Showing 66001 words to 69000 words out of 194715 words
kan face nata, sai zuba murmushi take hakwarar ta kamar gonar audiga saboda hasken su tas suke
ganin murmushi da ke kan face nata yasa shi jin sassauci a ransa yaji sanyi a zuciyar sa cike da so da kauna yace "Yes I will my Jelly" juyowa tayi ta rungume sa tana dariya, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da shafa kan ta, yana mai tausaya mata ya zata ji idan ta girma by mistake taji abun da baban ta ya aikata,
Da tunani cike fal ran sa ya ɗauke ta cak suka wuce wajen drawer kayan su, ya ciro mata wasu riga da wandon jeans, sauri sauri ya shirya, tsab suka wuce palo, dan cin abinci.
Already su Zuwaira sun gama shirya musu komai zama yayi ya ɗaura ta saman cinyar sa ya fara bata abincin a baki, tana ci tana wasa haka ya rinƙa biye mata har ta koshi san nan yaci na shi, sai da ya koshi san nan ya miƙe suka koma saman sofa ya jawo system nashi dake saman sofa table ya kunna musu suka fara buga game kamar yadda suka saba, shi dai buga game ɗin kawai yake ba wai dan hankalin sa na wajen ba, baya ma sanin me yake taɓa wa ba, kawai yana yi ne dan jelly taji daɗi tayi farin ciki, ita kuwa sai murmushi take abun ta.
________________________________
*KADUNA*
Cikin dare yinwa mai tsananin gaske ne ya tada Hajiya daga barci, tayi kokarin ta danne yinwan tayi barci, amma ina abun ta ci tura dan yin wa sosai take ji fiye da tunanin mai tunani
kamar zatayi kuka haka ta taso ta kunna wutar ɗakin, ba karamin tsorata tayi ba ganin Abba a zaune a tsakiyar gadon
"Alhaji lafiya?" Tayi maganar murya na rawa, kamar zai yi kuka yace "Yinwa nake ji Hajiya" shiru Hajiya ta ɗan yi kafin tace "To muje palo muci abincin mana" kasan san cewar sun manta komai ne yasa basu damu ba suka jera a tare suka nufi palon.
Ko da suka isa palon wutar a kunne babu komai shiru palon, kai tsaye table ɗin cin abincin suka nufa, suka zauna,
sai bayan sun zauna suka lura da abincin dake saman table ɗin
zaro ido waje sukayi suna kallon abincin, kayatattun girke girke ne masu bala'i kyau ga daddaɗar kamshin da abin cin ke dubawa, ga fruits kala kala an yayyanka su an jera a plate ga gasassun gaji sun ji kayan kamshi, wani abincin ma basu taɓa ganin irin sa ba, duk girman table ɗin nan sai da a ka shake sa tab da abinci na alatu masu kamshi da haɗuwa, har da gasassun pig (Alade) gasu ɓera da zomo duk an gashe su sai turirin zafi suke,
Hajiya ce ta fara fasa ihu tana kokarin miƙewa, wayan nan dodannin suka bayyana a sauran kujerun table ɗin suka mai da Hajiya suka zaunar da ita, shi kam Abba daman ban yi yunkurin rashi bama
Nan take Hajiya jikin ta ya fara kerma, ta rintse idon ta bata son haɗa ido da dodannin bata son kallon su, dan fuskokin su babban tashin hankali ne sai mai irin zuchiyar Sahabbai zai iya ganin su ma'ana sai mai karfin imani
Kamar daga sama Abba da Hajiya suka ji an fara ɗura musu abincin a baki, a sukwane Hajiya ta wari idon ta, kai tsaye idon ta ya sauka kan mummunar hannun ɗaya daga cikin dodannin nan yana dunbutso shinkafa yana danna mata a baki, kallon hannun nasa tayi da kyau, bakin kirin kamar gawayi ga hannun duk datti sai bala'i wari yake ga hannun nasa da girma kamar samudawa
Wage baki Hajiya tayi zata fasa ihu, kamar jira dodan yake, tana waje baki ya danna mata shinkafa a baki, wadda ya sata ba shiri ta haɗi saboda daya danna mata shinkafar ya toshe mata hanci, hakan yasa tayi saurin haɗiye abincin dan ta samu tayi mumfashi, yau ga ɗuren dole, haka dodannin nan suka rinƙa yiwa su Abba ɗuren abinci da wan nan mummunar hannun nasu kamar kwata.
Da sauri Imran ya shigo palon daga Part nashi yana faɗin "Abba kune daman a palon? Sai jin motsin nake ina ɗaki shi ne nace bari nazo na duba" wage baki Hajiya tayi tana ihu dan Imran yaji ya taimake su amma ina Imran baya jiyo komai, shi ma Abba sai magana yake wa Imran amma Imran baya jin komai, sai ganin bakin su yake suna motsi "Abba lafiya kuke motsa baki kuma baku magana? Ko nazo ne" Imran ya faɗa da mamaki a face nashi, ya kai karshen maganar tare da kallon saman table ɗin, zaro ido waje yayi yana faɗin "Abba me nake gani hakan? Ya naga kamar ɗan yen nama da kwari kuke ci?" Ya kai karshen maganar tare da karasowa wajen, sai magana su Abba ke masa shi kuma baya jin komai
ganin su Abba sun ƙi yi masa magana ne yasa ya sanya hannun sa yana kokarin cire hannayen su daga kan abincin da idon sa ke gane masa shi suke ci, dan shi ɗanyen nama da kwari da tsutsotsi yaga su Abba na ci, su kuma ganin abinci masu kyau suke a saman table ɗin. Tashin sense
Da karfi Imran ya ja hannun Abba da niyar cirewa daga plate ɗin, kamar daga sama yaji saukan bulala a tsakiyar bayan sa, ihu ya fasa bai san lokacin da yace "bura uban nan kai uban waye ya dake Ni?" Bai gama rufe baƙi ba aka sake shinfiɗa masa wata bulalar a wuyar sa da karfi, razanannen kara ya saki, cikin fitar hayyaci yace "Bismillahi tawakkaltu alallah wala haula wala kuwata illa billah kulhuwalkahu ahad kulya ayuhal kafirun Alhamdulilahil laji an zala fi hil Quran" tsabar azaban bulalar ne yasa shi furta wayan nan kalamai, da bai san me bakin sa ke faɗe bama, Abba da Hajiya Suna kallon meke faruwa da Imran ɗin har wanda ke zane sa suna kallo amma ba halin magana, shi kuma Imran baya ganin komai sai saukar zabga zabgan bulalu kawai yake ji a jikin sa, sai ihu yake yana sambatu, amma duk gidan ba mai jin sa sai su Abba,
Kewaye palon Imran ya farayi ya rasa gane kofar fita sai ihu yake su kuwa dodannin ba tausayi ba imani haka suka rinƙa shin fiɗa masa wan nan zabga zabgan bulalun nasu mai bala'i zafi a jiki, duk sun fashe masa jiki, duk in da yayi sai saukar bulala zai ji
da kyar ya samu ya gane kofar fita a guje kamar wani zararre yayi waje yana gudu yana ihu ya ɗage jallabiya sama, yana wurga dogayen kafofin sa bai san ma in da ya nufa ba, kai tsaye sai toilet ɗin baba mai gadi ya shige, ya samu bayan kofa ya tsaya yana mai da numfashi tare da jan majina.
Su kuwa dodannin yana fita suka kyalesa suka koma kan Abba da Hajiya, Hajiya na ganin sun nufosu da wayan nan zabga zabgan bulalun, habawa ai sai ta fasa ihu tana kokarin guduwa ta haye sama suka damkota suka jawota zuwa tsakiyar Palon suka fara....✍️
💞TRIPLET'S💞
https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo
*THE BEGINNING*
💞*STAR LADY*💞
EPISODE 16
________________________________
Hajiya na ganin sun nufosu da wayan nan zabga zabgan bulalun, habawa ai sai ta fasa ihu tana kokarin guduwa ta haye sama suka damkota suka jawota zuwa tsakiyar Palon suka fara zabga mata bulalun sai ihu take, sauran dodannin kuma suka damko Abba suka kwantar da shi kusa da Hajiya suka hau zabga musu bulalun,
dai dai lokacin Akil ya shigo palon yana sauraron kira'ar sudais a wayar sa ya kure volume, shi ma yinwan dare ta tashe sa, jin kira'ar yasa dodannin ɓacewa ɓat, kamar kuma yadda suka ɓace haka suka ɓace da tunanin su Abba.
Ganin su Abba kwance a tsakiyar palon ne yasa Akil karisowa wajen da sauri yana faɗin "Abba Ammie lafiya kuka kwanta a palo yau kuma?" Shiru sukayi basu amsa masa ba, mamaki ne ya kara kama shi yasa hannu yana taɓa su, yana kiran sunan su.
Hajiya ce ta fara tashi a nitse kafin Abba ma ya tashi, "Abba me yasa kuka kwanta a Palo?" Akil ya jefo musu tambaya, kallon juna sukayi kafin su ɗaga ido suna kallon Palon, da mamaki har suna haɗa baki wajen cewa "Me ya kawo mu palo kuma?" Miƙewa Akil yayi tare da rage volume na kira'ar da yake ji ya nufi table yana faɗin "Kila barci kuka yi a wajen kuna hira" ya kai karshen maganar tare da zama saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin, ya fara bubbuɗe takeaway ɗin dake saman table ɗin, dan ya duba wani abunci ya dace yaci.
Jiki ba kwari su Hajiya suka miƙe suka nufi bedroom nasu ransu cike da mamaki yaushe suka zo palo kuma, da kyar suke jan kafar su, har suka wuce Bedroom na su.
Shi kuwa Akil abincin sa ya fara ci yana yatsine fuska
After some minutes.
Wayar sa ta fara kara, dogon tsaki yaja kafin ya ɗauki wayar ya kawo ta sai tin face nashi Abla shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin sake jan dogon tsaki yayi kafin ya ɗauki kiran ya sata a hand-free ya ɗaura saman table ɗin.
Daga ɗayan ɓangaren cikin sanyin murya a kayi sallama, rai a ɓace Akil yace "Wai Abla baki ganin time ne da zaki kirani yanzu?" Murya kamar zata yi kuka tace "Kayi hakuri yaya Akil wallahi tun karfe 10 nake kiran yaya Imran yaki ɗaukan waya ta" "To naji me kike so yanzu kuma?" "Kuɗi nake so yaya Akil" guntun tsaki yaja kafin yace "Za'a turo" ya kai karshen maganar tare da katse kiran yana faɗin "Da daren nan zaki kira mutun kice masa wani kuɗi gari ba zai waye bane ku baku da aiki sai takurawa mutun, ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ɗau wayar sa ya fice daga palon ya koma part na su.
_____________________________
*WASHINGTON DC*
Motar Micheal na gaba motar James na bin sa a baya, har suka kai babban titin da zata sada su da unguwar su, wayar James ta fara kara, a hankali yayi parking na motar sa a gefen titi dan hakan yana daga cikin dokan Romeo ya hana su ɗaukan waya suna tuƙi.
Sai da ya kashe motar san nan ya ɗauki wayar tare da picking call ɗin ya manna wayar a kunnen sa, Jim kaɗan ya cire wayar daga kunnen sa, sauri sauri ya tayar da motar tare da juya kan motar da wata mahaukaciyar gudu ya figi motar ya bar layin ya sauka daga titin ya canza hanya, yayin da shi kuma Michael ya ɗauki shinfiɗaɗiyar titin gida.
Kai tsaye unguwar *Adams alley* ya wuce, ka ta faren unguwa ne mai cike da dogayen gine gine, na alfarma masu kayatarwa, kai tsaye wajen wani katon guest house ya nufa, tun bai kariso ba suka wangale masa gate ɗin gidan kamar daman sun san da zuwan sa, da gudun gaske ya kutsa hancin motar cikin gidan kamar mara gaskiya, yana shiga masu gadin suka mai da gate ɗin suka rufe, kai tsaye parking space ya wuce.
Yana kashe motar ya fito ya shige cikin gidan da yar gudun sa.
Still wan nan ogan nasu ne a wajen shi da wasu mutane, da alama wani abun mai muhimmanci suke tattaunawa, wucewa James yayi yaje ya zauna kusa da ogan nasu.
Cikin harshen turanci ogan nasu ya fara magana "Lokacin yayi da zamuyi Oder makamai a China dan kayan aikin mu sun yi kasa, san nan karku manta Jams kai zaka ja ragamar sayo makaman kamar dai yadda muka saba, ina son mu kai hari mumbai mu tura wa gomnatin su gargaɗi ta hanyar boom,
sai magana ta gaba, manyan mutane daga sama sun aiko mana da hoton wani matashin soja mai ji da karfin iko, a yanzu shi yake juya gomnati, suka ce mu kawar da shi dan babban barazane a gare su kasan cewar sa a raye, dan yana aiki da gaskiya kuma shi ci-gaba mutane yake so, mu kuma kun san bama son hakan, mun fi so muga talakawa cikin ukubar rayuwa, James na naɗa ka a kan wan nan aikin, kai zaka kashe sojan, dan nasan kai kaɗai zaka iya, zan tura maka hoton sa a WhatsApp sai kayi kokarin cika aikin, idan ka gama aikin kashe sojan ne sai ka jagoranci sayo makamai ɗin daga nan sai mu fara shirye shiryen meeting a kan cocaine da zamu shigo da su this year, sai muga container nawa ya kamata mu kawo kuma kasashe nawa ya kamata mu sayarwa"
jinjina kai James yayi tare da miƙe wa tsaye yana faɗin "I'm leaving now, saboda ina da meeting da brother na a gida, kuma bana son su fahimci abun da nake suna jirana ne" gyaɗa kai ogan nasu yayi kafin yace "Okey see you next time" sauri sauri James ya fice daga wajen, dan kar Michael yaje gida yayi ta jiran har ya fara tunanin wani abu, motar sa yaje ya shiga ya ja da gudun gaske ya bar wajen.
Yana cikin tafiya wayar sa ta ɗan yi yar kara alamar shigowar sako, sauke hannun sa ɗaya yayi daga kan staring ya ɗauki wayar yayin da ɗayan hannun nasa ke tuƙa motar,
Ganin sakon ogan sune yasa cike da zumuɗi ya buɗe sakon dan yaga menene zai kashe, a sukwane ya taka wata irinyar mahaukaciyar birki wadda tasa sai da ya buga kan sa da jikin staring motar, waro light ash eyes ɗin sa waje yayi yana kallon wayar, a fili cikin tsawa yace "GAR zan kashe kai ina never" lokaci guda yaji kan sa na sara masa kamar zata fashe, jikin sa har tsuma yake saboda ɓacin rai shiru yayi yana tunanin mafita, dan magana ta gaskiya ko wani ya gani zai cutar da GAR sai in da karfin sa ya kare, yau shi za'a cewa ya kashe GAR da kan sa, ina hakan ba zata yiwuba, gashi duk wanda ya shiga wan nan aikin nasu tofa bai isa yace zai fita ba, yana cewa zai fita to fa kashe shi suke har lahira, shi bama fitar bace a gaban sa ya za'ayi ya ceci GAR ya za'ayi ya sauyawa ogan su ra'ayin a kan su rabu da GAR, dan ya san yanayin aikin su, duk wanda a kasa hoton sa a layin wayan da za'a kashe tofa ba makawa sai sun kashe sa, sosai James ya shiga damuwa da fargaban ya za'ayi ya samu mafita.
Yana tsaka da tunani sai zufa yake yi yayi tsuru tsuru da shi lokaci guda, wayar sa dake hannun sa ta fara kara ala'mar shigowar kira yar firgigit yayi tare da ɗago wayar dan yaga wanene, blood Shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, jikin sa har kerma yake wajen yin picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen sa, ya tattaro dukkan nitsuwar sa waje ɗaya, cikin girmamawa yace "Hello" shiru a ka ɗan yi na yan sakanni kafin wata zazzakar murya mai batikar daɗi da sanyi yace "I'm on my way" zaro ido waje James yayi muryan sa har sarkewa take wajen furta "Wow, remain how many hours?" Shiru a ka sake yi kamar ba za'ayi reply ba, sai zaro ido waje James yake, can wan nan sexy voice ɗin yace "Few minutes" "What? James ya faɗa da karfi, katse kiran a kayi ba tare da an sake magana ba, a sukwane James ya ja motar kamar wani zararre ya bar wajen ya nufi gida.
Yana shiga gida ya wuce parking space, yana kashe motar ya fito da sauri har yana haɗawa da gudu ya nufi cikin gida, gaba ɗaya jubga jingan sojojin nan sai da suƙa tsorata ganin yadda James ke rikice sun san ba lafiya ba
Tun daga kofar babban Palon kasa James ke kwalawa daddy ƙira, a ruɗe daddy da Uncle Herry suka sauko daga sama, suna tambayar lafiya James ke kwala musu wan nan uban kira haka, dai dai lokacin Michael da John da Jay suka sauko suma
a ruɗe James yace "Romeo is back" daddy da Uncle har suna haɗa baki wajen cewa "What?" Shi kuwa John ihu ya fasa ya nufi hanyar fita a guje "where are you going John?" Daddy ya tambayi John dake kokarin nufar kofar fita, tsaki Jay yaja kafin yace "School zai je mana ina da tabbacin shaidar exam da Hangout zai je ya nemo" shiru Michael yayi yana tunanin yadda zai yi a ransa,
wuce su James yayi ya haye sama ya nufi bedroom na shi, kallon Uncle Herry daddy yayi kafin yace
"Let's go in, ko?" Girgiza kai uncle yayi yana faɗin "No let me check first, what and what I did last week might be i did something wrong, i don't know, I want to correct my mistake before lion reach here" wucewa daddy yayi dan shi ma yaje ya duba ko ya aikata wani abun da ba dai dai ba, shi kuma uncle ya nufi waje
kallon tsab Jay yayiwa Micheal kafin yace "To kai me ya tsayar da kai? Ko dai kai ma zaka je ka duba ko kayi wani abun ne?" wucewa Micheal yayi ba tare da yayi magana ba, wucewa shima Jay yayi ya koma bedroom na shi.
_______________________________
*KADUNA*
A toilet din baba mai gadi Imran ya kwana, a nan wajen barcin ya ɗauke sa, saboda donanin nan na ɓacewa dukkan su barcin ya ɗauke su, suma su Abba Akil ne ya tashe su ba dan shi ba da a haka za su kwana, shi kuwa Imran sai da baba mai gadi yazo shiga bayi da asuba san nan ya samu a ka tashe sa,
yana fitowa ya rinƙa tikar amai kamar zai mutu ga jikin sa duk ciwo yake masa, sai dai shima ya manta komai yayi kokarin ko zai iya tuna abun