Showing 171001 words to 174000 words out of 194715 words

Chapter 58 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

986

tsaye yana fiskantar balcony bedroom ɗin ya bawa kofar shigowa baya, James ɗan basaja nan fa ya fara basajan nasa ya murje kamar ba shi ba, har da murmushi yana faɗin "My blood how are you" Shiru Romeo yayi na yan mintoci

Ba tare da ya juyo ya kalli James ɗin ba yace "where did Josephine live" Wato mum ɗin su kenan, James yayi shock da jin tambayar da Romeo ya masa, dan Romeo kwata kwata bai taɓa yin wani magana da ta shafi mum ɗin su ba, yau kawai ya tambayi ai nane location ɗin ta lallai akoi matsala kenan

Cike da tsoro yace "Me ya faru? Me kuma tayi?" A takaice Romeo yace "zan je nayi warning ɗin tane" zaro ido James yayi dan yasan warning ɗin Romeo babu kyau a tsorace yace "Daman gobe zan yi tafiya zan biya ta wajen nayi warning ɗin nata please lion karkaje wajen ta ka bari naje" shiru Romeo yayi bai sake magana ba, James kuwa yayi amfani da kwarewar sa a fannin basaja ya rinƙa lallaɓa Romeo har ya hakura da zuwa New York wajen mum ɗin nasu, ba karamin daɗi James yaji ba, sallama ya yiwa Romeo ya fito ya nufi wajen Musharraf, ta cikin glass ɗin show glass dake gefen sa ta nan ta bi James da kallo yana son fahimtar wani abu, sosai ya zubawa watch ɗin hannun James dara daran idon nan nasa, har James ya fice, a ransa yana tunanin dole yayi bincike a kan James dan zuciyar sa ta dage da zargin James sosai, a hankali ya juyo ya koma saman bed nasa ya kwanta tare da lumshe dara daran idon sa yana tunani a kan James, yana jin babu daɗin a ransa har barci ta ɗauke sa.

Mu leƙo Nigeria mu dawo

💞KATSINA💞

💞SUPER RESTAURANT💞

Shabiyu da minti arba'in Jehan ta fito daga wajen girkin restaurant ɗin hannun ta rike da tray mai ɗauke da plate dake shake da jolof rice yaji kayan haɗi sai kamshi yake, ga soyayyen ayaba wato plantain a gefe plate ɗin, sai coca colar ɗaya da ruwan faro, wani table ta nufa wadda wani matashin ke zaune a wajen yana latsa wayar sa, kallo ɗaya zaka masa kasan ɗan karya ne, dan yadda yake wani bubbuɗe hanci yana kallon mutane kallon banza.

Gaban sa tazo ta ɗaura masa abincin saman table ɗin ta juya zata tafi, a wulakance yace "Ke wace iriyar dakikiya ce? Wannan shine abun da nayi oder?" Shiru tayi ma shi kamar bata ji shi ba ta ci-gaba da tafiyar ta

Tsawa ya daka mata "Ke ba dake nake bane?!!" Ci-gaba da tafiyar ta tayi dan ita bata cika kula ire iren wayan nan mutanen ba, a cewar ta basu da hankali, ita kuma bata kula mahaukata,
ta san wannan hargagin duk me yake wa, dan yaga wasu yanmata sun shigo restaurant ɗin ne yake wannan hargagin banzan dan su ɗauka shi wani shegene yazo sayan abinci mai tsada, alhalin shinkafa yar 2k yazo ci.

Ganin Jehan taki kula shine ga kuma yanmatan suna kallon sa hakan yasa yaji idan ya bar su Jehan haka yaji kunya wajen yanmatan nan, dan haka sai ya miƙe a fusace ya nufi wajen Ibraheem tun da shine mai controlling na restaurant ɗin, sai wani cika yake yana batsewa kamar wani shegen mai kuɗi, duk kuma yana yi ne kar yaji kunya a idon ƴanmatan nan.

Ibraheem bawan Allah tun da Jehan tazo yake aikin kashe wuta, daga ta jajumo masa wannan sai ta jajumo masa wancan, yanzu ma yana zaune shiru yana latsa wayar sa cikin nishaɗi yana murmushi da alama abun da yake gani a cikin wayar tasa tana sashi nishaɗi,

Kamar daga sama ya fara jin ruwan bala'i wannan mutumin da Jehan ta kaiwa abinci "Wannan wani irin iskanci ne? Nayi odar gasassun kaji da chip ma'aikaciyar ku ta kawomin yar gidan malam Shehu wato shinkafa, me za'ayi da wata yar gado itace gidan uban kowa, ni na wuce cin shinkafa wlh sai dai kaji, kuma abun haushi ina mata magana tayi banza dani, har kamar ni zaku yiwa wannan cin mutuncin, to wlh baku isa ba sai na sa an rufe wannan restaurant ɗin, kun san waye ni kuwa? To na ma fasa cin abinci a wannan kazamin restaurant ɗin, kun ɓata min rai!!!" Duk bala'i da yake Jehan na jin sa amma ko ajikin ta dan bai ishe ta kallo ba.

Sai hakuri Ibraheem yake ba wa mutumin nan, amma yaki hakura ya dage shi ba zai ci abincin ba ya fasa

Daga jin wannan zancen nasa kasan dama bai da kuɗin sayan abincin.

Ba yadda Ibraheem bai bashi hakuri ba amma yaki yace ba zai ci ba kuma ba zai sake zuwa restaurant ɗin ba, sannan sai yasa an rufe restaurant ɗin yaga uban da zai buɗe

Daga karshe dai shiru Ibraheem yayi yana jin sa, har ya kammala surfa ruwan masifar nasa ya juya zai bar wajen, karaf sukayi ido huɗu da Jehan dake tsaye a bayan sa

Dogon tsaki yaja kafin yace "Ki rubuta ki ajiye sai kinyi nadamar abun da kika min" daga kasa Jehan ta fara kallon sa zuwa sama, wani kazami da shi ta faɗa a ranta

A takaice cikin kwanciyar hankali tace "Kuɗin abinci" zaro ido yayi yace "Ban gane kuɗin abinci ba, ai ga abincin ku can ban ci ba kuje ku ɗauki kayan ku" shiru Jehan ta ɗan yi kafin tace "Kai kasan baka ci ba, ni dai kuɗi zaka bani, domin in dai Jehan ce ta kawo maka abinci to ko kaci ko baka ci ba dole zaka biya kuɗi"

Shi dai Ibraheem ido kawai ya zubawa wannan dirama na Jehan da mutumin,

Rai a ɓace mutumin yace "Wannan ne kuma baki isa ba, bazan biya abun da ban ci ba" shiru Jehan ta ɗan yi kafin tace "Zaka bani kuɗi nane ko dai sai rai na ya ɓaci?!!" A wannan karon tayi maganar cikin harshen turanci, nan take yaji tsoro ya kama shi

yadda Jehan ke magana da confidence yana sanya mutane da yawa tsorata suyi zaton ko yar wani ne ko kuma akoi abun da ta taka, amma kuma basu sani ba ita ma tsoron nata na ciki, kawai dannewa take tayi magana da confidence dan ta kwatar wa kan ta yanci, a tunanin ta idan ka nuna kana tsoro abune sai ya baka tsoron da gaske, amma idan kace baka san tsoro ba a filli sai abun yazo maka da sauki.

Mutumin dai yaji kunya domin ya tsorata da Jehan dan ta tsaya with her full confidence tayi masa magana kamar wata yar uban wani ko ta taki wani tsiya.

Ƙasa ya farayi da murya yana faɗin "Ni ba zan biya abun da ban ci ba" tsare sa da ido tayi bata sake masa magana ba, hakan ba karamin tsorata shi ya sake yi ba, dan gani yake kamar ko dai wannan kanwar maza ne, ma'ana irin kannen yan daban layin nan ne shi yasa take haka, ko kuma dai yar wani hamshakin ɗan daban ne, wadda idan ka taɓa ƴaƴan su suke kashe mutun

Allah sarki bawan Allah shi kuma ta nan ya kai Jehan, ita kuwa ta tsaya kyam a fili babu alamar tsoro a fiskar ta amma a ciki sai dukan uku uku zuciyar ta keyi kamar zatayi fitsari a wando.

Ibraheem na kokarin dannan Jehan a kan ta hakura mutumin ya tafi tun da bai ci abincin ba su su ɗauki asaran kawai, afili Ibraheem yayi magana kamar da gaske amma ba haka bane, yana tsoron kalaman mutumin ne da yake cewa zai iya sawa a rufe restaurant ɗin wadda idan hakan ta faru ogan su sai ya rufe shi a police station zai ce shi ya hadda sa komai, shine baya kula da costumers, sai dai ya manta wace ce Jehan dan in tayi magana ba wanda ya isa ya sata ta janye.

Hannu ta ɗagawa Ibraheem kafin tace "Malam ka manta nace kada ka sake min magana ne? Ogan ka shine dai'dai nayi magana da shi ba kai ba, please karka sake shiga harka ta" shiru Ibraheem yayi dan shi kan shi Jehan na bashi tsoro wani lokaci, shi ɗaukan mai aljanu ma yake mata.

Jehan kenan duk wanda ya zauna da ita tofa ɗaukan da zai mata daban.

Ɗago dara daran idon ta tayi ta kalli agogon dake manne a bangon wajen 12:50pm ɗaure fuska tayi sosai cikin tsawa tace "Ka bani kuɗin abinci lokacin tafiya ta gida yayi!!!" Zaro ido Ibraheem yayi "Lokacin tafiyan ta gida yayi kuma?" Ibraheem ya mai'mai ta a zuciyar sa yana mamaki.

Mutumin kuwa da yaga Jehan fa ba wasa take ba, sai ya hakura ya ciro 2k daga aljihun sa ya miƙa mata yana faɗin "kuje Allah ya isa na" karɓan kuɗin tayi abun ta ta wuce ta koma wajen girkin nasu, shi kuma mutumin haka ya wuce ya fice daga restaurant ɗin yana son cin abinci amma yana jin kunyar yaje yace zai ci yanmatan da yayi burga dan su su mashi dariya gashi kuma yinwa yake ji sosai haka ya hakura ya fice daga restaurant ɗin,

Yana fita waje yace "Allah ya isa na munafukai yar 2k na ya tafi ni ban ci abinci ba, kuma bala'i yinwa nake ji wlh, gashi 500 ya ragemin a aljihuna, wayyo Allah rayuwar tiktok bakiyi ba nazo nayi video mai kyau ina cin lafiyayyen abinci, yanzu gashi na kare ni ba ga video ba, ban kuma ci abinci ba ba kuɗi ba ga kuma yinwa, kai kwata kwata rayuwar karya dai baiyi ba, dole na tuba na koma ga Allah, in godewa Allah da arzikin da yamin, daga yau a gidan ubana zan rinƙa video sai dai followas na su zaje ni ko su daina following nawa ina dalili in wuni ina fama da buga katako duk ƙusa tayi ta fasa mana hannun da kyar muke samu da wuya mu haɗa kujera, oga ya sallame mu naje na karar da kuɗin a yawon restaurant da hotel dan yin video fake life" kamar zararre haka ya tsaya yayi ta suruntan sa a bakin gate ɗin restaurant ɗin, har ya gaji ya kama kan sa ya wuce yana jan tsaki.

A ɓangaren Ibraheem kuwa ba karamin daɗin yaji ba karɓan musu kuɗin da Jehan tayi wajen mutumin nan, sai dai kuma ta wani ɓangaren yana tsorace karfa da gaske mutumin nan zai iya sawa a rufe musu restaurant ɗin su, dan ɗan Adam ba abun renawa bane ta iya yiwu wa yana da hanyar da zai iya yin hakan.

Sai tunai Ibraheem yake bai ankara ba sai yaga Jehan ta nufi hanyar fita daga restaurant ɗin, cikin sauri yace "Ke ina zakije?" Ko kallon in da yake ba tayi ba bare ya sa ran zata amsa masa ta wuce abun ta ta fice daga restaurant ɗin, baki sake Ibraheem ya bita da kallo yana tunanin yadda zai yi da ita.

Jehan kenan mai abun ban mamaki ita da kan ta ta tsarawa kan ta lokacin zuwa aiki da lokacin tashi kamar restaurant ɗin nata ne ko na daddyn ta.

Tana fita ta tari abun hawa ta hau zuwa anguwar su, dan tace sai taje gidan su taci uban Alhajin nan sannan ta dawo asibiti ta duba jikin mum, ba karamin haushin taji ba abun da Alhajin nan yayiwa Hanan ji take kamar idan ta ganshi ta shaƙe ɗan banza sai ya mutu, yau ta ɗaura niyar duk wanda ya dakatar da ita wajen ciwa wannan Alhajin mutunci tofa bazata ɗaga masa kafa ba, sai ta haɗe da shi duk taci uban su.

Tun daga nesa take hango jama'a sun ɗan taru a kofar gidan su Sadiq wato gidan su na yanzu

Tsabar sauri irin nata gani take mai mashin ɗin baya sauri dan haka sai tace ya sauke ta a wajen ta karisa da kafar ta zata fi sauri, yana sauke ta ta miƙa masa 500 bata tsaya ta karɓi chanji ba ta wuce, yana ce mata ga canjin ki amma ina bata ji ba, hankalin ta yayi wajen jama'ar nan dan tana zaton su Sadiq ke rikici da Alhajin.

Ai kuwa zaton ta gaskiya ne hakan ne, Sadiq ne yake rikici da Alhajin da kuma baban sa, ga Hanan zaune saman dakali kofar gid tana kuka, jama'a suna ta bawa baban Sadiq hakuri, sai zuba ruwan bala'i baban Sadiq ɗin yake wai bai isa ya yiwa ƴaƴan sa magana ba, wannan mijin Hanan ne ya bashi auren ta zai ɗauke ta suje duba kaya a shopping Sadiq yace zai hana wlh ba zata saku ba, haka baban Sadiq ke ta surfa uban bala'i, shi kuma Sadiq ya kasa faɗin abun da Alhajin ke nufi da Hanan dan ya rufa wa kanwar sa asiri baya son kowa yasan abun da Alhajin ya mata jiya da daddare.

Shikuwa Alhajin babu kunya ba tsoron Allah ya tsaya ya kafe ya tsare zai tafi da Hanan suje sayayyar kayan auren su, a yadda yake faɗawa jama'a kenan

Jehan na isowa wajen kai tsaye wajen Sadiq tanufa, yana sunkuye kamar yayi ruku'e ya sunkuyar da kan sa yana kallon kasa kamar mai yin kuka, tana zuwa ta fara tambayar sa abun dake faruwa


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞


TRIPLET'S💞



💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)



*Gargarɗi*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_




WhatsApp me for more information 09162620621






Episode 38-39


Jehan na isowa wajen kai tsaye wajen Sadiq tanufa, yana sunkuye kamar yayi ruku'e ya sunkuyar da kan sa yana kallon kasa kamar mai yin kuka, tana zuwa ta fara tambayar sa abun dake faruwa, cike da damuwa da tashin hankali ya ɗago kai ya fara bata labarin abun da yake faru, baban sa ya tara musu jama'a wai basa jin maganar sa mijin Hanan zai fita da ita suje sayayya shi Sadiq ɗin ya hana, ɗagowa Jehan tayi ta kalli Alhajin.

Kara zaro ido tayi tana kallon sa tabbas tasan wannan fuskar amma ai na ta mance, shiru tayi tana tunanin ai na ta san wannan fuskar

Ganin ta zubawa Alhajin ido tana kallon sa tayi shiru ne yasa Sadiq yace "Jehan lafiya" dago da kallon ta kan Sadiq ɗin tayi tana girgiza kai alamar babu komai, shesshekar kukan hakan yasa ta juyo ta kalle ta

A takaice tace "Hanan tashi ki shiga gida" ƙin tashi Hanan tayi dan tana tsoron baban ta, Jehan ta fahinci abun da Hanan ɗin ke nufi, dan haka sai ta dawo da kallon ta kan baban Sadiq wadda yayi shiru saboda zuwan Jehan, yana tsoron aljanun Jehan na dare shiyasa yayi shiru

"Kace mata ta shiga gida" Jehan ta faɗa tana kallon baban Sadiq ɗin, ba musu baban Sadiq yace "Tashi ki shiga cikin gida Hanan" da gudu Hanan ta tashi ta shige cikin gida, dan dama kamar a kan kaya take zaune.

"Baba ya zaka ce ta shiga gida ban gane ba" cewar Alhajin, shiru Jehan tayi tana kallon su tana son taga ya zasu kare

Cikin girmamawa baban Sadiq yace "Kayi hakuri Alhajin wani lokaci zaku je yanzu dai ka kyale ta" da sauri Alhajin yace "A'a baba ni yau nake son muje, yau nayi niyya" satar kallon Jehan baban Sadiq yayi kafin yace "Dan Allah kayi hakuri Alhaji" girgiza kai Alhajin yayi yana faɗin "Ina ba zai yiwa ba gaskiya kawai ta fito mu tafi" sai hakuri baban Sadiq ke bashi amma Alhajin nan ya murje ido yace sam bai yarda ba dole Hanan ta fito su tafi.

Da dai Alhajin yaga da gaske baban Sadiq ba zai kira Hanan tazo su tafi ba, sai ya fara masifa yana faɗin baban Sadiq ya karɓe masa kuɗin sa akan ya bashi Auren Hanan, to wlh ba zai yarda ba dole yau Hanan ta fito su tafi,

Yadda zaka gane da wata manufa a ran sa game da Hanan ɗin shiyasa ya dage a kan tazo su tafi.

"Hanan ba zata fito ba kuma daga yau ma karka sake zuwa wajen Hanan idan ba haka ba duk abun da muka maka kai ka ja ma kan ka" cewar DPO wato Jehan, tayi maganar cikin kwanciyar hankali, kallon tsab Alhajin ya mata kafin yace "Idan Hanan ba zata zo ba ke zaki zo kenan? Dan naga kin fi Hanan ɗin hankali zaki fita iya zaɓen kayan sai mu tafi dake kawai a bar hanan ɗin" karo na farko da Jehan ta saki murmushi a rayuwar ta na yanzu, dan ita ko lokacin da suke tare da daddy ba ta murmushi bare dariya haka face nata yake a ɗaure tamau.

Matsowa ta ɗan yi gaba kaɗan kasa kasa tace "Anya zaka iya fita da Jehan kuwa?" Tayi maganar tana murmushi, shiru Alhajin ya ɗan yi kafin yace "Amma ke kin san me kika faɗa kuwa" kashe masa ido ɗaya tayi kafin tace "Eh niko na san me nake faɗe cewa nayi mu tafi, idan zaka iya fita da ni, Jehan a shirye take" Tashin sense, shiru Alhajin yayi Jehan ta jefa sa cikin tunani, "anya wannan yarinya lafiyar ta kuwa, kai ina ga bata san me na shirya a tafiyar bane shiyasa amma bari na gwada ɗaukan ta muje in gani, idan bata san me na shirya ba, na samu ɓagas daman tafi Hanan komai da komai zan more tsuntsu daga sama gasashen" duk Wannan zancen a zuciyar sa yake sakawa.

Yana cikin zancen zucin nasa ne muryan Jehan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login