Showing 132001 words to 135000 words out of 194715 words

Chapter 45 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

979

kai🤪



💞TRIPLET'S💞



💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)



*GargarÉ—i*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_




WhatsApp me for more information 09162620621






Episode 27






Kai tsaye bedroom na Romeo Tga ya nufa cikin fitar hayyaci da azabar raÉ—aÉ—i, ya manta in da ya nufa, yafi abun da yake gudun wa bala'i, dan in ya kuskura ya tashi Romeo daga barci baya ji da daÉ—i ba.

Yana shiga a guje ya haye saman bed ɗin Romeo, sai faman mammatse short na shi yake yana ihu kamar ƙaramin yaro.

A nitse Romeo ya waro dara daran blue eyes na sa masu É—auke da barci a kan face É—in Tga dake kankame da short É—in sa yana ihu, lumshe ido Romeo yayi ya sake buÉ—e wa, fuskar nan tasa a É—aure kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, tamkar bai san menene dariya ba, already daman shi Romeo haka face É—in sa take kullun a É—aure tamau kamar hadari, tsabar kyan sa yasa É—aure fuskar ke kara masa kyau kuma yasa hakan tafi dacewa da shi.

A hankali ya miƙe zaune tare da sanya kyawawan fararen hannun sa ya tara dark black curly hair sa da suka bazo masa a face, tara su yayi ya mai da su ta bayan sa, calmly da wannan sexy voice na shin, gashi yanzu ya tashi daga barci, voice ɗin kasa kasa mai ɗauke da barci gwanin daɗin sauraro, a nitse yace "What happened? What brought you here?" Kasa magana Tga yayi saboda ihun azaba da yake yana kallon kofar shigowa, slowly Romeo ya juya dara daran blue eyes nasa kan kofar, ganin babu kowa ne yasa in a cool voice yace "get out" yayi maganar yana kara ɗaure fuska kamar hadari, sai lokacin Tga ya kalli face ɗin Romeo da kyau, sai lokacin ya gane in da ya shigo

Ganin É—aurariyar face É—in Romeo kamar wani lion É—in gaske ne yasa Tga sake fasa razananiyar ihu tare da dirowa kasa daga saman gadon yayi waje da gudu, shiru Romeo ya É—an yi yana tunanin, me ya samu Tga, yake wannan ihun, tabbas yaji a jikin sa Triplets nasa sun yi wani abun, amma bai kawo a ransa abun da suka aikata ba kenan, guntun tsaki yaja tare da komawa ya kwanta.

Can kasa kasa yake jiyo ihun su daddy, kamar a mafarki, shiru yayi kamar ba zai miƙe ba, can kuma da yaji ihun yaki tsayawa, kuma ba voice ɗin mutun ɗaya bane, hakan yasa, ya miƙe zaune, a hankali ya zuro kyawawan fararen kafafunsa kasa tare da miƙewa kamar bai son taka kasa saboda barci dake idon sa, haka ya sanya kyakkyawan bedroom slippers na sa white color masu bala'i kyau da laushi da tsada, sannan ya nufi waje.

Yana fitowa palon sa, sai yaji ihun nasu ya kara yawa, kasan cewar part nasa yayi nisa da palon kasan ne yasa baya jin hayani sosai idan a nayi a palon kasa, Part na sa a hawa na biyu yake.

A farkon saukowa benen shigowa palon kasan ya tsaya tare da goya hannu a kirji ya zubawa su daddy dake birgima a kasa, dara daran blue eyes nasa yana kallon yadda suke ihu suna birgima suna neman taimako.

Slowly ya dawo da kallon sa kan su Michael dake ta faman ɓaɓɓaga dariya kamar wayan da suka zare, yar gyaran murya yayi wadda tasa duk wata halitta mai rai a palon ɗagowa yana kallon sa, har su daddy masu ihun, jin voice ɗin Romeo yasa sun mance da meke cizon su, sun mance da bala'i da suke ciki, dan gwara musu kwarin nan a kan hukuncin Romeo.

A ɗari James da Michael suka miƙe, kamar zasu tashi sama saboda gudu suka fice daga palon suka yi wajen harabar gidan, jinjina kai Romeo yayi yana tunanin ya zai yi da yaran nan wani hukunci zai musu, ihun uncle Herry ya dawo da shi daga duniyar tunanin me ya kamata yayiwa su James.

Guntun tsaki yaja tare da dakatar da kwarin, ya kalli Jinga jibgan sojojin dake cikin Kitchen suna Aikin girki "go and bring them for me" ya faÉ—a tare da fara taka staircase É—in a hankali, ya sauko zuwa cikin Palon, ya zauna saman sofa yana kallon yadda su daddy ke fama da sosa jikin su suna kuka.

A saman ka faÉ—ar su Sojojin nan suka É—auko Michael da James suka kawo su gaban Romeo, still har lokacin guntse dariya suke

kallon fuskokin su Romeo yayi, a maimakon yaji haushi ko ya musu wani hukunci, sai ya tsinci kan sa da jin zuciyar sa tayi sanyi ganin dariyar dake kan fuskokin su, yau first time yaga sun yi dariya a rayuwar su, dukkan su Triplets ɗin ba masu dariya bane, dan basu taso a yanayin dariya ba, tun suna yara renon sojoji uncle Herry da dad suka musu, sannan kuma sun taso da tsantsar tsanar mum ɗin su, hakan yana ɗaya daga cikin abun da yasa basa dariya kuma basu da yawan magana, basa shiga harkan kowa kuma basa son a shiga nasu, basa son baki, su kaɗai suke rayuwar su, dan basa yarda da kowa, sunce tun da mum ɗin su ta iya cin amanar su, to kowa ma zai iya, shiyasa ko daddyn su ba su yarda da shi ba, su ukun nan su kaɗai suka yarda da kan su, bayan su basu yarda da kowa ba, sai dai gara James da Michael su kana iya yi musu magana har su tsaya su saurare ka, shi kam Romeo ai duk gidan ba wanda ya ga fuskar da zai iya yi masa magana, bala'i tsoron sa suke, ba mai iya tinkarar sa ya masa wata maga, har daddy mutuwar tsoron sa yake, ɗan gara Michael da yake suna shiri sosai, kuma saboda matsalar Michael yasa ya jasa a jiki, ban da haka ba mai kwarim gwiwar iya tinkarar sa, a baya kafin yanzu ma idan daddy na son yi masa magana a kan wani abu to fa sai dai in ya sha giya, baya taɓa iya tinkarar Romeo ko da a waya ne baya taɓa iyawa sai ya sha giya ya bugu, saboda tsoron Romeo, ganin wannan ɗaurariyar face ɗin na Romeo ba karamin razana mutane yake ba, yana sanya hantan manyan maza ta kaɗa, shi yasa mum take cewa ganin Romeo yana cikin farinciki ma razana ta yake, dan shi koyana cikin farinciki fuska a ɗaure take, baga taɓa gane masa, yanzu kuma da yake bawa daddy dama ya faɗa masa duk wani abun da ke damun sa, idan daddy yaje daga can baya yake tsayawa, saboda tsoro, kuma ba duka ba zagi, ba ɗaya da Romeo ke masa, kawai dai Allah ya zubawa daddy tsoron wanan face ɗin na Romeo ne mai sanya hantan manyan maza kaɗawa.

Shiru Romeo yayi ya zuba musu wayan nan kyawawan dara daran blue eyes na sa nan yana kallon su, sai faman guntse dariya suke, shi kan shi abun ya É—an nishaÉ—an tar da shi ganin yan uwan sa haka ya kayatar da shi, da yake ba'a gane farin cikin sa yasa ba wanda ya gane hakan, lumshe idon nasa yayi, hakan yasa long eyelashes nasa suka kara bayyana, kamar wadda ya kara dana kanti, sake waro idon nasa yayi sosai har sai da suka kara kyalli, saboda ya zaro su sosai.

"Go and apologize to them" ya faɗa a sanyaye, ba musu suka miƙe still har lokacin guntse dariya suke, jikin daddy suka fara shafa masa dan ya samu saukin yaraɗaɗin, dan daman idan ba su suka shafa wannan cizon kwarin ba, babu wani magani da zai kashe kai fin dafin cizon ta dai na raɗaɗi, tsab suka shafe jikin daddy, hakan yasa daddy ya samu sassauci daga raɗaɗin azaban zafin cizon kwarin.

Romeo yana zaune yana kallon su, sai da suka bi kowa suka shafe su, sannan suka dawo gaban sa suka tsuguna suna sunnar da kai kasa, irin na marasa gaskiya, wayan da suka yi laifi
jingina kai Romeo yayi da jikin sofa tare da lumshe dara daran blue eyes nasa yana mai jin kaunar yan uwan nan nasa a ransa.

Almost 30mins kafin ya miƙe ba tare da ya musu magana ba, ya haura sama abun sa, kallon juna sukayi kamar wasu munafukai, a tare suka kwashe da dariya, kamar wayan da suka sha suka bugu, har da faɗuwa kasa suna ɓaɓɓaga dariya kamar ba lafiya ba, kasan cewar su daddy sun samu saukin raɗaɗin, hakan yasa suka samu damar dawowa cikin hayyacin su, suka zubawa su James ɗin ido sai faman dikar dariya suke, shi dai daddy addu'a kawai yake Allah ya shirya masa wayan nan yara, dan tun suna yara suke azabtar da shi da wayan nan kwari idan ya musu laifi, da suka girma ne suka dai na, har ya manta da kwarin nasu, a tunanin sa ma yanzu babu kwarin ashe ashe a koi su kawai basa fitar wa ne.

A tare suka miƙe har lokacin dariyar ya ki sakin su, haka suka wuce sama suka nufi part na James, binsu da ido daddy yayi har suka ɓace sannan ya lallaɓa ya miƙe yana bawa su Uncle Herry hakuri, nan fa daddy yaga Tga har lokacin sai murkusoso yake, kusa da shi daddy ya matso ya taɓa shi yana faɗin "General what's wrong with you? Are you okey?" Kasa magana Tga yayi kasan cewar su James ba su shafa masa wajen da ya samu harbi cikin Short na sa ba, to wajen ya kunbura sai azaban zafi yake masa.

Daddy da ya fahimci haka ta hanyar wajen da Tga ɗin ya riƙe da hannun sa, hakan yasa daddy yace da Bodyguard ɗin dake gadin wajen table ɗin cin abinci suzo su ɗauka masa Tga su kai shi ɗakin duba mara lafiya, dan ya bashi taimakon gaggawa, ko ya ɗan samu sauki, duk abun dake faruwa a palon tun daga farko har karshe bodyguard da sojojin suna gani amma ba halin yin magana dan ba shine aikin su ba.

Cikin sauri suka É—auki Tga suka wuce da shi word room na su, da kyar daddy ya iya takawa zuwa room É—in dan ya ceto kanin sa kuma É—an autan su, daga haÉ—ari.

Ba karamin dirama daddy ya shaba wajen dubawa Tga wajen, dan Tga yaki tsayawa saboda azaban zafin, har sai da dad yace zai kira Romeo sannan Tga ya yarda, daddy ya taimaka masa, duk da ba wani maganin da zai sa ya dai na zafin, amma ba laifi ya É—an rage.

Haka daddy ya bawa sauran ma kulawa kafin yayi treating na kan sa.

A takaice dai a wannan rana ba'aje wannan church É—in ba saboda aika aikan da Triplets sukayi, ko in ce James da Michael.

💞NIGERIA💞

💞KADUNA💞

Kai tsaye bank Aafia ta wuce, taje ta cirowa Rufee kuÉ—i sannan ta wuce school, kamar wasu wadda a ka gaji da su a gida, kullun sassafe suke zuwa school Rufee da Amal ko da basu da class sai sun zo, suyi ta zaman banza, kamar wayan da basu da mafaÉ—i, kai tsaye department na su Aafia ta wuce, nan ta isko su Rufee

Suna ganin ta suka fara rungumar juna Amal tana faɗin "I missed you two days?" Zama Aafia tayi saman kujerar dake wajen ta ciro kuɗi ta miƙa wa Rufee 100k tana faɗin "Missed you too my girls" amsan kuɗin Rufee tayi tana wash baki, ba ko na gode bare Allah ya yi albarka haka ta tura kuɗi cikin jakar ta kamar bashi ta bawa Aafia ɗin.

Sai bayan ta sanya kuÉ—in a jaka ne sannan ta zauna kusa da Aafia tana faÉ—in "Please Aafi ya maganar Alhajin nan ne? A matse fa yake yana son ganin ki dan Allah" shiru Aafia ta É—an yi kafin tace "Idan muka gama exam kice masa yazo mu haÉ—u a nan" washe baki Rufee tayi aikin bokan ta yayi kyau, ita kuma Aafia haka kawai taji bata ji daÉ—in amsa wa Rufee da tayi ba, dan tana jin kamar ba zata iya haÉ—uwa da Alhajin ba, amma ba zata iya yiwa Rufee musu ba.

💞Gidan Abba💞

09:00pm

Zaune Akila baiwar Allah take saman sofa a palon su, sai faman kiran layin daddyn Jelly take amma layin baya shiga, yau wajen week ɗaya kenan Akila na neman layin daddy dan suyi hira da Jelly, amma a kashe, yau sosai Akila ta shiga damuwar ko lafiya, tunani ta fara yi yadda zata ɓullo wa lamarin, "ko dai na je kanon na duba meke faruwa ne" ta jefowa kan ta tambaya da bata da amsa "To idan zanje Kano me zan cewa Abba da Ammie ina zance musu zanje" shiru tayi ta rasa mafita ta shiga damuwa, gashi in ta tambayi yaya Imran ma sai yace mata shi ma baya samun daddy a waya, amma sun kusa kammala exam zai dawo cikin Month mai kamawan nan zai ɗauke ta suje kanon tare, ta dai na damuwa In Sha Allah komai yana nan normal.

Ita dai amsa masa da to kawai tayi amma ba wai dan haji daÉ—in hakan ba, tayi shiru tana tunanin ko dai ta kira su Aafia ne, duk ta shiga damuwa tana kewar yan uwan ta, sai dai idan ta kira su Aafia ba wani jin daÉ—in su take ba, saboda basa mata magana mai daÉ—i.

Haka tayi shiru tana tunani, kamar a mafarki ta fara ganin wutar palon su na kawowa yana ɗauke wa, da farko ta ɗauka rikicin yan nepa ne dan haka bata wani damu ba, sai kuma taga abun gaba yake yaki tsayawa, har wani shekin wutar yake, yana abu kamar shocking na nepa, tsoro ta fara ji, jikin ta ya fara kerma, sai zare ido take, a hankali ta miƙe tana takawa kamar wadda koi ya fashewa a ciki, kai tsaye saman bene ta nufa, tana tafiya tana jin motsi kamar ana bin ta a baya, ji tayi kamar ta fasa ihu, sai dai kuma ta kasa yin ihun, sosai ta tsorata, ganin ta kusa haurawa sama ne yasa ta kwasa da gudu, ta nufi betroom ɗin Ammie.

Ko da tazo zata shiga bedroom É—in sai kofar bedroom É—in ya rufe kan sa da kansa, ihu ta saki tare da juyawa da gudun gaske ta nufi bedroom na Abba, nan ma ko da tazo zata shiga, sai kofar bedroom É—in ya rufe kan sa, nan fa tsoro ya kara dira mata a ran ta, jikin ta har wani kerma yake, sai zaro ido waje take, ta rasa ina zata sa ranta, tana tsaye a kofar bedroom na Abba kamar a mafarki gaba É—aya wutan gidan ya É—auke, wani bala'i duhu ya gauraye ko ina, a guje ta nufi bedroom nata tare da yin wurgi da wayar ta, da karfi ta fara kiran Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, tana furta hakan kan kace me, wutar gidan ya dawo, haske ya gauraye ko ina, hayewa saman gadon ta tayi, a É—ari ta shige cikin bargo tana kuka kasa kasa, tana ambato sunan Allah, da karfi ta runtse idon ta yau taga tashin hankali da kyar barci yayi awon gaba da ita, har tayi barci jikin ta bai dena kerman tsoroba.

💞KATSINA💞

Ko da Jehan suka isa Hospital ta sanar da gwaggo abun da ke faruwa, sosai gwaggo ta shiga damuwa, ga mum kuma har yanzu bata ko motsi, bata san in da kan ta yake ba, sun zauna jugum jugum a harabar hospital É—in sun rasa madafa, ban da sunan Allah ba abun da suke ambata a ransu,

kamar daga sama sukaji sallama a ta bayan su, gwaggo Jehan Sadiq har suna rige rigen juyawa

Sadiq ne kawai ya iya amsa sallamar, tare da miƙa wa matashin hannun sa suka gaisa, "idan ba damuwa zan iya zama, dan ina son magana da mama ce" matashin yayi magana yana kallon gwaggo, kallon gwaggo shima Sadiq ɗin yayi yana jiran suji me zata ce

Da hannu gwaggo ta yiwa saurayin nuni da wajen zama ba tare da tayi magana ba, kasan cewar matashin ba zai fi sa'an Sadiq ba a haihuwa, shi yasa gwaggo bata damu ba.

"Mama sunana Ibrahim, ni ma'aikacine a super restaurant, wadda aka buɗe kwannan nan, nasan kun san restaurant ɗin, to a takaice dai, daman an baki aikin samo yara yan mata wayan da zasu dace da aiki a wajen, to tun jiya da na shigo hospital nan, naga wannan yar taki a fiska ta dace da irin wadda muke buƙata, sai dai ta fannin karatu kuma zamu mata jarabawa, idan ba damuwa ina muku tayin aikin" cewar Ibrahim, yayi maganar yana karewa Jehan kallo, murya a dashe gwaggo tace "Muna cikin damuwar da ba zamu iya yin wani abun ba yanzu, ita kan ta yarinyar ba zata iya yi muku abun da kuke buƙata ba, duk da ma bamu san a kan wani restaurant kuke magana ba" Sadiq ne ya ansa zancen da cewa "Gwaggo ni nasan restaurant ɗin yana da kyau sosai kuma sabo ne, babban restaurant ne, wlh da Jehan zata ansa tayin su zai taimaka muku sosai" da sauri Ibrahim ya ansa zancen da cewa "Sosai mama wlh mai gidan mu yana da kirki sosai, kuma kinga sabon restaurant ne zata ji daɗi aiki damu sosai" kallon Ibrahim da kyau gwaggo tayi kafin tace "ba wai munki aiki bane, a'a muna cikin damuwar da ba zata iya yi muku abun da kuke bukata ba" "Mama menene damuwar taku?" Cewar Ibrahim, Sadiq ne ya bashi labarin halin da Mum ke ciki, yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login