Showing 147001 words to 150000 words out of 194715 words
ta, Ibraheem dai zuba musu ido yayi yana kallon Jehan kamar ya make ta yaji dan haushi, yar karama da ita sai iya shege.
A wanna karon abun hawa daban daban suka hau, dan Sadiq zai wuce gareji ita kuma hospital, ba yadda Sadiq bai yi da Jehan ba a kan ta amsa kayan uniform nata amma taki, ta kafe tace sam ita ba zata ansa ba, dan babu wanda ya isa ya zaɓa mata kayan da zata sanya in zata fita, haka Sadiq ya wuce da kayan garejin su ita kuma ta wuce hospital, daman haka suke kullun, idan Sadiq yazo ya gai da su gwaggo sai ya wuce gareji sai yamma idan zai koma gida sai yazo ya ɗauke ta su koma tare.
Tirgashi akoi fa cakwakiya Jehan dai tace bazata sanya uniform ba, wanna shine wasa farin girki, mu leƙo Washington DC mu dawo.
💞WASHINGTON DC💞
12:30Am
kamar kullum duniya dukka sun yi barci, shi kuwa yana zaune saman table chair na dining table na kasa yana latsa system, jikin sa na sanye da bathrobe fara kal kamar yanzu ya fito da ita a ledar ta, gata da laushi tilis kamar audiga, kasan cewar gaban rigar a buɗe hakan ya bayyanar da kyakkyawar lallausan dark black gashin mai tsantsi kwance a saman faffaɗar kirjin, gwanin ban sha'awa dan sai kwalli gashin yake kamar ya shafa mata baby oil, gashin hannayen sa da na kafafun sannan duk suna kwance lup a jikin sa, kasan cewar gashin dark black ne shi kuma fatar sa farane kal hakan yasa gashin bayyana sosai, ya tara dark black curly hair sa ya ɗaure a baya, ya bar wannan na gaban goshin nasa ta karawa face nasa kyau over, yau ma kamar kullun sky blue light ne kunne a palon, hasken wutar ba karamin kyau tayi ba a kan face nasa, ya zubawa system nasa dake saman table wanyan nan dara daran blue eyes ɗin nan nasa masu ɗaukan hankali, kasan cewar ya sauke idon nasa kasa kaɗan yana kallon system ɗin, hakan yasa, zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana dan idon nasa yayi kamar a rufe, yayi shiru yana ɗan cizan red lips nasa nan, kamar mai tunanin wani abu, ya kafe system da ido, ga jibga jibgan bodyguard na su a tsai tsaiye suna jiran yace abinci su bashi tissue ya goge bakin sa, already kamar kullun sun zuba masa duk wani abun da zai buƙata.
A hankali James ya fito daga bedroom nasa sai hamma yake alamar barci, wuce wa yayi ya nufi word room wajen Musharraf zai je yayi masa alwala, dan Musharraf yana sallar dare kullun, shi yasa ya roki James dan Allah karfe 1 dai dai ya rinka zuwa yana tashin sa dan ya samu yayi nafila, kasan cewar James Allah ya ɗaura masa kaunar Musharraf yasa baya wani damuwa kuma ya sanya abun a ransa, tun 12:30 yake zuwa wajen Musharraf su zauna suyi ta hira, sai 1 dai dai yake wa Musharraf alwala, kuma ya zauna yayi ta kallon sa har sai yayi nafila raka'a 8 sannan ya rufe da shafa'i da witiri, sai bayan ya gama dukka, James ke kwantar da shi ya wuce nasa bedroom yaje ya kwanta, kuma haka da asuba zai dawo yayiwa Musharraf alwalan sallar asuba, duk sojojin da bodyguard ɗin dake gidan basu iya yadda ake alwala ba shi yasa yake zuwa da kan sa yayiwa Musharraf ɗin, kuma yana laakari da shiya buge Musharraf ɗin da mota, dan haka alhakin kula da shi ya rataye ne a wuyar sa.
Zai wuce wajen Musharraf ya hango blue light na palo kasa a kunne, ko ba'a faɗa masa ba, yasan Romeo ne, dan shi kaɗai ne mai cin abinci da tsakar dare kamar wani aljani, wani lokaci kuma ba abinci yake ci ba haka kawai zai fito palon kasa ya zauna yana latsa system ko kuma wayar sa, da wuya ka gansa a palon kasa idan ba tsakar dare ba.
Fasa nufa wajen Musharraf yayi, ya sauƙo kasa wajen Romeo, saman chair ɗin kusa da Romeo ya zauna yana faɗin "well done lion" kamar dai kullun shiru Romeo ya masa kamar bai san da zaman sa a wajen ba, ɗaukan fruit yayi ya fara ci, a hankali ya matso da kan sa yana kallon cikin screen ɗin system da Romeo ke aiki a ciki, zaro ash eyes nasa waje yayi, har sai da fruits da yake ci suka kwaresa, nan take ya fara tari da karfi karfi, bodyguard ɗin dake tsai tsaye har suna rige rigen miƙa masa glass cup mai ɗauke da ruwa mai sanyi, da sauri ya ansa ya kafa a bakin sa yasha
Shi kuwa Romeo kamar bai san James na tari ba, aikin sa kawai yake, yana cizan lausasan laɓaɓɓan sa, sai bayan tarin James ya tsaya ne, ya ajiye fruit na hannun sa, ya miƙe zai bar wajen, gently in a cool Romeo yace "Come here" ba musu ya koma ya zauna, yana faɗin "here I am"....✍️✍️
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪
💞Star Lady💞
TRIPLET'S💞
💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)
*Gargarɗi*
_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_
WhatsApp me for more information 09162620621
Episode 30-31
💞WASHINGTON DC💞
Shi kuwa Romeo kamar bai san James na tari ba, aikin sa kawai yake, yana cizan laullausan laɓaɓɓan sa
sai bayan tarin nasa ya tsaya ne, ya ajiye fruit ɗin hannun sa, ya miƙe zai bar wajen, gently in a cool Romeo yace "Come here" ba musu ya je ya zauna, yana faɗin "here I am" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me James ɗin yace ba, shima James shiru ya zauna yana tunanin me yasa Romeo ya kiransa.
After 45mims
A hankali Romeo ya ɗan ture system ɗin gefe, yana ture system ɗin bodyguard sukayi sauri matso masa da plates ɗin abinci gaban sa, tsalleke abincin yayi ya ɗauko fruits ya fara ci a nutse kamar bai son tauna, hannu James yasa suka fara ci a tare, sai satar kallon Romeo yake dan ya fahimci ko akoi wani sauyi a face ɗin Romeo.
"Why are you looking at me like this?" Kamar saukar aradu haka James yaji wanna tambaya ta Romeo, ko taya akayi Romeo yasan yana kallon shi oho, sai ta nitsuwar sa yayi yace "Because your my blood, I like to watch my blood face like film" shiru Romeo ya masa bai sake magana ba.
Yau dai fruits kawai Romeo ya ci, gently ya miƙe ya nufi hanyar haurawa sama, binshi da ido James yayi yana mamakin, to akan me Romeo zai kirasa kuma bai yi masa wata magana ba, a ransa yace "Lion murɗaɗen mutun baka taɓa gane gaban sa bare bayan sa, kullun cikin gindayar da mutane yake, sai ka rasa ina ya dosa kwata kwata, Allah ya kawo masa sauki, yanzu kawai ya wani kirani kuma ya tashi ya barni zaune, ni ya ɗaga min hankali ma" ta kai karshen zancen zucin na sa tare da miƙa wa ya wuce word room.
Ido biyu ya isko Musharraf, bawan Allah ya jima da tashi babu mai masa alwala shiyasa ya kwanta shiru kamar wani maraya, hakuri James ya bashi sanna ya ɗauko ruwa da niyar yi masa alwala.
"No James just leave it, yau bana jin daɗin jikina, sai zuwa gobe zan yi sallar daren" kamar James zai yi magana sai kuma ya fasa, ya ajiye ruwar ya dawo gefen Musharraf ɗin ya zauna yana faɗin "Okey let's chatting" murmushi Musharraf yayi, zai yi magana wayar James ta fara kara, cikin sauri ya fito da wayar daga aljihun wandon barcin jikin sa.
Josephine shine sunan da ya bayyana a saman screen ɗin, guntun tsaki yaja kafin yace "Not know" yana kai karshen maganar ya katse kiran tare da sanya number a blacklist ya mai da wayar aljihun sa
Cike da karanbani Musharraf yace "who called at this time 1:20am?" (Waye ya kira ka a wanna lokacin) Ɗaure fuska James yayi kafin yace Josephine, "Who is Josephine?" Musharraf ya sake tambaya, a kule James yace "Our mum" ya bashi amsa a takaice, zaro ido waje Musharraf yayi kafin yace "gaskiya ina son sanin me mum ɗin nan taku ta muku, da har kuka mata wanna tsana haka" shiru James ya ɗanyi kamar mai tunani, kasan cewar su turawa ba ruwan su, kusan yaruwar su rabi dukka a faranti suke basu san kunya ba, bare rufawa wani asiri, sai James ya fara bawa Musharraf labarin abun da ya haɗa su da mum nasu, abubuwan da ta musu a baya in short dai ya bashi labarin "daddy tell us, lokacin da muke jaririrai, mum ɗin mu ta haɗu da wata friend ɗin ta yar kasar India kuma musulma ce, sun zama friend sosai, shi ne wan can ɗin tace wa mum ta kai mu wajen magicians, ta bada jinin mu su mata kuɗi da shi, lokacin dad bai da kuɗi, mum kuma sai ta biyewa wan can musulman ta kai mu wajen Magicians, thank God, muna da sauran kwana dad yaje ya karɓo mu ba'a riga an yanka mu ba, shine fa mum tace ba zatayi feeding namu breast nata ba, kuma ba zata zauna da dad ba dan bai da kuɗi, ta tafi ta bar daddy, haka ya rinƙa shan wahalar renon mu har muka girma, that is why bamu son ta, shiyasa su dad basa son Musulmai wai Musulmai mugaye ne, sannan yana ɗaya daga cikin abun da yasa bama son girl a area da muke, dan mata duk haka suke basu da gaskiya, shi yasa nace kada ka faɗa wa su daddy you are a Muslim, ba zasu yarda ka zauna a nan ba" girgiza kai Musharraf yayi kafin yace "Amma kana ganin gaskiya dad ya faɗa muku a kan mum ta kai ku wajen Magicians?" Da sauri James ya gyaɗa kai yana faɗin "Yes ita da bakin ta ma ta faɗa, she accepted her mistake, before now har kasa ta duƙa ta bawa dad da lion hakuri tana kuka, dad da lion sun ce ba zasu yafe mata ba because haka mata suke in sun yi abu zasu ce Sorry later kuma zasu sake repeating na the same wannan mistake ɗin, kuma this is the reason why kawai ba su yafe mata ba, dan ko sun yafe mata zata sake wani mistake ɗin, kuma ai kaga muna da gaskiya, tun muna yara bata son mu sai yanzu da muka girma, she saw we have plenty money now, shine kuma zata dawo tace tana som mu no we can't except her" jinjina kai Musharraf yayi yana faɗin "Eh haka ne kuna da gaskiya, kuma kunyi dai dai, amma in dai ita da kan ta ta yarda da kuskuren ta kuma ta baku hakuri, to please ku yafe mata mana" miƙewa James yayi yace "Good light uncle, and please don't talk about mum to me again" zuba masa ido Musharraf yayi a ransa yana faɗin "Tabbas sheɗan ya ruɗi Mahaifiyar ku tayi kuskure to amma bata cancanci hukuci mai tsauri haka ba, tun da har ta baku hakuri, kamata yayi ku hakura, domin uwa da ƴaƴan ta sai Allah, yanzu Allah ne kaɗai yasan irin raɗaɗin da take ji a zuciyar ta na rashin amincewa da ita da kuka yi, amma ina da tabbacin In Sha Allah kuka musulta, imani ya ratsa ku, kuka san darajan iyaye da amfanin su, da izinin Allah zaku nemeta da kan ku" shi kuwa James tuni ya wuce bedroom nasa ya bar Musharraf da zancen zuci, gyara kwanciya shima Musharraf yayi tare da tuntse idon sa yana son yin bacci.
James dai ko da ya kwanta sai yaji ya shiga damuwa kala biyu, bacci yaki zuwa masa, abu na farko, yana jin like bai kyautatawa Musharraf ba, na biyu kuma damuwa a kan gobe zasu yi taron su na yan ta'adda, kuma tabbas yaga Romeo ya shirya yadda za'a farmaki taron a system na sa, amma ba yadda zai yi dole yaje taron nan in ma ya mutu ko yayi rai, abun da ya fi sawa ran sa shi ne mutuwa zai yi, dan mawuyacin abu ne yaran Romeo su farmaki waje kuma basu yi nasara a kan aikin ba da kamar wuya, yasan tsab sai sun kashe kowa da kowa, a ransa yake jin shike nan zai rabu da yan uwan sa kenan.
Ya kasa bacci sai tunani yake, kamar yadda yaga rana haka yaga dare, sai kusan karfe 6 na safe sannan ya samu bacci wahala ta ɗauke sa.
A fannin shima Romeo bai yi baccin ba, ya kwanta yana ta tunanin yadda aikin zai kasan ce, sai yiwa yaran sa fatan nasara yake, duk da yana da kwarin gwiwa a kan su, Yasan sun samu horo, bai taɓa turasu aiki basu yi nasara ba, sai dai babban damuwar sa ɗaya ba tare da Tga zasu tafi ba, kasan cewar Tga na kwance a gadon masu jinya, daddy na dubasa, wajen da kwarin nan suka harbesa ya kumbura sosai, abun dai sai addu'a dan kuwa ko wando baya iya sawa, yana kwance yana baje yana shan iska, gashi yaki tsayawa a wani duba shi ma saboda raɗaɗin azaba, duk wannan Romeo bai sani ba, bai san cewa Tga yaki tsayawa a bashi kulawar da ya dace ba, da tuni yaje da kan sa ya danne sa ya bashi kulawa da kan sa, sai dai bai sani ba, kuma duk suna tsoron faɗa masa shi yasa, shi kuma bai cika shiga harkan yan gidan ba kullun yana ɗaki, in dai ba kai ka nemo sa ba, to shi baya neman kowa, ɗan gara Triplets na sa da kuma daddy, idan ya wuni bai ji motsin su ba yana kiran su a waya yaji lafiya.
Haka dai shi ma ya kwana ido biyu ba bacci, yana ta tunanin yadda tafiyan yaran nasa zai kasan ce ba Tga ,wannan ne dalilin da yasa jiya da daddare ya kira James dan ya duba masa jikin Tga ɗin sai kuma ya mance da me yasa ma ya kira James ɗin, shiyasa ya miƙe ya bar james zaune a wajen.
Asuba ta gari
Wannan kenan bari mu leƙo su Jelly mu dawo muga cakwakiyar familyn William jacop.
💞NIGERIA💞
JELLY
Yanzu ta ɗan fara sakewa da gidan tana iya zama ita kaɗai, inma a bedroom ko a palo, sai dai fa har yanzu bata wanka da kan ta kuma bata cin abinci da kan ta, sai dai Hajiya ta mata wanna dukka.
Yauma kamar kullun tana zaune a palo ita kaɗai tayi shiru tana kallon Tv ana labarai, duk da ba gane abun da ake faɗe take ba, ta zuba musu ido kamar ta san me ake cewa, yayin da news ɗin ke magana a kan ɓatar ta, dan daddyn ta ya shiga damuwa over, shiyasa har gidan Tv a ka kai zancen, ana cab da sanya hoton daddyn ta, wannan tantiriyar budurwan ta shigo palon babu ko sallama, hakan yasa hankalin Jelly ya kau daga kan Tv ta koma kallon yarinyar, while a Tv kuma an sako hoton ta dana daddyn ta
zubawa attachment ɗin kan yarinyar ido Jelly tayi tana mamaki, ganin babu kowa a palon yasa yarinyar tace da Jelly "Ke zonan" turo baki Jelly tayin kafin ta make kafaɗa tace "A'a ni ba zam zo ba" shiru yarinyar ta ɗan yi tana tunanin yadda zata yi da Jelly ta fara bin ta ɗaki, can wata dabara ta faɗo mata, hannu tasa cikin Jakarta ta fito da chewing gum da take yawan ci, ta miƙawa Jelly, ba musu Jelly ta miƙe ta karisa wajen ta, ta sanya hannu ta karɓa chewing gum ɗin tana dariya, dariya irin na yan duniya yarinyar tayi kafin tace "Yauwa ki saki jikin ki dani ko? Ni auntyn kice, daga yau in nace kiyi abu, ki rinƙa yi zan saya miki sweet kala kala kinyi?" Tayi maganar tana shafa kan Jelly zuwa wuyar ta, Gyaɗa mata kai kawai Jelly tayi tana faman tura chewing gum a baki, murmushi shakiyanci yarikyar tayi kafin ta ɗan duƙo da kan ta, dai dai saitin goshin Jelly kasan cewar ta fi Jelly tsawo, ta mannawa Jelly kiss a goshi tana shafa wuyar ta, ta wuce part nasu, wucewa itama Jelly tayi ta koma cikin bedroom na Hajiya.
Hajiya na kwance Jelly ta faɗo mata ɗakin babu ko sallama, Hajiya bata damu ba dan ta ɗauki hakan a matsayin dan Jelly bata da lafiya ne, bata san Jellyn daddy ba already haka take daman.
Hayewa saman gadon Hajiya tayi ta fara gaya mata yadda suka yi da wancan yarinyar, zubur Hajiya ta miƙe zaune tana kallon ta dan tasan halin afnan sarai, ta santa yar lesbian ce dan kuwa har ita kan ta Hajiya sai da afnan tayi mata tayin lesbian a baya, Hajiya batayi kasa a gwiwa ba taci mata mutunci fes shi ne yasa yanzu Afnan bata mata magana a gidan.
Miƙewa tsaye Hajiya tayi, ta diro kasa daga saman gadon rai a matukar ɓace ta fice daga ɗakin ta nufi part ɗin su Afnan, da sauri Jelly ta sauko kasa ita ma tabi bayan Hajiya.
A palon part na su Afnan Hajiya ta tsaya, ta fara kwalawa