Showing 162001 words to 165000 words out of 194715 words
sume wa a wajen sanna ta miƙe da gudu ta haura sama tana kiran Aafia a kan tazo ta taimaka mata su kai Aunty asibiti, nan fa Aafia ta murje idon ta tace bata san wanna zance ba, ita ba ruwan ta da wata aunty, Auntyn ta mutu ma idan ta ga dama.
Sosai Umaisha taji babu daɗi abun da Aafia tayi, da sauri ta dawo palo, tazo ta riƙo aunty da kyar suka nufi waje, taje ta buɗe kofar motar ta gidan baya ta sanya aunty, ta shiga gidan gaba, babu ko ɗankwali a kanta daga ita sai kayan barci haka taja motar suka nufi hospital
Ita kuma sarauniya Aafia tana ɗaki tana faman neman layin Rufee dan ta sanar mata Aunty na da ciki ya zasu yi.
Tayi Sa'a kuwa ta samu number Rufee a buɗe, kira ɗaya Rufee ta ɗauka, cike da kunan rai Aafia ta sanar mata da abun da ke faruwa na Aunty na da ciki, tun bata tabbatar da gaskiyar cikin ne ko ba shi ba, kai tsaye tacewa Rufee ciki ne,
Duk da rasuwar amal da akawa Rufee bai sa ta saduda ta koma ga Allah ba, haka ta ɗaura Aafia kan mummum shawara "Kina jina Aafia idan muka haɗu gobe a School zan baki wani magani sai ki zuba mata a abinci, cikin nata zai zube Shikenan" ita kuwa Aafia Allah sarki Rufee ta juya mata kwakwalwa, da murnan ta ta amsawa Rufee da to, tana kokarin katse kiran ne Rufee tace "Aafia ya batun Alhajin nan fa, kin ga next week zamu kammala Exam" shiru Aafia ta ɗan yi kafin tace "Okey idan mun fito class na karshe ranar da zamu gama Exam kenan, irin karfe biyun nan sai mu haɗu da shi, amma fa ba zan wuce 1 hour ba dan a ranar yaya Irfan zai yi diran dare kasar nan, kinga kuwa idan yaya Irfan ya dawo babu zancen fita ko kuwa hira a School, dan bincike yake wani lokaci muke da class yaushe kuma zamu fito class, kuma kinga ma next week zamu gama Exam idan muka gama ba zai taɓa barin mu mu fita zuwa wani waje ba tun da ba school, ko shopping sai dai ya kai mu da kan sa, haka yake ya cika takura shiyasa bana son ya dawo" yar tsaki Rufee tayi kafin tace "To shikenan zan faɗa wa Alhajin ba komai hour ɗayan ma yayi ai" daga haka sukayi sallama Aafia ta haye saman gadon tayi kwanciyar hankali kwance tana tunanin yadda cikin Aunty zai zube
Yayin da ita kuma Umaisha ke ta fama da Aunty a asibiti, dan an karawa Aunty ruwa da kuma alluran zazzaɓi, dan sunce akoi zazzaɓi a jikin ta, yar aikin da Abbi ya kawo itace tazo ta goge wajen da Aunty tayi amai ta gyare wajen tsab.
Wanan kenan abun dake faruwa a gidan Abbi bari mu leƙa Daular mutuwa mu gani meke faruwa a can.
👹DAULAR MUTUWA👹
Lokacin da su Ayla suka tashi daga sumar da suka yi, sun sha kukan ɗaukan Rimsha da akayi kamar ransu zai fita, baba da Mustapha ne suka yi ta basu hakuri, da kyar sukayi shiru, yayin da shi kuwa duna da kyar Queen ta yarda ta bashi ruwan tsafi su Barbushi suka bashi yasha kafafun sa suka koma kamar da, da farko Queen taki bashi ruwan tsafin nasu a cewar ta bata ga amfanin duna a gidan ba, sai da su Barbushi suka ta rokan ta sannan ta yarda ta ba shi, yana sha kuwa kafafun sa suka dawo dai dai, ya dawo bakin aikin sa wajen su Ayla kenan.
Yana shigowa part ɗin nasu, da sauri ya wuce ɗakin baba, a nan ya isko su Ayla sai faman shasshekar kuka suke, kusa da su ya musu sannan ya dubi baba yace "Baba ku dai na damuwa dan basu kashe Rismha ba, sun rufe tane a ɗakin duhu na Queen dan ba zai yiwu su yanka ta yanzu ba, saboda Queen zata yi tafiya zuwa kasar Israel tace ranar da zata dawo ranar take bukatar a mata ferfesun naman Rimsha, yanzu abun da nake so da kai baba, ni dai kaga ba cikakken mutun ne kamar ku ba, rabi mutun rabi aljani nake, shiyasa tsafin su baya kamani, yanzu zan musulunta saboda Rimaha dan mu cetota, ba kunce duk abun da kuka roki Allah ku zai muku ba?" Gyaɗa masa kai baba yayi "To na san dai su Queen ba zasu bari kuyi wani abun addini a nan ba, zasu rufe muku baki, ku rinƙa roka mana Allah a ranku nasan zai ji kukan mu, amma akoi wani abu ɗaya da nake so ka sani, zan gwada karfin tsafi na na tsinke sarakunan da aka ɗaure Rimsha da su, daga nan zan fitar da ita daga ɗakin zuwa nan, to ina son ka sani dole da tsafi zan yi wannan kuma ina son ka roka mana Allah da ya kawar wa da Queen tunanin cin naman Rimsha, su kyale ta su manta da ita" sosai baba yaji daɗin zancen duna, farinciki fal ransu baba da Mustapha suka rinƙa sawa duna albarka suna masa fatan alkhari da fatan nasara
Har ya miƙe zai fita, sai kuma ya dawo yace "Baba kafin muyi duk wanna aiki fa sai mun fara mantar da su wace ce Rimsha idan ba haka ba, muka ɗauko ta muka dawo da ita ma mun kira mutuwar mune gaba ɗayan mu dan dukkan mu zasu zo su kashe mu, yanzu zanje mayi aikin mantar da su komai shiyasa nace kuyi mana addu'a, sanna ba lallai na iya kai labari ba, dan tsafin su yafi nawa karfi, kuma idan nayi kuskure suka kama ni to wlh nasan kashe ni kawai zasu yi, dan haka tun yanzu muyi bankwana, zan iya mutuwa a kowani lokaci, amma ba zan mutu ban fitar da Rimsha daga fadar Queen ba" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin, sai daɗi su Ayla suke ji Rimsha zata dawo, sai addu'a suke mata a ransu.
A ɓangaren Rimsha kuwa, wani ɗaki ne mai bala'i duhun gaske suka kai ta, baka iya ganin komai a ɗakin saboda tsananin duhun dake ɗakin, ga wani fitinannen wari da karnin bala'i dake tashi a ɗakin, ga shi ɗakin ba'a zama sai dai tsayuwa kasan cewar kasan wajen wasu kifiyoyi ne masu bala'i kaifi da tsini a suke a wajen, iya in da suka tsayar da ita, iya wajen ne babu wayan nan kifiyoyi masu tsinin bala'i wadda suke iya fasa nama har kashi, sanna sun ɗaure ta da sarkoƙi masu bala'i karfi, sarka ne wadda aka yi shi da dafaffiyar karfe wadda babu wani abun da ya isa ya tsinƙa sa, da gani kasan wanna sarka na tsafin sune, farko da suka ɗaure ta da ta gaji da tsayuwa ta matso da kafar ta tana son zama
Tana sako kafar ta kasan wajen wayan nan kifiyoyin suka cake mata tafin kafar ta har ciki kusa da kashin kafar ta, kan kace me jinin ta ya fara malala a wajen, Allah ma yasa bata ida sauke kafar ta a wajen ba shiyasa wayan nan mayun kifiyoyi basu mata illaba sosai ba, ta gaji da tsayuwa ga yinwa da kishin ruwa, ga bala'i duhu gaske, gashi yanayin ɗaurin da suka mata dole ta gaji dan sun buɗe mata hannu ne suka mata ɗaurin cros ɗayan hannun ta yayi gabas ɗayan kuma yayi yamma, kafafun ta kuma sun haɗe su waje guda saboda wayan nan kifiyoyin, ba halin tayi wani motsin kirki, tayi kuka har ta godewa Allah, ga bala'i zufa da ke damun ta, saboda ɗakin babu hanyar da iska zata shiga sosai,
Tun tana iya kukan gajiya da yinwa da kishin ruwa har ta hakura ta fawwalawa Allah lamuran ta, dara daran sleeping eyes nata sunyi luhu luhu saboda kuka, duk sun kunbura sunyi jawaur da su, babban tashin hankali na biyu bata iya kiran sunan Allah, da zarar tayi yunkurin kiran sunan Allah sai Queen ta shaƙe mata maƙogwaran ta tayi ta fama tana shan azaba tana kuka, sai bayan wani ɗan lokacin sanna Queen ta sake ta, saboda wahalar da take sha wajen furta sunan Allah yasa ta dai na yunkurin furtawa ma kwata kwata, tayi shiru ta hakura tana kiran Allah'n a ranta, Allah sarki baiwar Allah, duna kuwa yana can yana kokarin fitar da ita da tsafin sa, dan shima abun ya sha kan sa yafi karfin tunanin sa, domin shu'umancin Queen ya wuci tunanin mai tunani.
Wannan kenan mu leƙo Washington DC mu dawo
💞 WASHINGTON DC💞
4:00am
Tsaye Romeo yake a balcony bedroom nasa ya goya hannun sa a saman kirjin sa ya zubawa garin nasu ido, yayin da iska dake kaɗawa yana ta watsa masa dark black curly hair sa kasan cewar bai ɗaure gashin nasa ba, jikin sa sanye da Ripped Jeans blue da Round neck polo shirt fara kal kamar yanzu ya ciro ta daga kwali, kasan cewar rigar nasa mai ƙaramin hannu ne hakan ya bada damar bayyanar murɗaɗun damatsan hannun sa, wayan dake cike kamar zasu fashe saboda ɗaga barfe da yake sosai, fuskar nan tasa kamar an aiko masa da sakon mutuwa a ɗaure take tamau babu alamar ya san menene dariya, hannun sa na ɗaure da diamond watch na su na Triplets, sai faman cizan lallausan lips nasa yake, alamar wani tunani yake
yana yin yadda iskan nan ke kaɗa masa wanna dark black curly hair nasa abun gwanin ban sha'awa, domin har fuskar sa gashin ke bazo masa, Brady na kwance daga ɗan nesa da shi kusa da wata yar karamar pool dake wajen, sai kallon cikin ruwan Brady yake, yanayin nasu dai gwanin burgewa da ban sha'awa tare da ɗaukan hankali mai kallo.
Almost 30mins yana tsaye a wajen shiru kamar ba shi a wajen, wayar sa dake ɗaure saman wata haɗaɗiyar karamar bed na kwanciya ka huta dake kusa da pool ɗin ne ta fara kara, tamkar bai ji ringing ɗin wayar ba yayi shiru, bai yi wani motsi da zata nuna yaji ringing ɗin ba, wayar ta katse kira na biyu ya shigo, haka kawai ya tsinci kan sa da jin yanayi mara daɗi a jikin sa, slowly ya juyo ya nufi in da wayar take, yana taku irin na jaruman maza, gently ya ɗauki wayar yana bin screen ɗin da kallo, heartbeat wato Michael shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, ganin sunan Michael yasa yaji wani irin yanayi mara daɗi ya karu a jikin sa, a nitse yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnen sa yayi shiru yana sauraron Michael ɗin.
"Hello lion" shiru Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, ci-gaba da magana Michael yayi dan idan da sabo sun saba, kuma yasan Romeo ɗin yana jin sa "Lion I'm feel like I'm not feeling fine, tun ɗazun ina jin jiki na yana min zafi zuciya na yana bugawa da sauri sauri gaba na yana faɗuwa kamar ba lafiya ba, na rasa meke min daɗi yanzu zan bar white house in dawo gida kawai" shiru Romeo yayi na ɗan lokaci kafin yace "okey come back now" to Michael ya amsa da shi, a tsanake Romeo ya katse kiran tare da mai da wayar ya ajiye saman wannan bed ɗin, ya koma in da yake tsaye ya tsaya tare da zura hannayen sa a aljihun wandon sa, yayi shiru yana tunanin meke damun Michael.
Tsayuwar 20mins yayi a wajen wayar sa ta sake fara rururi, shiru yayi yana jin yana yi mara daɗi a jikin sa, har wayar ta katse bai ɗaga ba, kira na biyu ya shigo, haka kawai ya tsinci kan sa da baya son ɗaukan kiran, shikuwa mai kiran nasa ya nace kamar dama yasan halin Romeo baya ɗaukan kira da wuri idan a ka masa, musamman idan yana wani abun sai ayi ta kiran sa ba zai ɗauka ba har sai ya gama abun da yake yi, baya haɗa abubuwa biyu lokaci guda a nitse yake yin komai nasa, ko tunanin wani abu yake aka kirasa tofa koma wanene mai kiran dole ya hakura har sai ya gama tunanin sa sannan.
Ganin mai kiran nasa yaki dai na kiran ne yasa ya juyo gently ya nufi wajen wayar, dan ya kai 10 miss call mai kiran ya masa.
Tyrone Shine sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar, lumshe dara daran ido sa yayi nan take zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana gwanin burgewa, a hankali ya sake buɗewa idon a kan screen ɗin wayar, gently ya kai hannun sa kamar bai son taɓa screen ɗin yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnen sa yayi shiru bai yi magana ba
Daga ɗayan ɓangaren Tyrone yace "Oga we are done the mission kuma munyi waning, mun kashe kowa dake wajen, sai dai akoi wani abu ɗaya da yake ɗaure mana kai" shiru Romeo ya ɗan yi kafin yace "What is this?" Cikin sauri Tyrone yace "Your watch sir, bayan mun kashe kowa, muna kokarin tattara bayanai da wasu evidence mun samu wani watch a wajen irin na hannun ka sak kamar shi ne ma" zaro blue eyes nasa waje yayi har sai da suka kara kwalli saboda zaro su da yayi
Da ɗan karfi yace "What?!!" Sorry sir kawai Tyrone yake faɗi "Ku kawo min watch ɗin gida yanzun nan" ya faɗa tare da sauke wayar daga kunnen sa ya nufi hanyar komawa cikin bedroom nasa, daga nan ya fice daga bedroom ɗin gaba ɗaya ya sauka palon kasa.
Palon babu kowa sai fitinannen kamshi air freshener da sanyin Ac dake tashi a palon, ko ina tsab tsab, ga haske ya karaɗe ko ina a cikin palon, dan har wutar jikin staircase a kunnen suke, shiyasa palon yayi haske sosai kuma hakan ba karamin kara kawata palon yayi ba.
Saman Sofa set milk color ya nufa ya zauna a saman three-seater tare da jingina kan sa da jikin kujerar ya lumshe dara daran idon sa kamar mai jin barci.
Zaman sa a wajen bai fi minti ashirin ba sai ga wasu jibga jibgan sojoji guda 6 masu jini a jika, jibga jibgan gaske ne masu ji da karfi da lafiya sun ƙoshi da training dan kowannen su ka gani kasan ya karɓi horo yadda ya dace, fuska nan tasu babu alaman imani bare tausayi a ɗaure take tamau, sai wani taku suke a jire, suka kariso gaban sa, sai da suka sara masa sanna suka tsugunna kasa, kasan cewar already yasan da zuwan su sai yayi shiru bai ɗago ya kalli su wanene bane.
Sai da ya ɗauki 10mins a haka yana lumshe da ido sa, su kuma suna tsugunne a gaban sa, sannan ya ɗago kan sa tare da waro dara daran idon sa har sai da sojojin suka ɗan tsorata
Gently yace "Tyrone where is the watch?" Cikin sauri Tyrone ya zura hannun sa cikin aljihun kakin jikin sa ya fito da watch ɗin ya miƙa wa Romeo, gently Romeo yasa hannu sa zai karɓa, sai kuma ya fasa ya zuwa ba Tyrone dara daran idon nan nasa, masu raza jaruman maza, kasan san cewar su Tyrone sun saba da shi, dan Tyrone ne baban yaron sa na biyu daga Tga ne na farko kenan, hakan yasa Tyrone ya dukar da kan sa kasa dan yasan me ya hana Romeo karɓan watch ɗin
Murya na rawa cikin girmamawa yace "Sorry sir I thought is your watch, that is the reason why ban sanya handkerchief wajen ɗauka watch ɗin ba kuma ban damu ba nasa cikin aljihuna ina....
Bai kai karshen maganar ba Romeo ya ɗauke sa da wata mahaukacin gigitatchen mari mai sanya mutun dai ma jin motsin komai na ɗan lokaci, har wasu taurari Tyrone ya gani a face na sa, sai da idon sa suka yi jawur kamar jini saboda marin, abun ka da farar fata nan take shatin yatsun Romeo suka bayyana kwance a kumatun Tyrone raɗau, wajen yayi jawur kamar jini, kan kace me sai hawaye masu bala'i zafi suka fara bin kumatun Tyrone ɗin, an san soja da jarunta, amma fa duk jaruntar su idan Romeo ya mare su sai sunyi hawaye.
A fusace Romeo ya miƙe ya damko wuyar kakin jikin Tyrone tare da haɗawa da wuyar sa ya shaƙe shi ya ɗaga shi sama, da karfi yayi wurgi da shi gefe, yau Tyrone ya ɓata masa rai, a kan me zai ce watch ɗin sa ne me yake nufi da hakan kenan , shima criminal ne kenan?
Kan kace me yana yin Romeo ya sauya, idanun sa sun rikiɗe sunyi jawaur kamar wuta, gaba ɗaya jijiyoyin saman idon sa sun tashi, gashin jikin sa har wani miƙewa suke saboda ɓacin rai, jijiyoyin kan sa duk sun miƙe zara zara dasu, lokaci guda ya riƙeɗe ya zama asalin lion da daddy ke kiran sa da shi, har wata irin huci mai bala'i zafi yake fitar wa tamkar zakin da yayi shekara biyu babu abinci yanzu kuma ya samu abinci an hana shi ci, haka Romeo ya zama.
Gadan gadan ya tinkari Tyrone, da hannu ɗaya ya damko wuyar sa tare da miƙer da shi tsaye, wani mahaukacin shaƙa yayiwa wuyar Tyrone ɗin har sai da idon Tyrone suka firfito waje kamar zasu faɗi kasa, wani irin zufar ɓacin rai ne ta fara gangarowa lion daga gefe da gefen kunnen sa, nan take wasu zara zaran jijiyoyi suka bayyana a wuyar sa yau ran maza ya ɓaci, Tyrone ya dangan tashi da manya manyan criminals na duniya, idan ya tuna hakan sai yaji zuciyar sa na tafasa kamar zata fasa kirjin sa ta fito waje
A fusace yayi wurgi da Tyrone saman centre table glass dake tsakiyar sofa set Milk color,
Watsa watsa tables ɗin yayi glass ɗin suka tarwatse pieces a wajen, wani razanannen ihu azaba Tyrone ya saki domin glass ɗin ya soke masa fuska, kan kace me jini ya fara fita daga face nasa, yana son bawa Romeo hakuri amma ya kasa, saboda wahalar da ya sha,