Showing 21001 words to 24000 words out of 194715 words
komai naji kishin kishin kamar zai dawo ne" waro ido waje Umaisha tayi tana faɗin "who told you?" "I'm on my way coming back to hause Abbi called me dan yaji mun koma gida ne or not nan yake ce min wai kamar yaya Irfan zai dawo" da sauri Umaisha tace "Allah yasa karya dawo yanzu" daga cikin toilet Aafia tace "A'a karma ya dawo gaba ɗaya" "Haba Aunty Afi ya zaki ce karya dawo kuma?" "Eh mana Umaisha karya dawo, uban me yake mana idan ya dawo in ba ya takura mana ba ya samu sanya katon hijabi muje School gashi sai ya samana ido ya hana mu sanya attachment a kai ya hana mu sanya eyelashes wai shi ustaz duk wani jin daɗi na rayuwa sai ya hana mu shi yasa nake masa fatan karma ya dawo yayi zaman sa a can dan ni dai bana bukatar sa" taɓe baki Umaisha tayi tace "A'a ni kam ina son ya dawo amma ba yanzu ba sai mun samu hutu" dogon tsaki Aafia taja dai dai lokacin da take shiga cikin baf na wankan tayi shiru bata sake ce da Umaisha komai ba ita ma Umaisha komawa tayi ta kwanta ta ci-gaba da chatting da take yi
💞💞💞💞💞💞💞💞
KANO
Karfe 5 na yamma dai dai dady ya shigo gidan jelly na zaune a palo tana rungume da dolly ga Nana da Zuwaira masu aikin girkin su nan suna zaune suna kallo a makeken Tv plasma dake saman TV stand, da sallama daddy ya shigo palon a gajiye da gudu jelly ta miƙe ta nufe sa tana faɗin "Oyoyo dady na" rungumota daddy yayi yana faɗin "My baby ya baki yi wanka ba?" Turo baki tayi kamar biro a shagwaɓe tace "Daddy kai nake jira ka dawo kamin ai" "Haba my baby na faɗa miki yanzu da kan ki zaki rinƙa yin wanka dan kin girma baki ganin ko su Nana na hana su miki wankan bane na faɗa miki tun last week bazan sake yi miki wanka ba ke da kan ki zaki rinƙa yi wato kenan kwana biyu da suka wuce ba kiyi wankan ba ko?" Kukan shagwaɓa ta sa masa a ruɗe yace "Haba my baby me abun kuka to yi shiru muje na miki" ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun ta tana rungume da dollyn ta suka nufi bene cikin girmamawa su Zuwaira suka gaida daddy tare da masa sannu da zuwa fuska a ɗaure ya amsa musu suka haye sama yana riƙe da hannun jelly,
jelly ta fara girma amma taki yarda ta rinƙa wanka da kan ta ba yadda daddy bai yi da ita ba da suka shiga ɗaki akan tayi wanka da kan ta amma taki sosai daddy yayi nadamar saba mata da wanka da yake mata da tun farko ya bar su Zuwaira suna mata da duk haka bata faruba yanzu gashi ta fara kirgan dangi, dafe kai yayi ya zauna a gefen gado yana neman mafita dan gaskiya ba zai iya cigaba da yiwa jelly wanka ba a halin yanzu ta fara girma, "Daddy yaushe Yaya Imran zai zo" tayi tambayar cikin shagwaɓa jin ta ambaci sunan Imran yasa yayi saurin ɗago kai yana faɗin "Yauwa my baby jeki yi wanka da kan ki Yaya Imran naki na hanya" tsalle tayi tana dariya ta nufi toilet da gudu tana faɗin "Daddy ka kula min da dolly bari to nayi wankan" shiru yayi ya kasa magana yana tunanin yadda zasu kwashe da ita idan yau Imran bai zo ba zata iya kin cin abinci ma ta kwana da yinwa in dai Imran bai zo ba gashi Imran baya kasan ma gaba ɗaya, tunanin mafita sosai daddy yake yadda zai yi da jelly da kuma yadda za'ayi ta yarda ta rinƙa wanka da kanta kullun.
Yana zaune awajen yana tunani ya kasa motsawa har jelly tayi wanka ta fito jikin ta duk kunfa bayan wuyan ta duk sabulu bata fita ba zuba mata ido yayi yana kara dana sani a ran sa "My baby jeki sake zuba ruwa da kyau a jikin ki sai ki dawo" turɓune fuska tayi ta juya tana turo baki ta koma cikin toilet ɗin a fili ya furta "dole mu dena kwana ɗaki ɗaya da ke kar nazo na miki aure nan ma kice sai da ni zaki kwana a gidan mijin naki" sosai daddy ya rinƙa dana sani a ransa yana kokarin miƙewa wayar sa ta fara kara a nitse ya fito da wayar tare yin picking ya manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Hello" daga ɗayan ɓangaren Alhaji Zahraddeen yace "Hello maik Ya kake ya baby jelly" "Jelly tana lafiya amma yaya ya naji muryan haka?" Dogon numfashi Alhaji Zahraddeen yaja tare da sauke wa a hankali kafin yace "Dole kaji murya na haka ba, nashi ga damuwa ne sosai a kan gawar da a ka nuna a News jiya wai ta Nawazudden ne Allah sarki bawan Allah mutun ne mai adalci da kaunar talawa duk wani mai adalci a kasar nan sai miyagun ɓarayin gwamnatin nan sun san yadda sukayi suka kayar da shi" shiru daddyn jelly ya ɗan yi kafin yace "Hakane amma nifa abun yana bani mamaki yadda ya ɓata lokaci guda sannan daga baya a kawo gawa a ce mana yayi haɗari ne ya rasu bayan shi bai sanar da kowa zai yi tafiya ba mutane ma sai cewa suke bashi bane duk da fuskar gawar tayi jaga jaga ba'a ganewa amma jama'a sun ce ba shi bane ni abun da yake kara bani mamaki ina family'n sa? Ina suke ya a kayi sukayi ɓatan lokaci guda?" Jinjina kai yaya yayi kafin yace "Maik kadai na wannan tunanin na banza Nawazudden fa abokan hamayya suka kashe sa shi ne kawai family sa kuma Allah ne kaɗai yasan In da sukayi ko suma an kashe su an ɓoye gawan sune oho Allah dai shi ne masa ni a kan komai In Sha Allah gaskiya zata yi halin ta ai amma ko ni gawar da aka fitar jiya a kace gawar Nawazudden ne ban yarda ba gaskiya dan Nawazudden bai da jikin wan can gawar san nan farine tas kamar balarabe kamar sa ɗaya da first born na shin nan ina rokon Allah daya sanya family'n sa suna raye na haɗu da su na taimaka musu kamar yadda ya min ya taimake ni a rayuwa ta sosai" shiru daddyn jelly yayi ya faɗa doguwar tunani "Maik baka jinane?" Yar firgigit daddyn jelly yayi kafin yace "Ina jin ka yaya" "Ya batun Jelly da Imran?" "Eh yaya ka tun Jelly na da 2 years a duniya Imran yace itace matar sa kuma ba wanda zan bawa ita In Sha Allah sai shi" "Imran yana da kirki sosai in dai yazo kasar nan sai yazo har gida ya gaida ni" "Sosai ma yaya yana da kirki, Alhadulillah ita ma Jelly tana son shi duk da bata san me soyayya yanzu ba amma tana bala'i son ganin sa suyi hira sun saba kaga bani da wata matsala ta wan nan ɓangaren sai dai ɓangaren Hajiya Umaiya bana jin zatayi accept Imran ya auri Jelly ni na sani gidan nan ma a ɓuye yake zuwa idan ta sani bazata taɓa yarda ba" "Hmmm kai dai Maik ka ci gaba da addu'a amma Umaiya ta wuci tunanin mai tunani yanzu zan wuce gida zamu yi waya in na kai gida ban son ina driving ina waya" to daddy yace tare da katse kiran ya ɗago ya kalli Jelly dake zaune saman mirror chair ta tsaresa da manya manyan idon ta kamar ball "My baby lafiya? Yaushe kika fito wankan?" Murmushin tayi kafin tace "Daddy da uncle kayi magana ko?" Gyaɗa mata kai yayi ba tare da yayi magana ba "Daddy me yasa Umaiya ɗin ba zata bari ka aura min yaya Imran ɗin ba? Ita muguwa ce ko? San nan me auren da yasa ba zata bari ba me auren ke nufi" girgiza kai Daddy yayi kafin yace "She is your mother also don't call her wicked" turo baki tayi tana faɗin "She is a wicked daddy i don't like her she has a big head and nose she don't like people to come close to her everyday she's shouting and abusing people" dafe kai daddy yayi daman yasan halin Jelly kwata kwata bai lura da ita a wajen bane yasa yayi ta hira da yaya da yaga fitowar ta ai da bai zagi Hajiya Umaiya a gaban idon ta ba "Daddy what are you thinking?" "Go and wear your clothes first my baby" "No daddy ni gaskiya kai ne zaka samin" tayi maganar kamar zata yi kuka yana kokarin yin magana suka jiyo sallamar Zuwaira a bakin kofar shigowa a takaice daddy ya amsa mata sallalar da "Waalaikumussalam" daga ta waje Zuwaira tace "Daddy kana da bako a palo" "bako kuma?" Daddy ya tambaya da mamaki a face nashi dan shi dai bai yi da kowa zai zo gidan sa ba "Eh daddy bako" Zuwaira ta ba shi amsa "Okey gani nan zuwa" ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya dubi jelly dake tsaye ɗaure da yar towel da bata gama rufe mata cinya ba "My baby ki sa kaya ki zo palo ki same ni muci abinci" bai jira amsar taba ya fice dan ya san halin ta yanzu idan ya tsaya jiran amsar tama wata rigimar zata tsayar masa.
Yana fitowa palo idon sa ya sauka kan wani matashi dake zaune saman sofa mai zaman mutun 2 sanye yake cikin wando jeans crazy da riga t-shirt fara yayi wata iriyar aski irin na shararrun yan duniya bakin nan nasa bakin kirin yasha sigari yayi tatul gashi fari tas da shi hakan yasa baƙin bakin nasa ta kara fitowa sosai lokacin guda face ɗin daddy ta sauya daga annuri zuwa ɓacin rai ya kariso cikin palon ya zauna saman kujera 1 sitar yana faɗin "Muneer yaushe ka dawo?" Cikin wata iriyar katon murya kamar na yan shaye shaye Muneer yace "Yau da safe na iso tun ɗazun naso zuwa office naka amma ban samu dama ba sai yanzu nace bari nazo gida mu gaisa" "Okey yayi kyau ka kyau ta ya baban naka?" Muneer zai yi magana Jelly ta fito sanye cikin doguwar riga zuwa gwuiwar ta kayan sun ɗan matse ta kaɗan kan ta babu ɗankwali tana tafiya tana yauki tana kwaɓe fuska har ta kariso wajen daddy ta zauna saman cinyar sa a shagwaɓe tace "Daddy ya har yanzu yaya Imran bai zoba?" Kallon Muneer daddy yayi kafin yace da Jelly "My baby je ki fara cin abinci ina zuwa yaya Imran kuma yana hanya" "To daddy amma ka faɗa wa yaya Imran dan Allah yau kam yazo tare da Akila kaji?" Gyaɗa mata kai daddy yayi ba tare da yayi magana ba miƙewa tayi ta nufi table tana faɗin "Daddy dolly tayi barci" shiru daddy yayi bai amsa mata ba dan bai son jan magana da Jelly yanzu miƙewa Muneer yayi ya nufi table ɗin shima yana faɗin "Daddy nima abincin zan ci ai" ji daddy yayi kamar ya koresa daga gidan amma ba hali, hakan ya sa ya kakalo murmushi dole yace "To Muneer kai da gidan ku bismillah kaci mana" ya kai karshen maganar tare da miƙe wa shi ma ya nufi table ɗin Nana ce tazo tayi serving na su a tare suka ci abinci daddy na ci yana bawa Jelly a baki shi kuma Muneer yana cin na shi.
Bayan sun kammala cin abincin ne Muneer ya musu sallama ya fice daga gidan ba karamin daɗin tafiyar sa daddy ya ji ba dan bai son Muneer bai son ganin sa ko kaɗan riƙo hannu jelly daddy yayi suka koma sama shi ya wuce toilet dan yin wanka ita kuma ta wuce ta haye saman katafaren gadon su ta kwanta kusa da dollyn ta dake barci.
💞💞💞💞💞💞💞💞
KADUNA
Bayan Aafia ta fito wanka ɗaure da towel a kirjin ta wadda a iya cinya yazo mata kai tsaye gaban mirror ta nufa ta zauna saman mirror chair ta fara shafa lotions ɗinta masu kamshi da kyau da tsada "Aunty Aafia ina son in miki wata magana" cewar Umaisha ba tare da Aafia ta juyo ba tace "To sarkin magana ina jin ki" miƙewa zaune Umaisha tayi kafin ta fara magana "Dan Allah Aunty Afi ki dai na kula Rufee da Amal wallahi duk ba class naki bane gwara ma Anisa ba kuma ina faɗa miki hakan dan Rufee da Amal sun fito daga gidan talakawa ba a'a ina gaya miki hakan ne sai dan nasan ba dan Allah suke tare da ke ba ni ban hana ki ki kyautata musu kamar yadda kike yi ba dan nasan kece karfin su saboda ke Abbi ya ɗauki nauyin karatun su kiyi hakuri ki dai ma yawo da su a cikin School kin sani halin su ba mai kyau bane kowa yana gulman su a School nan amma sai ki rinƙa biye musu zaki jawa Abbi zagi a wajen jama'a dan Allah ba dan ni ba ki fita har kan su sam basu da ce da ke ba" miƙewa Aafia tayi bayan ta gama shafa mai ta nufi drawer kayan sawan su cike da izza tace "Umaisha har kinyi girman da zaki faɗamin da wan da ya dace nayi abota?" Cikin sauri Umaisha ta girgiza kai "To daga yau idan kika sake shiga harkata sai na ɓallaki ba ruwan ki da friends na kiyi harkan ki a School nima nayi nawa idan mun dawo gida shine muke sister's kin gane ko?" Gyaɗa mata kai Umaisha tayi dan daman tasan halin Aafia ma wuyacin abune ta yarda da shawarar ta komawa tayi jiki ba kwari ta kwanta ta ɗauki wayar ta tana latsawa tana tunanin yadda zata raba yar uwar ta da su Rufaidat ita kuma Aafia shiryawa tayi cikin doguwar riga bubu tana ja mata a kasa ta feshe jikin ta da perfume sannan ta ɗau wayar ta, ta fice daga ɗakin ta nufi garden na gidan dan shan iska.
💞💞💞💞💞💞💞💞
KATSINA
Karfe 6 dai dai mum ta gama girki ta fito tayi wanka ta shirya musu abincin a saman taburma kamar yadda suka saba, sannan ta fito musu da daddumar da hijabi ita da gwaggo dan gabatar da sallar mangariba idan lokacin ya cika zama tayi saman tabarman tana faɗin "Jehan kizo ki ɗauki abincin nan ki kaiwa babana gidan su" Jehan dake zaune cikin ɗaki saman gado tana kokarin kunna wayar Rimsha tace "did you heard what you said mum? do you mean I should come and take food to that dirty boy place?" A kule mum tace "Jehan don't allow me to come and catch you, Allah ko kizo ki ɗauki abincin nan ko in zo in same ki" turo baki Jehan tayi tana jin bakin cikin yadda mum ke zubar mata da daraja, haka ta miƙe ba dan ta so ba ta ajiye wayar duka biyu daga nata har na Rimsha ɗin tana kunkuni ta fito babu hijabi tazo ta tsaya a kan mum tana faɗin "where is the food?" Da hannu mum ta mata nuni da ɗan ma dai dai cin foodflask dake gaban ta hannu jehan tasa ta ɗaki kulan ta nufi hanyar fita "Where is your hijab Jehan?" Cewar mum kara turo baki tayi kamar biro cikin murya kamar zata yi kuka tace "Mum I told you I don't like hijab please mummy stop talking to me about hijab" ta kai karshen maganar tare da ficewa daga gidan tana turo baki, sai da ta fita gaba ɗaya san nan tayi addu'ar fita daga gida ta nufi gidan su Sadiq tana kwaɓe fuska.
A dakalin kofar gidan su ta isko sa tana isa wajen Yusuf ya iso ko sannu bata ce masa ba ta ajiye masa kulan abincin a gaban sa ta juya yana faɗin sannu ki na gode kamar bata san da mutun awajen ba ta wuce ta koma gida kallon sa Yusuf yayi kafin yace "Yaya Sadiq kaji labarin da naji kuwa?" Waro ido waje Sadiq yayi yana faɗin "Me kaji" girgiza aki Yusuf yayi kafin yace "Sudais kanin Fadil ne naji yana Faɗe wai Fadil yace sai yabi dare yayi wa Jehan fyaɗe tun da ta mare sa ba zai barta ba sai ya ɗau fansa" zumbur Sadiq ya miƙe dan yasan halin Fadil zai iya ai kata fin hakan ma mugu ne sosai "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun yanzu Yusuf me mafita?" Miƙewa shi ma Yusuf yayi yana faɗin "Mu bari zawa da safe muyi magana da mama muji me zata ce" komawa Sadiq yayi ya zauna shi ma Yusuf ya koma a zauna tare da jawo kulan da Jehan ta kawo musu ya buɗe tuwon shinkafa ne da miyar ɗanyen kuɓewa yaji nama da kayan haɗi sai kamshi ke tashi mayar wa Yusuf yayi ya rufe yana faɗin "Muje muci da mama ko?" Gyaɗa masa kai Sadiq yayi suka miƙe a tare suka shige cikin gida
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai
Mai bukatan karanta book ɗin*TRIPLETS* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please
Share fisabilillah 👏
💋Star Lady💋
💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞
*💞 TRIPLET'S💞*
https://chat.whatsapp.com/DOMGC0F7nAm6qQt6zWFwcf
*STAR 🌟 LADY..✍️*
*💋The beginning💋*
*Episode 6*
Jehan na komawa gida babu ko sallama zata wuce ɗaki Mum tace "Come here" ba musu ta koma ta zauna kusa da mum tana faɗin "here I am" kallon tsab mum ta mata kafin tace "Whare is your fake face?" Sai lokacin Jehan ta tuna da furkar roban da ta sawo hakan yasa ta miƙe da sauri ta shiga ɗaki ta ɗauko ta dawo ta zauna kusa da mum dai dai lokacin gwaggo ta fito daga wanka ta zo ta