Showing 60001 words to 63000 words out of 194715 words

Chapter 21 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

967

ba ya samu ya kammala school ɗin, aiki ne dai kawai bai fara ba kuma baya ra'ayi yin koma ne hutu kawai yake sonyi a gida shi kuma fa, wuce wa Michael yayi ya fice daga wajen ya nufi bedroom na shi.

A hankali shi ma James ɗin ya miƙe ya wuce nashi bedroom ɗin dan yaje yayi wanka.

After some hours.

James ya fito sanye da wandon jeans baki da t-shirt navy blue masu bala'i kyau da tsada sai kamshi yake zubawa, kai tsaye parking space ya nufa, yaje ya shiga motar sa kirar *Bugatti centodieci* ya tayar

ko da yazo fita parking space ɗin sai da wan nan na'uran ta faɗi sunan motar da number ta da kuma sunan wanda ya ke cikin motar, san nan gate ɗin parking space ɗin ta buɗe, James ya danna hanchin motar waje.

Yana fita ya saki kiɗa mai tashin kai yana kaɗa kan sa yana tuƙi cikin kwanciyar hankali.

Kai tsaye *medina Hotel* ya wuce, horn ɗaya yayi a bakin gate ɗin masu gadi wajen suka buɗe masa, ya kutsa hancin motar sa a ciki ya nufi parking space, yana kashe motar ba tare da ɓata lokaci ba ya fito tare da sanya fake face a face na shi dan kar kowa ya gane sa san nan ya shige cikin katafaren hotel ɗin.

Manya manyan Alhazawan kasar ne a wajen sunyi cincirindo shi kaɗai a ke jira daya iso gaba ɗaya sun zauna saman luntsuma luntsumar sofan dake cikin ɗakin hotel ɗin, cikin taku irin na jaruman maza ya kariso wajen, ya kara ɗaure fuakar nan tasa tamau, zama yayi gefen wani jibgegen Bature wadda da ka gansa kaga wadda Naira ta zauna ma sosai, ba tare da ɓata lokaci ba suka fara tattaunawa.

Almost 40 mins suna tattaunawa nawa kafin daga bisani wan nan jibgegen Baturen ya jawo trolley dake gefen sa ya buɗe zip ɗin ya fito da wasu pistol gun ya fara rabawa mutanen dake wajen, ko wan nan su yana amsa yayi godiya amma da a kazo kan James sai yaki ansa, kallon sa Baturen yayi tun kafin yayi magana James yayi saurin cewa "Ba zai yiwu na shiga gidan mu da gun nan ba, idan nace zan shiga da ita tofa sai an kama ni dan gidan mu na da tsaro sosai" jinjina kai Baturen yayi kafin ya mai da gun ɗin cikin a kwanakin ya ajiye yana tunanin wai ma James ɗan waye ne dan bai san asalin wanene James ba kawai harkalla ta haɗa su,

Cike da tunani fal ransa ya fito musu da wani abu kamar daskararren jini ne a ka yayyan ka, ko wan nan su ya amsa da fara'a amma ban da James shi fuska a ɗaure ya amsa, kallon su Baturen yayi san nan ya basu umarnin a kan su cinye abun, ba musu suka sanya a bakin su suka cinye, shiru ogan nasu yayi na yan mintoci kafin yace zasu iya tafiya sai a zama na gaba kuma, da sauri James ya miƙe kamar mara gaskiya ya bar wajen ya nufi motar sa ya shiga ya bar hotel ɗin da gudun gaske.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*ABUJA*

Zaune Rimsha take saman sofa mai zaman mutun 2 a palon kasa tayi shiru ta kura idon ta a kan makekiyar Tv dake kunne ana labarai a kan wan nan Baturen,
da sallama daddy da mum suka shigo Palon sai murmushi suke kai da ganin su kasan suna cikin farin ciki da annashuwa.

My siha a na kallon labarai a kan TGA ne?" Cewar daddy yayi maganar tare da zama kusa da ita, a hankali ta kwanto jikin sa tare da ɗago dara daran sleeping eyes nata cikin shagwaɓa tace "Daddy yau ba TGA nake kallo ba na asalin nake kallo GAR shi ne asalin General of the army R ɗin kuma ban san ma'anar ta ba" shafa kan ta yayi yana murmushi, zama mum tayi gefen ta tana faɗin "Ni Rimsha wlh bana gane wa mutanen nan naki yau kiga wan nan gobe wan nan to shi kuma GAR ɗin waye shi?" Miƙewa tayi zaune daga jikin daddy cikin sauri tace "Mum GAR shine asalin jarumi na ai shima TGA ɗin yana burgeni amma ba kamar GAR ba" jinjina kai mum tayi tace "Ni kam Rimsha ba abun da na gane game da wan nan bayanin naki kyale ni kawai muje a kina san kallon TGA" komawa Rimsha tayi ta kwanta jikin daddy tana faɗin "Nima mum ba wani gane wa nake ba suna rikita min kwakwalwa sai yau na lura da mai light blue eyes ɗin nan da mai light ash eyes ɗin ashe ba mutun ɗaya bane na gano gakan ne ta sunan su, mu kullun bamu duba suna kawai idan mun ga hoton shi kenan ban taɓa tunanin GAR su biyu bane sai yau sun caza min kai, mai light ash ɗin idon nan shi ne TGA mai light blue idon kuma shi ne GAR wato General of the army kenan kuma shi ne jarumi na, ban taɓa luraba sai yau, suna kama over idon su ne kawai ya ban ban ta su" shi dai daddy shiru yayi yana jin ta amma ba wai dan ya fahimci kan zancen nata ba, dan shi ba wani zama yake yana kallon labaran Usa Army's ɗin nan ba, ita dai mum amsa mata kawai tayi amma ba wai dan ta gane kan zancen nata ba, shiru gaba ɗayan su suka yi suka zubawa Tv ido suna taya Rimsha kallo, while ita kuma Jehan tana ɗaki tana zubawa Gwaggo shagwaɓa da iya shege.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*KADUNA*

Abba da Hajiya Umaiya sun manta komai da ya faru da su da rana a cikin gidan, sosai abokan Abba ke kiran sa a waya suna tambayar sa Alhaji Mustapha sai dai yace musu tun da ya dawo basu haɗu ba domin kuwa tabbas babu abun da Abba da Hajiya suka iya tunawa, shi Abba ma ya kasa tuna lokacin ma daya kamo hanyar Kaduna shi iya sanin sa yana Abuja bai san ya akayi ya dawo ba.

Kamar kullun bayan sun gama cin abincin dare suka wuce bedroom na Abba dan su kwata, da kyar Hajiya ta iya samu tayi wanka saboda kasala da take ji jikin ta duk zafi yake mata kamar wadda a kawa mugun duka, a ɓangaren Abba shima hakan ne gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, haka dai suka lallaɓa suka yi wanka tare da shirin barci suka kwanta.

Cikin dare sai juyi suke dukkan su sun kasa barci, dafe ciki Hajiya tayi kamar zata yi kuka tace "Abban Imran yinwa nake ji sosai kamar zan mutu" da mamaki ya miƙe ya kunna lamp na gefe da gefen gadon, abun ya ɗaure masa kai cikin kasalalliyar murya yace "Hajiya yinwa kuma?" Gyaɗa masa kai tayi alamar eh, yasha ruwan mamaki sosai dan basu taɓa jin yinwan dare haka ba

A hankali ya koma ya kwanta yana faɗin "Muna da sauran takeaway a palo ai kije kici ni zan sha Yoghurt dan nima yinwa nake ji kuma banson cin abinci da tsohon daren nan, idan kin gama cin abincin naki ki tahomin da L&Z Yoghurt mai sanyi guda ɗaya" to kawai Hajiya tace tare da sauƙo wa daga gadon ta nufi Palo.

Ko da ta shigo palo wutar palon a kashe, kai tsaye ta wuce wajen switch ta kunna wutar palon nan take haske ya gauraye ko ina a cikin Palon,

Waro ido waje tayi kamar idon ta zai fito waje ya faɗi kasa, nan idon ta ya mata arba da tashin hankali da kwakwalwa ba zai ɗauka ba, jibga jibgan mutane su uku ne zaune saman sofa jikin su duk jini idon nan nasu launin jini ga fuskokin su bakake kirin abun tsoro, wata yar kyakyawan matashiyar yarinya ce zaune a tsakiyar palon ta na fukantar kofar palon ta bawa Hajiya baya, ta dukar da kai kasa kamar tana cin wani abun,

cike da ruɗu da tashin hankali murya na rawa Hajiya tace "A..Ab..Abla" cikin sauri yarinyar ta ɗago tare da wayan nan dodan nin dake zaune saman sofa, tabbas Abla ce ke zaune tana cin namar mutane ɗanye idon Hajiya ya gane mata, kai kallon ta hajiya tayi kan abun da Abla ke ci,

razanannen ihu Hajiya ta fasa ganin namar jikin mutun Abla ke ci, sai lokacin Hajiya ta iya tuna abun da ya faru ɗazun, dan kuwa naman Jikin Zainab Abla ke ci, Hajiya na kokarin guduwa ta koma sama idon ta ya sauka kan wasu dodan nin dake zaune saman kujerun table suna cin ɗanyen nama ga face nasu abun tsoro idon nan nasu kamar zai fito waje, ga launin idon jawur kamar jini suna da katon hanci Kamar kofa ga girman baki kamar masai ga idon na su ma manya manya masu firgitar da ɗan adam, ihu Hajiya ta kuma fasawa kamar makoshin ta zai fashe amma ina gaba ɗaya gidan ba wan da ya kawo mata ɗauki, a guje ta juya kamar zata mutu ta koma bedroom nasu.

Tana shiga tayi arba da wani tashin hankali, dan kuwa wayan nan dodan nin ta gani suna tsere da Abba sun hana shi fita, shima sai ihu yake amma ba'a iya jiyo sautin ihun nashi, ga dai bakin sa na ihu amma ba wanda ke jin komai, tsabar tsorata Hajiya yanke jiki tayi a wajen ta sume.

Shi kuma Alhaji ya daɗe yana tsere da wayan nan sheɗanun dodan nin gashi sai zane sa suke da wasu zabga zabgan bulalu a bayan sa, duk ta in da ya gudu sai yaji sun zabga masa wan nan bulala mai baki biyu dake hannun su a tsakiyar bayan sa, sai ihu yake amma ba mai iya ji.

Gaba ɗaya gidan sai rugugi yake kamar tashin sautin gangan sheɗanu amma ba mai iya jiyo rugugin sai Abba shi kaɗan dan Hajiya kam ta jima da sumewa

Tun Abba na iya gudun cetan ransa har ya kasa ya zube a kasa a bakin toilet ya sume a wajen, yana suma komai ya tsaya chak dodannin suka ɓace, amma kafin su ɓace sai da suka zanawa Hajiya wani karfe a bayan ta suka fasa mata baya, sai jini ke malala, san nan suka ɓace.

Tashin sense ba'a sa maka rana wai meke faruwa gidan Abba ne? Muje zuwa yanzu wasan zai fara.

Abba da Hajiya dai a wan nan daran a haka suka kwana, abun mamaki kuma ko da suka tashi da safe sun manta komai sun kasa tuna komai sai mamakin ciwukan da sukaji a jikin su suke, sai tambayar junan su suke wan nan ciwon fa, dukkan su ba mai bawa ɗan uwan sa amsa dan basu da amsan sun manta komai basu iya tuna komai.

Da kyar Abba ya iya miƙewa ya ɗauki wayar sa ya kira doctor sa dan yazo ya duba su.

Baa ɗauki lokacin sosai ba sai ga dr yazo, koda dr ya duba su sai yace shi bai ga komai ba, mamaki ne ya kara bayyana a face nasu Abba da kan sa ya sanya hannu dai dai sai tin in da dodannin nan suka zanawa Hajiya karfen nan yake ta jini, yasa hannu a wajen yana nunawa Dr, amma dr yace shi bai ga komai a wajen ba, clean yake kallon wajen, sun shiga ruɗani sosai daga su har dr, domin kuwa shi dai Abba shi da Hajiya ga ciwo na nan suna gani a jikin su amma a ce musu ba ciwo, ga jinin su nan sai zuba yake dr yace musu bai ga komai ba, shi Abba ma a face nashi ciwon yafi yawa duk dodannin nan sun zazzane masa face nashi da wan nan zabga zabgan bulalu nasu sai jini fuskar keyi amma shi dr baya ganin komai very smooth yake ganin face ɗin Abba, tashin hankali ba'a sa maka date

Abba da ya ga dr ya dage a kan shi bai ga komai ba sai ya fara tunanin to ko dai dr ya samu taɓin hankali ne, dan haka sai ya sallame sa, ya ɗauki waya ya kira driver sa a kan yazo ya kai su hospital, nan driver ke sanar masa ai yana Abuja a hotel ɗin da suka sauƙa tun jiya yake jiran sa bai gan shi ba ya kira layin sa bata shiga, zaro ido waje Abba yayi tare da dafe kan sa yana kokarin ko zai tuna wani abu da ya faru, yaushe ya dawo Kaduna meke faruwa da shi ne, sai jerawa kan sa tambayoyin da bashi da amsan su yake, hakan yasa ya gane ba dr ke da matsala ba shi ne ke da matsala

ita dai Hajiya ta kasa magana tana kwance shiru sai hawaye da take saboda azaban zafin da bayan ta ke mata in da dodannin nan suka yanke ta, gashi kuma dr yace bai ga komai ba alhalin ga ciwo nan karara kwance a bayan ta yana mata raɗaɗin azaba san nan ga jinin ta sai zuba yake amma dr yace bai gani ba kuma har ma da jinin dake zuba dukka bai gani ba wan nan wani irin masifa ne? Haka ita ma ta rinƙa jerowa kan ta tambayoyin da bata da amsar su, tana yi tana hawaye.

Wunin ranar dai haka suka wuni cikin tashin hankali da damuwa, Abba ya kira likitoci daban daban amma duk wanda yazo sai yace bai ga komai ba, tun abun na basu mamaki har suka dai na mamaki suka rungumi kaddara suka lallaɓa suka taimakawa junan su wajen yiwa kan su dressing na wajen, sunayi suna hawaye dukkan su.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*After some day's*

su Akila kowa ya koma gida sun gama yiwa daddyn jelly hutu, kafin su koma ba yadda su Imran basu yi da daddy ba a kan ya faɗa musu damuwar da amma yaki sai yace musu ba komai, da suka matsa masa da tambaya sai ya ɓata rai ya ɗaure fuska cikin umarni yace karsu sake tambayar sa, haka suka hakura ba dan su rinƙa so ba.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*KADUNA*

Irfan yasha ruwan mamaki ganin yadda aka gyara masu gidan su ga kuɗin da Abbi ya samu, san nan ga karatun master's degree nashi da zai je yayi a uk wow abun ya masa daɗi over har azumi godiya ga Allah sai da yayi, su Aafia kuma an samu babban waya ga babban makaranta nan rashin mutunci ya karu dozin dozin, ita kam Umaisha wayan ta biyu ga wan da Akil ya saya mata san nan ga wadda a ka kawo mata, murna awajen su ba'a magana

cikin kurna Aafia ta kira Kawar ta Rufaidat da suka gama secondary tare, ta sanar da ita abubuwan da suka samu na alkhari, sosai a fili Rufaidat ta nu mata farincikin ta san nan ta dora mata da cewa tana taya ta murnan samun babban makaranta, suma Allah yasa su samu mai dafa masu, da murna Aafia tace In Sha Allah zata faɗa wa Abbin ta zai taimaka musu, sai godiya Rufaidat ke yi sukayi sallama

dukkan kawayen ta da sukayi secondary sai da ta kira ta sanar musu da abun alkharin da ya same su, sosai suka rinƙa taya ta murna, ita kam Umaisha daman bata da kawaye. Wan nan kenan


*WASHINGTON DC*

zaune Michael yake a *Harvard community garden* ga lucky Copper Winston a gefen sa,
kan sa na kan wayar sa yana latsawa, su John suka iso wajen suka same sa, zama suka yi gefen sa Test na faɗin "I'm feeling hungry bro's" ya faɗa yana kallon Michael dake faman latsa waya, John ne yace "Okey kuje super restaurant mana kuyo oder sai a kawo muku nan" satar kallon Michael Dest yayi hakan yasa John ya gane me suke nufi, basu da kuɗi kenan, kallon Michael ɗin John yayi kafin yasa hannun a aljihun sa ya fito da kuɗi yana kokarin basu kenan wasu turawa su biyu suka iso wajen,

ganin yan matan yasa su John juyowa a sukwane suna kallon Michael da kwata kwata hankalin sa baya kan su, cikin sauri Dest yace da yan matan "Kuzo muje" yayi maganar a tsorace dan bai san hukuncin da Michael zai masa ba idan ya ga yan matan a wajen, tsawa ɗayar yarinyar ta daka masa tana faɗin "babu in da zanje har sai ka bani kuɗin zubar da cikin nan" tashin sense jin muryan mace yasa Michael ɗagowa da sauri yana kallon su, ihu Dest ya fasa yana ja da baya, ba Dest kawai ba har John sai da ya ja baya, nan take idon Michael ta canja launi zuwa ja cikin tsawa yace da yarinyar "leave this place before I open my eyes!!" Kallon sama da kasa tayi wa Michael kafin tace cikin faɗa "Kai ba da kai nake ba tukun nan kuma idan kaga na bar nan to na samu abun da nake so ne" girgiza kai kawai John yayi yana yiwa yarinyar addu'ar Allah ya ceceta, shi kuwa Michael a fusace yace da Copper "give her a good punishment" zaro ido waje Dest da Test suka yi, shi kuwa John godiya ma yayi ga Allah dan Michael bai bata horo sosai ba, yayi mamaki sosai, dan kamar yadda su Michael su ka tsani Mum ɗin su haka suka tsani duk wata mace a duniya shi yasa duk masu aikin gidan su sojoji ne kuma maza, mace bata zuwa ko in da inuwar su take dan suna ganin dukka mata irin ɗaya suke da mum ɗin su, hakan yasa duk wata macen da tayi gigin zuwa in da suke to kuwa ta shiga uku, sun tsani mata over kuma duk mum tasu ce silar komai.

Dirowa kasa Copper yayi tare da girgiza jikin sa, yana miƙa, durkusawa kasa Dest yayi ya riƙe kafafun Michael yana faɗin "Please Michael forgive my wife bata san kai wanene bane shiyasa kaga ba'a School nan take ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login