Showing 117001 words to 120000 words out of 194715 words

Chapter 40 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

988

har sai da kansa ta bugu da jikin glass ɗin motar, wani irin jiri ya gani lokacin guda, da sauri ya fito daga cikin motar, duk da kan sa sai faman sara masa yake haka ya karisa wajen mutumin da ya buge ɗin, kwance yake saman titi, sai dai da alama bai wani bugu sosai ba, bai ji ciwo sosai ba amma da alama ya samu karaya a kafa, da sauri James ya duƙa duk girman mutumin haka ya ɗauke shi cak, ya sanya shi cikin mota, kasan cewar unguwar na masu kuɗi ne hakan yasa ba hayani ya ba mutane kowa na cikin gida, tunani ya fara yi ina ya kamata ya kai mutumin nan.

Daga karshe dai ya yanke shawara ya wuce da shi gida duk da ya san zai fiskanci matsala daga Michael da Romeo amma bashi da zaɓi dole ya kai shi gida, haka ya ja motar sa da gudu ya juya motar ya koma gida.

Yana yin parking a parking space na gida ya fito ya ɗauki mutumin ya nufi hanyar shiga cikin gida, a guje jinga jingan sojojin dake tsakar gidan suna gadi, suka nufo shi, har suna rige rigen ansan wannan mutumin daga hannun sa dan su taimaka ma shi, ba musu ya miƙa musu dan dama bai son su Romeo su gan shi ya ɗauko mutumin zasuyi mamaki kasam cewar sun san shi da lalaci.

Haka suka shiga palon, a sukwame TGA ya miƙe tsaye yana mamaki, wucewa sojan da ya ɗauko mutumin yayi, yaje ya kwantar da mutumin saman sofa 3 seater sannan ya fice daga palon.

"James who is this man? What happened to him?" Tga ne ya jerowa James wannan tambayar, a takaice James ya faɗa masa abun da ya faru na buge mutumin da yayi, nan take Tga ya ɗaure fuska sosai, a fusace yace "carry him out from this house!!!" zaro ido James yayi yana kallon ikon god, yana jinjinawa karfin hali irin na Tga, sai kace gidan sa to ko Romeo mai gidan ma ai ba zai ce a fita da mutumin nan lokaci guda ba tun da ni na bugesa da mota, sai ya bari mun masa jinya.

James yayi nisa cikin tunanin da zancen zuci da yake, sai ji yayi Tga ya daga masa tsawa "James I'm I not talking to you?" Yar firgigit James yayi kafin yace "I can't uncle" zaro ash eyes ɗin sa Tga yayi kafin ya wuce ya nufi waje, James na tsaye yana mamaki hali irin na yan uwansa su kwata kwata basa son baki a rayuwar su, inma mace ko namiji duk su basa so, basa son kowa ya raɓe su, sun fi son suyi rayuwar su su kaɗai, gaba ɗaya gidan haka suke ba mai son wani yazo cikin su, basa son mutane musamman Romeo yafi kowa tsanar wasu suzo kusa da su, daga shi sai Michael da Tga sun tsani baki.

Sai tunanin ta yadda zai kare da Romeo a kan mutumin nan yake, gashi mutumin yana sume baya cikin hayyacin sa, zuba masa idon James yayi yana kallon sa.

A fusace Tga ya dawo cikin palon tare da sojoji biyu jibga jibga masu jini a jika, kai tsaye mutumin Tga ya nuna musu yana faɗin "carry this man out from this house" kallon sojojin James yayi suna kokarin ɗaukan mutumin cikin tsawa James yace "Are you mad, get out from here!!!" Cikin fushi Tga yace da sojojin "i said take this dirty man out" kafe su da ido James yayi kafin yace "Okey carry him let me see" shiru sojojin suka tsaya sun rasa maganar wa za su bi, dan duk wanda suka karyawa doka to zasu rasa aikin su, Tga ogan sune a wajen aiki, while shi kuma James sanyin idanniyar ogan kowa a gidan ne wato Romeo, sun gwammaci suki bin umarnin ogan su wato tga a kan su ɓatawa James rai dan gwara musu hukuncin Tga a kan na Romeo, dan haka sai suka juya suka fice daga palon dan sun san halin Romeo a kan yan uwansa sam baya adalci kuma zai iya yin komai a kan Triplets ɗin sa.

Ganin sojojin sun juya sun fice ne yasa Tga ya nufo mutumin da kan sa da nufi ya ɗauke sa ya fitar da shi, yana kai hannun sa zai ɗauki mutumin, a fusace James ya damki hannun nasa tare da turesa gefe guda, rai a matukar ɓace Tga yayi kan James da nufin dukan sa, nan fa James yace bai isa ba, kamar wasu zakuna haka suka fara faɗa.

Da karfi Tga ya kaiwa James duka a gefen ciki wadda hakan ya masa mugun zafi sosai, lokacin guda James ya sauya idon sa sukayi jawur nan fa ya riƙiɗe ya zama tamkar mayinwa cin zaki wadda yayi shekara biyu babu abinci ya fito farauta, nan yafara farauta Tga, a fusace ya sanya dukkan karfin sa ya ɗaga Tga yayi wurgi da shi gefe saman glass table na tsakiyar sofa milk color, nan take table ɗin ta tarwatse, gadan gadan James ya haye kan Tga ya fara kai masa bugu ta ko ina yana gurnanin ɓacin rai, ran maza ya ɓaci gaba ɗaya jijiyoyin kan sa dana wuyar sa sun miƙe sai dukan Tga yake sosai, da dai yaga duka da hannun ma bata masa ba sai ya ɗamko wuyar rigar Tga ɗin ya miƙar da shi tsaye, yana kokarin kai masa naushi a ciki, Tga ya riƙe hannun sa tare da kwashe kafafun James ɗin ya zube kasa, nan fa Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka shima

Kasan cewar James ya samu horon faɗa sosai wajen ogannin sa, hakan yasa ya san dabarun faɗa sosai, cikin dabara ya juyar da Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka.

kamar wasu mayinwatan zakuna haka suka rinƙa farautar junan su, sai dai Tga yaci karfin James, dan shi horon soja ya samu daga wajen Romeo, hakan yasa yayiwa James duka duk ya farfashe masa jiki da fuska, da kyar James ke mumfashi, amma Tga idon sa ya rufe duka kawai yake kai masa ta ko ina.

Zuciya ta jasa yana neman kashe James ba tare da ya sani ba.

Kamar daga sama yaji an riƙe hannun sa ta baya, yana kokarin juyowa, a fusace Romeo ya murɗe masa hannun da karfi ta baya tare da ɗaga sa sama daga kan James ɗin yayi wurgi da shi gefe, idon Tga ya rufe baya ji baya gani, bai san waye yayi wurgi da shi ba, a fusace ya taso ya nufi Romeo dan idon sa James yake gane masa, Romeo na tsaye, fuskar nan a ɗaure tamau kamar bai san menene dariya ba, dara daran blue eyes na san nan sun sauya zuwa ja saboda dukan James da Tga yayi, har wani tsuma jikin sa keyi, yau da Tga ba kanin daddy bane da ba abun da zai hana ya kashe shi, amma duk da haka dole ya basa hukunci mai tsanani, shi kuwa Tga idon sa ya rufe gadan gadan ya iso wajen Rome yana kokarin kaiwa Romeo duka a ciki, cak Romeo ya riƙe hannun sa tare da kai masa wawan bugu a ciki wadda ta sanya sai da ya fasa ihu mai sauti, bai kai ga gama ihun ba, Romeo ya sake ɗaga sa sama yayi wurgi da shi saman sofa, wadda sai da ya sanya ya fara dawo cikin hayyacin sa, karisawa wajen sa Romeo yayi rai a matuƙar ɓace ya ɗamko wuyar sa ya miƙar da shi tsaye, ya tsake masa wuyar tasa, nan fa Tga yaji kamshin mutuwa, cikin fitar hayyaci yasa hannu yana kokarin cire hannun Romeo daga wuyar sa amma ina ya kasa koda motsa hannun Romeo ɗin, sai faman zaro ido waje yake, Yana kokarin tantance wa idon sa ke gane masa, shin abun da ya gani da gaske ne, shin Romeo ne ko gizo ne, bai kai ga iya tantance wa ba

Romeo yasa kyakkyawar kafar sa ya taka shi da karfi a kirjin sa wadda sai da ya saki ihu mai ranaza kwakwalwa, tamko wuyar sa Romeo ya sake yi ya kai masa duka a ciki wadda sai da tasa shi dawowa cikin hayyacin sa da kyau, dan yasan ba mai karfin yi masa irin wannan damka da dukan duk gidan sai Romeo.

Kwashe kafafun sa Romeo yayi nan take Tga ya zube kasa kan gwiwowin sa, rai a ɓace Romeo ya sanya kyakkyawar farin hannu sa ya ɗamko gashin kansa Tga ɗin ya ɗago kan nasa sama suna fiskantar juna, zuba masa dara daran blue eyes nasa nan Romeo yayi yana kallon face nashi kamar mai tunanin wani abu.

Sai galabaitaciyar kukan wahala Tga yake, murya na sarkewa da kyar ya iya faɗin "I'm sorry lion" shiru Romeo yayi kamar bai ji saba, yayin da shi kuma James ke kwance kasa yana numfashin da kyar da kyar, ga fuskar sa nan duk Tga ya fashe masa sai jini yake, abun ku da fatar turawa ba quality sosai ba kamar bakar fata ba, fatar su bata jure wuya ko kaɗan.

Jin hayaniya yasa su daddy saukowa kasa, ganin abun dake faruwa yasa suka kariso cikin palon da yar gudun su, cike da tashin hankali a fuskokin su, kuka Michael yasa ya duka kasa yana bawa Romeo hakuri, dan yasan halin Romeo sarai duk yadda yake son sunnan idan suka ɓata masa rai ya zuciya to dukan mutuwa yake musu, gashi kuma da alama yaji haushin abun da Tga ɗin yayiwa James sosai, dan da alama ya ɗan ɓata rai ka ɗan, shiyasa ma ya murɗe wa Tga ɗin hannu kuma ya dake sa har sai da ya zube kan gwiwowin sa, kwata kwata Michael baya son yaga suna samun matsala da juna.

Su kuwa su daddy sai godiya suke dan yau Romeo bai ɗauki zafi sosai ba, da ya ɗau zafi yadda Tga ya bugi James ai da yanzu wani zance ake.

Ganin yadda Romeo ya ɗagawa Tga wuya sama sosai ne, gashi kuma Tga na shan wahala wajen jan numfashi, hakan yasa murya na rawa daddy ya kariso wajen ya ɗan tsaya daga ɗan baya, cike da kaunar ƴaƴan nasa yace "Please my lion leave him" shiru Romeo ya musu yana ta kallon face ɗin Tga kamar mai karantar wani abu

daddy zai sake magana, Romeo ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu alamar bai son jin wata magana kuma, shiru daddy yayi ya koma gefe ya tsaya
jin kukan Michael ya fara yin yawa ne kuma gashi Michael yana da matsala yasa Romeo ya juyo da dara daran blue eyes nasa kan fiskar Michael ɗin, a hankali ya saki gashin kan Tga ɗin tare da nunawa Michael hanyar bedroom nasa da hannu ba tare da yayi magana ba, dan bai son Michael ya shiga damuwa, kuma yasan halin sa sarai yanzu zai sa kan sa cikin damuwa,

matsowa Michael yayi da rarrafe ya kariso gaban Romeo yana faɗin "Please lion for giv....bai kai karshen maganar ba, Romeo ya daka masa wata gigitatchiyar tsawa wadda ya razana duk wata halitta mai rai dake cikin palon "I said get in!!!" Saboda tsorata Michael bai san lokacin da ya tashi da gudu ya haye sama ba ya razana sosai, yasan halin Romeo idan ya ɗau zafi ba wanda ya isa ya tinkaresa shi yasa su daddy duk suka tsaya a baya, shima Michael ɗin dan yafi su sanin halin Romeo ne, ya san bai ɗauki zafi sosai ba shi yasa ya tinkaresa.

Goya hannu a saman kirjin Romeo yayi gently ya fara magana "what is happened?" Yayi maganar yana tsare Tga da dara daran blue eyes nasa nan, da kyar Tga ya iya buɗe baki saboda wahalar yadda Romeo ya muɗe masa wuya ya sanya shi kallon sama, ba dan Romeo ne ya masa tambayar nan ba da ba zai iya magana ba, amma tun da Romeo ne ba yadda zai yi dole ya amsa Maganar ko ma tayaya ne, a hankali yace "please help me with water, i need water!!" kallon Romeo daddy da Uncle Herry sukayi suna jiran Romeo ya bada izinin su kawo wa Tga ɗin ruwan, amma sai sukaga Romeo yayi shiru alamar ba za'a kawo ruwan ba kenan, dan shi Romeo shirun sa ma magana ne, wani lokaci da shiru yake magana da Mutane, gaba ɗaya jama'ar gidan sun san ma'anonin shirun Romeo, idan anana magana da shi yayi shiru to akoi abun da yake nufi baya shiru haka kawai, sannan baya magana sai da kwakkwaran dalili, shima kafin yayi maganar sai ya ɗauki lokaci kuma ba wai dan bai ji me kace ba, yana ji, wani lokaci ka masa magana kana sauri sai yafi 5mins bai baka amsa ba, wata zubin ma har sai ka cire rai da zai yi magana sai kuma gaji ya baka amsa a nitse da sassayan murya, idan kuma bai game sa ba da wannan shirun zai baka amsa in ka gane to ruwan ka, idan ma baka gane ba nan ma kai ta shafa shi dai ya gama nasa.

Komawa yayi saman sofa ya zauna yayi shiru yana kallon Tga yana jiran amsar tambayar sa, dan shi baya mai mai ta magana idan yayi, idan baka ji bama dole dai ka bashi amsa, already Tga ya san da wannan dan haka sai ya rarrafa ya koma kusa da kafafun Romeo cikin nitsuwa da shakakiyar murya yace "I'm sorry lion it's was a mistake" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me Tga ɗin yace ba, ganin haka yasa Tga ya gane, bayani abun da ya haɗasu faɗa da James kawai Romeo yake buƙatar ji, cike da tsoron, murya na rawa ya fara bawa Romeo labarin abun da yafaru tum daga farko har kashe.

Slowly Romeo ya kai kallon sa kan mutumin, sannan ya kalli James dake ta faman juyi a wajen yana numfashi da kyar da kyar, dawo da kallon sa kan Tga yayi yana mamakin, wai ace James ya samu accident dan bai ji ciwo ba ya dawo gida kuma Tga ya masa irin wannan dukan, nan take yaji wani ɓacin rai ya rufe masa zuciya, a fusace ya miƙe rai a ɓace ya fara dukan Tga, daddy na bashi hakuri ya kyale Tga haka ai ya daku amma ina ba wanda ya saurara dan Tga ya bashi haushi, ace James yayi accident Allah ya tsare bai ji ciwo ba ya dawo sannan Tga ya kama sa ya masa irin wannan duka dan yazo da wanda ya buge da mota gida.

Sosai Romeo ya bugi Tga har sai da yaji ya ishe sa, yayin da shi kuma Tga ya sume baya ko motsi, yayi lilis a hannun Romeo, dan ma yayi Sa'a Romeo bai ɗau zafi sosai ba

Cike da jin haushin Tga Romeo ya wuce ya nufi in da James ke kwance yana mai da namfashi da kyar da kyar, ko kallon in da su daddy suke bai yi ba, ya ɗauki James ya saɓa sa a kafa ɗan sa ya haye saman bene ya koma bedroom na sa.

Yana tafiya su daddy sukayo kan Tga, dan bashi taimakon gaggawa kasan cewar daddy likitane.

Shi kuwa Romeo saman katafaren gadon sa ya kwatar da James kusa da Michael dake kwance yana kuka.

Ko kallon in da Michael ɗin yake Romeo bai yi ba, ya wuce ya ɗauko kayan aiki ya fara duba James.

Sai bayan James ya dawo hayyacin sane yace "Please lion ka taimaki mutumin nan da na buge da mota" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba, shi kuma Michael wai yayi fushi da shu shi yasa ya kwanta shiru yana hawaye.

After 40mins

Sai bayan Romeo ya gama duk abun da ya dace yayiwa James ne sannan yace su kira likita ya duba mutumin, amma shi ba zai duba kowa ba, da sauri James ya miƙe, jikin sa ba kwari ya fito ya nufi wajen daddy, dan ya rokesa ya duba mutumin, abun mamaki ko da ya fito palon sai bai ga mutumin ba, yaji tsoron ko dai sunje sun jefar da mutumin ne kamar yadda suka faɗa, da sauri ya nufi hanyar fita daga palon dan yaje ya tambayo security waya fita da mutumin nan

Yana kokarin fita muryan dad ta dakatar da shi "James where are you going" a sukwane ya juyo ya kalli daddy cikin sauri yace "Please dad where is the man I brought" murmushi daddy yayi kafin ya sanar da James mutumin yana ɗakin duba marasa lafiyar su, da sauri James ya nufi wajen dan alhakin kula da mutumin na rataye ne a wuyar sa.

Yaji daɗi sosai ganin yadda daddy ya bawa mutumin nan kulawa, har da karin ruwa daddy ya masa, sannan mutumin ya farka, kafar sa da ya karye kuma daddy ya sanya kafar cikin wata na ura na aikin su likitocin.

Karisawa cikin ɗakin James yayi, ya zauna a gefen mutumin yana faɗin "Sorry" kallon sa mutumin yayi kafin ya ɗan ɗaga masa kai kawai, "What is your name?" James ya tambayi sunan mutumin, a hankali mutumin yace masa "Musharraf" jinjina kai James yayi kafin yace "are you an Arab from saudia?" Gyaɗa masa kai mutumin yayi kafin yace "Yes" shiru James yayi kafin ya sake cewa "Are you a Muslim?" Nan ma eh mutumin yace masa "Okey how is your body now" James ya faɗa yana kokarin mikewa ya nufar hanyar fita "Alhadulillah" Musharraf ya faɗa yana bin James da ido kawai amma shi kaɗai yasan azaban da yake ji.

Ficewa James yayi daga room ɗin yana jin daɗi da mutumin bai mutu ba, a palo ya isko daddy, da fara'a ya yiwa daddy godiya, shima daddy ba karamin daɗi yaji ba, dama kuma ya kula da mutumin ne dan James yaji daɗi, yana son yaga yaran sa suna nuna masa soyayya kamar yadda yake son su amma basa hakan sai dai tsawa da faɗa, shi yasa yanzu yake kokarin yin duk abun da suke so dan ya jawo su jikin sa.

Wannan kenan ku koma Nigeria muga meke faruwa

💞NIGERIA💞

💞KATSINA💞



kallon Sadiq tayi idon ta a bushe, dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login