Showing 102001 words to 105000 words out of 194715 words

Chapter 35 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

977

bata dawo ba" sake wayar yayi ta faɗi kasa ta tarwatse a wajen, dafe kan sa yayi yana tuna irin rabuwar da suka yi da safe tabbas akoi matsala, kasan cewar shi daddyn Jelly ƙaramin abu yake iya birki tashi hakan yasa numfashin sa ta ɗauke ya zube kasa, kafin ya kai kasa uncle's ɗin su Jelly suka riƙe sa suna faɗin innalillahi wa inna ilaihir rajiun.

Da sauri suka yayyafa masa ruwa, dogon numfashi yaja tare da saukewa a hankali, ba tare da ya buɗe ido ba ya fara sambatu kamar zararre "why Jelly? Why zaki wa daddyn ki haka, daman tun da naga irin yadda muka rabu da safe na tafi gaba na na faɗuwa naje office ina ta tunanin anya lafiya kuwa ashe dai ba lafiya ba, dan Allah Jelly ki dawo nayi alkawarin sai dai komai ya faru da ni amma ba zan taɓa aura miki wanda baki so ba, dan Allah ki dawo tabbas na miki alkawari Imran zan aura miki" haka daddy yayi ta sambatu, sosai uncle's ɗin su Jelly suka tausaya masa tare da lallaɓashi da bashi baki.

Da kyar suka samu yayi shiru amma ya kasa miƙewa ma bare kuma a je ga tukin mota, wani uncle ɗin su Jelly ne ya jasa a mota suka wuce gida, dan ko magana daddy ya kasa yi, yana bala'i son jelly fiye da tunanin duk wani mai tunani, ita kaɗai garesa saboda ita yaki raɓar kowa, kuma yaki yin wani aure Ita ce duniyar sa ita kaɗai yake ɗaga ido ya kalla yaji daɗi a rayuwar sa itace farincikin sa komai nasa, baya jin zai iya rayuwa a duniyar nan idan har bai gan taba, sai fita da sauri sauri numfashin sa ke masa har suka isa gida.

Fita motar ma ya kasa sai uncle ɗin ya taimaka masa har zuwa bedroom na sa, ya kwantar da shi a saman gado, uncle ɗin na kokarin gyara masa pillow kenan suka ci karo da farar wasika da Jelly ta ajiyewa daddy, cikin sauri Uncle ya ɗauko takardan ya buɗe tare da miƙa wa daddy, daddy jiki har kerma yake wajen ansan takardan ya fara karantawa kamar haka "i love You my dad I love You my world" dogon numfashi daddy yaja da kyar ya iya cewa "ina wayata" da sauri uncle ɗin yace "wayar ta fashe ai tana cikin mota" shiru daddy ya ɗan yi kafin yace "yanzu na tabbatar da zargina, da gaske guduwa Jelly tayi ba sace ta akayi ba, tun da har wasiƙa ta ajiye min" shiru uncle yayi yana mugun jin tausayin daddy, dan tun Jelly na da 5 years uncle yake karantar wa a School ɗin nasu yasan irin soyayyan dake tsakanin daddy da Jelly, yasan irin son da daddy ke wa Jelly.

Sunyi shiri dukkan su Uncle yana son ya koma amma ya kasa faɗa wa daddy zai koma saboda tausayin da daddy ya bashi, suna cikin wannan halin kenan dolly ta shigo ɗakin tana yar kuka saboda ita ma tasan lokacin dawowar Jelly daga school yayi shiyasa tazo mata oyoyo, ba karamin karawa daddy tashin hankali dolly tayi ba, lokaci guda yaji karfi yazo masa cikin hanzari da kuzari ya miƙa ya nufi waje, ba karamin mamaki uncle yasha ba ganin yadda daddy ya miƙe da kuzarin sa kamar ba shi ba.

Da sauri uncle ya miƙe yabi bayan daddy, daddy da kan sa yaja motar kai tsaye sai police station,
yaje ya shigar da report a kan batar Jelly ɗin san nan ya wuce ya sauke uncle a school, ya zarce gidan Radio suma ya sanar da su, daga nan ya fara neman ta da kan sa a cikin garin Kano, gashi wayar sa ta fashe bare ya nunawa jama'a hoton ta, wani zuciya nace masa ya sanar da Imran wani zuciya kuma yace masa a'a ya kyale sa tun da Exam suke kada ya hana shi rubuta Exam nashi, gashi kuma Exam na karshe suke karya samu matsala gwara kawai ya kyale sa tun da sun kusa dawowa sai sun dawo kawai, haka yarinƙa sake sake a ransa yana yawon neman Jelly a cikin Kano bai taɓa kawowa a ran sa ta fita garin Kano ba shi yasa bai yi wani yunkurin neman ta a wajen Kano ɗin ba.


*KADUNA*

A kawo driver ya sauke su Jelly, nan fa Jelly taga duniya dan ko da ta fito daga motar ta kasa gaba ta kasa baya ta tsaya shiru a bakin hanya, ita daman a nata tunanin idan tazo Kaduna kawai gidan su Imran zata gani sai ta shiga amma sai taga a kashin hakan,

Tana tsaye tana ta kallon jama'a dake ta harkan gaban su har rana ya iso in da take, ganin rana ya iso in da take ne yasa ta tsallaka titi ta fara tafiya da kafar ta wadda bata san ina ta nufa ba, tana rungume da School bag ɗin tana tafiya.

Sosai tayi tafiya tsakanin ta da kawo har ta fita daga cikin jama'a ba tare da ta ankara ba, tafiya kawai take bata san in da ta dosa ba, bata fargaba sai jin tayi an damki jakar dake hannun ta ta baya, da sauri ta juyo tana kallon su, natasane su biyu, cikin tsawa wanda ya riƙe jakar yace "kawo ta nan" yan waige waige tayi sai lokacin ta lura da tabar cikin mutane, rai a ɓace ga yinwa na damun ta tace "bag ɗin kane da zaka ce na kawo" matasa ne biyu tsaye kai da ganin su kaga yan buguwa dan bakin nan nasu bakin kirin kamar gawayi sabida shaye shaye, san nan ga wani askin yan iska dake kan su sun bar dada a tsakiyar kai.

Wanke ta da wani wawan mari ɗaya daga cikin su yayi, ɗayan kuma ya fisge jakar suka hankaɗe ta ta faɗi kasa suka kwasa a guje suka bar wajen, kuka ta sa mai sauti tana faɗin "wayyo Allah daddy na" da kyar ta iya miƙewa zaune tana kuka tana kiran daddyn ta, yayin da shi kuma daddy ke can Kano yana haukan neman ta lungu da sako.

A wannan halin wani babban mutun mai ɗan yawan shekaru yazo wajen ya sameta, irin mazan tashan nan ne marasa mutuncin nan dan kallo ɗaya zaka wa face nashi ka gane hakan
kallon tsab yayiwa Jelly nan take ya fara washe baki, kusa da ita yazo ya tsaya yana faɗin "Yan mata me kike yi a nan kuma?" Cikin kuka da muryan shagwaɓa tace "wasu ne suka kwace min School bag ɗina" murmushi mugun ta yayi yana faɗin "ayya sannu ko? Yanzu dai to tashi muje gidana na baki wani jakar" jin yace zai bata wani jaka yasa ta yunkura tana kokarin muƙewa, cikin sauri yasa hannu yana kokarin ɗaga ta, a sukwane ta ja baya cikin tsiwa tace "Don't touch me" ko a jikin sa bai damu ba yace "Okey to tashi da kan ki" ba musu ta miƙe sai shagwaɓe fuska take tana turo baki, shi kuwa mutumin sai murmushi irin na yan bariki yake, ya nuna mata hanya wani yar lungu yace suje, ba musu ta wuce yabi bayan ta sai washe baki yake, yana murmushi irin na yan bariki.


Yayin da shi kuma daddy bai dawo gida ba sai 2 na dare, da kyar yake iya jan kafar sa ya shiga bedroom na shi, nan ya samu dolly saman gado sai kuka take, ba karamin tayar masa da hankali dolly keyi ba, dan in ya ganta sai yaga kamar Jelly na zaune a gefen ta, yau daddy ya kasa cin abinci ma bare wani zancen wanka, yana shigowa bedroom ɗin dolly ta taho da gudu ta haye jikin sa tana yar kara, runtse ido yayi ya wuce yaje ya sanyata cikin kejin ta sai kuka take amma ya share ta kamar bai jiba ya wuce ya dawo ya zauna saman gado ya haɗe kai da gwiwa yana tunanin mafita, ta ina zai fara neman Jelly gobe.

A wajen zaune ya kwana kamar yadda yaga rana haka yaga dare, babu alamar barci ko kaɗan a idon sa
ana kiran sallan asuba ya fice daga gidan ko wanka bai samu daman yi ba, yana yin Sallah ya wuce police station dan yaji ko ansamu wani information akan ta kwata kwata yama manta da wayar sa bai kaita gyara ba.

Ko da yaje police station ba wani information haka ya wuce neman ta lungu da sako ko abinci bai ciba dan baya jin yinwa ko kaɗan, bazama yayi cikin gari kawai yana neman ta.

💞KADUNA💞

💞Aafia💞

Zaune Aafia take a cikin department nasu department of law, tayi shiru tana latse latse a wayar ta, jikin ta sanye da atamfa riga da skit ɗinki ya kamata sosai, ya bi shape ɗin jikin ta ya zauna, yayin da tayi ɗaurin ture kaga tsiya a kan ta, ga uban attachment da ta zubo har baya kamat gashin ta, sai faman turɓune fuska take.

Baki ɗauke da sallama Rufee ta kariso wajen tana wani murmushi kamar ba na lafiya ba, hannu ta miƙa wa Aafia suka gaisa, Aafia na faɗin "Ina su Amal" "Amal tana tare da Mansur, ita kuma Anisa taje sayan drinks" Rufee ta bata amsa, shiru Aafia tayi bata sake magana ba.

"Aafia a koi wani Alhajin dake son magana dake ya takuramin, dan Allah a wannan karon kam kiyi hakuri ki bashi dama shi kam, na san halin ki yanzu zaki iya cewa ba haka ba shi yasa tun kan kice nake nema masa alfarma" ɗaure fuska Aafia tayi kafin tace "Rufee kin dai san bana son irin hakan ko? Karatun nazo yi school ɗinnan ba kula samari ba, bani da lokacin ɗa namiji a rayuwa ta ta yanzu, idan kuma na gama School kin san zaɓi na mutun ɗaya ne Prince Nawid duk da ban san shi ba, ban san ina zan ganshi ba, ban san wanene shi ba, amma dai shi nake so, tun ranar da na fara ganin taimakon da yayiwa wata mara lafiya a Tv daga ranar ya shiga raina bana ganin kowa sai shi, shiyasa ma bana kula maza kin san hakan, dan haka kada ki sake kawomin zancen wasu mazan bana so" yar dariya Rufee tayi kafin tace "To shi kuma TGA ɗin fa? Ko kin dai na son shi ne?" Guntun tsaki Aafia taja kafin tace "Ina mutuwar son shi mana, amma tun da na san ba samun sa zan yi ba ai dole na kama dahir, mutumin da Bature ne bai san Nigeria a ido ba sai dai a suna, kuma chiristen ne fa waya sani ma ko baya son bakaken fada, ko ya tsani Musulmai kin san fa turawan nan haka suke basa son Musulmai da kuma bakaken fata" dariya Rufee tayi kafin tace "Wallahi kuwa muna wahalar da kan mu wajen son turawan nan, gashi mafiyawancin su ba son bakaken fata suke ba, sannan dayawa daga cikin su basa son musulmai da addini musulunci baki ɗaya" Aafia na kokarin yin magana Umaisha ta kariso wajen bakin ta ɗauke da sallama

Aafia da Rufee har suna haɗa baki wajen amsa mata sallamar, kusa da Aafia ta tsaya sai faman kwaɓe fuska take tana turo baki kamar biro "lafiya Umaisha kike kwaɓe fuska haka?" Cewar Rufee uwar son jin gulma, kara turɓune fuska Umaisha tayi kafin tace "Wannan yaya Akil ɗin ne mana ya wani dami mutun da kira, nifa Aunty Aafia yanzu bana son shi, da ɗin ma soyayyar yarin tane, yanzu kuma ina big girl kama ta me zanyi da Small boy, ni gaskiya sai babban mutun irin mai 35 years ɗin nan zan aura" shekewa da dariya Rufee tayi tana tafa hannu tana faɗin "Gaskiya Umaisha yanzu ai ke ba matan yara bace sai manyan alhazawa dama kuma gashi suna ta bibiyar Aafia taki kulasu, ke tun da irin sune zaɓin ki wlh sai na haɗa ku kawai" Umaisha na kokarin yin magana Aafia ta rigata da cewa "Ke Umaisha wallahi ki kiyayi kanki ina rabaki tam, karki kuskura ki bari yaya Akil ya damkeki kin san dai halin sa, wallahi ina faɗa miki yanzu in da ya jima rabon sa da Nigeria nan ina da tabbacin ya kusa zuwa" dogon tsaki Umaisha taja kafin tace "Nifa a dane ya min wannan iko da iskancin nasa kuma na hakura na biye masa, yanzu ko wlh bai isa ba, ina da yancin nayi abun da nake so, kuma babu wanda ya isa ya aura min wanda bana so yanzu nasan me nake" Aafia zatayi magana wayar Umaisha ya fara kara, ansan wayar Aafia tayi, da mamaki ta ɗago ta kalli Umaisha "Ke Umaisha waye kuma Basir ɗan damuwa?" "Yaya Akil mana shi na sawa basir kuma ɗan damuwa" Umaisha ta faɗa tana jan tsaki, waro ido waje Aafia tayi tana salati, Umaisha tafi karfin ta, ita kam Rufee hannun Umaisha taja suka wuce tana faɗin "Ke dai Aafia ki zauna kan ki ya kulle ga kanwar ki nan ta gane gaskiya, muje Umaisha ke ba matar yara bace" baki galala Aafia ke kallon Rufee da Umaisha har suka kurewa ganin ta, sannan ta dawo da kallon ta kan wayar Umaisha dake ta faman ringing.

Bayan kiran Akil ɗin ya katse ne ta shiga binciken wayar da kyau dan taga me Umaisha ke yi,
ko ta ina Aafia ta shiga a wayar sai ta samu massage ɗin Akil, kama da ga WhatsApp, facebook, Instagram, Twitter, dukka massage ɗin Akil take cin karo da shi, in da yake wa Umaisha zazzafar warning a kan kar ta kuskura ya dawo ya samu tayi wani abun da ba dai dai ba, sai kuma massage na tambayar ta lafiya bata ɗaukan call ɗin sa tun last week.

Sosai Aafia ta binciki wayar dan taga ko dai Umaisha ta samu wani saurayi ne yasa tace bata son Akil, amma ina ba wani hiran ta da wani namiji da ta gani, Akil ɗin dai shi kaɗai ne, sosai Aafia ta sanya ƙwaƙwalwar ta cikin tunanin me yasa Umaisha zata ce bata son Akil yanzu, bayan tun tana da 15 years a duniya take dakon son sa bata taɓa cewa bata son shi ba sai cikin yan kwanakin nan, haka Aafia ta rinƙa tunani amma bata samu wani solution ba, gashi sai kira Akil yake ta kasa ɗauka dan bata da amsan da zata bashi in ya tambaye ta ina Umaisha kuma tasan halin sa yanzu tana ɗauka zai iya fara mata ruwan bala'i shi yasa ma bazata ɗauka ba, ranta cike da tunani ta tura wayar Umaisha cikin jakar ta ta ci-gaba da latsa nata wayar tana mamakin sauyawan Umaisha.


*💞WASHINGTON DC💞*


Zaune suke a palon kasa da daddy, uncle Herry, James, Tga, John, Jay, sai Michael da ya tada kai da cinyar Tga yana latsar wayan sa, Romeo ne kaɗai baya wajen kasan cewar shi daman bai cika zama a palon kasa ba, sai hira su uncle Herry suke cikin kwanciyar hankali, ga sanyin Ac da daddaɗar kamshin air freshener dake tashi a palon, gwanin ban sha'awa.

Baki ɗauke da excuse wata kyakkyawar maturiya ta shigo palon wadda idan ka ganta zakaga kamannin Micheal a face ɗin ta, jikin ta na sanye da wandon jeans baki sai t-shirt ta ɗaura fleece jacket a saman kayan nata wadda yazo mata har gwiwar ta, babbar mace ce ba yarinya bace.

Jin voice ɗin ta yasa Michael miƙewa a sukwane, yayin da gaba ɗaya palon suma suka miƙe suna kallon ta da mamaki.

Kallo ɗaya Michael ya mata ya kawar da kan sa, nan take face ɗin sa ya sauya kamar ba shi ba brown eyes nashi suka sauya launi zuwa ja jijiyon wuyar sa dana kan sa duk sun tashi cikin tsawa da ɓacin rai yace "get out before I open my eyes!!!" cikin sanyin Murya James yace "Please Michael stop saying h....Bai kai karshen maganar ba Michael ya daka masa tsawa mai firgitar da kwakwalwar mai sauraro "shut up James!!" Tashin sense a fusace James yace "are you mad Michael? are you heard what you are said"

damko wuyar rigar James Michael yayi tare da haɗe wa da wuyar tasa ya shaƙe sa da karfi yana kallon cikin idon sa, ga jijiyon kan nan nasa duk sun tashi sai zufa yake haɗawa duk da sanyin Ac dake palon, sai faman furzar da iska mai zafi yake daga bakin sa, ran maza ta ɓaci, rai a matukar ɓace yace "I hate her, I don't want to see close to me, tell her to leave this house, if not i will kill her with my hand" ya kai karshen maganar tare da kara shaƙe wuyar James ɗin da karfin gaske, cikin fushi James yasa hannu ya damki hannun Michael dake wuyar sa yana kokarin ɓanɓaren hannun Michael ɗin daga wuyar nasa yana faɗin "Oya go an kill her!!" Yayi maganar cikin ɓacin rai, tashin hankali su Jay basu taɓa ganin James yayiwa Michael magana cikin tsawa haka ba sai yau, basu taɓa ganin in da suka samu saɓani ba sai yau, daddy na kokarin yin magana cike ta tashin hankali a face nashi, bai kai ga buɗe baki ba yaga Michael ya ya kara shaƙe James da karfi kamar zai kashe shi, yayin da shi kuma James ke kokarin ɓanɓare hannun Michael daga wuyar sa, ita kuwa mum ɗin nasu ta kasa gaba ta kasa baya ta tsaya kawai tana hawaye tana kallon su, da sauri uncle Tga ya nufo su da niyar ya rabasu, sai ganin yayi Michael ya hankaɗe James ya nufi mum ɗin su da sauri

a fusace James ya miƙe ya riƙe Michael ɗin, a sukwane Michael ya juyo ya kaiwa James mugun bugu a wuya, wani irin azaban zafi James yaji ya ziyarce sa a wuyan nasa, cikin fitar hayyaci da ɓacin rai ya haɗe hannun Michael dukka biyu ya ɗaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login