Showing 186001 words to 189000 words out of 194715 words
sauke dai'dai lokacin kuma ruwan shinkafa data ɗaura a gefe ɗayan gas ɗin ya fara tafasa, store ta nufa tana faɗin "Bari na ɗebo shinkafa" shiru Jelly tayi bata amsa ba
Hajiya na shiga store Jelly ta ɗauko goran plate wash wani omo ne na wanke wanke, dan taga Hajiya ta saka su curry black pepper da sauran su, kuma taga kaɗan kaɗan Hajiya ta saka, ita kuma bata son harkan abu kaɗan tafi son dayawa shiyasa Hajiya na shiga cikin store ta ɗauko goran plate wash dake kusa da pots da Hajiya ta wanke yanzu, dan a tunanin ta shima kayan haɗin miyane
Buɗe miyar tayi ta zuba mai ɗan yawa sannan ta gauraya miyar, ta mayar da plate wash ɗin ta ajiye a in da ta dauko, ta ɗauko ledan gishiri shima ta zuba ta ɗan kara su carry da duk wani abu da Hajiya ta sa a miyar, jin Hajiya na zuwa yasa tayi saurin gauraya miyar ta mayar ta rufe tana jin daɗi ta zuba abubuwa dayawa dan ita bata son har abu kaɗan tafi son taga komai yaji sosai zam zam.
Koda Hajiya ta dawo bata wani lura da Jelly ba kawai ta ci-gaba da aikin ta, har suka kammala, da Hajiya tazo zuba abincin a cikin warmers data buɗe miyar taga ya ɗan canza kala amma da yake hankalin ta baya wajen tana sauri mangariba yayi zataje tayi wanka dan Abbo ya kusa dawowa hakan yasa ta zuba abincin kawai ta kwasa suka wuce palo
A saman table ta jere komai sannan tace Jelly ta zauna bari taje tayi wanka, ba musu Jelly ta koma ta zauna saman sofa tana tunanin ko dai ta ɗauko su curry ɗin nan ne ta kara dan kamar wadda ita ma tasa yayi kaɗan, sai sake sake take a zuciyar ta ita kaɗai, har Hajiya tayi wanka ta fito tace taje tayi alwaya suyi Sallah
Ba musu ta tashi ta nufi toilet nata ta ɗauro alwalar ta kamar yadda Hajiya ta koya mata sannan ta fito ta zo sukayi Sallah tare da Hajiya a palo.
Sai bayan sallar issha sannan Abbo da Nawid suka shigo, wanka sukaje suka fara yi first kafin su zo saman table su zauna, Hajiya ita tayi serving nasu dan tace bata son masu aiki ita take komai da kan ta.
Abbo shi ya fara kai abincin bakin sa, a ɗari ya tofoshi waje har yana kakarin amai, zaro ido Hajiya tayi tana tambayar menene a ruɗe da hannu ya mata nuni da ta ɗanɗana abincin taji dan ya kasa magana abincin har ɗaye fatar baki yake saboda gishiri da plates wash da kuma su carry da Jelly ta banka a ciki yayi yawa over yana ɗaye harshe
Nawid kam tun da yaga haka sai ya fasa kai abincin bakin sa ya mai da ya ajiye, Hajiya kuma ɗaukan spoon tayi ta ɗeba abincin ta kai bakin ta, a sukwane ta fito da shi waje tana salati, ita kam Jelly dama tun da suka zauna ta fara cin naman kasa hankalin ta baya kan su kwata kwata, sai bayan ta cinye cinyar kazar ne ta ɗauki spoon ta ɗebo shinkafar da labcecen miya ta kai bakin ta
Wani ihu ta fasa wadda yasa Hajiya da Nawid miƙewa suna kokarin gudu, shi ma Abbo ya tsorata da ihun sai dai bai miƙe ba.
Rai a ɓace Nawid yace "Ke baby me haka?" Abbo ne ya daka masa tsawa "Haba Nawid me ta maka zaka mata wannan tsawa haka?!!" Zaro ido waje Nawid yayi yana mamakin abun da Abbon yayi, Abbo bai taɓa yi masa tsawa ba ko da wasa, hakan da yayi yanzu ya kara ɗarsa zargin sa a zuciyar Nawid ɗin, ita kan ta Hajiya sai da tayi mamaki a wannan karon Abbo bai taɓa yiwa Nawid tsawa ba sai yau
Abbo kuwa ganin Hajiya da Nawid sunyi mamaki ne yasa yayi saurin basar da maganar da cewa "Ku tashi muje restaurant kawai muci abincin tunda wannan kam dai ya tashi aiki, sannan Nawid kai kuma ka dai na yiwa baby tsawa baka ganin tana cikin ciwo ne?" Shiru Nawid yayi yana tunanin yadda zan binciko me Abbo'n sa ke nufi da Jelly, dan yasan ba haka kawai zai rinƙa yin wayen nan abubuwa a kan taba, Nawid ba yaro bane a kalla zai kai 26 years a duniya gashi da saurin fahimtar abubuwa
Ganin sunyi shiru basu da niyar tafiya ne yasa Abbo ya miƙe yana faɗin "Muje ko?" Jiki ba kwari Hajiya ta wuce bedroom nata tana faɗin "Bari na ɗauko mayafi" to kawai Abbo yace suka wuce waje shi da Nawid ita kuma Jelly tana zaune tana cin namar gazan ta, dan tun da ta saka shinƙafar a bakin ta tayi wannan ihu daya razana su Hajiya sai ta ci-gaba da cin namar ta kawai bata ma san da su Hajiya sun tsorata ba.
Jim kaɗan Hajiya ta fito sanye da mayafin hannun ta riƙe da mayafin Jelly, zuwa tayi ta sanyawa Jelly mayafin sai faman figar nama Jelly keyi, riƙo hannun ta Hajiya tayi suka bi bayan su Abbo, motar Nawid suka shiga shi yaja su suka tafi zuwa restaurant ɗan cin abinci, sai mamaki Hajiya take, me ya samu abincin da ta girka.
To masu karatu mu leƙo Daular mutuwa mu dawo
👹DAULAR MUTUWA👹
Sosai duna yake aiki a kan yadda zai samu ya kuɓutar da Rimsha daga ɗakin duhu na Queen, baba da Mustapha kuwa sun dukufa sai addu'ar fatan nasara suke masa, Ayla da Kausar ma ba'a bar su a baya ba, sosai sukewa Rimsha addu'a a zuciyar su dan ba daman kiran sunan Allah a baki, amma fa sosai Ayla ke kuka duk lokacin da ta keɓe ita kaɗai sai tayi kukan rashin Rimsha, yan kwanakin kalilan da sukayi da Rimsha sunyi sabo sosai wadda rabuwar su abune mai matukar wuya wadda zai yiwa ko wannen su balai ciwo, Ayla akoi ta da hakuri ga kirki da son mutane shiru shiru bata da hayani ta.
Allah sarki Ayla baiwar Allah ko ya akayi tazo daular mutuwa ita kuma oho, sai dai ku kasance da alkalamin princess Teema dan ita kaɗai ce zata warware muku komai sannu a hankali, ammafa akoi cakwakiya, yanzu wasan zai fara.
To masu karatu kuma sai ku taya Rimsha'n ku da Addu'a kuyiwa duna addu'ar fatan nasara na barku lafiya, gobe idan Allah ya kai mu The beginning zai kare sai ku shirya, yanzu wasan zai fara bye sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu..
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪
💞Star Lady💞
TRIPLET'S💞
💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)
*Gargarɗi*
_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_
WhatsApp me for more information 09162620621
Episode 42-43
💞KADUNA GIDAN ABBI💞
Tun da Abbi ya ɗauko daddyn Jelly Aafia ta ɓata rai alamar bata ji daɗin zuwan sa gidan ba, dan shi ba fita zai yi ba yana gida ko da yaushe, idan kuma yana gida basu isa su fita da shigar da suke soba, zai takura musu lallai su saka hijabi idan kuma suka ki zai sanar da Abbi in suka masa rashin kunya kuma sun san Abbi uban su zai ci a kan ɗan uwan sa
sai faman hararar dad Aafia take, ji take kamar taje ta shaƙe sa dan haushi, shikuwa dad sai faman jan su a jiki yake da wasa da dariya wai ko zai samu raɗaɗin ciwon rashin Jelly ya ragu masa a zuciyar sa, sai dai bai samu haɗin kan Aafia ba domin ko magana ya mata ciki ciki take amsawa ɗan gara Umaisha ma tana amsa masa da gimamawa a matsayin sa na bappan ta kuma a matsayin baba ta ɗauke sa.
Abbi da kan sa ya kira Akila a waya ya haɗa ta da daddyn Jelly, sai murna Akila baiwar Allah mai kaunar yan uwan ta, sosai ta rinƙa dariya har da hawaye jin daɗi, ko da ta tambayi daddy ina Jelly sai yace mata tana barci, Akila bata ji daɗi ba taso yin magana da jelly amma haka ta hakura tace wa dad zata kira gobe da safe dan su gaisa da jelly, to kawai dad yace mata zuciyar sa na kuka, a pannin su Imran ma Abbi ya haɗa su da dad, da suka tambayi Jelly dad yace tana barci, Imran kamar zai yi kuka yace wa dad shikenan sai da safe zai kira, shima ya kusa dawowa saura masa kwana biyar, sosai daddy ya masa Addu'a da fatan alkhari, daga haka sukayi sallama, kowa ya kwanta, asuba ta gari.
Washegari kuwa tun karfe 7 su Umaisha suka shirya dan su bar gidan da wuri kar dad ya tashi barci ya hana su fita da kalar kayan da suke son sawa, Umaisha bata cika saka riga da wando taje school ba, sai dai tasa atamfa ko lace amma yau da gangan ta saka riga da wando wadda suka kama ta sosai duk dan tasa Akil yaji ya tsane ta yaji haushi tun da yace mata yana shigowa Kaduna gidan su zai fara zuwa gashi kuma da bala'i kishi, ita kuma Aafia yau doguwar riga na kanti tasa, kasan cewar rigar jikin ta kamar roba yake hakan yasa ya kamata sosai, duk wani sura na jikin ta ya bayyana, haka suka fito sauri sauri kamar marasa gaskiya suka fice, sukaje kowacce ta shiga motar ta suka bar gidan suka nufi school.
A ɓangaren Aunty kuwa lokacin da Abbi ya samu labarin juna biyun ta ba karamin murna bawan Allah nan yayi ba, sai dai abun da basu sani ba, su suna nan suna murna Aafia da Rufee suna can suna shirya yadda za'a zubar da ciki , wannan shine cakwakiya muje dai zuwa dan ganin yadda wannan rikici zai kare.
Daddy kuwa kwata kwata bai ji daɗin zaman gidan Abbi ba, dan yadda Aafia ke masa baya jin daɗi, ji yake kamar ya koma Kano ko kuma ya tafi gidan su Imran wato gidan babban ya'yan su dan ko ba komai Imran da Akila suna kaunar sa, amma kuma idan ya tuna yadda yayan sa wato Abbi yayi tattaki daga nan Kd har Kano yaje ya ɗauko shi, sai yaji kamar idan yace zai bar gidan bai yiwa Abbi adalci ba, hakan yasa ya hakura ya danne zuciyar sa ya ci-gaba da zaman hakuri, dan zama da su Aafia sai ka dangana da hakuri in ba haka ba zuciyar ka zata fashe.
Mu leƙo Jehan mu dawo
💞KATSINA💞
Ba karamin daɗi Jehan taji ba ganin yadda jikin mum ya fara kyau har wani cool murmushi take sake wa, shima Sadiq yaji daɗi sosai sai addu'a yake ta zubawa mum gwaggo na amsawa da Amin, yau sai karfe 9 na dare sannan su Jehan suka baro asibiti saɓa nin kullun da suke dawowa da yamma, yau saboda murnan anyiwa mum aiki jikin ta ya fara kyau yasa basu kamo hanyan dawowa da wuri ba.
Bayan sun baro asibiti, suna tafiya suna yar hira suka nufi bakin hanya dan taran abun hawa, basu kai ga isa bakin hanya ba, wasu mata sa irin ɓata garin nan suka tare su hannun su rike da sanduna irin goran nan, sai warin sigari wato taba suke da alama wasu daga cikin suma a buge suke
Tsawa suka dakawa su Jehan a kan su kawo wayoyin su da kuɗin dake jikin su, ba karamin tsorata Jehan da Sadiq sukayi ba, har wani fitsari Jehan take ji yana kokarin zubo mata,
Amma saboda karfin hali irin na Jehan sai ta ɗaure fuska tace "Kai nima fa yar daban nan ne ta bugawa a jarida kuma idan baku sani ba ku sani yaya na ƙasurgumin ɗan daba ne na gaske, shine kamar ni kan war sa zaku tare kuce na baku waya ta to wlh sai na faɗawa yayana kuma duk in da kuke sai ya nemeku ya muku yan kan rago" kasan cewar dukan su basa cikin hayyacin sosai, zokaga yadda ake shiga tashin hankali, har kasa wayan nan yan iskan gayun suka duka suka fara bawa Jehan hakuri dan tsoron kar ta faɗawa ya'yan ta dan yanzu ma bala'i dake cikin garin Katsina kawai ma ya ishe su inaga kuma ta sake faɗawa yayan nata abun ai ba zai yi kyan gani ba, su daman irin yan iskan nannen masu neman kuɗin sayan sigari da wiwi kawai ba dan wani abu suke tare mutane su musu kwace ba.
Jehan manya Jehan DPO an samu dama har da ja musu kunne da yi musu last warning a kan idan ta sake jin sun sake yin wani abu makamancin haka tofa kamar a kunnen yayan tane ne, sosai suka mata alkawari a kan bazasu sake ba, shidai Sadiq bawan Allah yanzu Jehan ta dai na bashi mamaki ma ya fawwalawa Allah lamuran sa yana bin Jehan a duk yadda ta bi da shi, sai dai ɗan zaman sa da ita yasa shima ya fara cire tsoro a ransa, yanzu yana jin jarunta har cikin jinin jikin sa.
Niko nace tab aiko baka san itama duk burga bace a fili amma daga ta ciki har fitsari take, gara maka ma ka ci-gaba da jin tsoron ka dan ba ilimi gare kaba karka je ka taɓo abun da ya fi karfin ka kasha dukan mutuwa a banza, ita Jehan akoi ilimi sai ta karanci yana yin mutun take yanke masa irin hukuncin da zata masa, kai kuma ba ilimi kawai zaka afkawa abu hmm akoi matsala!!!.
Sallamar guys ɗin Jehan tayi sannan tace "Muje Sadiq" sai godiya guys ɗin ke mata tare da fatan alkhari na dole, wannan shine idan ba kayi sharan masallaci ba kayi na kasuwa.
Suna tafiya a hanyane kafin su kai bakin titi Sadiq yace "Jehan me yasa zaki yi karya? Meyasa zaki danganta kan ki da yan daba?" ba tare da ta kalle saba tace "Akoi wuraren da yin karya ya halatta wadda idan kayi su baka da laifi har gaban Allah, ciki kuma har da wanda nayi yanzu, kayi karya domin ka kare rayuwar ka, zaka iya karya dan ku zauna lafiya a gidan ka, zaka iya karya dan ka sulhun ta mutane biyu da suke faɗa ko gaba, to a nan in da suka far mana nan kaga ai bumu da mafita dole mu musu abun da hankalin su zai kama, a yadda suke yan iskan garin nan, ba Allah da annabi zaka faɗa musu ba, domin bazasu saurare ka ba, dan ba hanyar Allah suke ba, amma idan ka faɗa musu kana da wanda ya fisu zama ɗan kwalta zasu nitsu ga misali dai ka gani, ko wani ɗan adam akoi direction ɗin da yake tafiya a kan sa, to kai ma dan ku zauna lafiya kasa ya yarda da abun da kazo masa da shi sai ka ɗauki direction ɗin da yake kai kaima ɗin, ba wai zakayi hakan dan kazama irin sa ba ko dan ka saɓawa Allah no a'a zakayi hakan ne dan kasa ya fahimci abun da kake nufi koda bai yi niya ba, yanzu yadda suka tare mun nan kana tunani idan shekara zamuyi muna ce musu dan Allah zasu hakura su kyale mune?" Girgiza mata kai yayi alamar a'a, kasan cewar yanzu Jehan Hausa ya ɗan fara zama zam zam a bakin ta tana ɗan yi magana da Hausa sosai tana ɗan kwaɓawa da English nata
Ci-gaba da magana tayi "Yauwa ashe ka gane ko kwana zamuyi muna haɗa su da Allah baza su kyale muba, dan ba aikin Allah suka fito yi ba, saboda babu in da Allah yace ɓarawo yaje yayi sata, hasalima sai dai in da yake sanar da mu hukuncin da za'a wa ɓarawo mai cin hakkin bayin Allah, ajiye wannan zancen muje in da nake so ka fahimtar ko dan ɓacin rana wata rana, aduk lokacin da wasu yan iska suka tare ka, ka nitsu sosai ka duba yanayin su a kan wani tsari suke, misali kaga wayan nan yadda suka tare mu ai sun nuna mana su yan daba ne, shiyasa na musu amfani da sunan ɗan ta'adda wato baban yan daba, amma idan ka duba kaga cikakkun yan iska ne masu son iskanci kamar ni mace ai nuna musu zan yi iskancin nima nake so kamar yadda mukayi da Farooq sai ka rabu da su lafiya ba tare da sun maka illaba, koda sun karɓa maka wani abun ba zasu maka illaba" shi dai Sadiq bin ta kawai yake da to domin wani Hausar a kwaɓe take wani kuma tana saka turanci
Shiru ya ɗan yi kafin yace "Jehan aina kika san yan daba ne ma? Ke da lokacin da kuke tare da daddy kullun kuna gida baku san wahala ba baku fita waje" guntun tsaki taja kafin tace "Na san shi mana a media before ai ina da waya kuma ina hawa net" shi dai Sadiq tun da ba sanin net ɗin yayi ba sai yayi shiru bawan Allah bai taɓa riƙe karamar waya bama bare babba, sun tsaya suna ta hira sai wucewa taxi suke saboda dare, da kyar suka samu wani suka tara zuwa gida.
Koda sukaje gida basu ci abinci ba dan sunci a asibiti da gwaggo wadda Jehan ta sayo musu, karatu kawai Jehan ta koyawa Sadiq da Hanan har da Yusuf kamar yadda suka saba, Sadiq yana son karatun sosai shiyasa ya mai da hankalin sa sosai yana ɗaukan abun da take koya masa musamman fannin addini yana kokari