Showing 129001 words to 132000 words out of 194715 words
a kan abubuwa da dama, ni bari na kira yaya Irfan ɗin ma na lafaza shi ya bani kuɗi koda 200k ne dan na ɗan yi broke" cikin sauri Aafia tace "Ai kuwa kin tunamin zan biya ta bank na cirowa Rufee 100k ɗazun ta kirani tace tana son 100k kuma kashe take bukata" turɓune fuska Umaisha tayi kafin tace "Kuma sai ki bata? Sai kace wata uwar ki, nifa wlh Rufee nan bata burgeni kawai dai ban son nuna mata hakan ne yasa nake biye mata, amma dai natsane ta wlh" "wlh Umaisha idan kika sake shiga tsakani na da Rufee sai ranki ya ɓaci, ba ruwan ki da ni" ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki, ta wuce wajen drawer kayan su, ta ɗauko wasu riga da wando ta sanya
kayan sun matse ta sosai, sannan ta ɗauko suwaga bag ɗin ta ta sanya Booth a kafar ta, wani ɗan handkerchief fari ta ɗaura a kan ta, sannan ta ɗauki key ɗin motar ta, a fusace ta fice daga ɗakin, ko breakfast ba ta tsaya ta yi ba bare kuma yiwa su Abbi sallama, haka ta wuce ta fice daga gidan, dan tana da class 8 dai dai.
Miƙewa Umaisha tayi ta kwanta dan bata da class ita sai 11 dan haka sai tayi kwanciyar ta sai 10 zata shiga school.
Bari mu leƙa Washington DC mu dawo.
💞WASHINGTON DC💞
12:20am
Zaune James yake a gefen Musharraf yana kallon ruwan da daddy ya sake kara masa, bayan na jiya ya kare, a hankali Musharraf yace cikin harshen turanci "Amma gaskiya mahaifiyar ku tayi Sa'ar aihuwa, kuna da kirki sosai, gaskiya naji daɗi taimakon da kuka min kuma ina godiya" ɗaure fuska James yayi kafin yace "Mmm ya ma kake da suna? This Your name is seems to be difficult for me, I will just call you uncle kawai, kar ka sake maganar mum a gidan nan, idan ba haka ba zaka mutu lokacin ka bai yi ba" zaro ido Musharraf yayi yana mamaki, cike da tsoro yace "Please may I know what happened to your mum, why did you say kar na sake maganar ta?" Kara ɗaure fuska James yayi kafin yace "Because we hated her, bamu son maganar ta, kai ma i don't know they reason why ka shiga rai na har nake iya baka amsa a kan ta, kuma nayi mamaki yadda a kayi daddy da lion duk suka yarda a kan ka zauna a gidan nan sai ka samu lafiya ka tafi, shawarar da zan baka shine karkayi mistake kayi zancen mum a gaban lion and tiger, dan zasu iya kashe ka" shiru Musharraf ya ɗan yi kafin yace "okey ina godiya, amma dai ban ji daɗi ba domin uwa ita ce jigon ko wani ɗan adam" da sauri James ya ansan da cewa "except our mother, my mother she's a wicked, ba mutuniyar kirki bace that's why we hated her, ta mana abubuwa na mugun ta dayawa" Shiru Musharraf yayi a ran sa yana son sanin me Mahaifiyar su ta musu haka suka tsane ta.
Miƙewa James yayi ya nufi hanyar fita daga room ɗin yana faɗin "Good night, daman i came to see your body ne" shi dai Musharraf ya shiga duniyar tunanin me mum ɗin su James ta musu suka tsane ta haka.
James na fitowa ya nufi part na sa, zai wuce ya hango hasken wuta a palon kasa wadda ko bai tambaya ba yasan lion ke cin abinci, dan wani time ma har 1 na dare yake kaiwa kafin yaci abinci.
Fasa shiga part nasa yayi, ya sauko kasa, ya nufi wajen Romeo dake zaune saman ɗaya daga cikin kujerun table yana latsa system, jikin sa na sanye da kayan barci, farare kal masu laushi marasa nauyi, riga ne da dogon wando, ya kulle dark black curly hair sa nan a baya, while wannan guntu na gaban goshin sa yana nan bai ɗaure shi ba, yana kwance masa a face ɗin sa, hakan ba karamin kyau ke karawa face ɗin sa ba, sai wani fitinanniyar kamshin perfume dake tashi a jikin sa, ya kafe system ɗin dake gaban sa saman table da dara daram blue eyes ɗin nan nasa, kasan cewar dare ne kuma wutar da ya kunna a palon sky blue ne ya kashe farin wutar dan yana son hasken light sky blue, shiyasa wutar part nasa dukka sky blue ne, hakan tasa kwayar idon sa suka kara haske sosai, har wani kyalli suke, yana aiki a system yana ciza red lips na sannan da kyawawan fararen hasoran masu kama da farin auduga, sai kyalli suke suna ɗaukan ido, while lips na sa kuma, duk in ya ciza su sai sun kara ja, kamar lipstick yake sanya musu, gashi sai faman ciza su yake alamar aikin da yake yana ɗan caza masa kai.
Ga jibga jibgan bodyguard ɗin sa nan a tsaye a kan sa, sun zuba masa duk wani abincin da zai buƙata a plate sun jere masa, suna jiran kawai yaci.
Kujerar kusa da shi James yazo ya zauna yana faɗin "How are you lion?" Shiru Romeo ya masa kamar bai san da zaman sa a wajen ba, aikin sa kawai yake, hannu James ya sa ya fara ɗaukan fruits yana kai wa ɗan bakin sa, shi kuma Romeo sai faman aiki yake.
Kai James yasa ya ɗan leko system ɗin Romeo yana faɗin "What are you going ne" kara waro ido James yayi ganin hoton manya manyan shuwa gaban nin su a cikin gaban screen ɗin system ɗin, da alama aiki Romeo yake a kan su, lokacin guda hankalin James yayi mugun tashi, tsoro ya bayyana karara a kan face nashi, wata irinyar zufar wahala ne ta fara karyo masa daga gefe da gefen kunnen sa, ji yayi kan sa na sara masa, har wani duhu duhu yake gani, tunani ya fara yi, me ya kawo hotonan manya manyan jiga jigan ogan nin su kuma a system ɗin Romeo, wadda ko shi kan sa bai taɓa haɗuwa da su fiska da fiska ba, sai dai suyi videos call idan za'ayi wata harkallah, lokaci guda wani tunani ya faɗo masa, to ko dai taron da zasu yi na shakaran nan ne Romeo ya samu information a kai, tun da ogan sa yace masa a wannan taron gaba ɗaya manya manyan jiga jigan ogan nin su zasu halarci taron, dan za'a karrama wasu daga cikin su, tab lallai a koi matsala, in dai Romeo yasan da taron dole zai sa yaran sa su wa taron dirar mikiya su kashe kowa, gashi ni kuma ban isa in ce ba zan halakci taron ba, dan ina ɗaya daga cikin wayan da za'a karawa girma a karramani, wannan taro na shekaran nan ni za'ayiwa.
Sosai James ya shiga damuwa yana ta zancen zuci bai san lokacin da Romeo ya kammala aikin ba, sai dai yaji sanyayyar murya Romeo yana faɗin "What are you going here?" Yar firgita irin na marasa gaskiya James yayi, har sai da yasa Romeo kara zaro blue eyes nasa yana kallon shi
Zubawa kumin dake gangarowa daga gefe da gefen kunnen James ɗin Romeo yayi, slowly ya mai da blue eyes na sa saman manya manyan Ac dake palon, dukka Ac a kunne suke ga palon da sai yi, amma ya akayi James ke zufa haka, kwata kwata Romeo bai kawo komai a ran sa ba, calmly ya bawa bodyguard ɗin dake tsai tsai ye a kan su, umarnin a kan su kara gudun Ac dake palon dukka, jikin su har kerma yake wajen aikata abun da ya sanya su
Kai kallon sa yayi kan abin cin da suka zuba masa, hot coffee kawai ya ɗauka, cikin nitsuwa ya fara kai cup ɗin ɗan bakin sa yana kurɓa yana cirewa cikin class da nitsuwa.
Da kyar James ya iya sai ta voice na sa ya fara magana "Please lion i want to know something about this pics that I saw on your system now" shiru Romeo yayi na yan mintoci, da kamar ba zai yi magana ba, sai kuma yace "What did you want to know about them?" "Everything" James ya faɗa cike da tsoro,
Ansan tissue da bodyguard ke miƙa masa Romeo yayi, ya ɗan goge kyawawan lausasan red laɓaɓɓan sa, kafin ya juyo da dara daran blue eyes nasa kan James ɗin, calmly ya fara magana "they are the most notorious criminals in the world, I'm investing about them, I want to know where they are residing and I want 2 know who and who theyre working with, and which organisation is funding them" kara tsorata James yayi dan yasan halin Romeo sarai idan har ya sa aiki a gaba tofa tsab yake kammala aikin cikin kankanin lokaci, sai dai daɗin abun ba shi yake fita aikin ba, yana zaune a gida yana fama da system yake bada command yaran sa suna aikatawa, sai dai kuma wani lokaci Tga ke jan ragamar tawagar, abu ɗaya James ya tuna wadda ya sanya shi sakin murmushi lokacin guda, tunawa yayi da cewa, da fake face yake amfani a wajen aikin nasu, dan haka ko Romeo ya binciko hotonan sauran criminals ɗin ba zai gane sa ba, saboda fake face, kuma daman yayi tunanin wannan rana zata iya zuwa shi yasa tun farko yayi dabarar using fake face, a wajen dan gudun kar Romeo ya iya gane sa.
Shi kuwa Romeo juyawa yayi ya ci-gaba da shan coffee ɗin sa yana tunanin wa ya kamata ya naɗa wadda zai ja ragamar aikin nan, dan yanzu gaba ɗaya tun da Tga ya bugi James yaji baya son sa, duk da kanin daddyn su ne.
Sun yi shiru dukkan su kowa da abun da yake tunawa a ransa.
Wayar James ne ta katse musu shirun ta hanyar fara ringing, a sukwane ya ɗago ya kalli Romeo dan yasan abokan harkallan sa ne kawai ke kiran sa cikin daren nan, to ya zai yi idan Romeo ya ansa wayar yayi picking call ɗin, ko ya tambaye sa wanene ke kiran sa, sai dai kuma shi Romeo ko a jikin sa kamar ma bai ji ringing na wayar ba, sai dai ya ɗago kyakkyawar farin hannun sa, ya duba time a diamond watch nasu na Triplets, 01:05am ci-gaba yayi da shan coffee ɗin sa, hakan ba karamin jefa James yayi cikin ruɗani ba, dan yasan shirun Romeo ba karamin abu bane, kuma gashi ya duba time, abun ku da mara gaskiya duk sai ya tsargu, tun Romeo bai tambaye sa ba sai yace abokan sa ke kiran sa dan bai je party su ba, shiru Romeo ya masa kamar bai ji me ya faɗa ba, ya ci-gaba da shan coffee ɗin sa.
Shi kuwa James duk a tsarge yake, yabi ya takura kan sai aikin zufa yake ya sanya wa kan sa tunani da damuwa, while shi kuma Romeo ko a jikin sa, kuma bai kawo komai a ran sa ba, saboda ya yarda da su.
Sai bayan ya kammala shan coffee ɗin sane ya miƙe, cikin sauri bodyguard suka bashi tissue paper ya goge bakin sa, ya wuce ya nufi sama yana faɗin "Stop telling me what I did not ask you" yayi maganar in a cool voice, ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi part nasa, yana taku irin na jaruman maza, masu izza da nitse.
Sosai James ya sake shiga damuwa, ɗan wannan cewa da Romeo yayi ya daina faɗa masa abun da bai tambaye shi ba, hakan ya kara sa shi cikin damuwa, to kenan me Romeo yake nufi, while shi kuma Romeo ko kaɗan ba da wata manufa ya faɗi hakan ba, kawai shi baya son a rinƙa masa maganar abubuwan da ba shi ya tambayi mutun ba ne, shi kuma James tsabar rashin gaskiya ya sashi faɗin abokan sa ke kiran sa kamar an tambaye sa.
Jiki ba kwari ya miƙe ya nufi bedroom na sa ransa cike fal da tunanin ko dai Romeo ya fara zargin sane.
Yana tafiya suma bodyguard ɗin suka wuce nasu bedroom ɗin dan suje suyi barci su huta aikin su na yau ya kare sai kuma gobe.
Washegari gari ta kama Sunday, tun 8 na safe daddy yayi shirin zuwa church shi da Uncle Herry, da Tga, da James, da John da Jay, sai dai me shi dai Michael yana zaune a palo yana latsa wayar Romeo ko alamar shirin zuwa bai yi ba, while shi kuma Romeo yana lafe saman lallausan katafaren gadon sa yana sharara barci, ya ja lallausan bargon ya rufe kan sa, su daddy sun gama shiri suna jiran su.
Da dai Jay yaga Michael fa bashi da niyar tashi yaje ya shirya sai yace "Michael we are waiting for you to ga to church" shiru Michael ya musu kamar bai ji me suka ce ba, ya ci-gaba da latsa wayar Romeo yana ɗaure fuska, cikin muryan rarrashe cike da so da kauna dad yace "My tiger we are waiting for you" cikin tsawa Micheal yace "Dad I can't go anywhere, I dnt want to waste my time going there, I have a lot of important thing to do, so please leave me!!!" tashin sense, zaro ido daddy yayi jikin sa har kerma yake yace "Michael are you heard what you said, I you our of sense?" Karo na farko Michael yaja dogon tsaki, dan shi ba mai jan tsaki bane.
Kallon James dad yayi jikin sa sai kerma yake, dan tsoron kar pasto ya tsinewa Michael su shiga uku, daman ga Michael ba wani isasshen lafiya gare sa ba, idan Pasto ya tsine masa ina zasu sa ran su, "James go and call lion for me" zama James yayi kusa da Michael yana cire suit ɗin jikin sa yana faɗin "I remember nima ina da abun da zan yi mai muhimmanci, lion kuma yana barci zaka iya zuwa da kan ka, ka tashe sa, kuma daga yau ni ina ga canza church za muyi, dan wannan Pasto he doesn't know anything, makaryaci ne kawai, duk abun da ya faɗa maka last week a kan mu karya yake, zai wani ce maka wai muna rayuwar farinciki da murna, kuma bamu wani aikata abun da ba dai dai ba, tun daga lokacin nasan karya yake saboda ni jiya da kyar nayi barci saboda damuwa" juyowa Michael yayi ya bawa James hannu suka tafa, kamar muna fukai, Michael yace "Well said my blood, nima saboda karyan sa yasa na dai na yarda da shi, kuma naji na tsani duk wata addni ma, dan makaryata na ɗauke su" daddy ya tsorata sosai, shi tsoron sa ɗaya kar pasto ya tsine wa Triplets ɗin sa, ya shiga uku, dan su kaɗai gare sa, sune jin daɗin sa sanyin idanniyar sa, duk da tsufar da ya fara yi hakan bai hana ya haura sama da gudun sa saboda damuwa ba. Kai tsaye part na Romeo ya nufa,
kallon Michael James yayi kafin yace "What are we going to do now, dan daddy yaje report na mu ne wajen Romeo kuma ni gaskiya a hate this pasto canza church zan yi" kashewa James ido Michael yayi kamar wasu muna fukai abun ka da Triplets, nan take Michael ya sakewa daddy wasu shegun kwari masu cizon bala'i, duk in da suka cize ka, tofa sai wajen yayi sati yana kumbura yana maka azaban raɗaɗi, gashi basu da magani, wajen yayi ta maka raɗaɗin zafi kamar cizon kunama ka rasa ina zaka sa ranka kaji sanyi.
Dad yana kokarin shiga part ɗin Romeo kwarin suka isa gare sa, kai tsaye cikin suit ɗin jikin sa suka shige gasu da yawa, haka suka fara ɗalla masa cizo, ihu ya fara yi, ya fara cire kayan jikin sa, dariya Michael ya fara yi, abun da bai taɓa yi ba a rayuwar sa dariya, saboda mamakin ganin dariyar Michael ya hana su Uncle Herry jiyo ihun daddy, while shi kuma James tausayin daddy yake, amma basu da zaɓi dole su rufewa daddy baki, ko ya dai na takura musu a kan zuwa Church ɗin nan dan basa son ganin Pasto.
Tun daga saman staircase daddy ya fara birgima a kasa, har izuwa kasan stair ɗin cikin palon, sai ihu yake yana kiran sunan Jesus, a guje su Uncle Herry sukayo kan sa suna tambayar lafiya, nan suma James ya sake musu nashi kwarin, zo kaga yadda ake rige rigen cire kaya, tuni sunyi wurgi da Bibles dake hannayen su, sun fara birgima suna ihu, shi kam Tga ma nashi yafi yawa dan haushin sa James ke ji, sai dariya Michael ke ɓaɓagawa kamar zararre.
Daddy gwanin ban tausayi tsohon nan, duk wayan nan kwari sun cize masa fuska, fuskar ta kunbura sumtum kamar ruɓaɓɓiyar alale, abun ku da fatar Bature ba quality sosai, gashi sai cizon sa suke, shi kam John bayan ihu har da zagi yake zubawa kwarin, shi kuma uncle Herry tsinuwa yake ta aikawa kwarin ba iya ka da turanci, duk kwarin sun kunbura musu jiki. Yau har da yaren mahaukata su kayi, ba iya turancin kawai ba
Uncle Tga bai ankara ba kawai sai yaji kwarin sun shige cikin Short ɗin sa, dai dai sai ti suka samu suka fara kai masa harbi da cizo, kuma James ya tura su saboda mugunta.
Wani mahaukacin ihu Tga ya fasa tare da miƙe wa kamar mahaukaci haka ya bazama, bai san in da ya nufa ba, saboda azaba, Allah sarki bawan Allah, sai gudu yake yana tsalle kamar doki, ya kan kame wajen, kai tsaye ya haye saman bene, ai ko awannan gaɓar na Tga sai da ya sanya James ma dariya mugunta, daman shi kam Michael kamar zararre ya dawo saboda dariya, uncle tga kuma ya kara haukata sa da dariyar, har da sulalowa kasa daga saman sofar saboda dariya. Michael akoi iya dariyar mugunta
Kai tsaye bedroom na Romeo Tga ya nufa cikin fitar hayyaci da azabar raɗaɗi, ya manta in da ya nufa, yafi abun da yake gudun wa bala'i, dan in ya kuskura ya tashi Romeo daga barci, hmmm.....✍️
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya