Showing 39001 words to 42000 words out of 194715 words
gini a kayi kamar rijiya a ka kewaye wajen san nan a kayi wanin gini a tsakiya kamar fai fai ruwa na zuba a wajen,
garden na gidan ya kai girman plot 2 cike yake da kana kanan flowers masu kamshi launin je da kore a dai dai kofar shiga garden ɗin daga ɗan gefe an rubuta *Romeo da flowers*, ga manya manyan kujeru masu numfashi na hutawa shirye a wajen, ga fitillu masu hasken gaske sun haske ko ina, gaba ɗaya garɗen ɗin kewaye yake da glass ƙasan sa kuma tiles ne wani gefen kuma grass carpet, tsayawa zayyana muku haɗuwar garden ɗin nan zai cimana lokacin sosai, wajen lambun daddy kawai yaci 2 plot, dan daddy mutun ne mai son lambu sosai, kowani ɗaki a gidan yana da balcony ta gaban sa an kawata wajen da furanni masu ɗaukan hankali, gaba ɗaya gidan kewaye yake da jibga jibgan sojojin masu jini a jika suna tsaye rike da manya manyan bindigu fuskar nan tasu kamar an aiko musu da sakon mutuwa, idan ba kana da dakakkiyar zuciya ba ka kalli face ɗin sojojin nan to zaka iya sumewa dan babu alamar annuri a face nasu ko kaɗan, kowani lungu da sako na gidan jibga jibgan sojoji ne riƙe da manya manyan bindigu kai kace wajen yaki zasu tafi, kai daganin hakan kasan ba gidan wasa kazo ba,
manya manyan swimming pools uku ne a gidan ɗaya na Romeo ne shi kaɗai ba mai zuwa wajen sai shi, biyun kuma na sauran yan gida, haɗuwar wan nan gida ba zai faɗu a baki ba dan gidan nan gari ne guda,
Kai tsaye parking space Michael ya nufa yana zuwa wajen, daga saman gate ɗin wata yar na'ura kamar yar baby ta fara karanto number motar sa daga farko har karshe san nan ta kira sunan wadda ya fita da motar, nan take gate ɗin ta buɗe kan ta, Michael ya shige, duk wani kofa na gidan sai da Romeo ya sai tata da nauran sa dan ya rinƙa samun information a kan waye ya fita waye ya shigo, ko mota zasu ɗauka sai yasan da wani mota suka fita kuma waye ya fita da motar, ko wani kofa a koi matakan tsaro a jikin ta, idan ba gate ɗin farko na shigowa gidan ba bawani waje dake da mai gadi shi ma gate ɗin farko ya bar shi ne dan criminal ya samu ya wuce gate ɗin farko ya shiga gidan, gate na biyu ya tonasa asiri, kuma ba halin guduwa sojojin dake gate na farko zasu yi ram sa shi wan nan shi ne dalilin da yasa ya bar jibga jibgan sojoji a wajen,
Michel na shigar da motar sa ya kashe ta ya fito tare da su lucky, ya danna wani waje kamar remote san nan ya fice daga wajen su lucky na biye da shi, nan take ruwa ya fara sauƙowa yana wanke masa motar tasa, a she ruwa ya danna dan ta wanke masa motar.
Yana fita ya wuce wajen ɗakin su lucky dake kusa da garɗen, ɗakin karnukan ma duniya guda ne har da katon gado a ka sanya musu kai kace ba kuɗi a ke sawa ake sayen abubuwan nan ba, yana kai su ɗakin su ya rufe su ya fito
Kai tsaye katafaren kofar da zata sada shi da cikin gida ya nufa shi kan shi kofar ma abun kallo ne, yana zuwa wajen ya buɗe yatsun sa ya ɗaura saman finger scanner yana kwaɓe fuska yana jin haushin wan nan matakan tsaro irin na gidan, ba karamin fama ya shaba kafin Romeo ya yarda ya dai na haɗa shi da bodyguard suna raka shi School har rashin lafiyar karya yayi dan a barshi ya rinƙa fita shi kaɗai yana shanawar sa, bayan finger scanner ta gama scanning na hannun sa ne katafaren kofar mai girman ta wangale kan ta, guntun tsaki yaja tare da kutsa kan sa cikin,
wani aljannar duniya ne a wajen palone mai girman plot 1 da rabi shi kansa palon yayi girman gidan wani, palon ɗauke yake da tampatsa tampatsan kujeru na alfarma masu numfashi set huɗu ko wani set kuma yana da nisa da ɗan uwan sa kai kace ma kujerun ba a palo ɗaya suke ba saboda ratan dake tsakanin su zaka ce palo huɗu ne kusa da juna amma kuma ba haka bane dukka palo ɗaya ne girman palon ne yasa a kai wa kowani set da mazaunin sa, kowani set da kalar sa sky blue fari milk golden color shine colors ɗin kujerun, wajen table ɗin cin abincin su ma duniya ne guda, table ɗin yana da tsawon 2meter ga haɗanɗun kujerun sa launin golden color masu ɗaukan hankali da ɗaukan ido guda 24, gaba ɗaya curtains na falon farare ne kal kamar yanzu a ka fito da su daga kwalin su saboda haske, Makekiyar Tv ɗaya ne a palon mai bala'i girma wadda idan kana kallon mutun sai kaga kamar ka kira shi ya amsa saboda girman Tv, fentin palon gaba ɗaya golden color ne sai ɗaukan ido yake kamar gidan gold, daga kusa da sofa set milk color nan wata iriyar tampatsetsiyar staircase ne mai kamar indomie raun haka kamar maganain sauro haka staircase ɗin yake, daga farkon staircase ɗin a miƙe yake straight daya ɗan yi nisa kamar nisan tsawon mutun daga nan sai ya tafi sama a nannaɗe kamar maganin sauro, shi kan shi staircase ɗin abun kallon ne duniya ne guda fentin jikin sa golden color ne kamar gold san nan ga wasu kwayaye fitillilu a jikin sa dake haske stair ɗin da kyau sai walwali yake yana kwalli kamar gold, staircase ɗin nan ya haɗu iya haɗawa sosai, gashi tsab da shi kamar kafa bai taɓa taka kan shi ba,
a kasan iya palo da katafaren kitchen ne kawai a wajen sai wajen dining table wadda shima duniya guda ne wajen, kitchen ɗin kawai kusan 1 plot ne a wajen babu abun buƙata da babu a kitchen ɗin jibga jibgan sojoji ne ke musu girki da duk wani aiki na gidan gaba ɗaya gidan daga farkon ta har karshen ta babu alamar mace a cikin ta
gaba ɗaya palon kasan kewaye yake da tsadaddun curtains masu bala'i kyau da ɗaukan hankali farare tas ko ta ina hasken gaske ne a palon saboda kyawawan fitullin dake bada haske daga sama POP,
palon nan a gyare yake tsab kai kace ba a taɓa taɓa komai na palon nan ba saboda tsab ɗin da yake, sai wani fitinan ne kamshi ke tashi a palon kamar an yi ɓarim turare,
Wan nan gida dai sai dai muce Masha Allah dan ta ko ina yayi ne
Kai tsaye staircase ɗin Michel ya nufa sai kwaɓe fuska yaƙe, yana hawa wani kyakkyawan Bature ya sauko wadda kallo ɗaya zaka masa kasan daddyn su ne dan kammanin sa ɗaya da Michel sai dai shi kwayar idon sa blue ne, ko kallon in da yake Michel bai yi ba ya wuce, cikin sauri daddy yace "Welcome My tiger" da yake haka daddy ke kiran sa a cewar daddyn wai idon Michel ɗin na shining like Tiger eyes shi yasa yake ce masa tiger "Thank you dad" ya faɗa tare da wucewa ya karisa hawa saman, a mai makon ya shiga palon saman sai ya kauce hanya ya shari kwana ya nufi wajen wata kofa wadda daga bakin kofar kana iya leko palon kasa, kofar ya sanyawa fingerprint na shi na tsakiya, nan take kofar ta buɗe ya shige abun sa, shi kuma daddy ya wuce ya sauƙa palon kasa ya nufi wajen sofa sky blue ya zauna tare da kunna News a makeken Tv plasma su.
💞💞💞💞💞💞💞💞
*KANO*
Sai 04:00 pm su jelly suka dawo gida a motar Imran, sauri sauri Imran ya sauƙe su a gida tare da yin sallama da daddy dan lokacin jelly tayi barci a jikin daddy sauri sauri ya juya kan motar sa ya bar gidan dan tsoron kar dare ta masa a hanya ba shi da amsan da zai bawa Ammie sa idan ta tuhume sa a kan ina yaje,
wucewa cikin gida daddy yayi kai tsaye bedroom na shi ya wuce su Zuwaira na gaida shi amma bai kula su ba saboda bai son amsa magana jelly ta tashi daga barcin da take, saman gadon ta dake bedroom na shi ya kwantar da ita a hankali dan karta tashi, sai bayan ya kwatar da ita ya tuna sun manta basket na ta a motar Imran, wucewa yayi ya ajiye jakar computer sa ya nufi toilet dan yin wanka.
💞💞💞💞💞💞💞💞
*👹 DAULAR MUTUWA 👹*
Yan sanda mota biyu ne suka shiga wajen wan nan dajin dan sun samu labarin akoi gidan magicians a wajen, tun daga ɗan nesa suka kashe motocin su, suka sauka suna tafiya da kafa a hankali hankali kamar wasu ɓarayi sai sanɗa suke suna tafiya, suna addu'ar Allah yasa nan shine address ɗin da a ka basu kuma Allah ya basu Sa'a su samu su tarwatsa wan nan gidan dan an sanar da su waje ne mai haɗari ga kuma a saran rayuka da basu ji ba basu gani ba da ake a wajen, a na zaluntar bayin Allah a wajen,
Sunyi tafiya mai nisan gaske sunayi suna duba map har sun gaji wasu daga cikin su suka cire takalmin kafarsu suka ci-gaba da takawa da tafin kafar su,
Dai dai wasu bishiyoyin masu tsawo ga wajen da ɗan duhu saboda cikan ganyen bishiyoyin, suna shiga wajen sun ɗan fara tafiya kenan suka fara jin wata iriyar gigitatchiyar takun sahu dan duk in da a ka taka sai kasa ta bada dum dum, a guje suka nemi wajen ɓuya kowa yayi ta kansa suka laɓe suna ɗan leƙowa wasu sun laɓe wajen bayan bishiya wasu kuma sun shige cikin ciyayi, suna tsaye sunyi tsurutasu suna jiran su ga wanene zai bayyana,
ba karamin girgiza sukayi ba ganin barbushi basu taɓa ganin irin wan nan halitta mai girma da muni har haka ba nan take tsoro ya bayyana a face nasu wasu daga cikin su fitsarin tsoro suka saki a wandon su, wasu kuma sumewa sukayi a wajen dan halittar Barbushi sai mai karfin imani zai iya kallon sa kuma yasha lafiya, wani ɗan sandan ma har da kashi yayi a wando saboda tsoro, jikin su sai kerma yake ido ya rena fata sai zufa suke sun kasa riƙe bingun hannun su wasu daga cikin su sai kalmar shahada kawai suke furtawa a ran su, shima kalmar shahadar basu iya furtashi dai dai ba dan akoi masu ɗauko farkon kalmar shahada su karasa da wata sura ko nasi ko falaki saboda tsoro,
ɗaya daga cikin sune yayi ta maza ya saita Barbushi da bindiga, hannun sa sai rawa yake haka ya daure ya danna kunamar bindigar ya harbi Barbushi a sai tin hannun sa, abun da ya kara rikita ƙwaƙwalwa su shine da bullet ɗin yaje sai ya daki hannun Barbushi ya faɗi kasa kamar wadda ya daki karfe,
ihu ɗan sandan da yayi harbin ya saki saboda tsorata dan bai taɓa ganin in da aka harɓi mutun kuma bullet ɗin taje ta daki jikin sa kuma ta dawo kasa ta faɗi kamar ta daki karfe ba, jin ihun ɗan sandan yasa Barbushi juyo da idon sa masu kama da wuta dai dai sai tin in da yaji ihun, kasan cewar wajen da ɗan duhu baka gani sosai yasa nan taƙe idon Barbushi ta rikiɗe ta zama kamar torchlight mai hasken gaske kai tsaye sai kan ɗan sandan da ya harbe sa hasken idon nasa yaje, a guje ɗan sandan ya fita daga maɓoyar sa yana kokarin guduwa
Girgiza jiki barbushi yayi ya fasa ihu mai rikita ƙwaƙwalwa da wan nan katuwar muryan tasa san nan ya zuro harshen sa waje wata iriyar doguwa harshen nasa tayi kamar igiya, yana tsaye a wajen ya aika harshen nasa ta capko masa ɗan sandan nan, ya kawosa gaban sa ɗago katuwar mummunar hannayen sa yayi ya damki ɗan sandan nan ya murɗe masa wuya ya ji kake kakas kas wuyar ta karye nan take rai tayi halinta ɗan sandan ya mutu, buɗe mummunar bakin sa duk wari kamar shadda yayi ya jefa ɗan sandan a cikin ta ga hakoran san nan zabga zabga kamar block a ka jera masa gasu da tsini kaifi kamar wuƙa nan take ya fara tauna ɗan sandan da gabza ganzan hakoran sa, kan kace me jinin ɗan sandan ya fara gangarowa daga bakin Barbushi hancin sa har ta ido
ihu sauran yan sandan da suka rage suka fasa tare da fita a guje suka bazama, suna neman cetar ransu, girgiza jikin sa Barbushi yayi kafin ya durkusa a wajen nan take ya rikiɗe ya zama katuwar maciji mai katon kai kamar faranti, ihu yan sandan nan suke basu san in da suke takawa ba guduwa kawai suke masu kashi a wando suna yi masu fitsari suna yi, kwanciya Barbushi da ya rinkiɗe ya zama katuwar maciji yayi ya kutsa ta cikin grass dake wajen yabi bayan yan sandan, duk wanda ya kama haɗiye su yake kamar paracetamol, yan sanda Shabiyar ne suka shigo cikin dajin Barbushi ya cinye uku yanzu biyar sun sume a wajen da suka fara ganin barbushi bakwai kuma suna gudun cetar rai sai kalmar shahada suke shima kalmar shahadar ba dai dai suke faɗe ba saboda tsoro da suke ciki
Sai da Barbushi ya cinye yan sanda biyar daga cikin su san nan yaji ya ɗan koshi sai ya fara kamasu yana murɗe musu wuya idan sun mutu sai ya goya su a bayan sa,
har ya gama kashe su dukka ba tare da ya lura da biyar ɗin da suka sume a wajen bishiyoyin ba ya ɗauki gawar wayan da ya kashe san nan ya rikiɗe ya koma asalin mummmunar halittar sa ya wuce ya koma in da ya fito
Su kuma biyar ɗin suna sume a in da suke.
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WASHINGTON DC*
*Harvard University*
Kamar kullun zaune suke saman kyawawan fararen kujerun dake gore place, Michael yana latsa wayar sa Johnson na riƙe da drinks shi da test, dest kuma na shafa gashin jikin lucky, basu da aiki kullun in sunzo school sai su zauna suyi ta shaye shaye suna addabar ƴaƴan mutane,
School ɗin ma dan dole suke zuwa Michel bai isa yace ba zai zo school ba saboda Romeo zai ɓallasa duk wan nan iya shegen da suke Romeo bai sani ba kuma ba wan da ya isa a School ɗin ya tunkari Romeo yace zai sanar da shi dan bala'i tsoron sa suke ji, shi yasa Michel keyin abun da ya ga dama kuma dole a masa biyayya ko ana so ko ba'a so
Wani lecturer ne yazo wucewa ta in da suke zaune bai lura da su a wajen ba yazo zai wuce cike da iya shege John yace "Dr Simon kwana biyu baka watsa jini ba kenan da har zakazo ka wuce baka gaida mu ba" kafin Dr Simon yayi magana John yace "Copper punish him" ihu Dr ya fasa yana faɗin "I'm sorry I'm sorry Johnson please karku haɗani da wayan nan tashin hankali" ya kai karshen maganar tare da duƙawa kasa yana kuka, hannu kawai Michel ya ɗaga masa ala'mar ya tafi ya basu waje, a guje Dr Simon ya miƙe ya bar wajen shi kuma Copper yana zaune ko motsawa bai yi ba dan daman idan ba Michel bane ya basu umarnin basa taɓa yin abu umainin Michel kawai suke bi
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai
💞Star Lady💞
Share fisabilillah 👏
*💞TRIPLET'💞10
Masu son magana dani su min magana ta wan nan number 09075846926 wan can layin ya samu matsala
*💞The beginning💞*
*Episode 10*
Masu tambaya ta menene ma'anar sunan Rimsha da Jehan to gashi nan *Rimsha means Beautiful or face like moon* *Jehan means the world* san nan duk wan da na kira sunan sa a book nan zanyi kokari na rubuta muku ma'anar sunan Nagode Princess Teema Musa...✍️✍️
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞ABUJA💞
*RIMSHA*
Kwance Rimsha take a ɗakin su saman katafaren gadon ta taja lallausar blanket ɗinta ta rufe daga ƙafa zuwa cikin ta tana sanye da rigar shan iska zuwa gwiwa fari kal da shi mai laushi, tana rungume da ƙatuwar teddy ɗin ta, ɗaki ne na Alfarma komai na ɗakin bibbiyu ne kama daga kan katafaren gadon su wardrobe dressing mirror komai bibbiyu ne na Rimsha pink color na Jehan ash color toilet ne kawai guda ɗaya, dressing mirror su cike yake da lotions kala kala masu kyau da tsada ga perfume masu bala'i kamshi komai a jere tsab sai kamshin ɗakin ke zubawa, daga saman dressing mirror glass ne wadda kana iya hango sarkakunan gold da abubuwan hannun su dake cikin drawer mirror, daga cikin drawer mirror kuma a kwai fitilla mai bada haske yana haske sarkoki da abun hannun nasu, sai ya karawa wajen kyau da ɗaukan hankali,
kwance take tana Chatting da friends nata a Telgram Group nasu na makarantar su, suna magana akan *Prize-giving* day daza suyi a makarantar su Ranar Saturday mai zuwa Auntyn su ta basu zaɓi akan kayan da zasu saka Black and white ko Black and blue kowa na faɗar ra'ayin sa basu yarda akan abu ɗaya ba daga ƙarshe tace za su yi voting waɗanda suka fi yawa shi zasu ɗauka haka akayi ƴan Team na *First lady*(Rimsha) da ƴan Team *Miss Assistant*( Maryam).
Abun da yasa suke kiran Rimsha da first lady saboda kaman da take da mum, idan dad yaci zaɓe mum ce zata zama first lady shiyasa suke kiran Rimsha da first lady dan kamannin mum
....Tun kafin Rimsha ta zaba duk suka ce zaɓin First lady shi ne nasu, Black and White ta zaɓa sabida sune favorite color ɗin ta. Bayan Auntyn su taji zaɓin ta shi ne ta ce kowa yayi dressing in Black and white. Daga ƙarshe ta masu nasiha akan karsu bar karatu su dinga duba littattafai lokacin hutu sannan tace masu akwai online lesson