Showing 120001 words to 123000 words out of 194715 words
yanzu gaba ɗaya ta dai na jin kuka zuciyar ta ya bushe, cikin sauri tace "Sadiq ka nemomin masu sayan gidan nan" sannan ta dawo da kallon ta kan gwaggo dake ta faman kuka tace "Gwaggo bamu bukatar mu fitar da Mum waje kuɗin aiki kawai zamu nema mu wuce babban asibiti, na san dai kuɗin gidan nan zai isa ai mata aiki, daman kuɗin jirgin fita wajen shi ne mai tsada, dan haka a sayar da gidan nan a mata magani daga baya zamu san abun yi bayan ta samu lafiya" ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi cikin ɗaki.
Jim kaɗan ta fito sanye da abaya a jikin ta tana faɗin "Gwaggo ki koma hospital ni da Sadiq zamu nemo mai sayan gidan" kasa magana gwaggo tayi dan ta jinjinawa Jehan wannan shine dalilin da yasa a kace ilimi na da amfani yau gashi ilimin Jehan ya taimaka musu, dan kwata kwata bata kawo zancen sai da gida ko kuma karsu fita waje da mum ba sai gashi Jehan ta kawo musu mafita.
Jiki ba kwari gwaggo ta miƙe ta wuce hospital wajen mum, su kuma Jehan da Sadiq suka wuce nemam dillalai.
Babban tashin hankali shine duk wanda su Jehan suka kira dan ya sayi gidan idan ya fahimci kuɗi suke buƙata ruwa a jallo, sai yayiwa gidan kuɗin wulakanci, a wannan karon ba karamin tashin hankali Jehan ta shiga ba, dan abun da take tunani shine mafitar su shima yana neman ya gagara, ga mum kuma kwance rai a hannun Allah kowani lokaci daga yanzu tana iya mutuwa, dan da gaggawa ake buƙatar a mata aiki saboda ciwon yaci jikin ta sosai, dan likitan yace ciwon ya jima a zuciyar ta tun bata kai haka ba, cikin watan nan ne kuma ciwon ya kara tsanan ta saboda tashin hankali da ta shiga na rasuwar daddy da kuma ɓatan Rimsha.
Kamar zararriya haka Jehan ta dawo lokaci guda ta fita hayyacin ta rasa mada fa.
Da kyar suka samu wani ya sai gidan 2 million haka suka sallama masa ya zuba musu kuɗin a account ɗin mum, haka Jehan taje ta ciro 1.5m misalin karfe 5 na yamma, duk wannan yawon da suke tare da Sadiq suke, haka suka shiga a daidaita sahu suka kama hanyar asibiti dan taje ta ɗauki mum su wuce babban hospital, tana rungume da jakar kuɗin tana tunanin halin da suke ciki.
A kan hanyar su ta zuwa asibitin ne suka samu accident da wata mota, cikin kwata Jehan ta faɗa yayin da shi kuma Sadiq ya faɗi can gefen titi, saboda juyin da a daidaita sahun tayi da su, shi ne ta watsar da su, kan kace me jama'a sun taru sai salati suke yayin da shima mai motar da sukayi accident ɗin da shi ya sume sakamakon buga kan sa da glass ɗin marfin motar da yayi.
Allah ya kiyaye Jehan da Sadiq basu ji ciwo sosai ba, a sukwane Jehan ta miƙe bata damu da kwatar dake jikin taba, ita dai kawai burin ta mum ɗin ta tafita daga haɗari ta samu lafiya.
Kai tsaye bakin hanya ta koma tana neman wani mai a daidaita sahu dan su wuce asibiti, ta ruɗe ta manta da jakar kuɗin ma, haka Sadiq yazo ya same ta, suka ɗan kara gaba da in da sukayi accident ɗin suka samu wani abun hawan, zasu hau kenan Sadiq yace mata "Jehan ina kuɗin kuma" a sukwane ta juyo, tana faɗin "Yana cikin wannan abun da muka hau ɗin" a guje Sadiq ya juya ya koma, da sauri ta bi bayan sa.
Ko da suka zo wajen babu jakar, tsab suka duba cikin mashin ɗin duk da cewa mashin ɗin ma ya faɗi dan sai da sukayi juyi biyu kafin mashin ɗin ya faɗi.
Tsab suka duba cikim mashin ɗin babu komai, a razane Sadiq ya ɗago yana tambayar jama'ar dake wajen, kowa yace masa bai gani ba, mutuwar tsaye Jehan tayi ta kasa motsawa, ta rasa me zatayi, daman ta ciro kuɗin ne a nata tunani dan tana zuwa kawai su wuce babban asibiti ta biya kuɗi kawai a yiwa mum aiki ba sai sun kai gobe ba, a yau zaayiwa mum komai shi yasa tayi sauri ta ciro kuɗin dan kar banki su rufe, gashi a daren nan take son ayiwa mum aiki kuma banki basa aiki da daddare bare tace zata bar kuɗin a bank har sai an buƙata, a takaice dai bata son ɓata lokacin shi yasa ta ciro kuɗin, yanzu gashi wanda ya fisu iya ajiyar kuɗin ya ɗauke,ko in ce mara imani.
Shi ma Sadiq kasa magana yayi dan yasan ba karamin wahala suka shaba, wajen neman kuɗin nan, jiki ba kwari ya kariso wajen da Jehan ɗin ke tsaye, a hankali yace "Ya Zamuyi" shiru Jehan ta masa dan bata da bakin magana, ganin haka yasa ya riko hannun ta suka hau abin hawan da suka tare suka nufi asibiti, cike da tashin hankali da fargaban abun da zasu gayawa gwaggo.
wannan shi ne ba ɗaya kanin biyu, ba gida kuma ba kuɗi sannan ba yiwa mum aiki, tashin sense, muje zuwa yanzu wasan zai fara, karki bari a baki labari.
👹Daular mutuwa👹
Rimsha bata sake fita ba tun ranar da abun nan ya faru tsakanin ta da duna, yau kwana biyu kenan.
Yauma kamar kullun suna zaune cikin ɗakin su, sunyi jugum jugum, ita Rimsha sai faman kokarin ɗaure dark black curly hair ta take, gashin nata na da tsantsi sosai yaki ɗauruwa, ita kuma bata son barin sa a sake haka saboda ƙuran dake ɗakin nasu. Cikin sauri Ayla tace "La Meesha muje mu gaishe da baba, kwana biyu ban je ba" juyo da dara daran sleeping eyes nata Rimsha tayi kan Ayla kafin tace "waye kuma baba?" Miƙe wa Ayla tayi tana faɗin "Zo muje ki gan shi" miƙa wa Ayla hannu Rimsha tayi, Ayla tajata ta miƙe tana faɗin "Meesha kin fini quality fa" shiru Rimsha ta mata ba tayi magana ba, mukowa Ayla hannu itama kausar tayi, Ayla ta kama, ta miƙar da ita.
A tare suka jera suka fita a ɗakin, suna fita suka hango Mustapha a bakin kofar ɗakin sa yana ɗaure takalmin sa da igiya, da yar fara'ar su suka karisa wajen sa, suka gaida shi, shima da fara'a ya amsa musu tare da tambayar ina zasu je, Ayla ce ta sanar da shi wajen baba zasu je "to kuje nima ina zuwa bari na ɗan gama aiki na" to suka amsa masa da shi kafin su wuce su shiga ɗaya daga cikin ɗakunan dake wajen, yanzu sosai Mustapha ke sake musu fuska suyi hira, tun ranar da Rimsha ta masa magana, shi kenan sai suka zama ɗaya.
Kusa da wani tsohon mutumi suka je suka zauna, tsoho ne sosai, ya manyan ta, gashi fari tas kamar bature ga dogon hanci da dara daran ido, duk da tsufa da wahala da yake ciki, hakan ba zai hana kaga kyan saba, ga gashin kan nan nasa da ya zama farin saboda tsufa kwance luf mai tsantsi har goshin sa, Rimsha ta sha mamakin ganin mutumin nan, ji take kamar ta san shi, lokaci guda taji kaunar tsohon ya shiga ranta.
Ayla ce ta fara gaishe sa, ya amsa cike da kulawa yana tambayar ta kwana biyu ina ta shiga ta dai na zuwa wajen sa suyi hira, nan take bashi labarin su Rimsha, sosai ya jajan ta musu, kafin suma su gaishe shi ya amsa, sai kallon shi Rimsha keyi tana tunanin ina ta san wannan fuskar, amma ina ta kasa tunawa, amma dai koma me tabbas tasan wannan fuskar.
Suna zaune suna hira har Mustapha shima yazo nan suka ci-gaba da hiran su, baba na basu labarai suna dariya, a nan wata yarinya tazo ta same su, suka ci-gaba da hira..
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪
💞Star Lady💞
TRIPLET'S💞
*THE BEGINNING*
💞STAR LADY💞
WhatsApp me for more information 09162620621
Episode 25
Kai tsaye *Florida avenue* James ya nufa sai sharara gudu yake da motar sa a saman shinfiɗaɗiyar titin da zata sada shi da*Florida avenue* ya sanya kiɗa na tashi yana tuƙi yana tunanin yadda zai yi da ogan su, dan yanzu sun dawo masa da zancen kashe GAR sabo, kuma sun matsa masa a kan maganar sosai, saboda sun san duk cikin yaran su shi kaɗai ne zai iya yi musu wannan aikin cikin sauri, kan sa ya kulle sosai ya shiga damuwa neman mafita.
Bai ankaraba ya buge wani mutumi da yazo tsallaka titin, a sukwane ya ja wata mahaukaciyar birki har sai da kansa ta bugu da jikin glass ɗin motar, wani irin jiri ya gani lokacin guda, da sauri ya fito daga cikin motar, duk da kan sa sai faman sara masa yake haka ya karisa wajen mutumin da ya buge ɗin, kwance yake saman titi, sai dai da alama bai wani bugu sosai ba, bai ji ciwo sosai ba amma da alama ya samu karaya a kafa, da sauri James ya duƙa duk girman mutumin haka ya ɗauke shi cak, ya sanya shi cikin mota, kasan cewar unguwar na masu kuɗi ne hakan yasa ba hayani ya ba mutane kowa na cikin gida, tunani ya fara yi ina ya kamata ya kai mutumin nan.
Daga karshe dai ya yanke shawara ya wuce da shi gida duk da ya san zai fiskanci matsala daga Michael da Romeo amma bashi da zaɓi dole ya kai shi gida, haka ya ja motar sa da gudu ya juya motar ya koma gida.
Yana yin parking a parking space na gida ya fito ya ɗauki mutumin ya nufi hanyar shiga cikin gida, a guje jinga jingan sojojin dake tsakar gidan suna gadi, suka nufo shi, har suna rige rigen ansan wannan mutumin daga hannun sa dan su taimaka ma shi, ba musu ya miƙa musu dan dama bai son su Romeo su gan shi ya ɗauko mutumin zasuyi mamaki kasam cewar sun san shi da lalaci.
Haka suka shiga palon, a sukwame TGA ya miƙe tsaye yana mamaki, wucewa sojan da ya ɗauko mutumin yayi, yaje ya kwantar da mutumin saman sofa 3 seater sannan ya fice daga palon.
"James who is this man? What happened to him?" Tga ne ya jerowa James wannan tambayar, a takaice James ya faɗa masa abun da ya faru na buge mutumin da yayi, nan take Tga ya ɗaure fuska sosai, a fusace yace "carry him out from this house!!!" zaro ido James yayi yana kallon ikon god, yana jinjinawa karfin hali irin na Tga, sai kace gidan sa to ko Romeo mai gidan ma ai ba zai ce a fita da mutumin nan lokaci guda ba tun da ni na bugesa da mota, sai ya bari mun masa jinya.
James yayi nisa cikin tunanin da zancen zuci da yake, sai ji yayi Tga ya daga masa tsawa "James I'm I not talking to you?" Yar firgigit James yayi kafin yace "I can't uncle" zaro ash eyes ɗin sa Tga yayi kafin ya wuce ya nufi waje, James na tsaye yana mamaki hali irin na yan uwansa su kwata kwata basa son baki a rayuwar su, inma mace ko namiji duk su basa so, basa son kowa ya raɓe su, sun fi son suyi rayuwar su su kaɗai, gaba ɗaya gidan haka suke ba mai son wani yazo cikin su, basa son mutane musamman Romeo yafi kowa tsanar wasu suzo kusa da su, daga shi sai Michael da Tga sun tsani baki.
Sai tunanin ta yadda zai kare da Romeo a kan mutumin nan yake, gashi mutumin yana sume baya cikin hayyacin sa, zuba masa idon James yayi yana kallon sa.
A fusace Tga ya dawo cikin palon tare da sojoji biyu jibga jibga masu jini a jika, kai tsaye mutumin Tga ya nuna musu yana faɗin "carry this man out from this house" kallon sojojin James yayi suna kokarin ɗaukan mutumin cikin tsawa James yace "Are you mad, get out from here!!!" Cikin fushi Tga yace da sojojin "i said take this dirty man out" kafe su da ido James yayi kafin yace "Okey carry him let me see" shiru sojojin suka tsaya sun rasa maganar wa za su bi, dan duk wanda suka karyawa doka to zasu rasa aikin su, Tga ogan sune a wajen aiki, while shi kuma James sanyin idanniyar ogan kowa a gidan ne wato Romeo, sun gwammaci suki bin umarnin ogan su wato tga a kan su ɓatawa James rai dan gwara musu hukuncin Tga a kan na Romeo, dan haka sai suka juya suka fice daga palon dan sun san halin Romeo a kan yan uwansa sam baya adalci kuma zai iya yin komai a kan Triplets ɗin sa.
Ganin sojojin sun juya sun fice ne yasa Tga ya nufo mutumin da kan sa da nufi ya ɗauke sa ya fitar da shi, yana kai hannun sa zai ɗauki mutumin, a fusace James ya damki hannun nasa tare da turesa gefe guda, rai a matukar ɓace Tga yayi kan James da nufin dukan sa, nan fa James yace bai isa ba, kamar wasu zakuna haka suka fara faɗa.
Da karfi Tga ya kaiwa James duka a gefen ciki wadda hakan ya masa mugun zafi sosai, lokacin guda James ya sauya idon sa sukayi jawur nan fa ya riƙiɗe ya zama tamkar mayinwa cin zaki wadda yayi shekara biyu babu abinci ya fito farauta, nan yafara farauta Tga, a fusace ya sanya dukkan karfin sa ya ɗaga Tga yayi wurgi da shi gefe saman glass table na tsakiyar sofa milk color, nan take table ɗin ta tarwatse, gadan gadan James ya haye kan Tga ya fara kai masa bugu ta ko ina yana gurnanin ɓacin rai, ran maza ya ɓaci gaba ɗaya jijiyoyin kan sa dana wuyar sa sun miƙe sai dukan Tga yake sosai, da dai yaga duka da hannun ma bata masa ba sai ya ɗamko wuyar rigar Tga ɗin ya miƙar da shi tsaye, yana kokarin kai masa naushi a ciki, Tga ya riƙe hannun sa tare da kwashe kafafun James ɗin ya zube kasa, nan fa Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka shima
Kasan cewar James ya samu horon faɗa sosai wajen ogannin sa, hakan yasa ya san dabarun faɗa sosai, cikin dabara ya juyar da Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka.
kamar wasu mayinwatan zakuna haka suka rinƙa farautar junan su, sai dai Tga yaci karfin James, dan shi horon soja ya samu daga wajen Romeo, hakan yasa yayiwa James duka duk ya farfashe masa jiki da fuska, da kyar James ke mumfashi, amma Tga idon sa ya rufe duka kawai yake kai masa ta ko ina.
Zuciya ta jasa yana neman kashe James ba tare da ya sani ba.
Kamar daga sama yaji an riƙe hannun sa ta baya, yana kokarin juyowa, a fusace Romeo ya murɗe masa hannun da karfi ta baya tare da ɗaga sa sama daga kan James ɗin yayi wurgi da shi gefe, idon Tga ya rufe baya ji baya gani, bai san waye yayi wurgi da shi ba, a fusace ya taso ya nufi Romeo dan idon sa James yake gane masa, Romeo na tsaye, fuskar nan a ɗaure tamau kamar bai san menene dariya ba, dara daran blue eyes na san nan sun sauya zuwa ja saboda dukan James da Tga yayi, har wani tsuma jikin sa keyi, yau da Tga ba kanin daddy bane da ba abun da zai hana ya kashe shi, amma duk da haka dole ya basa hukunci mai tsanani, shi kuwa Tga idon sa ya rufe gadan gadan ya iso wajen Rome yana kokarin kaiwa Romeo duka a ciki, cak Romeo ya riƙe hannun sa tare da kai masa wawan bugu a ciki wadda ta sanya sai da ya fasa ihu mai sauti, bai kai ga gama ihun ba, Romeo ya sake ɗaga sa sama yayi wurgi da shi saman sofa, wadda sai da ya sanya ya fara dawo cikin hayyacin sa, karisawa wajen sa Romeo yayi rai a matuƙar ɓace ya ɗamko wuyar sa ya miƙar da shi tsaye, ya tsake masa wuyar tasa, nan fa Tga yaji kamshin mutuwa, cikin fitar hayyaci yasa hannu yana kokarin cire hannun Romeo daga wuyar sa amma ina ya kasa koda motsa hannun Romeo ɗin, sai faman zaro ido waje yake, Yana kokarin tantance wa idon sa ke gane masa, shin abun da ya gani da gaske ne, shin Romeo ne ko gizo ne, bai kai ga iya tantance wa ba
Romeo yasa kyakkyawar kafar sa ya taka shi da karfi a kirjin sa wadda sai da ya saki ihu mai ranaza kwakwalwa, tamko wuyar sa Romeo ya sake yi ya kai masa duka a ciki wadda sai da tasa shi dawowa cikin hayyacin sa da kyau, dan yasan ba mai karfin yi masa irin wannan damka da dukan duk gidan sai Romeo.
Kwashe kafafun sa Romeo yayi nan take Tga ya zube kasa kan gwiwowin sa, rai a ɓace Romeo ya sanya kyakkyawar farin hannu sa ya ɗamko gashin kansa Tga ɗin ya ɗago kan nasa sama suna fiskantar juna, zuba masa dara daran blue eyes nasa nan Romeo yayi yana kallon face nashi kamar mai tunanin wani abu.
Sai galabaitaciyar kukan wahala Tga yake, murya na sarkewa da kyar ya iya faɗin "I'm sorry lion" shiru Romeo yayi kamar bai ji saba, yayin da shi kuma James ke kwance kasa yana numfashin da kyar da kyar, ga fuskar sa nan duk Tga ya fashe masa sai jini yake, abun ku da fatar turawa ba quality sosai ba kamar bakar fata ba, fatar su bata jure wuya ko kaɗan.
Jin hayaniya yasa su daddy saukowa kasa, ganin abun dake faruwa yasa suka kariso cikin palon da yar gudun su, cike da tashin hankali a fuskokin su, kuka Michael yasa ya duka kasa