Showing 159001 words to 162000 words out of 194715 words

Chapter 54 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

966

dogon tsaki yaja tare da sa hannu ya ɗauki wayar, irin wayar nan ne da ake ajiyewa saman table wadda costumers ke kira dan bukatar abu. Picking na call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnen sa.

Jim kaɗan ya ajiye wayar ya ɗago ya kalli Jehan yace "Kije room 22 akoi wani costumer da yake bukatar ma aikaci ɗaya" rai a ɓace tace "to me zan masa" mai da wayar yayi ya ajiye yana faɗin "Idan kinje ai koma menene zakiji" guntun tsaki taja ta wuce ta tafi ta bar Ibraheem da binta da ido yana mamaki.

Ko da taje bakin kofar Room 22 ɗin sai da taja dogon tsaki kafin tayi knocking na kofar, bugu ɗaya tayi aka buɗe kamar daman jira ake.

Wani Alhaji ne kato bakin kirin da shi gashi da katon ciki, yana sanye da gajeren wando, kaya ya miƙo mata yana faɗin "Wanki ne zaki min" zaro ido tayi ta kalle sa kafin ta kalli kayan dake hannun sa yake miko mata, singlet and boxers ne, dawo da kallon ta kan face nasa tayi a kule tace "Yanzu saboda baka da hankali nice zan wanke maka shot naka? Ko kunya baka ji ba kato da kai, hauka nake zan wanke wandon kato kamar ka, tab lalai to Jehan dai ba za tayi wanna kazantar ba sai dai wata, daman wanna aikin shine aka kawo ni nayi, to wlh ba zata saku ba, ba zan iya ba"

Tashin hankali zaro idon mutumin yayi kafin ma yayi magana, Jehan ta sa kai ta wuce ta bar wajen, da sauri mutumin ya leƙo da kan sa waje yana kallon ta, mamaki ya sa ya kasa komawa cikin ɗaki, a ransa yana faɗin "wannan yar yarinyar dai a shekaru da wuya ta wuce sha bakwai tsawo ne kawai gare ta, shine zata cemin katon banza, anya wannan a gaban iyayen ta ta taso kuwa, anya ta samu tarbiya, to wlh ba zan zauna a hotel ɗin nan ba, basu san darajar costumer ba, har ma'aikaciya tana da bakin cewa costumer ba zata yi masa abun da yake so ba, tab lalai da sake" da wannan tunani ya koma cikin ɗaki ya ɗauki waya ya sake kiran Ibraheem,

Ita kuwa Jehan kai tsaye wajan sauran ma'aikatan tan restaurant ɗin ta nufa dan ta tambaye su ko shine aikin da suka zo yi kenan wato wankin kayan costumers.

Da sallama ɗauke a bakin ta ta karisa wajen da sauran ma'aikatan ke zaune, har suna rige rigen amsa mata sallamar nata, sunga kyakyawa, dan Jehan akoi farinjini na fitar hankali, duk in da taje sai an so ta, haka itama Rimsha

Sai wani washe baki ma'aikatan suke suna ɗaga mata gaisuwa, ita kuwa kara ɗaure fuska tayi kafin tace "dan Allah zaku iya faɗa min aikin me muka zo yi a nan?" Kallon kallo suka fara yiwa junan su, lallai wato wanna ma bata san aikin da ya kawo ta nan ba tab akoi cakwakiya.

Ɗaya daga cikin sune ta miƙe ta dafa kafaɗar Jehan ta fara yi mata bayanin irin aikin da ya kawo su nan "Wanke wanke, shara, mopping, kai wa mutane abinci idan suka zo ci, sanna kaiwa yan ɓangaren hotel abinci room nasu idan suka buƙata, wasu costumers ɗin zasu buƙaci mu musu wanki su biya mu, wanna ma yana daga cikin aikin mu, sanna dole ki san ta yadda zakiyi wajen kontarwa da costumers hankali har suji daɗin wanna restaurant ɗin gobema su dawo cin abinci, dole ki koyi sakin fuska da murmushi dan jawo ra'ayin costumers su sake dawowa cin abinci, danna dol.... Bata kai karshen maganar ba Jehan ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Ya isa haka, da yake sayata sukayi ba ai dole su ce nayi kaza nayi kaza, to wlh ni idan ba kaiwa costumers abinci ba, ba wani aiki da zanyi a nan, dan ni Ibraheem bai cemin da Hotel ba iya restaurant yace min, kuma a restaurant ɗin ma iya serving abinci kawai ya cewa iyaye na, dan haka iya shi kawai zan yi" ta kai karshen maganar tare da juyawa ta bar wajen ta nufi wajen girkin restaurant ɗin. Mamaki ya hana sauran ma'aikatan magana, yau sun haɗu da abun da yafi karfin su.

A hanyar ta na zuwa wajen girkin restaurant ɗin ne suka haɗu da Ibraheem, rai sa a matuƙar ɓace, cikin tsawa yace "Ke zonan!!" Ba musu taje "Ke dan uban ki baki da mutunci ko? Baki da albarka ko? Mu rufa miki asiri mu ɗauko ki mu kawo ki nan dan ki samu abun da zaki rufawa kan ki da iyayen ki asiri, shine bai miki bako? Yanzu dan baki da kirki baki da albarka costumer kikaje kikayiwa ɗiban albarka haka eh? Keda muka kawoki dan ki jawo mana costumers shi ne zaki kora mana wayan da muke dasu ko? To wlh baki isa ba dan uban ki, tun wuri kije ki bawa mutumin nan hakuri ki karɓo kayan sa kizo ki wanke idan kina son zaman lafiya kinji na faɗa miƙi!!!"

Tsare sa da wayan nan dara daran idon nata tayi babu ko kyap tawa, har sai da ya kai aya a maganar tasa, sannan gently tace "Ba zan yiwa wani katon banza wanki ba, dan ba wanna aikin mukayi da kai ba, masu sayan abinci kawai zan kaiwa abinci idan sun zo saya, bayan su ba wani aikin da zanyi, sai kuma maganar uniform karka sake min maganar sa dan ba zan saka ba" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi in da take da niyar zuwa wato wajen girkin su.

A fusace Ibraheem ya bi ta ya je ya sha gaban ta, dan yana takamar ya ranta mata 500k ne yasa ya ɗaga hannu a fusace zai mare ta, cak ta rike hannun sa, cikin fushi ta ɗaga hannu zata mare sa, sai kuma ta fasa saboda ta tuna da cewa ko ba komai ya taimaka musu ya basu aron kuɗi gashi yau ana yiwa mum aiki saboda shi, dan haka bai kamata ta masa irin wannan rashin kunya ba.

A hankali ta sake masa hannu sa tare da sauke nata hannun cike da ɓacin rai tace "Ina ganin mutuncin ka amma kana neman ka kaini bango, ka kiramin ogan naka zanyi magana da shi, domin kuwa bashi da iko dani, daga yanzu ba zan sake yin magana da kai ba, da ogan ka zanyi magana, dan na lura duk wanna hargagan da kake kana yin sane dan tsoron kar ogan ka ya maka faɗa a kan ban sanya uniform ba dan sauran su, to ni ka kiramin shi bari na masa bayani da baki na, a kan cewa ba zan saka uniform ɗin ba, kuma iya kai abinci zanyi, sanna shawara da zan baka shine, ka daina jin tsoron wani ɗan adam kamar kai, kaji tsoron Allah kaɗai, idan kana jin tsoron Allah tofa babu wani ɗan adam da zai baka tsoro ko ya maka wani abun da Allah bai kaddara maka ba, bana son hayaniya amma kana son sani cikin ta, bana son yawan magana shima kana sani yi, please ina ganin girman saboda taimakon da ka mana, dan Allah ka fita harka ta!!!" Tana kai karshen maganar ta wuce ta bar Ibraheem yayi mutuwar tsaye a wajen, yau ya ɗauko wadda ta fi karfin sa


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞


TRIPLET'S💞



💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)



*Gargarɗi*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_




WhatsApp me for more information 09162620621






Episode 34-35


Tana kai karshen maganar ta wuce ta bar Ibraheem yayi mutuwar tsaye a wajen, yau ya ɗauko wadda ta fi karfin sa.

Nima dai Jehan tafi karfi na dan haka mu leƙo su Jelly mu dawo.


💞KADUNA💞

Yau dai Hajiya Turai tace ba zatayiwa Jelly wanka ba, dan Jelly ta girma, yanzu ta doshi 15 years amma ba abun da ta iya, saboda daddyn ta bai koya mata ba, komai shi yake mata da kan sa, bata iya komai ba sai shagwaɓa, sai dai daddy bai barta haka ba ya koya mata karatun Alqur'ani mai girma dana boko, Hajiya Turai tayi tunanin kodan saboda ciwon da take ciki ne yasa ta manta har da yadda ake wanka da sauran su, sai dai bata san dama already Jelly kam haka take ba, ciwon ne ya kara haukatata, ta zama asalin shagwaɓaɓiya haka, gashi tun da tazo gidan Hajiya Turai ke kokarin koya mata yadda ake wanka da sauran abubuwa, amma duk a banza domin kuwa ba wani abun da ta mai da hankali wajen koyan sa sai shirme, shi kuwa Abbo shi yake kara ɓata abun, dan kuwa idan Hajiya Turai tace ta koyi abu da kan ta, sai Abbo yace a'a dan Allah a kyale ta, taji da ciwo ne ko kuma taji da takura dan haka su kyale ta ta sha iska, hakan yasa Hajiya Turai wato Ummi bata takura mata da lallai sai tayi abu.

Yauma kamar kullun suna zaune saman dining table suna breakfast suna hira sama sama.

"Abbon Nawid ina son asamin baby a school dan ta ɗan koyi wasu abubuwa" cewar Ummi,

Nawid ne ya karɓi zancen da cewa "Eh Ummi haka ne, in ta shiga school zai taimaka mata wajen kara tunatar da ita abubuwan da ta manta a baya, dan ina da tabbacin a baya kafin wannan accident ɗin ya faru yarinyar nan tayi karatu, idan kika lura da yanayin jikin ta, ni wlh ina ganin ba yar gidan talakawa yar malam Shehu wadda aka gaji da ita saboda rashin abinci kamar yadda kuke faɗe bane, da ganin ta Allah kin san wanna renon madara da su Ice cream ce" shiru Ummi ta ɗan yi kafin tace "Haka ne kuma, amma fa ni ina ganin kamar ba yar nan Kd ba ce" Nawid zai yi magana Abbo ya riga sa da cewa "A'a ba za'a sata school ba, kuma ku dai na wani maganganu a kan ta, mu dai Allah ya bamu ƴa kuma mun gode, dan haka ya isa haka, makaranta kuma ba zata je ba, saboda laluran ta ko taje school ba wani abun da zata fahimter kawai ku kyale ta a nan ɗin" shiru Ummi tayi tana tunanin zancen Abbo gaskiya ne, karsuje a garin hira da tone tone har su tono wace ce Jelly suyi sanadiyyar barin ta wajen su, dan haka garama kawai su kyale ta kar ma su sata a School taje ta haɗu da wanda ya santa yaje ya faɗa wa iyayen ta suzo su ɗauke ta kawai a banza gara suyi shiru.

A ɓangaren Nawid kuma tunani yake akan me ya sanya Abbon sa yake yawan damuwa da Jelly haka ne, why kullun baya son a takura mata, baya son gaskiya a kan ta, abun ya fara yawa, amma da yake Ummi soyayyar da take wa Jelly ya rufe mata ido bata fahimci illar abun da Abbo ɗin keyi ba.

A ɓangaren shi kuma Abbo yayi saurin cewa kar a kai ta school ne dan baya son a kai ta makaranta wani wadda ya santa ya ganta ya gane ta har yaje ya faɗa wa iyayen ta, suzo su ɗauke ta ba tare da ya bayyana mata soyayyan sa ba, dan yasan in dai iyayen ta suka ɗauke ta tofa ko zai mutu ba zasu bashi auren taba, shiyasa yake son su barta a nan har lokacin da zai bayyana mata soyayyar sa.

Duk kan su dai kowa da abun da yake tunani, ita kuwa Jelly sai faman cin nama kaza take bata ma jin abun da suke faɗa, zancen su baya shiga kunnen ta.

Har su Abbo suka gama cin abincin su Jelly bata sani ba, tana can duniyar naman kaza, ta mance da su ma zaune a wajen.

Lokacin da ta gama cin naman ta, ta ɗago kai sai taga table ɗin wayam babu kowa, turo baki tayi ta miƙe ta wuce bedroom nata, dan yanzu ta ɗan kara sakin jiki tana iya zama a bedroom ɗin nata ita kaɗai.

Shi kuwa Nawid tunani fal ransa game da Jelly, haka ya shirya ya tafi office, Abbo kuwa ko ajikin sa sai wani daɗin ma yake ji, Hajiya Turai baiwar Allah da zuciya ɗaya ta riƙe Jelly har cikin ranta tana mutuwar kaunar Jelly, bata wani tunanin mugunta ko wani abu wa Jelly, haka zalika a nata tunanin Abbo ma a ƴar cikin sa ya ɗauki Jelly bata kawo komai a ranta ba, shiyasa idan yana yiwa Jelly wasu abubuwan bata damuwa, kuma duk hukunci da ya yanke a kan jelly bata taɓa damuwa, sai tace ai yar sace yana da damar yanke mata duk hukuncin da ya ga dama.

A ɓangaren daddyn Jelly kuwa, bawan Allah duk ya fita hayyacin sa, duk wanna murmushi kullun dake kan fuskar nan tasa ta kau, ya sauya kamar ba shi ba, ya zama so silent ko magana bai cika yi ba, sai in zai sayi wani abun, tun ranar da Jelly ta ɓata bai sake zuwa company ba har yau, Engineer Muhammad Imam ke kula da company yanzu, daddyn Jelly yana gida, yace ba zai sake zuwa ko ina ba har sai Jelly ta bayyana, saboda ɓatan Jelly har jini sai da aka kara masa, yayi baki ya rame sosai, sai manya manyan idon sa irin nata zaka gani a face nashi, saboda ramar da yayi har kasusuwan wuyar sa sun bayyana sosai, ya sanar da su Zuwaira duk wanda yazo neman sa suce baya nan, hakan yasa baban Muneer yazo neman sa yafi sau a kirga baya samun sa, dan kuwa su Zuwaira ce masa suke daddyn Jelly baya nan kuma basu san in da yake ba, idan ya kira wayar sa a kashe kasan cewar daddyn Jelly yaki gyara wayar tasa da ta fashe, kuma yaki gyarawa ne saboda Imran, baya son ya hana Imran rubuta Exam da zai yi da kyau, baya son jefa shi cikin damuwa, sai dai kuma abun da daddy bai sani ba, rashin samun su a waya da Imran bai yi ba yafi jefasa cikin tashin hankali fiye da komai, Imran ya shiga damuwa sosai a kan ko lafiya number bappan sa bata shiga, damuwar har tana nema tayi affecting nasa, baya wani karatu sosai, bai da aiki sai tunanin Jelly da daddy, yau saura 2 weeks dai dai su gama komai su dawo gida Nigeria, sosai shima Imran ɗin yayi rama saboda tunanin wani hali bappan sa da matar sa Jelly suke ciki.

Ba Imran kawai ba har Irfan da Akila sun shiga damuwar lafiya number bappan su bata shiga, shikam Akil daman ko number bappan nasa bai da shi bare ma yasan tana shiga ko bata shiga, ko number bappan sa kuma sirikin sa wato Abbin su Umaisha shima bai da shi, number Umaisha kawai gare sa.

Yau ne Abbi ya shirya tsab zai je Kano ya duba lafiya number daddy bata shiga, dan Irfan da Imran sun dame shi a kan yaje ya duba musu meke faruwa dasu Jelly, tun karfe 10 na safe ya fice yayiwa Aunty sallama yace ta sanar da su Aafia idan sun tashi barci.

Abbi na tafiya tamkar ya tafi ne da lafiyar Aunty, nan fa ta fara laulayin ciki wadda bata san tana da shi ba, tun fitan Abbi take ta faman amai a tsakiyar palon kasa, dan kuwa ta raka Abbi kofar palo ta masa Addu'a ya tafi ne ta juyo zata dawo, nan fa amai yace bata isa ba, tana kokarin gudu ta haura sama amma ina yaci karfin ta shi ne ta zauna a tsakiyar palon kawai tana tikar amai ɗin, kamar zata amayar da kayan cikin ta dukka, shi kuwa Abbi bai ji lokacin da ta fara amai ɗin ba, ya shiga motar sa ya tafi.

Sautin kakarin amai ɗin da take ne ya tashi su Aafia daga barci, daga su sai kayan barci suka sauko palon kasa, sai faman tura baki suke

Tun basu karisa sauko wa ba Aafia tace "Kutumar uban can, ke Halima dan jahila ce ke sai ki zauna a tsakar palo kinawa mutane amai dan ki samu amai ɗin muma ko? To wlh baki isa ba" Umaisha kuwa wucewa tayi ta kwata saman sofa tana faɗin "Amma gaskiya Aunty baki kyauta min ba, ina barci na kawai zaki tashe ni, gaskiya wanna zalunci ne, idan ma amai ɗin ne kije toilet naki kiyi mana amma sai kizo tsakiyar Palo, dan rashin hankali" tsawa Aafia ta dakawa Umaisha "Ke dallah ki mana shiru!! ba wani zancen adalci a nan yar iska dai iskanci ne yasa ta fito palo ta fara amai ɗin nan, kuma ni nasan da biyu tayi shi, kin san wanna amai ɗin da take wlh da alaman ciki gareta, shine ta fito ta nuna mana idan zamu mutu mu mutu to ba zamu mutu ba, zaki yabawa aya zakin ta" ta kai karshen maganar tare da wucewa fuuu ta haye sama ta koma ɗakin su, aunty kuwa ji take kamar ran ta zai fita, cikin ta sai murɗa mata yake, duk abun da su Aafia ke faɗe ko kaɗan baya shiga mata kunne dan ta fara fita a hayyacin ta

Umaisha na zaune tana kallon ta, sai da taga da gaske Aunty na kokarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login