Showing 135001 words to 138000 words out of 194715 words

Chapter 46 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1001

magana Jehan na kuka gwaggo na rarrashin ta.

Shiru Ibrahim yayi kafin yace "To nawa ne yanzu ya rage kuɗin" da sauri Jehan ta bashi amsa, tana sharan kwallai "500k saura kuɗin gida da muka sayar, sai kuma 200k da daman already yana cikin account ɗin" "idan aka haɗa ya zama 700k kenan ko?" Cewar Ibrahim, da sauri Jehan ta gyaɗa masa kai, "to nawa daman ake buƙata wajen aikin nata?" Gwaggo ce tace "Dr yace mu tana ji kuɗin aiki kawai 1.5 sai kuɗin jirgin fita waje" jinjina kai Ibrahim yayi kafin yace "Zan iya cika muku amma aro bashi, idan ta fara aiki a restaurant ɗin mu, 40k za'a na biyanta ko wani wata, to idan an biyata ni zan rinƙa cire 20k a ciki ina barin mata 20k tana taimaka muku a gida, har Allah yasa ta gama biyana kuɗi na" da murna su gwaggo suka rinƙa zuba masa godiya, a tunanin su dan Allah ya musu hakan, sai dai basu sani ba idan ya kai Jehan kuɗin da za'a bashi sai ya fi haka, dan mai restaurant ɗin ne yace masa ya samo masa yan mata kyawawa masu jini a jika, wayan da kyan su zai rinƙa jawo masa costumers, shi yasa Ibrahim tun da ya kwalla ido yaga Jehan shikenan, har da hoto ya ɗauke ta bata sani ba, ya turawa mai gidan nasa, aikuwa mai gidan nasu na gani yace Jehan tayi ya kawo ta zasu bashi 500k, dan kyan Jehan dole jama'a suyita tururuwan zuwa cin abinci, mu sammanma matasa da manyan masu kuɗi, sai dai abun da mai gidan nasu bai sani ba, Jehan ba kamar yadda suke tunani bace, dan bata da fara'ar da zata ja musu costumers kamar yadda suke tunani, sannan bata daukan raini bata ɗaukan wulakanci haka zalika tana da raini da kirman kai ga izza, sannan tana kallon kowa kamar a karkashin ta yake, saboda yadda ta taso a gida lokaci daddyn su naman.

hmmm akoi cakwakiya a wannan restaurant ɗin yasin, muje zuwa.

Ibrahim da kan yaje ya muɗe musu motar sa kirar *Corolla* suka sanya mum gidan baya, suka shiga suka wuce babban Hospital sai daɗi Jehan take ji, shima Ibrahim sai daɗi yake ji, zai samu kyautar 500k daga ogan sa.

A takaice dai sun yi Sa'a za'a iya yiwa mum aikin a kan 1.2 Ibrahim ya cika musu 500k a ka sanya rana, nan da 1 week za'a mata aiki, sai murna Jehan take, ta mance da duk wani bakin ciki da kuncin da take ciki, ita dai burin ta ya cika mum zata samu lafiya.

💞KADUNA💞

Su Aafia suna zaune suna hiran su na kawaye kamar yadda suka saba kafin lokaci class nasu ya cika, da sallama wani kyakkyawan mata shi ya kariso wajen su, fari tas da shi kamar balaraɓe, da fara'a Rufee da Amal suka amsa ma shi sallamar, while ita Anisa daman bata damu da yawan magana ba, kuma bata cika shiga harkan mutane ba, kusan halin ta ɗaya da Aafia.

Kusa da Amal matashin ya zauna yana faɗin "Ina babban yarinya ne" yayi maganar yana kallon Aafia, guntun tsaki Aafia taja tana turɓune fuska tace "Tana gida, amma anjima kaɗan zata shigo" murmushi yayi kafin yace "Allah Aafia Umaisha babban yarin ya tana matukar burgeni" dogon tsaki Amal taja tare da miƙewa tsaye tana faɗin "Yanzu Man a gaba na kake cewa wata tana burgeka? Ko kunya ta baka ji ba, wannan ai cin fuska ce" ita dai Aafia shiru ta musu kamar bata a wajen, Anisa ce tace "Kai Amal amma baki da kunya, yanzu dan Mansoor yace Umaisha na burge shi ne zaki ɓata rai? To Umaisha ɗin ba kanwar ki bace? Ai ko dan ganin idon Aafia kya mata kara, kuma ai man ba cewa yayi yana son Umaisha ɗin ba, kawai cewa yayi tana burge sa" Rufee ce ta dakawa Anisa tsawa da cewa "Ke Anisa kiyiwa mutane shiru, ke me kika sani game da kishi? Amal na da gaskiya wannan cin fuska ya mata, akan me zai ce wata mace na burgesa a gaban matar sa In Sha Sha" shiru Anisa tayi taba tanka Rufee ba, ita kuwa Aafia ka san cewar bata cika son hayaniya ba, sai ta miƙe kawai ta bar musu wajen, da sauri Anisa ta miƙe tabi bayan ta,

dogon tsaki Rufee taja kafin tace "Wlh Amal karki yarda son Umaisha yake tun da ya faɗi hakan" ta kai karshen maganar tare da miƙewa tabi bayan su Aafia.

Matsowa gaban sa Amal tayi suna fuskantar juna ta fara surfa masa uwar masifa, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, cikin masifar nata har da cewa karya sake yi mata magana sun rabu kenan, shi dai man shiru ya mata yana kallon ta, har ta gama ruwan bala'i nata, ta wuce ta bashi waje, tana tafiya ya ɗaure fuska tare da zaro idon sa, nan take idon suka sauya zuwa purple color, jikin sa har kerma yake, ɗan jujjuyawa yayi dan yaga ko a koi mutane, ganin babu mutane sosai a wajen ne, yasa ya faki idon yan kalilan student dake wajen ya buɗe bakin sa, wasu dankara dankaran macizai guda biyu suka fito daga cikin bakin nasa, bakake kirin masu kan faranti, kai tsaye bayan su Aafia macizan nan suka bi, cikin sauri kamar munafiki ya miƙe ya bar wajen tare da mai da asalin kalar idon sa wato fari da baki.

Su Aafia kuwa, suna barin wajen kai tsaye wajen wani ɗan karamin wajen hutawa dake cikin school ɗin suka nufa, waje ne mai ɗauke da kujeru wadda aka gina su da siminti, kasan wajen grass ne kanana masu kyau green color. Saman kujerun su Aafia suka je suka zauna, Anisa na bawa Aafia hakuri

Yar dariya Aafia tayi kafin tace "Ba komai kuma idan kika duba ai Amal na da gaskiya, taya za'ayi Man yace wata tana burgesa kuma a gaban budurwar sa wadda yake ikirarin zai aura, duk da cewa basu wani jima da haɗuwa ba, ai hakan bai dace ba" Anisa zata yi magana sai ga Rufee, kasan cewar tasan halin Rufee da masifa, sai tayi shiru kawai suka basar da maganar, zama kusa da su Rufee tayi ba tare da tayi musu magana ba, sai wani kwaɓe fuska take kamar wadda taga kashi.

Shiru suka zauna har Amal ta kariso wajen, Amal na zama wayan nan mayun macizan suka iso, masu karfin dafin bala'i ga idon su nan kamar na mutane, gasu da kattin kai kamar faranti, idan ka gansu kai kace mutane ne saboda ison su, sulalewa sukayi ta cikin grass dake wajen, kai tsaye suka kaiwa Amal sara a kafa, suna saran ta kuma suka ɓace ɓat, ihu Amal ta fasa tare da sulalowa ta zube kasa, kamar an ɗauke wutar nepa tayi tsit, daga wannan ihu ɗayan shikenan bata kara wani ba, ta zama gawa.

A razane su Aafia suka miƙe sukayo kan ta, yayin da shi ma, man ɗin ya kariso wajen a lokacin wai yazo bawa Amal hakuri kamar bai san komai ba.

Aafia na kokarin taɓa Amal Man yayi saurin dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa "A'a Aafia karki taɓa ta!!!" A sukwane dukkan su suka ɗago suna kallon sa...


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪




💞Star Lady💞




💞TRIPLET'S💞



💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)



*Gargarɗi*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_




WhatsApp me for more information 09162620621






Episode 28



Aafia na kokarin taɓa Amal Man yayi saurin dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa "A'a Aafia karki taɓa ta!!!" A sukwane dukkan su suka ɗago suna kallon sa, cikin sauri ya kariso wajen ya sanya hannun sa ya ɗaba Amal ɗin, shiru bata ko motsi, su Aafia basu sani ba, sanya hannun sannan da yayi, ya kwashe dafin da ke jikin tane, ba dan haka ba suka taɓa ta mutuwa zasu yi suma.

Munafiki nan fa ya sanya musu kukan munafurci yana faɗin "Amal bata numfashi, Amal bata tare da mu, Shikenan munshiga uku" Aafia ta kasa magana ganin abun take kamar mafarki, ita kuwa Rufee ihu ta sa ta duƙa tana girgiza Amal ɗin tana kiran sunan ta, baya baya Anisa ta fara yi tana hawaye, ganin abun ita ma take tamkar a mafarki.

Shikuwa Man yana tsugunne sai kuka suke shi da Rufee, kan kace me jama'a sun taru a wajen, nan fa a ka ɗauki Amal a ka wuce da ita Hospital, a in da likita ke tabbatar musu da cizon maciji ne ya kashe ta.

Haka a ka ɗauke ta zuwa gida, dan aje a sallace ta a kai ta gidan ta na gaskiya, Aafia tsabar tsorata ta kasa driving na motar ta da kan ta, ta kai kan ta gida, sai dai Anisa ce ta jata zuwa gidan nasu.

Ko da ta shigo palo, a zaune ta samu Aunty tana kallo a Tv, taci kwalliyar ta kamar yadda ta sama tana zaune ta aza kafa ɗaya kan ɗaya.

Ganin Aafia wata zololo da ita jiki ba kwari ko sallama bata yi ba ta shigo palon, ba karamin ɗagawa Aunty hankali tayi ba, cikin sauri Aunty ta miƙe tsaye tana faɗin "Aafia lafiya meke damun ki" kuka Aafia tasa tare da zama saman sofa, dai dai lokacin Umaisha ta sauko kasa cikin shirin ta zata wuce school, jikin ta na sanye da atamfa ɗinkin doguwar riga A shape ta sanya karamin gyale a kan ta sai kamshi take zubawa.

Da yar gudun ta, ta kariso cikin palon ganin Aafia na kuka, ita kan ta Aunty sai da taji jikin ta ya mutu, yau dai Aafia ke kuka to me ya faru da ita, ita kuwa Aafia kuka take tsakanin ta da Allah kamar yarinya karama, dan ta tsorata sosai shi yasa ma ta kasa zuwa gidan su Rufee ɗin, ba zata iya ganin sallar jana'izar Amal ba, hakan yasa ta nemi dawowa gida kawai.

Rungumeta Umaisha tayi tana faɗin "Aunty Afi lafiya meke faruwa?" Cikin kuka da kyar Aafia tace "Umaisha Amal ta mutu, Amal ta mutu Umaisha" zaro ido waje Umaisha tayi cike da tsoro tace "Ban gane Amal ta mutuba, ai na ta mutu ɗin? Ko dai mafarki kike ne?" Kara sautin kuka Aafia tayi tana faɗin "Umaisha da gaske nake wlh Amal ta mutu yanzu nan muna zaune da ita kawai tayi ihu ta faɗi kasa, sai gawa, an kai ta asibiti, dr yace saran maciji ne ya kashe ta, kuma su guyson sun duba ko ina a wajen basu ga snake ɗin ba" salati Aunty tasa tana faɗin "Kiyi hakuri ki mata addu'a ne kinji Aafia" cikin kuka Aafia taje dogon tsaki kasan cewar already Rufee ta shiga tsakanin su da Aunty ɗin kome zata musu ba zasu taɓa ganin farin taɓa.

Miƙewa Aafia tayi ta haye sama ta ci-gaba da kukan ta, ita ma Umaisha saman ta koma dan ta fasa zuwa school ɗin, dan lokaci guda itama tsoro ya kama ta, sai dai gani take kamar Amal bata mutu ba, tana raye, ita dai Aunty addu'ar nemawa Amal Rahma wajen Ubangiji tayi sannan ta koma ta zauna taci gaba da kallon ta, tana mamakin hali irin na su Aafia.

💞JELLY💞

Ba laifi jikin nata ya samu sauki sosai dan har ta farfaɗo, sai dai kuma me ta mance komai she lost her memory, saboda buguwar kai da ta samu, amma likita yace idan ta haɗu da abun da ya taɓa faruwa da ita a baya ko kuma wani da ta sani zata komawa dai dai, yanzu duk wani abun da wannan Hajiya ta tambaye ta sai tace bata sani ba, sai dai kuma still wannan shagwaɓa da bakin surutun nata yana nan bai mutu ba.

Haka dr ya sallame su, suka wuce gidan Hajiyar da Jelly, gida ne babban gida irin na manya manyan atrajirai masu faɗa a ji a kasar, mata huɗu ne a cikin gidan, gaba ɗayan su suna haɗe waje guda, ma'ana ba amusu part part ba, part ɗaya a kayi, mai ɗauke da katafaren palon kasa, to daga palon kasan ne zaka iya wucewa Part ɗin duk wanda kake so, amma duk a cikin palo guda.

Kai tsaye ɓangaren ta Hajiyar nan ta nufa da Jelly, sai kallon gidan Jelly ke yi kamar bata taɓa kallon wani abu makamancin hakan ba, suna shiga ta kai ta wani haɗaɗɗiyar bedroom mai bala'i kyau, yaji komai da ake buƙata.

Sai da ko da ta kai ta zata fita sai Jelly tace bata san wannan ba, ita dai Hajiya bazata fita ta barta ba, sai dai su zauna tare, sosai Hajiya ta lallaɓata tace taje tayi wanka tazo taci abinci, nan fa Hajiya taga ikon Allah dan kuwa Jelly dai ba abun da ta iya ga bala'i shagwaɓar tsiya ,ga bakin surutu kamar reza.

Kuka ta sawa Hajiya kamar yar karamar baby, dama yaya lafiyar kura bare tayi zawo, daman ita Jelly da lafiyar ta ma ya a ka kare da ita bare kuma an samu matsala ta manta komai tayi losing memory ai sai dai abun da hali yayi, sai hakuri kawai.

Haka Hajiya ba dan taso ba ta shiga toilet tayiwa Jelly zan kaɗeɗiyar budurwa wanka, ita a tunanin ta saboda matsalar da Jelly ta samu ne yasa ta zama haka, bata san cewa dama already jelly kam haka take ba.

Kayan da Nawid ya sai mata lokacin da suke hospital Hajiya ta sanya mata ɗaya daga ciki, sannan ta riƙo hannun ta suka fito palo dan ta zuba mata abinci sai taje itama tayi wanka ta ɗan miƙe.

Koda sukazo palo ta zubawa Jelly abinci tace taci, kafin ta dawo bari tayi wanka, kuka Jelly ta sanya mata tana faɗin "A'a ni karki tafi ki barni" Hajiya dai taga abun da yafi karfin ta, tunani ta fara yi karfa Jelly tace da ita zata kwana a ɗaki, in ko haka ne shi kuma Abbon Nawid ta kai shi ina kenan, tab lallai a koi babban matsala.

Haka Hajiya ta hakura ta zauna ta fara bawa Jelly abincin a baki, dan Jelly taki yarda taci abincin da hannun ta, wai sai dai a bata a baki, hakako Hajiya ta hakura ta rinƙa bata abaki, jelly na ci tana wasa, dan da alama abincin bashi a kan ta, ba yinwa take ji ba.



💞WASHINGTON DC💞


Zaune Romeo yake kusa da daddy saman bed ɗin dad, hannun sa riƙe da cup da kuma drugs, ya tsare dad da wayan nan dara daran idon nasa, yana jiran dad ya shanye drugs da ya bashi, sai faman kwaɓe fuska dad yake alamar baya son drugs ɗin, daman Romeo yasan halin sa shiyasa yake tasa shi a gaba har sai ya sha a gaban sa sannan yake kyalesa, da kyar da kyar dad ke tura drugs ɗin a bakin sa Romeo na bin masa da ruwa mai sanyi dake cikin kyakkyawan cup ɗin hannun sa.

Babu ko excuse Michael ya faɗo cikin bedroom ɗin yana kwaɓe fuska, ko kallon in da yake Romeo bai yiba, kusa da dad yazo ya zauna yana turo

Dark brown curly hair sa dad ya shafa yana faɗin "How far My Tiger?" Kara turo baki Michael yayi yana wani turɓune fuska, jawosa jikin sa daddy yayi yana ɗan bubbuga bayan sa alaman rarrashi, kamar wadda akayi wa wani abun, shiko Romeo a jikin sa ya ci-gaba da buɗe wa dad drugs yana bashi, idan dad yasa drug ɗin a baki, sai Romeo ya sanya masa cup na ruwa a ban nasa dan ya haɗiye maganin.

Calmly yace "Where is James?" Yayi maganar ba tare da ya ɗago ya kalli Michael ɗin ba, cikin sauri Michael yace "he is in the word room" miƙewa Romeo yayi bayan dad ya kammala shan maganin, ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin hannun sa rike da sauran drugs ɗin yana faɗin "you and James meet me in my room" ya kai karshen maganar tare da ficewa, shiru Michael yayi kamar mai tunanin wani abun, zuba masa ido dad yayi yana kallon sa, ba tare da wani yace da ɗan uwan sa uppan ba.

A ɓangaren James kuma.

Zaune yake kusa da Musharraf yana kallon sa, wani irin yana yi yake ji duk lokacin da ya kalli kwayar idon Musharraf, ji yake kamar ɗan uwan sa na jini, haka kawai yake jin kaunar Musharraf sosai.

Kallon sa Musharraf yayi kasa kasa yace "I want to pray, it's time for prayer" kallon diamond watch ɗin hannun sa James yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Musharraf yace "Okey now what do you want?" "I want to perform ablution" miƙewa James yayi ya ɗauko ruwan roba a fridge, ya dawo ya ɗauko wani kwano na silver mai faɗi irin wadda marasa lafiya ke amfani da shi idan zasu yi alwala ko wani abun, saman gadon ya haye, da yake gadon yana da girma.
Hannu yasa ya ɗago Musharraf ya ɗan zaunar da shi tare da sanya masa pillow a bayan sa, abun da ya bawa Musharraf mamaki shine alwalar da James ya masa babu tangarɗa ko wani kuskure, kasa hakuri Musharraf yayi har sai da ya tambayi James, ya akayi yana Kristen ya iya yin alwala dai dai haka, yar murmushi James yayi yana faɗin "I knew it through my friend, i have a Muslim friend, he is of good character, i like him more than your expectations, I understood a lot of

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login