Showing 126001 words to 129000 words out of 194715 words

Chapter 43 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

965

da hannun sa, yana mamakin ina yasan wannan fuskar, da kyar Rimsha ta yi shiru tare da sah hannun Mustapha dasu Ayla suka samu tayi shiru.

"Ya sunan ki?" Baba ya tambaya yana tsare ta da ido, da sauri tace masa "Rimsha" a hankali ya mai mai ta sunan kafin yace "daga wani gari a ka kawo ki nan" nan ma da sauri ta bashi amsa, shiru ya ɗan yi kamar mai nazari, can kuma sai yace "Da farko naji kamar na san ki, amma yanzu danaji daga in da kike sai na fahimci kawai kamace da yanayi yasa naji kamar na san ki, kuma ba zai yiwu ma a ce na san ki ba, dan tun kan a haife ki nake gidan nan, ni bani da wani ɗan uwa a Abuja da Katsina" cikin sauri Rimsha tace "To baba zan iya tambayar ka" gyaɗa mata kai yayi yana murmushi "Baba ya akayi kazo nan?" Shiru ya ɗan yi kafin yace dogon labari ne, zan faɗa miki daga baya, to kawai Rimsha tace masa tare da kara matsowa kusa da shi ta zauna tana tunanin ina ta san face ɗin wannan baban, dan tabbas ta san shi ko kuma mai kama da shi, to ai na kuma wanene, haka ta rinƙa jerowa kan ta tambayoyi, suna zaune shiru.

Babu ko excuse duna ya faɗo ɗakin, gaba ɗayan su sai da suka ɗan tsorata, kusa da Rimsha yazo ya tsugunna, sai washe baki yake yace "Two days beautiful girl why are you not coming out?" Rimsha ji take kamar ta kwasa masa mari dan haushi ɗan iskan banza haka take ta faɗi a ranta, tayi shiru tayi banza da shi kamar bata ji me yace ba.

Kokarin riko hannun ta yayi dan ya bata hakuri, cikin sauri ta ja baya tana faɗin "don't touch me" mai da hannun sa yayi yana faɗin "because of what?" A kule Rimsha tace "Because I'm a Muslim" zaro ido gaba ɗayan su sukayi, dan gaba ɗayan su ji sukayi kamar sabon abu ta faɗa, baba ne kawai bai ji komai ba kasan cewar shi bai manta komai ba, game da addinin sa, sai dai sun hana shi, sun zaunar da shi baya iya tashi, amma sun kasa mantar da kwakwalwan sa komai, shi kuwa Duna, washe wannan bakin nasa kamar kofar gari yayi kafin yace "Okey Musulmai ba sa son a taɓa jikin sune?" Da sauri ta gyaɗa masa kai tana faɗin "Yes of cause" "alright, anyway dama I came to ash you lafiya baki fitowa two days, but please may I know the reason why Muslim people the don't want someone to touch them?" Gyara zaman ta tayi, ta fara masa bayani a kan addinin musulunci "No ba wai bamu son ko babu kyau a taɓa mu bane, a koi wayan da ya halakta ka taɓa akoi kuma wayan da basu halakta ba" tsare ta yayi ya wayan nan jajayen idon nasa yana kallon ta, ci-gaba da magana tayi "idan mutun ɗan uwan kane na jini, ma'ana kanin ka ko kanwar ka ko yayan ka, wannan ya halakta ka taɓa shi, maman ka da baban ka suma sun halakta su taɓaka, sannan idan mutun matar kace ko mijin ki wannan ma ya halakta" zata cigaba da magana yayi saurin ce mata "What is mata ko miji and mama da baba? I knew brother an sister" baba ne ya amsa zancen da cewa "wanan kam ni zan baka amsa" shiru Rimsha tayi suka fara sauraron jawabin baba a kan menene mata da miji, sosai Rimsha ta kara samun ilimi a kan hakan, kallon baba duna yayi kafin yace "Amma dai naji daɗin addnin musuluncin nan kaɗan dan na lura yana da tsab ta, to kenan mu da muke kwanciya da duk matan da muke so babu wannan aure da kuka ce me laifi?" Nan ma baba ne ya kara yi masa bayani a kan hukuncin zina, "duk wanda yayi zina bai tuba ba yakoma ga Allah a ranar tashin alkiyama, zai shiga wuta, bayan ya shiga wuta za'a ɗaure sa da wasu manya manyan sarka a cikin wutar jahannama Allah ya turo wasu halittu masu kama da ɓeraye suzo suna cin gaban sa suna cakwaɗa yana ihu, ga azabar wuta babu mai kawo masa ɗauki, kafin aje ga wutar ma sai ya fiskanci ukuba acikin kabari" shiru duna yayi da alama jikin sa yayi la'asar

ganin hakan yasa baba ya kara zafafa masa abun ta hanyar cewa "ba zai taɓa fita wutar nan ba, koda wutar ta kone masa jikin sa dukka to za'a sake halittar sa sabo, wuta ta ci-gaba da cin jikin sa har illa masha Allah" sai dai a wannan gaɓar da kyar baba ya iya ambatar sunan wadda zai sake halittar wato Allah, shima ciki ciki ya ambato, duna dai duk jikin sa ya mutu, a sanyaye yace "to yanzu zan iya auren wannan kenan" yayi maganar yana nuna Rimsha, a zabure Rimsha ta kara ja baya da shi, tana kallon sa wani mummuna da shi, ɗan datti sai wari yake,

dariya yayi dan yasan munin sa Rimsha ke gudu, cikin yan sakan ni ya juya kamannin sa ya riƙiɗe zuwa kyakkyawan mutun, kyakkyawar gaske kamar shi yayi halittar kan sa, ba karamin tsorata Rimsha tayi ba, ita kam Ayla dama ta saba ganin suna sauya kamanni, kan kame baba Rimsha tayi tana kuka kasa kasa, "Kin ga yadda muke komawa sai mu kwanta da duk macen da muke so, kuma dole ta yarda ko dan kyan mu" cewar duna yana kokarin ci-gaba da magana, baba ya rigasa da cewa "Musulmai mata basa auren namiji krista, amma musulmi maza suna iya auren mace Kirista" "menene Kirista?" Duna ya tambaya yana kokarin gyara kyakkyawan zobe dake hannun sa, har da zobe ya fitar, yayi kyau da shi sosai kamar shi yayi kan sa, kamar wani balarabe, ya zama matashi mai jini a jika

nan dai baba ya fara yi masa bayanin menene krista da kuma yadda aka yi suka zama Kirista, tare da haɗa masa har da yahudawa, sai dai duk lokacin da yazo kiran sunan Allah a bayanin nasa sai yasha wahala "Kiristoci sune wadda suka ce Allah na da ɗa wato annabi isa, sune wadda suka raunata Allah domin wannan babban rauni ne suce Allah na da ɗa, hakan kuma ya samo asaline ta dalilin su guda biyu, na farko wanda suke kira da ɗan Allah, wato annabi Isa, an haifesa ne babu uba, wannan ba shi ne babban matsalar ba, dan ana haifan ƴaƴa dayawa ta cikin shege wadda suma kiristoci da farko irin kallon da suka yiwa annabi isa kenan, suka ce shegene, cikin shege mahaifiyar sa tayi, babban abun da yasa suka ce shi ɗan Allah ne, saboda yayi magana yana jariri, wadda yayi maganar ne ya wanke kan sa da mahaifiyar sa daga ɗan shege da kuma mahaifiyar sa tayi zina kamar yadda suke faɗa, sannan ya faɗa musu shi bawan Allah ne, tun a lokacin suka suma, bayan sun farfaɗo ne suka dage a kan lallai ɗan Allah ne saboda an haifesa babu uba kuma gashi yana jariri yayi magana" cikin sauri duna ya katse baba da cewa "kaji wani tatsuniya ya za'ayi jariri yaro yayi magana" girgiza kai baba yayi, ko kaɗan bai damu ba, dan yasan jahilcine cike da kan duna, banda shan jini da cin namar mutane ba abun da suka iya, dan haka sai bai damu ba ya ci-gaba da yi musa bayani ta yadda zai gamsu, "Ba annabi Isa bane kawai yayi magana yana jariri akoi wani ma wadda lokacin da ake kashe musulmai yayi magana yana jariri, lokacin da kafurai suka tona rami suka hura wuta sosai a ciki, su kace duk wani musulmi in dai ya yarda da shi musulmi ne yazo ya faɗa wutan nan da kan sa tun kafin a jefasa, sau uku wata mata tana zuwa zata faɗa, sai kuma ta fasa saboda yaron ta jariri dake bayan ta a goye, a wannan lokacin ne Allah ya buɗe wa yaron baki yayi magana in da yake sanar da ita ta faɗa shi ne mafita a gare su, to wannan ba abun mamaki bane, kaɗan ne daga cikin ikon Allah" "su waye kuma Yahudawa?" Duna ya sake jefowa baba tambaya, kuma duk wannan tambayoyin da yake wa baba yana yin sune dan yaji ta yadda zai samu Rimsha dan shi gaskiya yarinyar ta burge sa yana son ta, nan fa baba ya shiga yi masa bayani a kan yahudawa, wadda kusan sunfi kowa ilimi a duniyar nan, sai dai kashe ilimin su duk a banza ne saboda basu yarda da Annabi Muhammad (SAW) ba kasan cewar sun karanta a littafin su annabin karshen, wato Muhammad (SAW) zai bayyana ne a cikin su, sai kuma annabi ya bayyana a cikin Larabawa kuraishawa hakan yasa suka kafurce masa suka ki binsa sukaki yarda da shi, kuma suka nemi kashe sa, wannan shi ne sukuma dakilin su na kin yarda da addini musulunci, shiru duna yayi shi dai duk wannan bayani da baba ya masa bai fahimci komai ba, bayan cewa ba'a auren mata sai dai in mutun musulmi ne.

Tabbas baba ya fahimci babu abun da duna ya fahimter dan gane da bayanan sa dama kuma yasan mawuyacin abune dunan ya fahimter kasan cewar sa jahili sosai wadda bai taɓa sanin wani abu ba face shan jini, hakan yasa baba yayi shiru kawai yana addu'a a ransa Allah yasa duna ya gane gaskiya, Allah yasa yana da rabon shiriya, ita kuwa Rimsha ta kan kame baba saboda tsoron ganin yadda duna ya rikiɗe ya dawo kyakkyawan saurayi, faritas da shi ga dogon hanci har baka, har da wani curly hair kwance masa a kai har zuwa gaban goshin sa, kyau iya kyau duna ya haɗu, sai satar kallon sa Kausar take tana tsoro su haɗa ido.

Kallon ta duna yayi kafin yace "Fine girl why kika cika tsoro ne haka?" Kara matsawa jikin baba tayi dan tsoro, saboda har muryan duna sai da ya sauya, ya dawo mai cool voice, ita ma Kausar ta tsorata sosai, ita kuwa Ayla ko a jikin ta, dan ta saba ganin abun da yafi wannan ma, sai dai tasha mamaki yau saboda son da duna kewa Rimsha ya biyota har nan yazo tambayar kwana biyu lafiya bata fito waje ba, tab lallai akoi kura, aure tsakanin mutun da aljani, aljanin ma magician tab lallai Rimsha kin cire tuta, shi kuwa duna ba abun da yake tunawa sai kyan fuskar Rimsha da kuma dimple nata idan tana magana.

Ganin duna yayi shiru ne, yasa baba yace "lafiya duna" miƙewa yayi yana faɗin "zan dawo anjima sai ka faɗa min me ya kama ta nayi kafin wannan yarinya ta dawo nawa" to kawai baba yace masa, sannan ya fice daga room ɗin.

Dawo da kallon sa baba yayi kan face ɗin Rimsha dake ta zazzaro sleeping eyes nata, cikin nitsuwa ya fara magana "kina jina Rimsha, na san baki son shi kuma bana miki fatan ma ko hannun ki ya taɓa, amma karki nuna masa hakan, dai basu da imani ko ɗigo a ransu, idan yazo ki biye masa kuyi hira, a hankali har mu ja shi ya shiga cikin addinin mu, idan ya shiga addinin Musulunci, imani ta ratsa shi to komai zai yi sauki, amma yanzu idan kika yi avoiding na shi to tsab zai iya kashe ki, kuma kafin ya kashe ki, zai iya biyan bukatar sa a kan ki tun da kinga ra'ayin hakan ya nuna, zai biya bukatar sa sannan kuma ya kashe ki da kan sa, kuma zai dafa namar jikin ki ya cinye" kara tsorata Rimsha tayi nan take taji hanjin cikin ta ya kaɗa shi ru tayi tana tunanin yadda zata kaya tsakanin ta da wannan bakin aljanin.

💞KADUNA💞

Aafia

Yau tun safe Aafia ke ta surfa uban bala'i a gida wai an sace mata waya, hayaniyar ta ya tashi Abbi da Aunty daga barci, suka sauko Palon kasa nan suka same ta, ta tasa mai aikin da Abbi ya kawo a gaba wai ita ta sace mata waya, sai kuka yarinyar take tana ta rantsuwa a kan wlh ba ita bace, abun gwanin ban tausayi, sai wani girgiza Aafia keyi da kugu, tana surfawa yarinyar masifa, while ita kuma Umaisha tana zaune saman sofa ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya, sai faman latsa nata wayar take taba turɓune fuska, "Meke faruwa Aafia" Abbi ya tambaya yana kallon ta, kukan makirci ta sawa Abbi tare da tafiya ta rungume sa tana faɗin "Abbi jiya da daddare ina barci naji motsi dana ɗago kai na, sai naga wannan mai aikin ne, to ban kawo komai a rai na ba kasan cewar nasan wani lokaci tana kawo mana tea da daddare, yau da safe na tashi banga waya taba, kuma wlh Abbi ita kaɗai ta shiga bedroom na mu, kuma kafin nayi barci nayi amfani da wayar, dana gama na ɗaura saman bedside drawer nayi barci" already ita kam Aunty tasan sharri Aafia keyiwa mai aikin, dan wlh ba wani tea ɗin da yarinyar nan ke kai musu da daddare, mawai makircine dan sun ga ba mai iya ce wa karya suke, ita kuwa yarinya sai kuka take tana faɗin "wlh ban ɗauki wayar taɓa" shiru Abbi ya ɗan yi kafin yace "to muje ki sai wata wayar mana" turo baki Aafia tayi tana faɗin "Ni Abbi wancan wayar nake so, saboda ina da abubuwa da dama masu amfani a cikin ta" kasan cewar shi Abbi namiji ne kuma babba mai hankali, sai ya gane karya Aafia keyi, hakan yasa yace "to jeki ni zan ansa miki wayar" turo baki Aafia ta kara yi cikin shagwaɓa tace "Abbi muje room nata mu duba mana, nasan ba zata wuce ɓoye wayar a room ɗin ba, kuma wlh idan yana wajen Abbi barin gidan nan zatayi dan ba zamu zauna da ɓarauniya ba" "ke dai jeki kiyi shirin zuwa school zan ansa miki wayar da kai na na ce ko, batun zaman ta a gidan nan kuma ni zan yanke hukunci" ba dan haka taso ba, ta wuce rai a ɓace ta haye sama,

Dawo da kallon sa kan Umaisha yayi kafin yace "Ke ba zaki tashi bane, kin zauna kin tasa mu a gaba" tun bai gama rufe baki ba Umaisha ta miƙe ta wuce tabi bayan Aafia, dawo da kallon sa kan Aunty dake tsaye a bayan sa tana mamaki yayi, a nitse yace "Je ki duba ɗakin yarinyar ki ɗauko min wayar" ba musu Aunty ta wuce dan ita ma tasan can Aafia ta kai wayar ta ajiye, dan tayiwa yarinyar sharri

Dawo da kallon sa kan yarinyar Abbi yayi a nitse yace "Kiyi shiru" cikin kuka tace "Wlh baba bani na ɗauka ba, ni bana sata kuma ban taɓa yi ba, ka tambayi mamana kaji, dan Allah kada ku koreni daga gidan ku, wlh babana ya rasu bamu da mai bamu abinci, da kuɗin aikin nan nake saya mana abinci" tsugunnawa Abbi yayi ya goge mata hawaye yana faɗin "Ya isa tashi kije kiyi kwanciyar ki, ni ba yaro bane kinji ko? Kuma babu wanda ya isa ya koreki daga gidan nan, dan ba su suka kawo ki ba, ko bana nan wata tace ki bar gidan nan kice ba in da zaki je sai wanda ya kawo ki ya dawo ya mai dake" Gyaɗa masa kai tayi tana ta zuba masa godiya, ta wuce ta koma ɗakin ta.

Abbi na wajen har Aunty ta dawo hannun ta riƙe da wayar Aafia, amsar wayar Abbi yayi ya nufi bedroom na su Aafia, ita kuma Aunty ta wuce nasu bedroom ɗin.

Tsaye gaban mirror ya isko Aafia, tana tsaye tana faman feshe jikin ta da perfume, cikin nitsuwa ya fara magana ta hanyar amfani da matsayin sa na babba kuma mahaifi a gare su "ina son ku sani duk abun da mutun yayi a duniyar nan kan sa yayiwa, in ma mai kyau ko mara kyau, kuma kullun ina mai tsawatar muku a kan ku rinƙa jin kan nakasa da ku, sannan ku tausaya masa amma bakwa ji, ku dai na ɗaukan duniya da zafi, dan ba wata tsiya a duniyar nan, kun san da haka, tun da duk da wayon ku Mahaifiyar ku ta bar gidan nan, sannan kuna sane da dalilin da yasa ta bar gidan nan, ta guje mu ne saboda bani da kuɗi na shiga jarabawar Ubangiji, amma hakan da tayi yasa na samu nakaso ko wani abu, gashi kwance tashi ba wuya a wajen Allah, Allah ya azurta ni da arzikin da ban mallaka a baya kafin na aure taɓa, kuma kuna sane 3 years back, mun sake shiga jarabawar Ubangiji, Allah ya aiko Husain ya taimake ni, ba dan haka ba ai da yanzu kuma sai dai ku tafi aikatau gidan wasu, wannan bai ishe ku ishara ba? To ina mai kara jan kunnen ku, kubi duniya a sannu, dan ko wani lokaci duniya na iya juyawa daku" ya kai karshen maganar tare da miƙa mata wayar ya fice da bedroom ɗin.

A tunanin sa maganar sa ya shiga kunnen su, sai dai abun da bai sani ba, maganar Rufee ta riga nasa zama a kunnen su, sun riga sun yi nisa, Abbi yayi kuskure wajen rashin binciken da waye suke kawance, idan su fita ina suke zuwa, me da me suke aikatawa a School, duk wannan bai sani ba kuma bai damu da ya sani ba, ka san cewar ba wani zama yake a gida ba, wannan shi ne ɗaya daga cikin babban illar rashin uwan a kusa da mutun.

Abbi na fita Aafia ta ja guntun tsaki tare da turo baki tana faɗin "wlh Abbi bashi da wani aiki sai yiwa mutane wa'azi kamar wani malami, sai kace mu bamu yi karatu ba" Umaisha ce ta ansa zancen da cewa "Ki godewa Allah Ummi da Yaya Irfan basa nan, ai sun fi Abbi masifa musamman ma Ummi, ni gwara ma da ta tafi, da yanzu tana nan tan faman takura mana,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login