Showing 45001 words to 48000 words out of 194715 words

Chapter 16 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

962

gidan nan" yayi maganar yana kallon daddy, kashe masa ido ɗaya daddy yayi kafin yace "Kai Imran yanzu sai da ka bari kyan baby Jelly ya rikitaka dama na faɗa mata sai tafi kowa kyau, na faɗa mata bazaku gane ta ba dan kyau ɗin da kwalliyar ya mata" sai lokacin Imran ya gane matsalar komawa yayi ya zauna tare da jawota jikin sa yana faɗin "Kai baby Jelly duniyar kyau, irin wan nan kyau ai dole ki rikita yaya Imran kaiii chanchaɗi" kallon gefen ido daddy yayi wa su Irfan nan take suka tsaya da dariyar dan kar jelly ta hassala, cike da farinciki suka kariso suka zazzauna saman sofa tare da ɗagawa daddy gaisuwa, cikin hanzari su Nana suka zo suka ɗauka musu trolley's dasu ka zo da shi,

kallon Akila Imran yayi kafin yace "heartbeat jeki gyarawa Auntyn ki make up ɗin ta ya ɗan ɓaci" cool murmushi Akila ta saki tana faɗin "Yaya wan nan ne daman Auntyn mu? Ita ce kullun kake faɗa mana?" Gyaɗa mata kai yayi ala'mar eh cike da jin daɗi Akila tace "Yaya Akil yau dai ga rabin rai ɗin da yaya Imran ke ta magana a kan ta" kwaɓe fuska Akil yayi har suna haɗa baki da Aafia wajen cewa "Wan nan mummunar" a sukwane Irfan ya ɗago kai yana mamakin rashin kunya irin na Akil da Aafia a gaban baban yarinya kuce mata mummuna, Irfan na kokarin yin magana Jelly ta rigashi da cewa "Ku da kuke maganar kyawawane ku? Da wasu fuskan ku kamar an gasa big (Alade) ya kone tayi baki" shi dai Imran shiru ya musu dama bai tanka musu bane dan yasan Jelly zata kwatarwa kanta yanci dan ba'a mata ta kyale,
tsawa Aafia ta daka mata "Ke mara kunya idan kika ce zaki min rashin kunya sai na fasa miki baki!!" shi dai daddy yau yaga ikon Allah, girgiza kai kawai yayi dan baruwan sa da faɗan su yan uwan juna su karata can, Irfan zai yi magana Imran ya ɗaura yatsa a saman lips na shi alamar yayi shiru, murmushi Akila sarkin fara'a da kaunar mutane musamman yan uwan ta tayi cike da fara'a a face nata tace "Aunty Aafia abun ai bai kai ga haka ba, dan Allah ku bari, ni fa tun jiya da yaya Imran ya faɗa min zanzo wajen yan uwan Abba wallahi ko barci banyi ba saboda murna zanzo naga yan uwana da ban sansu ba, ban taɓa ganin su ba kuma nake mararin ganin nasu, ni ada duk tunanina Abba bai da wasu yan uwa sai jiya da yaya Imran ya sanar da ni to dan Allah karku ɓata mana wan nan farin cikin" Akila bata gama rufe baki ba Jelly tace "Ke ce mara kunya kuma wallahi ba'a haifi wadda zai fasa min baki ba" a fusace Aafia ta miƙe da niyar ta bugi jelly, sai dukan uku uku kirjin daddy ke yi dan da a dakar masa Jelly gwara a sanya shi frog jump, gashi kuma bai son shiga faɗar nasu kar a ce ya shigarwa yarsa kar su ce dan sun zo gidan shi ne dama ga yadda zumuncin nasu ke rawa, Aafia na zuwa ta sanya hannu zata fisgo Jelly daga jikin Imran a fusace Irfan ya ɗaga hannu zai mareta Imran ya riƙe masa hannun nasa yana faɗin "Ke Aafia kuce kije ki zauna heartbeat jeki gyara min babyna" ya kai karshen maganar tare da sakin hannu Irfan, shiru Irfan yayi sabida Imran yayan sa ne duk kan su ya girme su, shi dai Akil ko ajikin sa sai kwaɓe fuska yake a ransa yana faɗin "Wan nan gidan talakawan ne za'a ce mu zauna har one week wallahi ba zan iya ba kuma sai na faɗa wa Ammie sai dai yaya Imran ya kashe ni, amma sai Ammie taji in da ya kawo mu gida sai wari yake gashi ɗan karami kamar keji tsuntsaye na" ita kuwa Aafia a fusace ta juya ta koma ta zauna saman sofa tana kunbura kumatu, miƙewa Akila tayi ta riƙo hannun Jelly ta kalli daddy tace "Bappa ina ne ɗakin ta" murmushi ya saki har cikin ransa yake jin kaunar Akila saboda kirkin ta ga kuma fara'a ga son yan uwanta, yau tazo gidan amma har ta rungumi Jelly ta riƙe ta hannu bibbiyu, da hannu ya nuna mata bedroom na su da murna ta ja hannun Jelly suka wuce sama,

dawo da kallon sa daddy yayi kan su Irfan kafin yace "Ku tashi kuje ɗaki kuyi wanka kuzo kuci abinci" ya kai karshen maganar tare da kiran Zuwaira da Nana a kan su zo su kai su masaukin su miƙewa Akil yayi, yayi gaba yana faɗin "Ni banga abincin ci a gidan nan ba haka kuma ban ga wajen kwana ba dan haka hotel zan tafi na kama" yayi maganar cikin harshen turanci murmushi daddy yayi yana mamaki Akil, Abban su Imran yana da kuɗi na fitar hankali haka ita ma Ammie su dan tafi Abban su ma kuɗi nesa ba kusa ba, to amma shi ma daddy Jelly bazaa kirashi talaka ba koda kuwa a gaban su Ammie ne ya wuci su kirasa da talaka kuma wan nan gidan nashi yafi karfin a ce ba'a ga wajen kwana ba, kawai dai Ammie su ta ɓata su da kuɗi ne suna abun da suke so shi dai Imran yana da kyakkyawar zuciya ne kawai shi yasa baya biyewa abun da Ammie ke yi musu baya damuwa da kuɗin da suke da shi

shi dai Irfan gaba ɗaya sai yaji babu daɗi sai ma yaji da bai sa Imran ya tawo da su Akil ba gashi sunzo suna yiwa bappa rashin kunya, jiki ba kwari shima Imran ya miƙe Zuwaira ta musu jagora zuwa boys quarters su Aafia kuma Nana ta kai su ɗakin kusa da na daddy Aafia Umaisha Akila, ita kuma Jelly daman gadon ta na bedroom ɗin daddy

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

*💞TRIPLET'💞11




*💞The beginning💞*


*Episode 11*

*🛫WASHINGTON DC🛬*

*LOT 33.*

*07:30*

Iskan sanyin safiya na kaɗawa yanayin weather garin gwanin ban sha'awa, iskan na kaɗawa a hankali hankali, duk da cewa a koi sanyi hunturu amma hakan bai hana kaji daɗin iskan dake kaɗawa ba, a hankali Michael ke tattako staircase yana saukowa jikin sa sanye yake da wando 3 cutar blue da t-shirt mai laushi mara nauyi fari kal kamar yanzu ya fito da ita daga kwalin ta saboda haske ta ya ɗaura jacket blue color mai ɗan girma a saman kayan nasa, hannun sa na ɗaure da dankareriyar gold watch mai bala'i kyau da tsada sai kyalli yake yana ɗaukan ido, ya tara kyakyawan dogon gashin can nan nashi daya sha gyara ya ɗaure a bayan wuya ya zubo kaɗan ta gaban goshin sa kamar mace, fuskar nan a ɗaure tam kai da ganin sa kaga Tiger ne da gaske,

katafaren palon su a gyare tsab sai daddaɗar kamshin air freshener da sanyin Ac ke tashi, kai kace yanzu a ka zuba komai na palon saboda yadda suke tsab kamar hannu bai taɓa taɓasu ba,

kai tsaye wajen table ɗin cin abinci Michael ya nufa, wasu jigba jibgan Bodyguard ne tsaye a wajen table ɗin sanye suke cikin suit baki da glass baki a face nasu fuskar nan tasu kamar hadari a ɗaure tamau babu alama imani ko ɗigo a ransu, sun jeru yali gefe da gefe sun sanya table ɗin a tsakiyar su, bodyguard 12 ta gefen nan 12 ta gefen nan,

tun Michael bai iso wajen ba suka fara sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba ya nufi saman kujerar table ɗin, a sukwane ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya ja masa kujerar baya, ya zauna, cikin sauri ɗaya daga cikin su yace cikin harshen turanci "Sir me za'a zuba maka?" Da hannu ya musu nuni da wata dan kareriyar warmer mai ɗauke da Nasville hot chicken, nan take suka fara serving na shi, nan daddy da Uncle Herry suka isko sa, da sauri bodyguard suka ja musu kujera suma suka zauna,
suna zama sai ga John da Jay suka iso wajen, suma haka bodyguard suka ja musu kujera suka zauna

Cike da so da kauna daddy yace "My Tiger where is James?" ba tare da ya kalli in da daddyn yake ba yace "I don't know" cikin sauri John yace "he had gone out" shiru daddy ya ɗan yi kafin yace "Why two days ɗin nan James ke fita since morning kuma baya dawowa sai can dare" shi dai Michael bai tanka daddy ba abincin sa kawai yake ci hankalin sa kwance

waya daddy ya ɗauko ya shiga contact ya fara kiran number da a kayi saving da my lion, sai ringing wayar take amma ba'a ɗaga ba, har wayar ta katse ba'a ɗaga ba, sake kira daddy yayi, a karo na biyu ma ba'a ɗaga ba, sai a karo na uku shima sai da wayar ta kusa katsewa san nan a ka ɗaga, kara wayar a kunne daddy yayi ya tattara nitsuwar sa cike da so da kauna yace "Hello my lion" shiru a ka ɗan yi na 40 second kafin wata zazzakar voice mai tashin kai mai bala'i daɗi yace "Good morning dad" nauyayyar ajiyar zuciya dad ya sauke kafin yace "my lion how are you doing this morning?" Shiru ya ɗan yi, su Michael duk sun nitsu, shi Michael ma har abincin ya dai na ci yayi shiru ya nitsu dan yaji ko karar sa daddy zai kai, shi kam John har kerma jikin sa keyi Uncle Herry sai zazzare ido yake, Jay kam ba'a magana, ba su kaɗai ba har ta jibga jibgan Bodyguard dake tsaitsaye a kan su dan basu kulawa sai da suka kara shiga hankalin su kowannen su sai zazzare ido yake sun kasa kunne suna sauraron daddy, kowa sai addu'a yake Allah yasa ba wani abu a kan sa daddy zai faɗa ba

"What's going on daddy you called me this early morning hope there is no problem?" Lion yayi maganar cikin sanyin muryan ga sexy voice nashi mai bala'i daɗin sauraro ciki ciki yake magana kamar bai son buɗe bakin sa,

cikin sauri dad yace "I want you to investigate for me where James is out every early in the morning and coming back home in the evening" shiru lion yayi kamar bai ji me dad yace ba, bin wayar da kallo daddy yayi dan yaga ko lion ya katse kiran, bai kuma katse kiran ba ganin haka yasa daddy ya gane lion na nufin ko a koi wata matsala bayan wan nan, hakan yasa cikin sauri dad ɗin yace "There's no other problem" dad na kai karshen maganar ɗif lion ya kashe wayar sa, dogon numfashi daddy yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya ya ɗago ya kalli su Michael da suka zuba masa ido suna jiran suji ko lion ya bashi wani sako a kansu, su kuwa bodyguard sai sauke ajiyar zuciya suke tun da sunji ba karan su dad ya kai ba

Kallon Uncle Herry daddy yayi cikin harshen turanci suke magana "Herry ina mamakin Romeo sosai yanzu, ba ma shi kaɗai ba dukkan su suna bani mamaki over" cikin sauri Uncle Herry yace "Nima dai gaskiya ina mamakin Romeo da James how comes yanzu yake ɗan respecting naka how? why?" Shiru daddy ya ɗan yi kafin yace "Tun last 5 Month ago Romeo ya fara ɗaukan kirana in yayi tafiya har ma ya min magana cikin girmamawa har ma ya tambaye ni ko a koi wani problem abun da a baya ko zan shekara ina kiran sa sai ya ga damar ɗauka kuma ban isshe shi kallo ba to why? Why suka canza haka? Ina son sanin dalili" guntun tsaki Michael yaja tare da cire hannun sa daga cikin abincin ya ajiye spoon da yar karamar wukar hannun nasa, da sauri ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya ciro masa tissue paper ya goge masa bakin sa, sai kwaɓe fuska Michael ɗin yake ya miƙe ya nufi hanyar fita daga palon

"My tiger what about church?" Daddy ya tambaya, ba tare da Michael ya juyo ba yace "I can't go" cikin sauri daddy ya miƙe tsaye yana faɗin "Are you mad? Are you heard what you said?" A fusace Michael ya juyo a ƙule yace "I'm not mad, I knew what I said, let me repeat it again maybe you will understand what I mean, I said i can't go anywhere, in fact as from today i can't go to the church again" tashin sense cikin sauri Uncle Herry ya miƙe yana faɗin "William ina ganin mu kira Pasto yazo yayiwa Michael addu'a dan ina ga ya samu matsala a brain nashi" Johnson ne ya cabki zancen da cewa "Yes daddy saboda ya faɗa a School wai ya dai na shan wine" jiki na rawa daddy ya ɗauko wayar sa ya shiga contact tsabar ɓacin rai har idon sa baya gani sosai,

ganin daddy zai yi kirane kuma yasan mutun ɗaya zai kira yasa Michael saurin cewa "Sorry dad rai na ne ya ɓaci amma I'm sorry today i have an exam so ba zan samu damar zuwa church ba amma gobe zanje" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga palon yana mai jin haushi, shi ba wani abu yasa bai son zuwa church ɗin ba pace Pasto su daya tsani gani, bai son pasto ko kaɗan tun yana yaro sai an sha fama da shi yake zuwa church ɗin,

Jin abun da Michael yace yasa daddy sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da komawa ya zauna sai ajiyar zuciya yake ta faman sauƙewa a ran sa yana faɗin "Thank you Jesus"

*Michael*

Kai tsaye School ya nufa, sai sharara gudu yake a kan shinfiɗaɗiyar titin mai laushi wadda babu kwarzane ko kaɗan, da motar sa kirar *Aston Martin*.

Yana shiga school ya kashe Motar sa a parking space na *Harvard Square Parking Garage*, ya fito tare da Lucky Copper Winston, kai tsaye office na dr tyrian ya wuce, babu ko excuse bare jiran umarnin haka ya faɗa cikin office ɗin fuska a ɗaure, tsabar tsorata Dr har yana kokarin guduwa dan banyi expecting ganin kowa a lokacin ba,

kai tsaye wajen sa Michael ya nufa fuskar nan tasa a ɗaure tam kamar hadari dan dad ya ɓata masa rai over,

Yana zuwa ya damko wuyar rigar Dr cike da bada umarni ya fara magana cikin harshen turanci "Idan har this time ma ka faɗar dani baka bani Mark ba kasa na kara samun carry over kasa Romeo ya bani punishment idan... Michael bai kai karshen maganar ba Dr yace "A'a ni na isa ai kana rubuta Exam nan dole na baka mark" kallon banza Michael ya masa kafin yace "Chemaka a kayi zan rubuta Exam ɗin? Ni ba wani Exam da zan rubuta kai zaka rubuta min da kan ka, kuma kayi marking ka bani mark full" ya kai karshen maganar tare da sakin wuyar rigar dr ya juya ya fice daga office ɗin yana wani kwaɓe fuska, nauyayyar ajiyar zuciya Dr ya sauƙe kafin yace "Oh wan nan bala'i da me tayi kama dole muyi meeting na malamai mu san yadda zamuyi mu bawa Michael result mai kyau dan ya bar School nan mu huta" haka dai Dr ya rinƙa surutan sa shi kaɗai,

Shi kuwa Michael yana fita kai tsaye gore place ya wuce yaje ya zauna su lucky suka zauna kusa da shi.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*KANO*

Bayan sallar issha zaune suke gaba ɗayan su a palon daddy amma ban da Akil, sai Jelly da Akila da basa wajen suna cikin ɗaki suna can Akila tasawa Jelly wan nan ta canza mata wan nan sai shiri suke kamar wayan da zasu je party

Daddy na zaune kusa da Imran da Irfan suna hira, wayar sa tayi kara alamar shigowar kira, cikin sauri ya duba wayar dan daman yana expecting na kira, Engineer Muhammad Imam shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar jikin daddy har kerma yake wajen picking na call ɗin ya manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Engr ya ake ciki" tsabar zumuɗi ya manta da sallama ma, daga ɗayan ɓangaren Engr yace "Congratulation sir company mu gomnati ta bawa contract na aikin nan" miƙewa tsaye daddy yayi tare da dukawa ya ajiye wayar yayiwa Allah sujudur shukur yana zubawa Allah kirari da godiya mai tarin yawa, ganin daddy yayi sujudur shukur yasa Irfan da Imran suma suka sauko suka taya sa yiwa Allah godiya ta hanyar yin sujudur shukur ɗin suma duk da basu san me ya faru ba me daddy ke wa sujudur shukur ɗin,

Daddy ya ɗan jima yana yiwa Allah godiya kafin ya ɗago ya ɗauki wayar sa yayi ta zubawa Engr Muhammad Imam godiya da fatan alkhari, san nan sukayi sallama ya katse kiran,

cike da murna ya sanar da su Imran abun da ya faru, sosai suka taya shi murna da yi masa fatan alkhari, sosai suka ji daɗi su Aafia duk sun masa addu'ar fatan alkhari yaji daɗi sosai,

Cikin wan nan farincikin Jelly da Akila suka fito daga bedroom suka same su, jelly tasha make up mai bala'i kyau Akila ta sanya mata wandon jeans blue mai stone a jiki sai yar karamar riga mai karamin hannu pink color tayi kyau sosai da sosai,

wow shi ne abun da Imran ya iya furtawa kenan, kyau iya kyau Jelly tayi Akila ta tsantsara mata kwalliya, sosai Aafia da Umaisha suka zuba mata ido dan Jelly ba baya ba wajen kyau bare kuma kyan ya haɗu da make up kai Masha Allah, kasa jurewa Imran yayi yana bala'i son Jelly tun tana yar jaririya, miƙewa yayi ya riƙo hannun ta yana jin kamar yace daddy ya ɗaura musu Aure yanzu sai a barta sai ta girma sai yazo ya ɗauki matar sa dan gani yake kamar za'a kwace masa ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login