Showing 18001 words to 21000 words out of 194715 words

Chapter 7 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

954

Aafia da Umaisha suka wuce wajen motocin su kowa ta shiga nata Aafia na kokarin kunna motar ta Rufee ta kariso wajen da yar gudun ta tana kiran sunan Aafia sauke glass ɗin motar Aafia tayi tana faɗin "Lafiya Rufee kika yi wan nan gudun haka?" Girgiza kai Rufee tayi kafin tace "A'a ba lafiya ba daman ina son in ɗan tambaye ki kuɗi ne ɗazun sai na manta sai yanzu na tuna" jinjina kai Aafia tayi kafin ta ciro kuɗi daga jakar ta ta kirga 10k ta miƙa wa Rufee tana faɗin "Ban da sayan kayan haɗin shisha" Ansa Rufee tayi tana faɗin "In Sha Allah abu mai mahimmanci zan saya" tada mota Aafia tayi ba tare da ta sake yiwa Rufee magana ba ta figi motar ta bar wajen da gudu already ita Umaisha ta jima da tafiya Aafia na barin wajen Rufee tayi tsaki kana tace "Yar wahala uwar muce ke da zaki rinƙa hana mu shan shisha kema In Sha Allah sai na koya miki ba shan shisha kawai ba har da sha kwayoyi da bin maza sai kin koya sai na lalata miki rayuwa san nan na auri uban ki na mori dukiya duk na koreku daga gidan kin ɗauka a banza nake saki kike wa matar baban ki abun da kike matan nan ne yarinya dan kawai ki fitar min da ita ne ni kuma na shiga dan banson zama da kishiya wawayen yara kawai" ta kai karshen maganar nata tare da juyawa tana kaɗa 10k da Aafia ta bata tana murmushi ta bar wajen ta koma cikin department na su.

KATSINA.

Tafiya take hannun ta riƙe da leda baka mai ɗauke da kayan miya irin su tomator tattasai attarugu sanye take cikin doguwar riga abaya baka ta yafa gyalen rigar a kanta tana tafiya tana kwaɓe fuska kamar wadda taga kashi tun daga nesa Sadiq dake tinkarar majalisan su shi da wani mutun ya hangota murmushi ya saki yana faɗin "Nasir kaga waccan yarinya dake zuwa? Wallahi haka kawai yarinyar nan ta shiga rai na kome nake tunanin ta nake" kallon Jehan dake tin karo su Nasir yayi kafin yace "Lallai yarinyar nan tayi Sa'a kai da baka kallon mata baka taɓa kula ya mace ba har faɗa muke maka shi ne yau....bai kai karshen maganar ba ya dakata tare da kara waro idon sa waje yana kallon Jehan da ta kusa isowa in da suke dai dai lokacin su kuma suka isa majalisar tasu "Nasir lafiya kake kallon ta haka lafiya ka tsaya da magana?" Cewar Sadiq da kyar Nasir ya iya zama saman bencin majalisar tasu still idon sa na kan Jehan muryan sa har sarkewa yake yace "wan nan ba yar Alhaji Nawazudden Salman Sultan bane?" Da sauri Sadiq yace "Wanene kuma Alhaji Nawazudden?" Dai dai lokacin Jehan tazo zata wuce su cikin sauri Nasir yace "Jehan Nawazudden Salman" cak jehan ta tsaya kamar zata juyo sai kuma ta tuna abun da uncle Shitu yace musu akan su ɓoye kan su tuna hakan yasa cikin sauri ta wuce ba tare da ta juyo ba, cikin ƙaguwa Sadiq yace "Nasir meke faruwa ai na kasan Jehan?" Girgiza kai Nasir yayi yana faɗin "Sadiq shi ne matsalar ku, ku yan nan unguwar ba masu manyan wayoyi sosai awajen ku shi yasa baku ganin News da sauran su amma ina da tabbacin kasan Alhaji Nawazudden ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Apc ko?" Cikin sauri Sadiq yace "Eh ina jin labarin sa ance mutun ne mai adalci da kaunar talakawa salihin bawa bai da hayani ga taimakon na kasa da shi bai da girman kai" "Good to bari kaji Sadiq wan nan yarinyar da kake gani sunan ta Jehan Nawazudden ina followed nata a tik tok dasu Instagram Twitter dukka ina followed account nata i think itace kaɗai yar sa akoi ta da jiji da kai ga izza bata kula mutane bata ɗauki halin baban ta ba gata yar karama da ita sai izzan bala'i da rashin kunya" shiru Sadiq yayi yana tunanin to me ya kawo su Jehan nan kenan dafa shi Nasir yayi yana faɗin "Kasan cewa tun last week zancen baban ta ne ke trending a media wasu sunce ya ɓata wasu kuma sunce ya janye takarar sa ya barwa abokan hamayya to duk ma ba wan nan ba ajiye zancen Jehan a gefe ya maganar mu? ya kamata fa kai ma ka shiga irin sana'ar nan tamu akoi samun kuɗi over" dogon numfashi sadiq yaja tare da saukewa a hankali kafin yace "Wai wani irin sana'a ce wan nan da ka dameni tun satin da ya wuce?" Ɗan wawwaigawa Nasir yayi dan yaga ko akoi mutane,
Ganin babu kowa ne yasa ya matso kusa da Sadiq sosai kasa kasa yace "Mutane muke kamawa mu kai su daji mu ɓoye su mu kira yan uwan su akan su kawo kuɗi mu basu yan uwan su idan ba haka ba zamu kashe su muna faɗa musu zamu kashe yan uwan su zakaga sun tsorata sun haɗo kuɗi da wuri sun kawo mana sai mu basu yan uwan su" kallon Nasir da kyau Sadiq yayi kafin yace "Wan nan ai sata ce Nasir ba sana'a bace kuma bai kamata kuna yiwa ƴaƴan talakawa haka ba" kara kasa da murya Nasir yayi yace "Haba Sadiq ya kake abu kamar wawa ne wannan ba sata bace amsan hakkin mu muke wajen masu kuɗi dan ba mu kama ƴaƴan talakawa ai sai ƴaƴan masu kuɗi dan mu ansa hakkin mu tun da basu bamu saboda Allah kaga ai hakan ba laifi bane kayi tunani ka gani yadda rayuwan yanzun nan ya zama ba mai taimakon yan uwan sa ko yana da hali kowa kansa kawai ya sani ko dan saboda maman ka da kanin ka suji daɗi su huta ya kamata ka fara wan nan sana'ar kuma kaga idan ka samu kuɗin nan zaka iya saya wa mamanka har gida da duk wani abun da zata ji daɗi ta buƙata" Jin Nasir ya ambato maman sa zata ji daɗi ne yasa ya tuna irin cin kashin da baban sa da amaryan sa ke mata saboda kuɗi hakan yasa yaji yana bukatar samun kuɗi shiru ya ɗan yi kafin yace "Ba komai Nasir na gode Allah ya bar zumunci In Sha Allah zanje na shirya sai musan ya zamuyi nan da gobe dai zan gama shiri" da murna Nasir yace "To abokina haka ake son namiji da zuciyar nema sai nazo gobe zan zo maka ma da babban waya ta yadda ma zaka san ba karamin kuɗi nake samu a harkan ba amma fa karka yi maganar nan da kowa kar ka faɗa wa kowa" ya kai karshen maganar tare da miƙewa yace "To sai mun haɗu gobe" hannu Sadiq ya ba shi sukayi musabaha san nan Nasir ya bar wajen ya miƙi hanyar fita daga unguwar, shiru Sadiq yayi yana tunani a kan Jehan shi ma Nasir yana tafiya yana tunanin ta yadda zai yi bincike a kan Jehan me ya kawo ta nan ta ɗayan ɓangaren na zuciyar sa kuma murna yake da ganin Jehan a nan sai ayyana wa yake a ransa kuɗi fansa da zai ansa idan ya sace Jehan ɗin a matsayin ta na yar ɗan siyasa, da wan nan tunani ya bar unguwar su Sadiq ya tare ɗan a caɓa ya hau ya bar layin gaba ɗaya

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu

Mai bukatan karanta book ɗin*TRIPLETS* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please

Share fisabilillah 👏

💋 Star Lady💋

💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞

*💋 TRIPLET'S💋*

https://chat.whatsapp.com/DOMGC0F7nAm6qQt6zWFwcf


STAR 🌟 LADY..✍️


*💋The beginning💋*


Episode 5


Nasir na tafiya ba jimawa Sadiq ya miƙe ya bar wajen ya nufi gidan su Jehan.

A ɓangaren jehan kuwa gudu gudu sauri sauri ta shiga gida babu ko sallama tun daga kofar gida take kwalawa mum kira da sauri mum ta fito daga cikin kitchen tana tabayar ta lafiya take kwala mata kira haka da sauri gwaggo dake zaune saman tabarma a tsakar gidan ta miƙe tana faɗin "Jehan are you okey?" A ruɗe Jehan tace "Mum yanzun nan kafin na shigo na haɗu da wancan dirty boy ɗin shi da wani dirty boy ɗan uwan sa kuma wancan ya gane ni har ya kira sunana da na daddy" waro ido waje mum tayi tana kokarin yin magana gwaggo ta riga ta da cewa "What? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun what are we going to do now?" shiru mum ta ɗan yi kafin tace "Jehan as from today kar ki sake fita ko ina just stay at home" gwaggo ne tayi saurin taran numfashin mum da cewa "Hakan yayi daman duk cikin ku nice face na bai zama popular ba so zan rinƙa zuwa cefene da sauran su" girgiza kai mum tayi tana faɗin "A'a Aunty A'isha hakan kuma ba zai yiwu ba gaskiya dole dai mu samo mafita batun kije ki rinƙa yo mana cefene da kan ki kam bayyi ba" "Mum why not na rinƙa using face mark to?" "Gaskiya Aunty A'isha munyi ganganci tun farko da muka manta da waye mu, muka saki face namu ga kowa muka bar Jehan tana zuwa in da ta ga dama lokacin da take so" jinjina kai gwaggo tayi cike da tashin hankali da damuwa tace "Maryam ina ganin Jehan ta rinƙa using face mark ko kuma mu sai mata face na roba da zata ɓatar da kamanin ta ko ya kika gani?" Jinjina kai mum tayi tana faɗin "Duk yadda kika yanke yayi" dawo da kallon ta gwaggo tayi kan Jehan tace "Go and wear face mask and go to market buy fake face" cikin sauri Jehan ta wuce cikin ɗaki, ta buɗe trolley ta ta ɗauko face mark ta sanya ta fito ta wuce ta fice daga gidan ta nufi kasuwa, tana fita sukayi karo da Sadiq zai shiga gidan nasu ko kallon in da yake ba tayi ba ta wuce yana ce mata sannu ko kallon sa ba tayi ba ta wuce murmushi yayi shi ko kallon ta ma yayi daɗi yake ji tsayuwa yayi ya suba mata ido tana tafiya har sai da ta kurewa ganin sa san nan ya wuce ya shaga gidan bakin sa ɗauke da sallama zaune ya isko gwaggo a saman tabarma a tsakar gida ita kuma mum ta koma cikin kitchen dan ci gaba da aikin ta saman kujerar da Jehan ke zama ya zauna yana faɗin "Ina wuni gwaggo?" Da fara'a gwaggo ta amsa da "Lafiya ya kake ya gida ya maman ka" "Lafiya Lou Alhamdulila ina mum?" "Tana kitchen" gwaggo ta bashi amsa "To bari na jirata magana nazo muyi da ita ne" jinjina kai gwaggo tayi ba tare da ta sake magana ba mum na kitchen bata san da zuwan Sadiq ba yana zaune shiru ita ma gwaggo na zaune shiru har Jehan ta dawo hannun ta riƙe da leda kasan cewar kasuwar nasu bai da nisa da gida kuma ta hau abin haka ne wato mashin shi yasa tayi sauri dawowa ba ko sallama ta shigo gidan ganin Sadiq zaune saman kujera da take zama ne yasa taja guntun tsaki ta wuce kusa da gwaggo ta zauna tare da kwanto da kan ta saman cinyar gwaggo tana faɗin "My gwaggo I'm tired" shafa curly hair ta gwaggo tayi tana kokarin yin magana mum ta fito daga cikin kitchen tana faɗin "Har kin dawo Jehan?" Gyaɗawa mum kai tayi ba tare da tayi magana ba "A'a babana yaushe kazo" kasa yayi da kai yana murmushi "Yanzu nazo mum ina wuni" da fara'a mum ta amsa masa tare da karisowa wajen ta zauna gefen gwaggo saman tabarma "Mum daman ina son yin magana da ke ne idan ba damuwa" ba tare da ta kalli in da yake ba hankalin ta na kan Jehan tace "To babana in taso muje gefe ne?" Girgiza mata kai yayi yana faɗin "A'a a nan ɗin ma yayi" "To ina jin ka" nan Sadiq ya kwashe yadda sukayi da Nasir akan kidnaping da yake son Sadiq yayi join na shi ya sanar wa mum san nan ya ɗaura da cewa "Naga ku kunyi karatu kuna da ilimi boko da na islamiya shi yasa nake son ki bani shawara shin yin hakan abune mara kyau ko kuma dai kamar yadda Nasir ya faɗa ba laifi hakkin mu zamu ansa" cike da tashin hankali mum tace "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunallahu wani'imal wakil haka fa mutanen nan suke amfani da wayan da basu yi karatu ba kuma talakawa masu neman na abinci su cucesu su lalata musu duniyar su da lahiran su kayi kyan kai babana da kazo ka tambaya da wani ne yaji kuɗi haka zai faɗa halaka wa iya zubilla ni yanzu gashi ban isa da zuwa police station ba kuma bamu da hujjan report na shi da mun sa an kama shi wan nan babban laifi ne babana, wadda idan aka kama mutun yana aika tashi kashe shi ake har lahira shawaran da zan baka a rayuwar ka kawatsar da duk wani aboki kayi rayuwan ka daga kai sai ɗan uwan ka san nan da kai da ɗan uwan naka duk ku rinƙa zuwa idan kun samu time Aunty A'isha ta rinƙa koya muku karatun Arabic har ma da boko dan ku fita cikin duhun jahilcin nan jahilci babban ciwo ne babana, babban bala'i ne jahilci yanzu ba yace maka zai dawo gobe ba idan yazo kace ya kara maka lokaci karka nuna masa kayi maganar ma da wani kuma karka nuna masa bazaka ansa tayin nasa ba idan kayi kuskuren nuna masa hakan tofa zai iya maka wani illar koma ya kashe ka dan gudun karka tona masa asiri a kama sa kabi da taka tsantsan kana ja masa rai duk lokacin da ya kawo maka maganar kace yayi hakuri kai ma kana son sana'ar amma ya ɗan kara maka lokaci a haka har ka rabu da shi san nan idan yazo anguwar nan ka rinƙa ɓuya karka na bari kuna haɗuwa kowani lokaci karkuma karinƙa gudun sa sosai har yazo ya gane In Sha Allah hukuma zata kama shi" da sauri Sadiq yace "Hukumar da bata da adalci bata wani yi mana Aiki basa son gaskiya bayan masu kuɗi kawai suke bi" girgiza kai mum tayi kafin tace "A'a babana falyakul Kairan auli yasmut karka haɗa hukuma dukka ka musu kuɗin goro ba dukka suka taru suka zama ɗaya ba akoi na kirki kamar yadda a ko ina akoi na kirki da na banza suma hukuma haka suke idan kayi Sa'a ka haɗu da na kirki zaka ji daɗi, kuma zancen gaskiya hukuna na iya bakin kokarin su wajen ganin su gudanar da aikin su yadda ya dace wani lokaci abun ne yake fin karfin su amma suna kokari bance akoi wayan da basa aikin su yadda ya dace ba sai dai kasani su mutane ne ba Mala'iku ko aljani ba dole suna da a jizanci irin na ɗan adam wan nan shi ne kawai" ta kai karshen maganar tare da yin shiru tana kallon Jehan shiru wajen yayi ita dai gwaggo ta kasa magana saboda ganin abun take kamar a mafarki ita kuma Jehan bata ma san me suke cewa ba ta lumshe dara daran idon ta har barci ya fara ɗaukan ta can kome ta tuna tayi saurin waro dara daran idanun nata waje tana faɗin "Gwaggo this dirty boy he know everything about me because that stupid guy that talked about me is his friend they are together the time that the guy talked about me and dad" kallon Sadiq gwaggo tayi tace "Sadiq kasan wace ce Jehan yanzu ko?" Kasa yayi da kan sa kafin yace "Eh gwaggo" "Okey to kabar maganar iya tsakanin mu" jinjina kai yayi san nan ya miƙe yana faɗin "Mum Nagode sosai kuma zan yi yadda kika ce In Sha Allah" murmushi mum tayi san nan tace "To shike nan Allah yasa mufi karfin zuciyar mu" Amin ya amsa da shi san nan ya fice daga gidan miƙewa mum tayi ta nufi kitchen "Maryam ina son muyi magana a kan issue da Sadiq ya kawo yanzu" cewar gwaggo "To Aunty A'isha mu bari sai dare yanzu bari na ƙarisa girkin nan tukun nan" shiru gwaggo tayi bata sake magana ba ita kuwa Jehan barci ya ɗauke ta kan cin yar gwaggo.

💞💞💞💞💞💞💞💞
KADUNA

Lokacin da Aafia ta dawo gida babu ko sallama ta shigo palon Auntyn su na zaune saman sofa mai zaman mutun 3 tana kallo a makeken Tv plasma dake sama TV stand sanye take cikin doguwar riga na dakakkiyar shadda blue color yasha aikin daga sama har kasa ta yi ɗaurin ture kaga tsiya tayi kyau sosai reras da ita tana zaune tana jiran Abbi ga kayan fruits a gaban ta time to time tana ɗauka taci, kallon sama da kasa Aafia ta mata cikin mutunci Aunty tace "Sannun ki da dawowa Aafia" dogon tsaki Aafia taja ta nufi bene tana faɗin "Babu a house ba dole a ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya a na ɗurawa ba dan ba tsoho ke nemowa ba" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi ɗakin su babu ko sallama ta banko kofar ɗakin tashige tana jan tsaki Umaisha na kwance saman gado har tayi wanka ta sauya kaya zuwa wando mai ɗan faɗi kamar palazo da yar riga mai karamin hannu kanta babu ɗankwali tana riƙe da wayar ta tana chatting, ta tada kai da pillow "Ke Umaisha yau kin yi magana da Yaya Irfan ne?" Aafia ta tambaya miƙewa zaune a tsakiyar gadon Umaisha tayi tana faɗin "A'a bamu yi magana da shi ba me ya faru?" Wurgi da jakar hannun ta Aafia tayi a saman gado tare da ɗaura key din motar ta da wayar ta saman bedside drawer ta nufi toilet tana faɗin "Babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login