Showing 114001 words to 117000 words out of 194715 words

Chapter 39 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

989

ne suka taimaka mata zuwa ɗakin su suna mata sannu.

Cikin dattin ɗakin nasu suka koma suka zauna suka buga uban tagumi sukayi jugum jugum kai daga ganin su kasan suna cikin tashin hankali da ba zai misaltu ba.

💞RUFEE💞

cikin kungurmin daji ne mai yelwan bishiyoyi da ciyayi dogaye, waje ne mai bantsoro, haka Rufee ta keta wayan nan grasses ɗin ta wuce ta nufi bayan wata katuwar dutse mai ɗauke da yar karamar kogo a wajen, kan saman dutsen taje ta hau, da kyar ta iya hawa, ta zauna zaman dirshan saman dutsen tana haki kamar wadda tayi gudu.

Tana zama ba jimawa wani tsohon mutumi ya ɓullo a saman wata yar dutse dake wajen, tsohone sosai yana da dogon jenu fari kal, sai dai da alama gemun sawa yayi ba nasa bane, mummuna da shi bashi da kayan gani yana da ido jajawur kamar jini gasu manya manyan kamar ball abun tsoro, ga hancin nan nasa a ɗage kamar irin nasu Barbushi abuɗe kamar kofa, mutumin nan abun tsoro ne, face na sa ba kyan gani ko kaɗan

babu ko tsoro a idon Rufee ta fara masa bayani a kan abun da ya kawo ta "Baba daman na zone ne yau ma a kan wacan Aafia" da muryan mara daɗin ji kamar an tada injin niƙa baban yace "Me kuma ya faru? Bata baki kuɗin ne?" Girgiza kai Rufee tayi tana faɗin "A'a tana bani kuɗi ina so ne yanzu a juyamin tunanin ta tadawo sai abun da nace mata shi zatayi dan gaskiya tana kawo min cikas a lamurana, akoi wani Alhajin da yace zai bani 10 millon idan har na kawo masa ita amma ba yadda ban yi da ita ba taki yarda ta masa magana ma bare kuma har ta bishi ta biya masa bukatar sa, ni kuma na samu abun da nake so" shekewa da dariya baba yayi kafin yace "Karki damu kin san aiki na ai yanzu dai ki zube kuɗin ni kuma zan dawo miki da Aafia cikin tafin hannun ki" washe baki Rufee tayi kafin tace "Yauwa baba kuɗi kam yanzu ma kuwa zan zube maka su dan jiya 100k Aafia ta bani" washe baki shima baban yayi, buɗe jaka Rufee tayi ta ciro masa kuɗi ta ajiye masa a gaban sa, tana ajiye kuɗin baban ya ɓace da shi da kuɗin, dariya tayi ta miƙe ta sauƙo kasa daga saman dutsen ta nufi hanyar da tabi tazo sai dariya take tana jin daɗi tana faɗin "Aafia kenan idan kin san wata ai baki san wata ba haka kawai zaki hana manya masu kuɗi su bani kuɗi ga dama na samu amma kina neman hana ni, shegiya gaki da farinjini kamar me, ko wani Alhaji sai yace sai ke yake so, ke kuma kina wulakan tasu to Wlh baki isa ba sai na mai daki tantiriyar yar duniya ki bi maza a guje sannan ki bi kayan maye a guje, kafin na shigo gidan uban ki a matsayin mata kin riga da kin bi duniya kin lalace" kamar wata zararriya haka ta kutsa cikin grasses nan ta wuce sai surutu take ita kaɗai.

*KADUNA*

Kwance saman gadon majinyata Jelly take jikin ta na sanye da kayan majinyata, an mata ɗin ki a kan ta duk in da taji ciwo an ɗinke mata an sanya mata bandeji, a takaice dai ta samu kulawa sosai sai dai bata motsi, har yanzu tana sume, ita kuma Hajiyar da ta bugeta tana zaune a gefen ta ta buga uban tagumi da alama ta shiga damuwa sosai da sosai, dan sai haɗa zufa ma take duk da Ac dake ɗakin hospital ɗin.


*KATSINA*

Tun jiya sai yau su Jehan suka samu likita ya zo ya duba mum, nan ya gaya musu tashin hankali da yafi karfin tunanin gwaggo, dan da farko ma likitan yaki yarda ya faɗa musu yace su turo masa namiji, sai da gwaggo ta kafe tace basu da kowa dan haka ya faɗa musu kawai, shine ya kira gwaggo office na sa nan yake faɗa mata abun da kan ta ya kasa ɗauka, mum na ɗauke da wani babban ciwo a zuciyar ta wadda dole a mata aiki cikin gaggawa idan ba haka ba zata iya mutuwa, duk ba shine damuwar ba, babban damuwar a nan shi ne dole waje za'a fitar da ita dan wannan asibitin basu da kayan aikin da zasu mata aikin, wannan kwararrun doctors ake buƙata, har wani duhu duhu gwaggo take gani a idon ta, ita damuwar ta ɗaya shine samun lafiyar mum kuɗin ba damuwa bane dan mum tana da manya manyan gwala-gwalai da idan a ka haɗa a ka sayar a kalla zasu kai 10 millon so kuɗi bai dame taɓa, lafiyar mum shi ne a gaban ta.

Da sauri ta fito daga office ɗin dr Jehan na tambayar ta amma ina bata bi ta kam kowa ba ta nufi hanyar fita hospital ɗin dan taje gida, har ta kai bakin gate ɗin hospital ɗin sai kuma ta juyo tayiwa Sadiq da yazo tun safe dan duba jikin mum, alama da hannu gwaggo ta masa a kan yazo su tafi dan bata san hanya ba, a tare Sadiq da Jehan suka miƙe sukabi gwaggo, idon Jehan ya kunbura sosai saboda kukan da ta sha duk ta sauya kamar ba ita ba.

Tare suka wuce gida da mai a daidaita sahu, suna shigowa gida kai tsaye ɗakin mum gwaggo ta nufa dan ta ɗauko gwala-gwalan mum suje su sayar su san yadda zasu yi su fitar da mum kasar waje a mata aiki da wuri.

Gwaggo na shiga ɗakin mum taga ikon Allah nan taga ba komai duk wani abu mai amfani an kwashe har da wayan mum, ba abun da aka barmusu sai kayan sawan su, kamar mahaukaciya haka gwaggo ta fito waje tana ihu, da sauri Jehan da ta tsaya ta jingunu da bango ta taho ta tare gwaggo tana faɗin "Gwaggo me ya faru menene?" shima dai Sadiq abun da yake tambaya kenan, me ya faru

kamar karamar yarinya haka gwaggo ke kuka tana faɗin "Shikenan nan komai ya kare sun kwashe komai sun kashe mu Jehan babu komai innalillahi wa inna ilaihir shikenan yanzu muna ji muna gani zamu rasa Maryam bayan mum rasa Nawazudden ga Rimsha babu ita ya Allah ka ɗauki rayuwa ta kafin ka ɗauki na Maryam" tashin hankali kalma ɗaya Jehan ta kasa furtawa dan ta rasa ta ina zata fara kuka kawai take, shi ma Sadiq kuka yake musu sosai yana addu'ar Allah ya kawo musu mafita.

Da kyar ya iya saita kukan sa yace "Gwaggo meke faruwa ne? Me mum take bukata yasa kuke neman kuɗi?" Cikin kuka Gwaggo tace "Ya zama dole na faɗa muku dan ina ji a jikina zan riga Maryam mutuwa, to ko na mutu kuyi kokarin wajen ganin kun taimaki Maryam idan kuma Allah yasa itama kwanan ta ya kare to Sadiq ga amanar Jehan ka riƙe ta kamar kanwar ka" nan gwaggo ta basu labarin abun da ke damun mum san nan da kuɗin da suke bukata almost 5 million dan su fita kasar waje ai wa mum aiki, ta kai karshen maganar da kyar saboda kuka da ya ci karfin ta, sosai Sadiq ke hawaye yayin da ita kuwa Jehan hawayen idon ta suka tsaya cak idon ta ya bushe gaba ɗaya taji bata bukatar ci-gaba da kuka kuma dan komai ya kare mata me zata yiwa kuka kuma, komawa tayi duk tsabta irin nata haka yau tayi zaman yan bori a kasa ta jingina kan ta da bayan gwaggo ta ɗaga kai sama kamar mai tunani, while ita kuwa gwaggo sai hawaye take haka shi ma Sadiq.


💞WASHINGTON DC💞

Yana yin garin gwanin ban sha'awa a hankali iska ke kaɗawa mai nishaɗan tar da zukatan masoya, sanyi Ac ne ya ratsa shi kasan cewar Romeo ya kara gudun Ac dan su tashi daga barcin, ya san cewa dukkan su basa son sanyi idan sanyi yayi musu yawa basa iya barci shi yasa ya kara gudun Ac.

A hankali Michael ya waro brown eyes nashi masu ɗauke da barci, kai tsaye kan kyakkyawar face ɗin Romeo suka sauka, yana zaune a saman bedside drawer jikin sa na sanye da bathrobe fara kal kamar yanzu ya cirota daga letar ta saboda tsabtar ta, bai ɗaure kyakkyawan dark black curly hair sa ba ya bar shi ya kwanta masa har baya while wannan guntu na gaban yana nan a gaban goshin sa, soft skin na sa nan sai kyalli take a kwance luf taji hutu, sai wani fitinanniyar kamshin dake tashi a jikin sa, lallausan red lips na san nan idan ka gani kace ya sanya lips balm saboda kyalli da yake kuma yayi red sosai, kyawawan hannun sa na sanye cikin hand gloves masu kyau yana riƙe da allura yana kokarin haɗawa.

Zubawa Michael wayan nan dara daran blue eyes ɗin nasa yayi yana kallon sa, ganin abun dake hannun sa yasa Michael miƙewa zaune yana kwaɓe fuska yana turo ɗan karamin bakin nan nasa,
da ya kalla alluran sa Romeo ke haɗawa, sai yayi sauri ya diro kasa daga saman gadon yana kokarin guduwa, gently Romeo yasa hannu ya riƙo hannun sa, turo baki Michael yayi kafin yace "I want to go and ease my self" lumshe ido Romeo yayi kafin ya buɗe su a kan face ɗin James dake ɗan motsi yana son farkawa "No, do it here" ya furta in a cool voice kara turo baki Michael yayi har ga Allah baya son alluran nan amma duk lokacin da aka ɓata masa rai ko wani abun da badaɗi ya faru sai Romeo ya masa wannan alluran, kamar zai yi kuka ya koma ya zauna yana jin haushi dan dai ba yadda zai yi ne bai isa yace wa Romeo baya so ba, da James ne da ba abun da zai sa shi ya tsaya ya masa.

Shi kuwa Romeo ko a jikin sa ya ya ɗaure hannun ya nemi jijiya ya masa alluran san nan ya miƙe ya nufi dressing room na shi ya bar Michael rike da wajen da a ka masa alluran yana turo ɗan karamin bakin sa kamar biro.

Dai dai lokacin James ya farka saboda sanyin Ac da ya masa yawa, kallo ɗaya yayiwa Michael ya gane me ya faru dama kuma yasan da kwanan zancen alluran, dan haka sai ya miƙe yana tsokanar Michael ya fice daga bedroom ɗin ya nufi palon kasa.

Nan ya isko daddy da Tga suna gardama a kan daddy ya dage sai yaje hospital dan an kirasa a waya yar abokin sa tasha poison tana bukatar taimakon gaggawa, gashi kuma shi daddy Romeo ya hana shi zuwa aiki, yanzu ma ya rikice ne yana tsoron kar yarinyar ta mutu sannan kuma bai san Romeo ya dawo ba, dan fitan Romeo kawai ya gani bai ga dawowan sa ba lokacin yayi barci shi yasa yace zai je wajen aikin.

Ganin abun dake faruwa yasa James karisawa wajen da sauri yana faɗin "Uncle what is happening" a fusace Uncle Tga yace "where is lion?" "He's inside his room" James ya bashi amsa yana kallon daddy, wucewa Tga yayi ya haura sama, daddy kuma ya wuce ya nufi waje abun sa dan a tunanin Romeo bai dawo ba, da sauri James ya riƙe sa yana faɗin "Please dad don't..bai kai karshen maganar ba daddy ya dakatar da shi ta hanyar marairaice murya yace "Haba James my friend daughter fa tayi poison na kan ta, please ku bari naje na ceto rayuwar ta" girgiza kai James yayi kafin yace "Daddy you already know that lion baya magana biyu so just kawai ka hakura wasu likitoci su dubata" daddy na kokarin yin magana idon sa ya sauka kan face ɗin Romeo dake tsaye a sama bakin kofar shiga part ɗin sa furkar nan tasa a ɗaure tamau kamar hadari babu alamar wasa a tattare da shi ko kaɗan, tsabar yadda ya ɗaure fuskar har sai da gashin gerar sa suka haɗu daman kaɗan ya hana basu haɗe ba, shiyasa daya ɗaure fuska suka haɗe, nan take jikin daddy ya fara kerma ba shiri ya yasar da jakar hannun sa

Gently Romeo ya fara magana da wannan sexy voice ɗin nasa sannan ya tsare daddy da sexy eyes ɗin nan nasa masu ɗaukan hankali "where are you going?" Cikin sauri Tga dake gefen sa ya buɗe baki ya fara magana, hannu Romeo ya ɗaga masa alamar ba shi ya tambaya ba, daddy ya tambaya, shiru Tga yayi ya kama bakin sa yana kallon daddy, a tsorace daddy ya yiwa Romeo bayani a ta kaice, yar abokin sane tasha poison saboda son da takewa Romeo shi kuma daddyn ta da daddy suna tsoron ma Romeo yaji maganar dan zai iya harbe ta da kan shi, gashi yarinyar bata samun ganin Romeo a zahiri sai dai a Tv dan ko daddyn ta zai zo gidan su Romeo baya taɓa yarda yazo da ita saboda ya san halinsu Michael ma kawai in ya ganta tsab zai iya harbe ta da bindiga, dama dai James tace to shi yana da ɗan saukin kai, hakan yasa daddyn ta kullun yake ce mata zai faɗa wa Romeo idan sun haɗu, amma kuma bala'i tsoron Romeo yake kamar me, ko gaishe da Romeo baya iya yi saboda tsoron sa da yake ji, ita kuma yarinyar ta gaji da jira shi ne tace wa daddyn ta in dai bai faɗa wa Romeo ba zata sha poison, da a ka kwana biyu taga daddyn ta bai faɗa wa Romeo tana son shi ba shi ne tasha poison ɗin a ka kai ta hospital ɗin daddy, to shi daddy Romeo ya hana shi zuwa aiki kwata kwata, saboda ya hana daddyn shan wine, domin daddy idan yaje hospital baya iya yin aiki sai yasha wine wannan dalili yasa Romeo ya hana shi zuwa aiki gaba ɗaya yace ya zauna a gida dama ai ya tsufa, gashi kuma kwararen likitane mumber ɗaya a garin nasu, ana ji dashi sosai, doctor William jacop, sai dai baya iya aiki sai yasha wine yayi tatul ya bugu sosai.

Da hannu Romeo ya yiwa daddy nuni da hanyar bedroom na sa ba tare da yayi magana ba kasan cewar bai son yawan magana, jiki ba kwari daddy ya wuce bedroom na sa, zuciyar sa sai dukan uku uku yake yana addu'ar Allah yasa kar yar abokin sa ta mutu, yasani kab asibitin nasa ba wani likitan da zai iya yiwa yarinyar nan aiki cikin ƙan ƙanin lokacin ya cito rayuwar ta sai shi amma sai dai gashi yau yana ji yana gani shan giya ta ja masa ba zai taimaki yar abokin sa ba, ba zai iya tinkarar Romeo yace masa ba zai sha wine ba yayi hakuri ya barshi yaje ya mata aiki ba, yana jin tsoro dan ya san ma Romeo baya magana biyu ko mai zai faru idan yayi magana yayi ne.

Wucewa James yayi ya nufi hanyar fita daga palon dan suna da meeting da abokan harkallan sa karfe 6 dai dai, shi yasa zai yi sauri yaje saboda Romeo ya hana su wuce 9pm a waje shi yasa yanzu ya lallaɓa ogannin na sa akan a dai na meeting ko wani harkalla da daddare sai da safe, kasan cewar James shine babban yaron su da sukafi ji dashi yasa suka hakura suka dai na meeting na dare, dan James yana da girma a idon su suna son sa sosai, shine babban yaron su da idan suka bashi aiki cikin kankanin lokaci yake wannan aiki ya gama, har mamaki suke domin ko shugaban kasa suka ce James ya kashe zai iya kashe shi tsab ya samu horo daga wajen su sosai kama daga harbi da bindiga faɗa da hannu da sauran su, sai dai shi James ɗin yana ɓoye ya iya duk wayan nan abubuwan a gida saboda kar Romeo ya fahimci a koi wani abu, hakan yasa yake zama kaman wawa a cikin su ya nuna musu baya son tashin hankali kuma yana da hakuri, dan karsu kawo wani zargi a ransu amma ba abun da bai iya ba kuma shima ba wai saukin kai gare sa ba kawai basajane amma yana da zafi.

"Where are going James" Romeo ya tambaya in a cool voice yana tsare James ɗin da sexy eyes ɗin nan nasa masu firgitar da marasa gaskiya su kwantar da hankalin yan mata su razana zukatan jaruman maza, cikin sauri James yace "I just want to go out and chill" wucewa Romeo yayi ya koma bedroom na sa ba tare da ya sake magana ba, shi kuma James ya fice waje da sauri, Tga ya kuma ya sauko kasa ya zauna saman sofa, while shi Micheal daman bai fitoba yana lafe a saman katafaren bed ɗin Romeo, su kuma Jay da John basa nan uncle Herry na barci.



Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞







TRIPLET'S💞




*THE BEGINNING*



💞STAR LADY💞




WhatsApp me for more information 09162620621




Episode 25


Kai tsaye *Florida avenue* James ya nufa sai sharara gudu yake da motar sa a saman shinfiɗaɗiyar titin da zata sada shi da*Florida avenue* ya sanya kiɗa na tashi yana tuƙi yana tunanin yadda zai yi da ogan su, dan yanzu sun dawo masa da zancen kashe GAR sabo, kuma sun matsa masa a kan maganar sosai, saboda sun san duk cikin yaran su shi kaɗai ne zai iya yi musu wannan aikin cikin sauri, kan sa ya kulle sosai ya shiga damuwa neman mafita.

Bai ankaraba ya buge wani mutumi da yazo tsallaka titin, a sukwane ya ja wata mahaukaciyar birki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login