Showing 99001 words to 102000 words out of 194715 words
yayin da wuyar sa ke sanye da gold chain necklace masu bala'i kyau da tsada, sai kyalli suke suna ɗaukan ido, hakan ba karamin kyau ta kara masa ba, kyawawan fararen kafafunsa na sanye cikin wata laullausan bedroom slippers fari tas mai bala'i kyau da laushi kamar jikin mage, sai fitinanniyar kamshin wannan perfume ɗin nasa ke tashi daga jikin sa.
Wannan fitinanniyar kamshin ita ta kai wa su James sakon Romeo ya fito, a tare su ɗago kai suka kalle sa, wucewa yayi ya zauna gefen gadon kusa da Micheal tare da jawo system na shi dake saman bedside drawer ya kunna ta
cikin sauri har suna haɗe baki wajen cewa "Good morning lion" shiru ya ɗan yi na yan mintoci, ba tare da ya kalli in da suke ba, kasa kasa da wannan sexy voice ɗin nashi mai kwantar da hankalin mai sauraro yace "How are you doing this morning?" A tare suka amsa da "we are doing well what of you" shiru ya musu ba tare da ya sake magana ba.
Matsowa kusa da shi Micheal yayi tare da kwantar da kan sa saman cinyar James cikin murya kamar mai yin shagwaɓa yace "lion please I need money I'm broke" "same here" James ya faɗa, yana matsewa Michael kumatu da hannun sa, shiru Romeo ya musu bai yi magana ba, shiru suma suka zauna basu sake magana ba sun zuba masa ido suna kallon sa.
Almost 30mins suna zaune shiru in da sabo sun saba,
gently yasa hannu ya ansa wayar sa dake hannun James tare da juyowa ya kalli Michael dake ta faman turɓune fuska irin na shagwaɓa, "i need hot coffee" ya faɗa in a cool voice, kallon time James yayi a jikin diamond watch na shi 11:00am dai dai yana kokarin niƙewa dan yaje ya kawo wa Romeo breakfast na shi, dan lokaci yin breakfast na shin tayi, bai kai ga miƙewa ba Michael ya rigasa miƙewa, da sauri ya diro daga gadon ya nufi waje
Michael na fita James ya juyo ya dubi Romeo "a nan zaka yi breakfast ne?" Gyaɗa masa kai Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, daman can shi Romeo bai cika zuwa table cin abinci ba dan time ɗin cin abincin sa daban dana kowa a gidan 11 na safe yake breakfast, yayin da su kuma su Michael suke breakfast 8, sai 4 na yamma yake cin abincin rana yayin da su kuma su Michael suke cin na su 2, da daddaren kam bashi da takamaimen time na cin abinci wani lokaci yaci da wuri wani lokaci har 2 na dare yake kaiwa wani lokaci ma baya cin abincin daren maltina kawai yake sha, bai damu da cin abinci sosai ba, musamman abinci mai nauyi bai damu sosai da ci ba da daddare.
"Bro I want go somewhere" cewar James shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba yayin da hannun sa ke kan wayar sa ga system nasa a saman lallausan cinyar sa.
A haka Michael ya dawo ya same su, hannun sa ɗauke da katuwar tray mai shake da kayan abincin su na turawa, saman Chinese carpets dake kusa da gadon ya ajiye tray ɗin sannan ya faɗa saman gado yana faɗin "I'm tired" miƙewa James yayi ya fara serving na Romeo tun kafin ya sauko, daman idan har a bedroom na shi zai yi breakfast to su suke serving na shi dan bai yarda wani bodyguard ya shigo masa ɗaki ba, ko gyaran bedroom ɗin ma TGA ke masa, idan kuma TGA baya nan to sai dai uncle Herry ko daddy, dan James da Michael kam basu iya gyaran bedroom ba, suma gyara musu a ke, mu samman ma Michael da yafi kowa lalaci da son jiki bai san aikin wahala, shi yasa baya karatu dan yana ganin karatun ma wahala ce caza masa kai zata yi, ba abun da ya iya sai ya ɗauki wanka yaci gayu ya zuba chain a wuya ya kwashi kuɗi da mota ya tafi yawo da abokai, idan kuma ya dawo sai cin abinci da barci, baya neman faɗa sai ka neme sa, idan kuma ka nemesa faɗa in ya fara yi baya bari, har sai in anyi Sa'a James ko Romeo suna kusa, su kaɗai ke iya dakatar da shi, ban da su ko daddy bai isa ya dakatar da shi ba, ban da wannan ba wani abun da Michael ya iya, shi kuma James ga kwakwalwa da kaifin basira sai dai kashe ya jefa kan sa cikin haɗari, ya kammala karatun sa, a School da Michael ke karatu a nan suka yi karatu dukkan su.
Gently Romeo ya ajiye system na sa saman bedside drawer ya miƙe ya nufi saman Chinese carpets ɗin ya zauna tare da lanƙwashe kyawawan kafafun sa, James ya tura masa abincin a gaban sa, cup ɗin coffee ya fara ɗauka slowly ya kai ɗan karamin bakin sa ya ɗan kurɓa ya cire.
Baki ɗauke da excuse TGA ya shigo bedroom ɗin, jikin sa sanye da pajama launin sky blue, yayi kyau sosai, in the first place idan kaga face na shi sai ka rantse da Allah face ɗin Romeo kake gani sai ka zuba masa ido sosai sannan zaka iya ganin ban ban cin su, idan ka gansa da kyau zaka ga basu wani kama sosai irin wannan kamman ne da a ke cewa kaman jini,
Kusa da Romeo yazo ya zauna yana faɗin "Good morning My lion" shiru Romeo ya ɗan yi na yan sakanni kafin yace "Morning uncle how are doing this morning?" Fuska a ɗaure TGA yace "I'm fine what of you?" Shiru Romeo ya masa bai sake magana ba, cikin girmamawa Jame da Michael suka haɗa baki wajen cewa "Good morning Uncle" murmushi TGA yayi kafin yace "My Tiger, your eyes is shiny like Tiger eyes" kara lafewa a gado Michael yayi yau da alama yan shagwaɓan nasa suna gaban goshin sane, sai wani narkewa yake yana wani yauƙi
hannu uncle TGA yasa suka fara breakfast tare da Romeo, yayin da shi kuma James ke zaune yana ta aikin serving na su, duk abun da suka nuna sai ya zuba musu
cikin nitsuwa Romeo ke cin abincin sa hankali kwance, kamar bai son taunar abincin haka yake ɗan tauna, shi kuma uncle TGA sarkin sauri komai nasa sauri sauri yake ayi kawai a wuce wajen, ya riga Romeo ma gama cin abin cin, james ya miƙo masa tissue paper ya ansa ya goge bakin sa sannan ya miƙe ya nufi dressing room na Romeo, yayin da shi kuma Romeo yake taunan abincin cikin class da kwanciyar hankali kamar bai son tauna haka yake ɗan motsa lausasan laɓaɓɓan sa.
Jim kaɗan Tga ya fito sanye da face mask a face ɗin sa, sai dai ya gangaro da face mask ɗin zuwa gemun sa bai sanya dukka ba, kai tsaye gadon Romeo ya nufa, cike da so da kauna ya mannawa Michael kiss a goshi yana faɗin "Ilove you my Tiger, take good care of yourself" kamar Tga yace ya kara lafewa a gado haka ya kara rungume pillow yana ɗan turo baki yana kwaɓe fuska, sai hararar wasa James yake masa.
Har Tga ya kai bakin kofar fita bedroom ɗin ya jiyo voice ɗin Micheal can kasa kasa yana faɗin "uncle I'm not feeling fine" "what?" Tga ya faɗa tare da juyowa da sauri, shi kam Romeo ko a jikin sa dan ya san rashin lafiyan me Michael keyi, ya kwashe kuɗin account nashi ne kap ya saiwa friends nasa motoci da wasu abubuwan shine yanzu ya zo ya kwanta ya dawo shagwaɓaɓɓe wai bai da lafiya.
Da sauri Tga ya juyo ya dawo wajen bed ɗin tare da sanya hannun sa saman lallausan kumatun Michael ɗin yana faɗin "What is wrong with you?" "My head" yayi maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka
ɗaura hannun sa Tga yayi saman goshin Michael ɗin yana waro ash eyes nasa waje, James ji yake kamar ya kwashe su da mari dukkan su daga Michael ɗin har uncle T ɗin, dan haushi ma suka bashi, wai duk iskancin da Michael yazo da shi sai su biye masa suna wani lallaɓa sa yanzu uncle ya sani sarai ba wani ciwo dake damun Michael fa ce iskanci irin nasa kawai, amma sai uncle ya biye masa.
Dawo da kallon sa Tga yayi kan Romeo a nitse yace "please my lion ka duba min Tiger kaji?" Cikin sauri Michael yace "No uncle I'm okey now" James bai san lokacin da murmushi ta kubce masa ba, shi kan shi Tga abun yaso sashi murmushi amma sai ya danne, shi dai Romeo ko kallon in da suke ma bai yi ba kamar bai san da mutane a bedroom ɗin ba,
Waya Tga ya ciro daga aljihun sa, ya ɗan latsa kamar na 2mins sannan ya mai da aljihun na sa ya juya ya nufi hanyar fita,
a sukwane Michael ya miƙe zaune yana kallon wayar sa da ya fito da ita daga aljihun sa saboda yar kara da tayi, da sauri ya diro kasa daga saman gadon ya tafi da yar gudun sa ya haye bayan Tga yana faɗin "Thank you uncle" tangal tangal Tga yayi kamar zai faɗi kasa dan bai yi expecting Michael zai haye masa baya ba
A hankali ya sauke Michael ɗin daga bayan sa yana faɗin "My Tiger now your okey kenan?" Turo baki Michael yayi ya wuce ya fice daga bedroom ɗin daman kuɗi yazo nema wajen Romeo tun da ya samu wajen uncle Tga shikenan ai bukatar sa ta biya
wucewa shima Tga yayi ya nufi waje yana faɗin "I'm waiting for you at the garden My lion" jinjina kai kawai Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, dai dai lokacin ya kammala cin abincin na sa ya miƙe ya zauna a bakin gadon sa, yayin da shi kuma Tga ya fice daga bedroom, James kuma ya tattare kayan abincin yayi waje da su.
**💞NIGERIA💞**
_👹DAULAR MUTUWA👹_
Cikin wannan ɗakin Rimsha ta kwana, kwanan zaune sukayi, tun tana kuka hawaye na fita har ya dai na fita, yanzu kukan ma ta kasa yi ga bala'i yinwa da kishin ruwa da take ji, sukam sauran yaran sun sume saura yarinya ɗaya, tare sukayi kwanan zaune da Rimsha, gashi Rimsha ta kasa iya ambato sunan Allah sun rufe mata baki, ji take an shaƙe mata maƙogwaran ta, haka ta hakura ta takure waje guda tana jin wayan nan dodannin suna ta gurnani suna ihu a dab kunen ta amma ba yadda ta iya haka ta zauna a kasa cikin dotti, da daskararren jini busasshe, bata da zaɓi dole ta zauna a wajen.
Allah sarki Rimsha renon madara da chocolate dasu ice cream, kwanciyar gadon lausi da Ac a rufu da bargo nai laushi, yau ta kare da kwanan zaune cikin daskararren jini ga wari sannan ga wayan nan dodannin masu razanar wa da ɗan Adam kwakwalwan sa.
Washegari sai da rana ya ɗaga sannan magicians ɗin suka zo suka buɗe su, ba ƙaramar razana sukayi ba ganin still Rimsha na cikin hayyacin ta, ita da ɗayar yarinyar, sun sha mamaki sosai, haka suka fito da su suka kai su wani keɓaɓen waje mai kama da gida, yana da girma sosai, a nan suka turasu cikin wani ɗaki suka juya suka koma, suka ɗauki wayan can sauran yaran da suka suman kuma suka tafi da su in da suke yanka mutane.
A hankali Rimsha ta fara rarrafawa a cikin ɗakin ɗan ba zata iya miƙewa ba, saboda yinwan da take ji, kamar a mafarki ta ga kamar halittar mutun zaune an kifa kai da gwiwa, ta kasa gane mace ce ko namiji Saboda idon ta baya gani sosai saboda yinwa da take ji, Dan ma ɗakin nada haske sosai ba kamar ɗakin da a ka fito da su daga cikin shi ba, hakan yasa Rimsha ta iya karewa wan nan halitta kallo, da kyar ta iya rarrafawa a kan gwiwowin ta, ta ƙarisa wajen wan nan halitta wadda ta kasa gane wace halitta ce, babu ko tsoro a rattare da ita ta sanya hannu ta taɓa wannan halitta,
a razane wannan halittar ta ɗago kan ta wadda ta kasan ce....✍️✍️
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪
B 💞Star Lady💞
TRIPLET'S
https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo
*THE BEGINNING*
💞*STAR LADY*💞
Mai neman karin bayani yamin magana ta wan nan number 09162620621
Masu tambaya ta ma'anar sunayen danake using dasu a book ɗin gasu nan
Names and their meaning
1Ayla Moonlight. 2Aafia Confident .
3Umaisha soft hearted 4 Ayla Moonlight
5 Rimsha means Beautiful or face like moon
6 Jehan meana the world
EPISODE 22
a razane wannan halittar ta ɗago kan ta wadda ta kasan ce mutun ce mace ce yarinyar yar karama, wadda wahala ta mai da ta kamar kashi da rai, duk ta rame ta bushe gaba ɗaya face nata ya rama ga idon ta sun yi manya manyan kamar zasu faɗo waje saboda raman da tayi, a tsorace Rimsha ta ja da baya tana kallon yarinyar nan wadda a shekaru ba zata wuci 14 years ba, baya baya Rimsha ta ja ta koma ta zauna ɗan nesa da yarinyar, a hankali ita ma wan can yarinyar ta rarrafo ta kariso wajen Rimsha ɗin suka haɗu suka zauna shiru, dukkan su sai ƙugi cikin su ke musu saboda yin wa.
Kamar da ga sama sukaji wan nan yarinyar tana faɗin "Sannun ku da zuwa Daukar mutuwa, daular da ba wani mai rai da yake shiga ya fita, na jinjina muku da ku ka iya tsallake level 1 da 2 ku ka iso nan na taya ku murna sosai, amma sai dai daga nan babu in da zaku sake zuwa kai tsaye lahira zaku wuce" duk da ba wani Hausa kirki Rimsha ke ji ba ta fahimci abun da yarinyar take faɗi, sosai murmushi ya bayyana a face ɗin Rimsha jin yarinyar tayi magana da da farko ta ɗauka kawai ba mutun bane idon tane ke nuna mata kamar mutun ne a wajen.
Cikin zumuɗi ta rarrafo ta matso kusa da yarinyar ta sanya hannu ta dafa kafaɗar yarinyar tana faɗin "zamu fita In...ta kasa fitar da In Sha Allah ɗin maganar ta tsaya kamar wadda a ka shaƙe, hannu tasa a wuyar ta tariƙe da karfi tana jin yadda wuyar nata ke mata raɗaɗi kamar ana zare jijiyoyin wajen, nan take ta fara hawaye sirara masu ɗumin gaske, ganin haka yasa yarinyar ta riƙo ta tana faɗin "Ki dai na wahalar da kan ki, babu wanda ya taɓa shiga ɗaular mutuwa kuma ya fita, rayuka sun fi a kirga suka zo nan kuma suka tafi lahira kamar ba'ayi su ba, abun da nake so dake kawai yanzu ki shirya daga yanzu kowani lokaci za'a iya samun mai son wani abu daga jikin ki" ita dai Rimsha gaba ɗaya ta kasa magana sai hawaye take masu zafi saboda raɗaɗin da wuyar ta ke mata.
Rarrafowa ɗayar yarinyar ma tayi ta kariso wajen su, suka zubawa Rimsha ido, yayin da ita kuma Rimsha take kokarin ceto muryan ta dan ta samu ta musu magana.
Almost 30mins suna haka, sannan Rimsha ta samu sauki daga shakan da a kayiwa wuyar ta, a hankali murya ciki ciki tace "Wayyo na shiga uku na" da sauri suka rirriƙeta suna mata sannu, shiru ta ɗan yi kafin ta iya furta "Zan sha ruwa" a takaice yarinyar da suka samu a ɗakin tace "kullun sau ɗaya suke kawo min abinci da ruwa, kuma already sun riga sun kawo na yau na cinye sai kuma gobe dan haka kiyi hakuri kawai" shiru Rimsha tayi tana mamakin me ya hana ta iya kiran sunan Allah kuma gashi tana iya faɗi a ranta amma a fili ta kasa faɗe.
Kallon yarinyar da a ka kawo ta tare da Rimsha yarinyar da suka samu a ɗakin tayi tace "Ya sunan ki?" Da sauri yariyar da aka kawosu tare da Rimsha tace sunana Kausar" yanayin yadda tayi maganar ne yasa yarinyar tace "amma ke ba bahaushiya bace ko?" Gyaɗa mata kai kausar tayi kafin tace "Eh ni bayarbiya ce" jinjina kai yarinyar tayi kafin tace "Ni kuma sunana Alia amma mamana tana kirana da Ayla so kawai ku ma ku kirani da Ayla ɗin koba komai zan iya samun damar in rinƙa tuna mamana" sai lokacin Rimsha ta sanya musu baki a cikin maganar da suke tace "how many days have you being here" girgiza kai Ayla tayi kafin tace "Good 3 years" zaro ido waje Rimsha tayi ta ma kasa magana tayi shiru ta koma ta jingunu da jikin bangon ɗakin tana jin matsanancin ciwon ciki saboda yinwa, haka ta dafe cikin ta da hannun ta dukka biyu tare da runtse idon ta gam tana matsar kwallan dole, zuba mata ido kawai su Ayla sukayi basu da wani hanya da zasu iya taimaka mata fa ce su zuba mata ido kawai, dan suma taimakon suke nema
ba abun da Rimsha ke tunawa sai mum dad gwaggo da Jehan sune duniyar ta, yayin da time to time tunanin GAR yana ratsa tunanin su Jehan a cikin ƙwaƙwalwar nata, haka suka zauna jugum jugum, sai matsar kwalla take wadda a halin yanzu sai tayi da gaske ma kwallan ke fitowa daga idon ta.
_KANO_
Time ɗin ɗaukan Jelly a school yayi daddy ya ajiye duk wani aikin sa ya nufi School nasu dan ɗaukan ta, nan ya ji tashin hankali da bai taɓa jin makamancin sa,
uncle's ɗin su Jelly sun shaida masa Jelly bata zo school ba yau, lokaci guda yaga duniya na juya masa dafe kan sa yayi ya fara neman layin su Zuwaira dan yaji ko dai ta koma gida.
Bugu ɗaya Zuwaira ta ɗauka murya sa har rawa yake sai haɗe words yake wajen tambayar ko Jelly ta dawo gida, cikin girmamawa Zuwaira tace masa "A'a