Showing 165001 words to 168000 words out of 194715 words

Chapter 56 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1005

sanna kuma ya san halin Lion idan yana hukunta ka kace masa sorry kara fusata shi zakayi har ya maka abun da baka taɓa tunani ba.

Lion wato Romeo baya son kalmar sorry kwata kwata a rayuwar sa, hakan kara arzuƙa sa da fusata sa yake, idan yana hukunta ka kayi kuskuren ce masa yayi hakuri, to kashiga uku, kara masa ɓacin rai zakayi har ya kashe ka ba tare da ya sani ba, ya tsani kalmar sorry ne saboda mum ɗin sa, tun ranar da ta tsugunna a gaban su tace musu sorry yaji ya tsani wannan kalmar.

Ko kaɗan lion bai damu da glass dake wajen ba tsabar ran maza ya ɓaci, ta kan fasassun glass ɗin yabi ya wuce ya damko wuyar Tyrone, sai faman nishi Tyrone yake kamar zai mutu, su kuwa sauran sojojin da suka zo tare da Tyrone tun Romeo bai biyo ta kan su ba sukayi neel down suka kama kunne suna jiran nasu hukuncin.

Riƙo Tyrone da lion yayi ashe akoi glass a jikin rigar Tyrone ɗin, kasan cewar fatar Romeo soft skin ne sosai hakan yasa glass ɗin tayi masa wani wawan yankan a hannun ga kuma wanda ya bi ta kan su ya wuce duk sun suke masa kafa kasan cewar ɓacin rai yasa ya cire takalman kafan sa, wajen duk ya fara ɓaci da jini, amma lion ko ajikin sa, kamar ba jikin sa glass ɗin ta yanka ba, ɓacin rai yasa bai ma ji wani abu wai yanka a jikin sa ba, banda huci ba abun da yake fitar wa.

Wani mahaukacin naushi ya kai wa Tyrone a gefen ciki, kasa kasa Tyrone ya saki ihun azaba, dan ya galabai ta sosai ko mumfashi baya iya yi da kyau bare ihu, da karfi lion ya shaƙe masa wuya, sai hucin yake sauke wa yana furzar da isaka mai bala'i zafi daga bakin sa, yana ji a ran sa ko kashe Tyrone yayi ba zai huce ba.

A wannan hali su daddy suka fito da yar gudun su suka same su, dan sun ji hayaniyar fashewar glass a palon

Ganin yadda Romeo ya shaƙe Tyrone kamar zai kashe shi ne, ga kuma Tyrone ɗin yana ta zaro ido waje alamar rai ya kusa yin hakin sa, hakan yasa Jay yayi shahada ya nufi Romeo da sauri yana faɗin "Please lion please and please let him go" ya kai karshen maganar dai dai lokacin da ya kariso wajen, cikin sadaukar da rayuwar sa ya sanya hannun sa yana kokarin cire hannun Romeo daga wuyar Tyrone, amma ina ko motsa hannun Romeo Jay ya kasa yi, sai fama yake.

A fusa ce Romeo yasa ɗayan hannun sa ya damko wuyar Jay ɗin ya haɗa su da Tyrone ya gwara kan su ji kake gwaram, wani gigitatchiyar ihu Jay ya fasa, kafin ya rufe baki, lion yayi wurgi da shi gefe guda saman dining table, shi kuwa Tyrone har lokacin yana shaƙe masa da wuya yaki sakin sa, dan ji yake ko kashe sa yayi ba zai huce ba, a kan me zai ce watch nasa ne a wajen wayan nan jiga jigan criminals ɗin, dan me zai dangan tasu, yanzu idan a gaban wasu ko yan jarida ya faɗa hakan ba shikenan sai suyi ta yaɗawa suce ashe The general of the army babban criminal ne na duniya ba shi ma

Su daddy kuwa tun da sukaga yau Romeo wato lion ya daki wani soja da kaki a jikin sojan suka san lallai yau ran maza ya ɓaci, domin kuwa lion baya hora sojijin sa da kaki a hijin su dan kamar yadda suke girmama tutan kasar su haka suke girmama kakin sojojin su, amma yau ya daki Tyrone da kaki a jikin sa bai cire masa ba ya fara dukan sa tab yau ran Lion ya ɓaci.

Sai da su daddy sukaga da gaske lion zai kashe Tyrone sanna sukayi kan sa da sauri suna faɗin "Please and please lion... Basu kari sa ba ya daka musu wani mahaukacin tsawa, wadda ya sanya dad da John sume wa a wajen, shi kuma uncle Herry ya kwasa da gudu yayi sama abun sa, shi kam Jay tun da Romeo yayi wurgi da shi daman ya sume a wajen

Gaba ɗaya bodyguard dake wajen table sun fice daga palon tun farko da lion ya fara dukan Tyrone dan suna mutuwar tsoron lion fiye da tunanin mai tunani.

A hankali Tga yake saukowa daga benen saboda har yanzu wajen na masa ciwo, sai dai yanzu yana iya sanya wando kuma ba laifi ya ɗan samu sauki, saboda Michael yaje ya shafa masa wajen yau da safe, yanzu ma hayaniyan da yaji a palon ne yasa ya lallaɓo ya sauƙo kasa dan yaga menene.

Ganin abun dake faruwa na lion na shirin kashe Tyrone ne yasa Tga karisowa wajen da sauri, already Tyrone ya sume, hannun Tga yasa yana ɗan bubbuga bayan lion alamar rarrashi a fusace lion yayi wurgi da Tyrone tare da juyowa ya damki wuyar Tga, idon sa ya rufe ransa ya ɓaci, baya ji baya gani, bai san suwaye ke gaban sa ba, haka ya ɗaga Tga sama yayi wurgi da shi, gefe guda, Tankar zakin gaske Romeo ya zama yau

Cikin fushi da ɓacin rai ya sanya hannun sa ya ɓanɓaro Makeken Tv su dake kunne yana magana ya dame sa da kara, da karfi ya ɗaga Tv sama yayi wurgi da shi a jikin bango, ji kake tarrsss Tv ya tarwatse kaca kaca, wani irin ihu yayi, har yanzu idan ya tuna maganar Tyrone sai yaji kamar ya sanya gun ya harbe kan sa dan haushi, gashi duk gidan ba wani wanda ya isa ya tinkari sa idan yana cikin farinciki ma bare kuma idan ransa ya ɓaci

Da karfin gaske ya buga kan sa a jikin bango yana mai sauke wani irin numfashin wadda jin ta kawai ya isa yasa mutun suman tsaye, yau ina James ina Michael sune kaɗai ke iya sanyayawa lion rai idan ya shiga ɓacin rai gashi dukkan su basu nan.

Kaca kaca lion yayi da palon nan, sai da ya fashe komai, har kujerun palon ɗaya bayan ɗaya ya rinƙa ɗaukan kujerun yana wurgi da su jikin bango, duk ya watsa komai ya fashe komai, duk da haka bai huce ba lokacin ne ma zuciyar sa ke kara tafarfasa tana masa zogin zafi, har Sojojin da suka zo da Tyrone sai da ya sumar da su gaba ɗayan su, ga hannun sa da kafafun sa sai zubar da jini suke, amma ina kamar ba jikin sa ba sam bai ji ba, yau ran maza ya ɓaci, sai faman fashe komai na palon yake, dan ya gama sumar da kowa dake palon, har goshin sa sai da ya fasa saboda buga kansa da jikin bango da yayi tayi, dan ɓaci rai.

A hankali Tga ya miƙe dan shi bai suma ba, lallaɓawa yayi kar lion ya gansa, ya wuce ya haura saman bene da sauri ya wuce word room na su, Musharraf yana kwance yana barci bai san meke faruwa ba

Sauri sauri Tga ya haɗa allura ya fito, a hankali ya lallaɓo ta baya ba tare da lion ya ankare ba, cikin sauri Tga ya caka masa alluran a wuya, nan take lion ya sulale kasa sumamme, nauyayyar ajiyar zuciya Tga ya sauƙe tare da ɗago ido yana bin palon da kallo, duk girman palon nan babu wani abu ɗaya da ya rage a mazaunin sa, duk Romeo ya watsa komai, yayi kaca kaca da ko'ina, duk wasu kayan fashe wa ya fashe su.

Girgiza kai Tga yayi a filli yace "Lallai da alama yau muna da sauran kwana a duniya, haka shima palon nan yana da sauran kwana a duniya, badan haka ba da ba wani abun da zai saura wanda zaka iya gane wa kace wanna kaza ne a palon nan, to wai ma me ya haɗa lion sa da su Tyrone ne har ransa ya ɓaci?" Ya tambayi kan sa tambayar da bashi da amsa, a hankali ya dawo da kallon sa kan su daddy girgiza kai ya kuma yi kafin yace "daddy kai ma kana da problem kasan baka da lafiya kuma kasan halin lion idan aka ɓata masa rai baya ji baya gani riƙiɗewa yake ya zama lion ɗin da gaske, amma sai ka rinƙa zuwa wajen sa yana cikin ɓacin rai, kai kake ja ma kan ka ai" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi waje harabar gidan.

Jim kaɗan ya dawo tare da jibga jibgan sojojin su masu jini a jika, manyan sojoji biyu suka ɗauki Romeo Tga ya musu jagora zuwa bedroom ɗin Romeo, dan ba wani sojan da ya san in da bedroom ɗin lion yake a cikin gidan, dan bai yarda dasu san in da bedroom ɗin nasa yake ba.

Saman katafaren gadon sa suka kwatar da shi, sanna suka fito sukaje suka ɗauki su dad ko wanne suka kai shi ɗakin sa, sannan suka dawo suka kwashi su Tyrone suka wuce da su hospital A&E Accident and emergency, dan a basu taimakon gaggawa, dan dukkan su suna gaɓar mutuwa, sun ji bugun namiji, ai lion ba wasa ba,

Ko da sukaje hospital ɗin ma sai da doctors ɗin suka tambayi sojojin shin da mota su Tyrone sukayi accident ne? Nan fa sojojin ke sanarwa doctors ɗin a kan cewa GAR ne ya dake su wato The general of the army, jin sunan Romeo yasa doctors ɗin su ka ja bakin su suka yi shiru suka fara aikin duba su, a ran kowannen su suna tunain ai in dai GAR ne ma ka ɗan ya musu, dan hukucin sa yafi haɗarin mota muni, idan ya zuciya ran sa ya ɓaci duk wani halitta mai rai dake wajen sai hantar cikin sa ta kaɗa, sai yaji kamshin lahira, domin Romeo fa yaci sunan sa da dad yace lion


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞




TRIPLET'S💞



💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)



*Gargarɗi*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_




WhatsApp me for more information 09162620621






Episode 36-37



Ko da sukaje hospital ɗin ma sai da doctors ɗin suka tambayi sojojin shin da mota su Tyrone sukayi accident ne? Nan fa sojojin ke sanarwa doctors ɗin a kan cewa GAR ne ya dake su wato The general of the army, jin sunan Romeo yasa doctors ɗin su ka ja bakin su suka yi shiru suka fara aikin duba su, a ran kowannen su suna tunain ai in dai GAR ne ma ka ɗan ya musu, dan hukucin sa yafi haɗarin mota muni, idan ya zuciya ran sa ya ɓaci duk wani halitta mai rai dake wajen sai hantar cikin sa ta kaɗa, sai yaji kamshin lahira, domin Romeo fa yaci sunan sa da dad yace lion


A ɓangaren Tga kuwa, waya yayi a kan masu decoration na gida suzo su cire komai na palon nan su zuba sabbi, dan wayan nan duk sun tashi a aiki, duk Romeo ya fashe su.

ba afi 10mins da kiran su da Tga yayi ba sai gasu da jibga jibgan motoncin masu ɗauke da manya manyan sofa masu numfashi wayan da suka amsa sunan su sofa, da kuma sauran kayan decorations, Tga ne ya lallaɓa kafar sa yaje ya tarbo su zuwa cikin palon ya nuna musu sanna ya wuce zai haura sama kenan idon sa ya sauka kan watch da Tyrone ya bawa Romeo

A tunanin Tga watch ɗin Romeo ne dan yaga jikin watch ɗin duk jini, kuma ya san Romeo yaji ciwo a hannu, hakan yasa ya ɗauki watch ɗin ya wuce part ɗin Romeo.

A saman bedside drawer ya ɗaurawa Romeo watch ɗin sanna ya fito ba tare da ya lura da watch dake hannun Romeo ɗin ba.

Yana fita ya wuce bedroom nasa, dan yaje ya kwanta ya hutawa ran sa, saboda gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, wurgi da shi da Romeo yayi ba karamin zafi yaji ba, hakan yasa gaɓoɓin jikin sa duk suke masa ciwo.

After some hours.

Gaba ɗaya komai na palon kasa an sauya harta labulayen palo duk an zuba zabbi kal kal, sanna an kara sofa set, set ɗaya yanzu sun zama set biyar ne a cikin palon, ko ina yayi tsab gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali ga wani fitinanniyar kamshin air freshener da sanyin Ac dake tashi, an kunna sky blue light a cikin palon gaba ɗaya, hakan ba karamin karawa palon kyau yayi ba, ba zaka taɓa cewa palon da Romeo ya tarwatsa ɗazun bane, komai yayi need yanzu.

Su daddy kuwa duk sun farfaɗo daga suman da suka yi Tga ne ya bawa dad maganin sa yasha dan jikin nasa kamar yana son tashi,

A hankali lion ya sauko daga saman benen, yana tafiya kamar baya son taka kasa hannun sa na riƙe da watch da Tyrone ya kawo masa, ga kuma na sa watch ɗin a ɗaure a hannun sa, jikin sa na sanye da wando jeans guntu zuwa gwiwar sa, da yar riga mai ƙaramar hannun, hakan ya bawa damatsan hannun sa damar bayyana, suna cike tam kamar zasu fashe, fiskar nan tasa tayi fayau kamar wanda yayi rashin lafiya, a ɗauren fuskar tasa kamar kullun, bai ɗaure wanna kyakkyawan dark black curly sa ba, ya sake ta sai wani kyalli yake kamar ya shafa mata baby oil, sai tashin fitinanniyar kamshin perfume na sa yake perfume nasa mai kwantar da hankalin mai shaƙa da nitsar da zuciya, har yar rama yayi saboda abun da ya faru ɗazun, soft skin na san nan sai wani sheki yake, still hannun sa na ɗan zubar da jini, dan yaki duba hannun nasa, kafar sa kuma yana sanye cikin bedroom slippers masu kyau da tsada ga laushi.

Saman sofa mai zaman mutun 2 yazo ya zauna ya jingina kan sa da sofar tare da ɗaga kan nasa sama yana tunain watch ɗin wanene wannan, yasan dai dole watch ɗin ɗaya daga cikin sune dan su uku kawai ke da irin watch ɗin, shi da kan sa yayi tattaki zuwa company nin apple ya basu design da yake so suka masa sanna kuma ya ja kusu kunne a kan karsu kuskura su yi wa wani design mai kama da nasu, dan baya son anko da wasu bayan Triplets nasa, shiyasa duk wani abu in dai nasa ne to ko kaje sayan irin sa ba zaka samu ba, dan shi baya sayan kaya kamar yadda kowa yake saye, aa shi sawa yake a buga masa design da yake so, kuma shi da Triplets nasa kaɗai akewa.

Yayi nisa cikin tunanin sa na neman gano ya akayi watch ɗin ɗaya daga cikin su yaje wajen, dan shi bai yarda a cikin su ako criminal ba, ko da sunan wasa baya kawo wannan tunanin a ransa.

Babu ko excuse Micheal ya shigo palon ya dawo daga white house, ganin an sauya komai na palon bai wani bashi mamaki ba dan yasan dama duk bayan 6 month suna canza komai na palo da ɗakunan su.

Bai lura da Romeo a zaune a palon ba, ya wuce zai hau bene, kamar daga sama yaji zazzakar voice ɗin lion yace "Come here" da sauri ya juyo dan bai yi zaton ganin Romeo a palon kasa by this time around ba, cikin sauri ya juya ya koma kusa da Romeo ɗin ya zauna yana kallon face ɗin Romeo.

Shiru Romeo ya ɗan yi na yan mintoci kafin ya ɗago ya kalle sa yace "Where is your watch?" Da sauri Michael ya duba hannun sa, babu watch na sa, ɗago ido yayi ya kalli Romeo, a nitse yace "Ban san in da watch ɗin yake ba" kwata kwata Michael ya mance da ya cire watch ɗin ya sanya a aljihun sa lokacin da president ya basa wata watch ɗin

Kwata kwata Romeo bai kawo zargin su a ransa ba saboda yana musu kallon har yanzu basu mallaki wasu abubuwan da zasu iya shiga wannan harkan ba, bugu da kari kuma kullun yana tare da su, basu fita sai dai in zasu je wajen president a white house da kuma wajen partyn abokan su, shike fitar da su daga gidan kawai, bai damu ba kuma bai kawo wani tunani mara kyau nasu a ransa ba, shi tunanin ma da yake tun da Michael ya yasar da watch ɗin sa bai san in da yake ba, kila ɗaya daga cikin yaran criminals ɗin can su suka ɗauki watch ɗin tun da agogo ne mai bala'i tsada, sannan kuma criminals ɗin suna shiga mutane sosai kila da Michael ya yasar da agogon bai sani bane suka tsinta suka tafi da shi wajen.

Miƙa wa Michael watch ɗin yayi yana faɗin "Gashi ka rinƙa kulawa" miƙo hannu Michael yayi zai karɓi agogon, lokacin idon Romeo ya sauka kan agogon da president ya bashi

Kallo ɗaya Romeo yayiwa agogon yasan cewa daga wajen president agogon ya fito, dan akoi wani tambari a jiki, bai kawo wani abu a ransa ba, dan yana ganin kila Micheal da ya yasar da watch na sa ne yaje wajen president babu watch shine president ya basa wannna kyauta, dan haka sai bai ce komai ba,

Karɓan watch ɗin Michael yayi yana turo ɗan karamin bakin nan nasa, yana son tashi ya tafi yaje ya kwata dan jiri yake ji, amma ba halin tashi domin kuwa bai isa Romeo ya kirasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login