga jibgan sojojin sa suka ɗaura musu wayan nan mayun karafuna a kan su da kuma hannayen su, sannan Romeo ya sanya su suyi tsayuwar sojoji, idan sukayi kuskuren sakin karfe ɗaya, to fa a kafar su zai faɗa musu, sai ya musu daga daga da kafa, saboda nauyin sa da girman sa, sai ya fashe musu kafa tsab, haka suka hakura suka riƙe karfen nan da iya karfin su na karshe, gashi Romeo yace tsayuwar 1h zasuyi a wajen, tuni Michael ya fara kuka, wi, wai, wi, kamar ƙaramin yaro, har da majina, ya saki ɗan karamin bakin nan nasa yana zubar da yawu ga majina ga hawaye, gwanin ban tausayi, shi kuwa James sai haɗa zufa yake amma bai yi kuka ba, kasan cewar ya samu ire iren wannan horo daga wajen ogannin sa.
Romeo ganin kukan Michael na neman ɗaga masa yankali ne yasa ya ɗauko Bluetooth ya sanya a kunnen sa, ya mai da kan sa kan screen ɗin wayar sa, ya daina kallon su, shi kuwa Michael sai kuka yake ya kasa shiru.
Gaba ɗaya tausayin Michael ya hana James samun nitsuwa, ji yake kamar ya sanya sojojin dake kewaye da su suna gadin sun nan, su ansa karafunan Michael su kara masa, su bar Michael ya koma ya zauna ya huta, sai dai kuma bai isa yayi hakan ba kasan cewar Romeo ne ke basu horon da kan sa.
Masu fi 30mins da fara tsayuwar ba, jikin Michael ya fara kerma, ya kasa tsayawa waje guda, kan kace me ya fara tangal tangal, gashi kuma idan ya faɗi kasa karafunan nan suka danne sa, sai dai wani ba shi ba dan mutuwa zai yi, Romeo kuwa ya sanya Bluetooth a kunnen sa hankalin sa na kan waya, bai san meke faruwa ba, su kuwa sojojin basu isa suyi wani abuba idan ba Romeo ne ya basu izini ba, koda kuwa faɗuwa Michael zai yi ba su isa su tare sa ba sai dai in Romeo ya basu izini.
Tafiya gaba ɗaya Michael yayi zai zube kasa, kamar wani walkiya haka Romeo ya miƙe ya tarosa yayin da wayan nan jibga jibgan sojojin suka ansa karafunan hannun sa a sukwane, rungume Micheal Romeo yayi, da kyar da kyar Michael ke mumfashi, nan take jikin sa yayi ya ɗau zafi over kamar wuta, sai kerma jikin sa keyi kamar ba lafiya ba, da hannu Romeo yayiwa sojojin nuni da su karɓi karafunan hannun James karya faɗi shi ma, a sukwane suka karɓawa James ɗin, da Romeo yayi niyar idan suka gama part two zasu wuce part three, dan yana son ya horasu da kyau, sai dai kuma ina hakan ba zai yiwu ba saboda Michael.
Cak ya ɗauki Michael saman kafaɗar sa suka wuce cikin gida, da kyar James ke jan kafa yabi bayan su, sai faman haɗa zufa yake yaji wuya sosai.
Saman katafaren bed nasa ya kwantar da Michael ya fara duba sa, yana mai jin ba daɗi a ran sa, James kuma bedroom nasa ya wuce dan yaje yayi wanka ya huta.
Mu leƙo Nigeria mu dawo
💞NIGERIA💞
A ɓangaren Hajiya da Jelly kuwa, Hajiya dai taga ikon Allah iya ganin idon ta, dan kuwa duk in da taje sai Jelly ta bita, taki yarda ta zauna ita kaɗai, har toilet idan Hajiya ta shiga sai Jelly ta bita, Hajiya na son tayi wanka amma ba hali dan kuwa Jelly dai taki yarda ta zauna ita kaɗai, ko abinci Jelly bata ci da hannun ta sai dai a bata a baki, daga karshe dai Hajiya da taga ba zata iya da Jelly ba sai ta kira ɗan ta Nawid da kuma Mijin ta a waya dan suzo ko zasu san yadda zasu yi da Jelly.
Ko da Nawid yazo sai cewa yayi, zai zane ta da bulala, nan fa Jelly tace ba'a haifesa ba ,dan kuwa tsayawa tayi ta riƙe kugu tace wlh in dai ya daketa sai ta rama, har ya zaro belt zai fara zaneta Hajiya ta dakatar da shi ta hanyar ce masa "Haba Nawid bakaga bata da lafiya bane? Dan Allah ka bita a hankali, kasan yadda nake son yarinyar nan kuwa, kasan yadda nake son ya mace kuwa, kai ka ɗai gare ni, ina burin samun ƴa mace Allah bai yi ba sai yanzu Allah ya bani kace kuma zaka takura mata, a'a ni na kira kane kawai dan kazo ka tayani lallaɓata ta zauna nayi wanka" zaro ido Nawid yayi yace "Haba Ummi ni da nake cewa idan ta samu sauki, miƙata wa hukuma za muyi dan su nemo iyayen ta" girgiza kai Hajiya tayi tana faɗin "Tab lallai Nawid, ai wannan yarinyar marainiya ce dan kuwa kaga a kan titi take yawo na bugeta, kuma wlh ko da ma ba marainiya bace dole iyayen ta su bani ita, dan ina son ta ba zan iya rabuwa da ita ba, kana ga yarinya kamar yar india tab, ni ai har na hango auren ka da ita" kasan cewar Nawid ya san halin Ummin sa, da bala'i son ƴaƴa mata hakan yasa yayi shiru kawai ya zuba mata ido tana ta fama lallaɓa Jelly, kamar wata yar Baby har da ce mata "my baby ki zauna ko idan na fito wanka zan goyaki muje muyi wasa" mamaki Nawid yake Jelly ta haukata masa uwa lokacin guda, girgiza kai kawai yayi ya fice daga ɗaki haushi kamar ya shaƙe Jelly.
Haka Hajiya ta rinƙa lallaɓa Jelly har Abbon Nawid ya dawo, suka haɗu sai lallaɓa Jelly suke, dan shima Abbo Jelly ta tafi da shi, lokaci guda yaji kaunar yarin yar a ransa, sai dai shi kauna na daban yake mata.
Da kyar Jelly ta yarda ta aminci suka zauna tare da Abbo a cikin bedroom ɗin, Hajiya ta wuce toilet da sauri dan taje tayi wanka.
Sai kallon Jelly Abbo yake, ya kasa cire idon sa daga kallon ta, ita kuwa sai faman turo baki take, ita kaɗai tana kunkuni, sai wani cool murmushi Abbo ke sakewa yana kallon face ɗin ta, dan turo wannan ɗan bakin nata da take ba karamin tafiya da shi take ba, ji yake kamar ya jawota jikin sa.
Haka Hajiya ta fito ta same su, Hajiya na fitowa Jelly ta miƙe ta rungume ta tana faɗin "Ke bakin ga wannan mutumin ba sai kallo na yake yana min dariya" ko kaɗan Hajiya bata damu ba, dan tasan shi ma Abbo yana bala'i kaunar ƴaƴan mata, dan haka sai tace "Sunana Ummi ba ke ba, shi kuma sunan sa Abbo baban ki ne, kin ji ko? Idan ya kalle ki ya miki dariya kema ki masa, zai ji daɗi, dan yanason farincikin yarsa" yar dariya Jelly tayi tace to, sannan ta saki Hajiya ta koma kusa da Abbo ta zauna tana murmushi
a ɓangaren shi kuma Abbo, gaban sa sai dukan uku uku yake lokacin da Jelly ke faɗa wa Hajiya yana kallon ta, ya san halin Hajiya da bala'i Kishi zata iya fara ruwan bala'i, sai dai kaunar da take wa ƴaƴa mata yasa bata kawo komai a ranta ba, kuma a tunanin ta Jelly bata da lafiya duk wani abun da zata faɗa kawai shirmene.
Tab akoi fa cakwakiya gidan su Nawid, dan da alama shi dai Abbo ya faɗa muje dai zuwa
Ɗaukan kayan ta Hajiya tayi ta koma cikin toilet dan shiryawa, saboda su Jelly suna ɗakin, shiryawa tayi tsab cikin wata dankareriyar shadda milk color ɗinkin doguwar riga, tasha aiki daga sama har kasa.
Bayan ta gana shiri ne ta fito ta riƙo hannun Jelly suka wuce Palo, miƙewa Abbo yayi ya biyo bayan su.
Saman sofa suka zauna Hajiya ta fara ƙoƙarin koyawa Jelly wasu abubuwan, irin su yadda ake gaida mutun da kuma matsayin su a wajen ta, na iyayen, sai kuma yadda zata rinƙa zama da mutane da yadda zata yi wanka da kan ta da sauransu, ba wani abun da Jelly ke ɗauka, Hajiya ke zancen ta kawai, shi dai Abbo da yaga abun nasu bana karewa bane sai ya miƙe ya musu sallama ya wuce office na sa, daman Hajiya ta kira shi ta sashi ya dawo.
Sai faman surutu Hajiya take wai tana yiwa Jelly bayani a kan yadda zata zauna a gidan, ko word ɗaya bai shiga kunnen Jelly ba, bare kuma kanta, a wanna hali wata budurwa ta fito daga ɗaya daga cikin part dake cikin palon, kallo ɗaya zaka wa yarinyar kasan yar duniya ce ta bugawa a jarida, dan wasu shegun riga da wando ne a jikin ta sun matseta, duk wani halitta dake jikin ta ya bayyana, ta zuba attachment a kai kamar wata dodanniya, ga wani uban glass da ta maka a ido kamar wata roka da glass, abun ba kyan gani wai an yi kwalliya
Kai tsaye hanyar fita daga palon yarinyar ta nufa, ko sannu bata cewa Hajiya ba kamar ma bata san da zaman ta a wajen ba
Kwatsam idon ta ya sauka kan, Jelly dake zaune sai faman turo baki take, a hankali matashiyar budurwan ta sauke glass ɗin fuskar ta ta ɗan kalli Jelly from head to toe na yan wasu mintoci kafin nan ta mai da glass ɗin ta fice daga palon, tana tafiya tana juyowa ta kalli Jelly tana wani lashe baki kamar tsohuwar mayya.
Ganin yarinyar yasa Hajiya ta kara zawa Jelly kunne a kan babu ruwan ta da yan gidan nan, dan basu da mutunci a cewar Hajiya, sai dai abun da Hajiya bata sani ba shi ne, Jelly fa bata jin ma me take faɗe hankalin ta na kan Tv dake kunne sai faman turo baki take.
Kai jama'a me kuke tunanin zai faru a gidan Hajiya baban Nawid, hmmm muje zuwa amma dai akoi show
Mu leƙo Rimsha mu dawo
👹DAULAR MUTUWA👹
Sanyin safiya ne ya ratsa ta, kasan cewar lokacin hunturu ya fara shiga, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata masu ɗauke da barci, a razane ta miƙe zaune ganin kyakkyawar face ɗin matashin nan wato duna da ya canza halittar sa zuwa kyakkyawa, da sauri ta miƙe zaune tare da taja baya tana zaro ido, murmushi yayi kafin yace "Fine girl kin cika tsoro" yar wawwaigawa tayi kamar mai neman wani abu, a hankali tace "Ayla ina kuke?" Ɗan matsowa kusa da ita yayi yana faɗin "Suna ɗakin baba, ya kamata yanzu ki dai na jin tsorona" ja da baya Rimsha ta fara yi tana ambato sunan Allah a zuciyar ta