Showing 42001 words to 45000 words out of 194715 words

Chapter 15 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

969

da zasu fara Friday, Saturday and Sunday su sanar ma Iyayen su.
Da jin ɗadin suka amsa mata da In Sha Allah zasu Rinƙa karatun suka nuna mata farin cikin su akan lesson daza su fara.

Aunty na Sallamar su Rimsha ta miƙe aguje ta fice a ɗakin nasu rungume da ƙatuwar teddy ɗin ta, ta nufi office ɗin daddy dake palour ɗin ƙasa wajen da yake zama yana duba mahimman abubuwa sa.

Zaune yake a saman 2 Sitter dake office ɗin yana duba wasu takardu, Da sallama ta shiga office ɗin tana nishi kaman wacce kare ya biyo, ɗago wa yayi da sauri ya sauke idanunsa akan ta kara waro ido waje yayi yana faɗin "My sima kiyi a hankali don't hurt yourself am about to come and surprise you ai and then you came" ya faɗi yana kamo hannun ta ya zaunar da ita a gefen sa "Daddy let's go to the shopping now I want to be the best among everyone" ta faɗi tana mai da numfashi, miƙewa Daddy yayi ya ɗauko mata ruwa a fridge ɗin da ke office ɗin ya dawo ya ɗauke ta ya dorata saman cinyarsa ya buɗe ruwan ya kafa mata a baki, kaɗan tasha ta janye bakin ta "Haba my Siha you are now a big girl stop running anyhow like that is not proper kinji" ya faɗi yana shafa curly hairs ɗinta daya gangaro mata har bayan ta, gyaɗa masa kai tayi ta kwantar da kanta a kirjinsa tana mai da numfashi tare da jujjuya dara daran sleeping eyes nata.

After some minutes Jehan ta shigo office ɗin bako sallama ta ƙaraso gun daddy ta zauna a gefen sa tare da kwantar da kanta a kafadar sa, hannun sa ya kai ya shafa lallausan gashin kan ta, cikin shagwaɓa tace "Daddy our party outfit is black and white" "same as ours" Rimsha ta faɗi tana ɗago kanta daga chest ɗin daddy "Alright go and make the lists of all you need well go to shopping later" ya kai karshen maganar tare da rungumar su a jikinsa, kiss suka manna masa a kumatunsa har suna rige rigen tashi su fita suna faɗin "That's why we Always love you daddy" Suka faɗi suna ficewa a ɗakin murmushi yayi shi ma yana mai jin kaunar yaran nasa har cikin ransa, ci-gaba da duba takardun da yake yi yayi.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*KADUNA*

A yaune Abbi ya kira dillalai masu sayan filaye da gidaje, a kan suzo su sai company'n sa, yana tsaye sanye cikin shadda nevy blue kayan sun masa kyau sosai ɗinkin full jompa, while Irfan na tsaye a gefen sa sanye cikin wandon jeans baki da t-shirt blue gashin kan nan nashi yasha gyara sosai, dukkan su fuskokin su babu annuri kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin damuwa da tashin hankali, su kuwa dillalan sai kewaye company suke suna dubawa, har zufa Abbi yake haɗawa shi Irfan ma ba'a magana dan tashin hankali sa yafi na Abbi yawa saboda abun ya haɗun masa biyu ne na farko a baya Abbi bai da kuɗi yasa Ummin su ta gudu ta barshi, bayan tafiyar ta Allah ya azurta Abbi har company ya saya yanzu kuma wani yazo ya zalince sa, ga zafin ciwon abun da Ummi tayiwa Abbi ga kuma zafin ciwon abun da ya samu Abbin yanzu.

Suna tsaye a wajen har dillalai ɗin suka gama kewaye kewayen da dube duben su suka dawo wajen su Abbin, Shiru Abbi ya zuba musu ido yana jiran yaji nawa zasu fara taya masa wajen, da buɗar bakin ɗaya daga cikin dillalan sai cewa yayi mun saya 5 million a sukwane Irfan yace cikin tsawa "What!! 5 million fa kukace ai ko wan nan fillin kawai yafi karfin 20 millon, company guda mai girman filli plot 15 shine zaku ce 5 million bayan har da gini a wajen kuji tsoron Allah bayin Allan" dogon tsaki ɗaya daga cikin dillalan ya ja kafin yace "Kai da kake mana wani lissafin banza da na wofi mu ina ruwan mu da abubuwan da kuka kashe kuka saya yanzu dai sayarwa zaku yi, kuka kiramu to mu kuma 5 million muka ce zamu saya idan ya muku, mu baku kuɗin ku cash mu ansa takardu idan kuma bai muku ba sai mu wuce ku nemi wasu, a zamanin yanzun nan waye ma yake ta wani filli ko gida kowa ta abincin da zai ciwa cikin sa yake na rantse muku ba wanda zai sayi wan nan kangon 6 millon!!" Ya kai karshen maganar cikin faɗa, kallon Irfan Abbi yayi yace "Muje gefe mu ɗan yi magana" ba musu Irfan ya wuce sai huci yake dan yadda suka taya wajen ba karamin ɓata masa rai suka yi ba filli mai girman gaske har ka kuma a cikin garin kaduna ba'a kauye ba kai wan nan ma ai rai nin hankali ne.

Kasa kasa da murya Abbi yayi ya fara magana dan kar dillalan suji "Irfan suna da gaskiya yanzu ba kowa yake da kuɗin sayen gida ba al'umma ta abincin da zasu ci suke dan haka mu hakura da asarar kawai mu sallama musu" riƙo hannun Abbi Irfan yayi yayi kasa da murya cikin girmamawa yace "Abbi wallahi karya suke ta haka suke fakewa suce ba kuɗi kowa na ta abinci ne sai su kashewa mutun jiki susa ya sallama musu kayan sa kamar kyauta ina da tabbacin suna mutuwar son company nan dan haka Abbi ka rabu da su idan ba zasu bada 20 millon ba wallahi su bar mana abun mu ni zan ɗauki degree certificate na naje neman aiki, ai ta Allah bata karewa kuma bai kamata bawa ya yanke tsammani daga samun Rahman Ubangijin ba" "Hakane Irfan to ni dai zan koma cikin motar ka najira ku ka yi magana da su kaji kai na ciwo yake ba zan iya tsayawa a wajen ba" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya bar wajen ya nufi motar Irfan ɗin, shi kuma Irfan ya koma wajen dillalan a ƙule yace musu "Zamuyi tunani idan mun gama zamu nemeku" ya kai karshen maganar tare da juyawa zai bar wajen, cikin sauri ɗaya daga cikin su yace "To mujira zaku sayar mana ne ko dai" Irfan ba tare da ya juyo ba yace "Zamu neme ku idan mun gama tunani" yana kai karshen maganar ba tare daya jira amsar su ba ya bar wajen cikin sauri yaje ya shiga motar sa, suka zauna shiru shi da Abbi har sai da dillalan suka tafi san nan su Abbi ma suka fitar da motar su waje, Irfan ya kashe motar ya fito ya rufe gate ɗin company nin ya koma mota suka bar wajen

A takaice dai dillalai har kala uku su Abbi suka kira amma duk wadda suka zo tayin wulakanci sukewa wajen ba wanda ya taya sama da 7 millon a cikin su, dukkan su Irfan yaki sallama musu ya ɗauki takardun sa ya fara naman aiki,

💞💞💞💞💞💞💞💞

*KANO*

Zaune take saman tsakiyar gadon daddy tana latse latse a system na shi da ya ajiye saman bedside drawer ya fita, sai latsa masa take bata ma san in da take shi ga ba kawai duk in da ta samu latsawa take, da sallama daddy ya shigo bedroom ɗin, ganin abun da take masa da system yasa ya kariso wajen da sauri yana faɗin "Jelly me kike min a system kuma? Ke da nace ki cire kaya ina zuwa in miki wanka" turo baki tayi kamar biro cikin shagwaɓa tace "Daddy amma yau tare zamuyi wanka ko?" Waro ido waje yayi yana kallon ta cike da mamaki yace "A'a ba dani ba" kuka ta sa masa tana faɗin "Daddy ni gaskiya idan ba da kai ba ni ma bazan yi wankan ba" kara waro ido waje yayi yana kallon ta, ganin da gaske take kukan ga hawaye sun fara bin kuncin ta ne yasa yayi kasa da murya yace "My jelly Allah ya hana mutane biyu su shiga toilet" cikin sauri tace "Daddy ai to tare muke shiga ba kai kake min wankan ba kaga kenan mu biyu muke shiga ai" ɗaure fuska yayi sosai kafin yace "Ni ai daddyn ki ne zan iya yi miki wanka amma ba muyi tare ba Allah ya hana hakan" kara turo baki tayi tana faɗin "Daddy nima zan iya maka wankan ke nan ai" saura kaɗan dariya ta kubce masa amma sai ya danne ya wuce ya nufi toilet yana faɗin "kiyi sauri kizo namiki wanka anjima kaɗan su Yaya Irfan dash yaya Imran zasu zo" ya kai karshen maganar tare da shigewa cikin toilet ɗin yana mamaki wai zata masa wanka ita da ko brush bata iya yiwa kan ta ba ne zata ce zata masa wanka,

ita kuwa jin daddy ya ambaci su yaya Imran zasu zo ne yasa ta miƙe da sauri ta diro kasa daga gadon ta shige toilet ɗin da yar gudun ta tana dariya,

After some minutes.

Daddy ya fito ɗauke da ita a saman kafaɗar sa ya naɗo ta a towel mai laushi sai murmushi take, kai tsaye saman chair ɗin gaban mirror ya ɗaura ta tare da ɗauko karamin towel ya goge mata jiki tsab, san nan ya fara shafa mata lotion nata masu kamshi da daɗi da tsada, bayan ya kammala ya shafa mata mayukan gashin ta masu kyau da tsada ya gyara mata gashin ya feshe ta da perfume masu bala'i kyau da kamshi, san nan ya sauƙo da ita kasa ya wuce ya nufi drawer sanya kayan su ya ɗauko mata wani dankareren blouse gown ja mai manya manyan flowers fari daga ta kasan rigar, rigar kasan ta a buɗe yake kamar umbrella, san nan ya haɗo mata da pant, ya dawo bakin gadon, ba tare da ya mata magana ba ya fara sanya mata pant ɗin, bayan ya gama sai ya sanya mata rigar a wuyar ta yana kokarin sanya mata hannu tayi sauri cirewa tana faɗin "Daddy baka samin wan nan abun da nagani a film matan suna sawa ba" tayi maganar cikin shagwaɓa cikin nuna ko in cula yace "Wani abu kenan?" Hannu tasa saman kirjin ta tana faɗin "that thing that looks like ball a kirji naga suke sawa and then the thing is big" sai lokacin daddy ya gane breziya take nufi hakan yasa yaja dogon tsaki a kule yace "Sai kin girma" kuka ta sa masa tana faɗin "Ni yanzu ma na girma ai, kuma da suka sa suma sunyi kyau ni kasa min nima nayi kyau" dafe kai daddy yayi yana nadamar barin ta ma da yake tana kallo India film, ganin yayi shiru ya kyaleta ne yasa ta fasa masa ihu tana kokarin sauka daga gadon, cikin sauri ya riƙota cikin muryan rarrashi ya fara magana "To ai my Jelly baki da abun sai naje Shopping sai in sawo miki yanzu dai kisa rigar ki karsu yaya Imran suzo su ganki haka, kuma kinga har da su Umaisha yaya yace min zasuzo, ko so kike su fiki kyau ne?" Cikin sauri ta girgiza masa kai tana faɗin "A'a daddy banson su fini kyau" da murmushi a kan face na shi yace "Yauwa my Jelly to kisa kayan naki idan ba haka ba zasu fiki kyau" ya kai karshen maganar tare da sanya mata rigar, ba musu ta tsaya ya sanya mata tsab ya riƙo hannun ta yana faɗin "Muje kasa na baki abinci" maƙe masa kafaɗa tayi cikin shagwaɓa tace "Daddy what about make up fa? Baka min ba ai" girgiza kai kawai yayi tare da sakin hannun ta ya koma gaban mirror ya ɗauko lipstick da powder da kwalli yana tafiya yana tunanin ya za'ayi kwalliyar tayi kyau dan wancan karon ma daya mata kwalliyar kamar dodo ta zama, haka dai ya karisa wajen ta da tunani fal ransa gefen ta ya zauna ya fara shafa mata powder, sai murmushi take, shiko sai rawa hannun sa keyi, sosai ya lapka mata powder a face nata kafin ya ɗauko kwalli ya sanya mata, a mai mai kon yasa mata kwallin a cikin ido sai ya sanya mata a kasan ido dan gani yake kamar zai tsole mata ido idan ya sanya mata a cikin ido, kamar wata matsafiya haka ta dawo haka ya labka mata lipstick ja a baki har ma gefe da gefen bakin, nan take bakin nata ya kara girma, shi kan shi ya tsorata da kallon ta amma ba yadda ya iya da ita, yana kokarin miƙewa tayi saurin cewar "Daddy baka sanya min a saman gerata ba, a na sawa a wajen ma mummy'n su hudan School na mu tana sa musu" ba musu ya koma ya fara zana mata lapka lapkan gera yana tunanin waye zai samu ya koya masa yadda ake wa mace make up dan ya rinƙa sanya Jelly farinciki dan tana bala'i son make up musamman idan taga friends nata a School iyayen su sun musu sai ta yi ta damun sa sai ya mata, da wan nan tunani ya kammala mata make up ɗin, kamar wata aljana haka ta dawo ya zana mata gerar lapla lapka har kusa da ido ga shi sama da kasa ya zana mata gerar, ɗaya yayi kasa ɗaya yayi sama, ita kuwa sai washe baki take tana dariya, cikin sauri ya kawar da kan sa dan idan tayi dariya kamar boka ko wani katon mummunar aljani take dawowa, haka ya kama hannun ta ya ɗau wayar sa suka fice palo

Ko da sukaje palo sai kallon ta su Zuwaira suke, sun kasa gane ta sun san dai ba wadda daddy zai riƙo haka in ba jelly ba,

kallon sama da kasa tayiwa su Zuwaira kafin tace "Ku idan mutun yasha make up sai kuyi ta kare masa kallo to ni karku kwashe min kyan make up na yaya Imran nayiwa duk wadda ta sake kallo na sai na kwakwale idon ta" cikin sauri suka yi kasa da kai shi kuwa daddy ko ajikin sa ya ja hannun ta suka wuce saman table, Nana tazo tayi serving nasu suka fara cin abinci, idan tana taunar abincin kai kace rakumi ne ke cin abinci saboda yadda daddy ya lapka mata lipstick a baki, sai kau da kai daddy yake bai son ganin ta a wan nan yanayi ita kuwa sai murmushi take tayi make up.


👹DAULAR MUTUWA👹

Ruwan sama mai karfi ne ya ɓarke a dajin a firgice yan sanda da suka suma suka farfaɗo, tare da fara ihu mai tarwatsa kwakwalwan ɗan adam, a sukwane suka bazama cikin dajin basu san in da suka dosa ba kwata kwata gudu kawai suke sun rarraba hanya kowa ya kama nashi hanya,

Abun da ya basu mamaki ya kara ɗaure musu kai sai kawai ganin su sukayi dukkan su a cikin asalin *Daular mutuwa* a ruɗe suka tsaya suna zazzare ido kamar ɓera a tarko, suna tsaye suna waige waige suna karewa gidan kallon, sai ganin wasu jibga jibgan wasu halitta masu kama da shanun daji wayo ɓauna amma sai dai wayan nan sunfi ɓauna girma jibga jibgan gaske ne wadda zasu kai girman giwa, a guje wayan nan halittu sukayi kan yan sandan nan alama a yin wace suke, kafin yan sandan suyi wani yunkuri wayan nan halittun sun farmusu, sun fara yin kaca kaca da naman jikin su suna gurnani kamar wasu mayin watan zakuna,

tas suka cinye yan san dan nan ko kashi basu bari ba har jinin da ya zuba a kasa sai da suka lashe tas, san nan suka girgiza jikin su tare da sakin wata mahaukaciyar ihu mai tarwatsa kwakwalwan ɗan adam san nan suka riƙiɗe suka zama mutane matasa kyawawa kamar larabawa, suka wuce suka shige wani ɗaki mai kama da keji.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*KANO*

Da sallma su Irfan suka shigo palon, daddy da Jelly suna zaune saman sofa suna buga game a system ɗin daddy, daman kullun idan daddy ba zai je office ba sai ya zauna ya kunna musu game ɗin kwallo suyita bugawa tare, Jelly ta iya buga game ɗin kwallo sosai, wani lokaci ma har winning ɗin daddy take,

Jin sallama yasa ta ɗago ido ta kalli bakin kofar da kwalliyan ta kamar boka, ganin su Imran ne yasa ta miƙe a guje tana ihu ta nufi Imran, ta faɗa jikin sa tana dariya, ba tare da ya lura da face nata ba ya ɗaga ta sama yana faɗin "Oyoyo rabin rai na" yayi maganar yana kokarin zama saman sofa, dai dai lokacin idon sa ya sauka kan face ɗin ta, ihu ya saki tare da sauke ta daga jikin sa yana faɗin "Wace ce ke? Wa innahu min sulaimanu wa innahu bismillahi rahmanin rahim ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba bappa wace ce wan nan?" Saboda dariya Irfan har da faɗuwa kasa yayi, dan duk da bai san face ɗin Jelly ba ya fahimci ita ɗin ce tasha make up dan Irfan yana da ƙwaƙwalwa sosai ga dogon tunani, Aafia Umaisha Akila Dukka sai dariya suke ban da Akil da face na shi a ɗaure kamar hadari

AKILA

kanwar Imran ce itace autar su yanzu haka tana da 15 years kamar Umaisha, kyakkyawa ce sosai irin ta ɗaya da Imran.

Akil

Matashin saurayi ne mai jini a jiki kanin Imran ne shima daga Imran sai shi a yanzu yana da 22 years while Imran nada 28 years dukkan su kamannin su ɗaya sai dai shi Akil farine tas, da yake family su daddy ruwa biyu ne fari da chocolate.

Shi kan shi daddy sai da dariya ta kubce masa, ita kuwa Jelly cikin shagwaɓa tace "Yaya Imran me ya faru?" Miƙewa tsaye Imran yayi ya fasa zama a kujerar cikin tsoro yace "Bappa wallahi muryan ta irin na Jelly ce, dan Allah ina Jelly ta me ya kawo aljana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login